Showing 285001 words to 288000 words out of 403653 words

Chapter 96 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

142

koma ta kwanta zuwa san da drip ɗin ya kare, sannan ya cire mata, a gaggauce ta sauko ta nufi toilet dan yi wanka ta ɗauro alwala ta hau biyan bashin sallolin dake kanta, shi kuma Ronnie ya fita ya nufi bedroom na Black Tiger dan ya yi sallah a can, baya sallah a ɗakinsa saboda kada Black Tiger ya gano ya musulunta.

After some hours da basu wuci biyu ba, shirye take tsab cikin sleeping dress masu shegen kyau, riga ce mai ƙaramar hannu da dogo wando launin ash mai ɗan duhu, hakan yasa ta yi balai'n kyau saboda hasken fatarta, ta gyara golden hair ɗinta sai sheki yake yi, sai tashin kamshi take zubawa, ta yi sallar isha'i saura cin abinci, tana tsaye a gaban mirror tana kallan kanta tana kuma tinanin su Pretty, kewarsu ce a ranta yau sosai, har ta ji hawaye sun cika mata idanu, ta matsu ta ga Kamran ɗinta ido da ido, har mafarkinsa take yi, yana ranta a kowani dakika na rayuwarta. Ta nausa cikin tinaninta sai ji ta yi ya ɗan rungumeta ta baya yana faɗin. "Lovely sis tinanin me ake yi har na shigo baki ji ni ba?".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗago kallanta, ta cikin mirror suka kalli juna, cool murmushi suka sakarwa juna kafin ta amsa mashi da. "My twins sis and my Kamran nike tinawa, yau da kewarsu nike tare"....... Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa mata da. "Soon zaki je ki gansu, yanzu dai bari in dubi Floris ina dawo, tun jiya da safe da na ganta ban sake ganinta ba"........ Allah sarki, bai san tun jiya ɗin ta mutu ba, tana kunshe cikin toilet master na gidan yari.

"Okey nima zan je duba big bro, amma ni fa ina ganin kamar Floris fushi take yi da kai". Tana magana tana kallansa ta cikin mirror. Jinjina kansa ya yi kafin ya amsa da. "Tabbas haka ne, nima na lura da tana fushi dani, shiyasa zan je bata hakuri, kin san yadda nike kaunar Floris kuwa my sister?"...... Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata sani ba..... "Ina kaunarta fiye da kai'na, komai nata birgeni yake yi, amma ta ci saurin yin fushi, kuma ita tana kaunata over, before ki zo ita take bani abinci a baki fa, na yi missing na wannan moment ɗin, bari in je in bata hakuri daren yau ta ciyar da ni abinci a baki".

Faɗaɗa murmushin dake saman face ɗinta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Gaskiya kam ka je ka lallaɓa mana ita ta zo mu ci abincin dare a tare, nima ina missing ɗinta sosai". ...... Jinjina kansa ya yi tare da manna mata sumbata a gefen kumatunta, kara faɗaɗa murmushin ta yi tana kai hannu ta ɗan shafi gefen nasa kumatun. Saketa ya yi tare da fara tafiya baya baya yana kallanta, ganin irin tafiyar da yake yi ta cikin mirror yasa ta juyo dan ta gansa da kyau. Tana jiyowa suka haɗa ido, kashe mata ido ɗaya ya yi yana cigaba da sakin cool murmushi har ya kai jikin kofa. Kamar dai kullum, sumbata ta manna a hannunta ta hura mashi, ajiyar zuciya ya sauke haɗe da juyawa ya cire password na kofar ya fita. Tana ta murmushi bata zare kallanta daga kansa ba har sai da ya kurewa ganinta. Ajiyar zuciya ta sauke tare da raba jikinta da jikin mirror, cikin natsuwa ta taka ta nufo waje ita ma.

Kai tsaye master room na Black Tiger ta nufa, tana tafiya tana tinanin a wani irin yanayi zata same shi?. Tana zuwa ta buɗe kofan without any scare and any excuse ta afaka cikin ɗakin.

Tsaye yake a tsakiyar ɗakin ɗaure da towel a waist ɗinsa, da alama daga wanka ya fito, dan ga dark black curly hairnsa nan yana ɗigar da ruwa, hannunsa rike da wani ɗan ƙaramin towel yana goge kyakkyawan gashin kan nasa. Da yake ta kudurta a ranta kome zai faru babu gudu babu ja da baya sai ta daure bata juya ta gudu ba, kada ku manta ta taɓa ganinsa a yanayin da ya fi haka, a farkon ganinta da shi da ɗan ƙaramin short ta gansa, gara yau towel ɗin tana da ɗan tsawo ta kai mashi har zuwa gwiwa.

Tun daga kan tafukan kafafunsa ta fara kallansa har izuwa sama, ita kanta ta shaida he's so sexy, handsome and cute, yanayin jikinsa sai yasa ka fola..... Tana sauke kallanta a kan face ɗinsa sai taga shi ma ita yake kallo, dan fa ba karya ta yi kyau cikin shigarta. Suna haɗa idanu ya yi gaggawar kawar da nasa kallan yana ɗaure fuska, ta fahimci sam sam baya san ta kama shi yana kallanta, dan haka sai ta yanke shawarar zata rinƙa dannewa ba zata bari ya san ta san yana kallanta ba.

Kai Black Tiger da Sweetie duniya, wato babu maganin Black Tiger sai Sweetie, a gana mata azaba amma kuma yana jin daɗin kallanta, musamman idan tana tare da Ronnie tana sakin cute smile ɗin nan nata mai narkar da zuciya.

Cikin dauriya da natsuwa ta tako ta nufo in da yake, bai yi kamar yasan tana zuwa ba, ya cigaba da yin abin da yake yi. A dab gabansa ta tsaya, hannu ta kai ta karɓi ƙaramin towel dake hannunsa, zuciyarta na harbawa da sauri sauri, ta yi ƙasa da murya cikin siga mai jan hankali da salo ta ce. "Dama ni nasan kai adali ne, kai ɗin mai tausayi ne, kai ɗin jarumi ne, kai ɗin mutum ne da dik in da ake neman cikakken namiji ka kai nan har ma ka wuce, ba zan taɓa mantawa da alkhairinka na yafewa mutanen birnin nan ba, tabbaa yadda kake da balai'n kyau zuciyarka ma haka take". Ta ɗan dakata da yin maganar tare da kai kallanta a kan face ɗinsa, sannan ta fara goge mashi Lion chest ɗinsa da towel ɗin.

Mutuwar tsaye ya yi yana tinanin shi kuma a yaushe ya yi wa mutanen birnin nan afuwa da har take yi mashi irin wannan yabo? Sai dai kuma yabonta a garesa ta ratsa zuciyarsa, ya ji daɗin hakan sosai, sai ya ji dama ta cigaba da yi kada ta dakata...... Batu na gaskiya yabo tana karya zuciyar koma wani irin mutum ne, ki gwada ware rana guda ki yi yabo da zafafan kalamai ga wanda yake kusa dake kiga yadda zai shiga cikin farinciki a wannan lokaci, gaskiya ne abin da hankali bai bayar ba rashinsa ba zai bayar ba, abin da kwamciyar hankali bai bayar ba rashinsa ba zai bayar ba.

Haƙiƙa Sweetie ta fahimci yabon da ta yi mashi ya yi tasiri a cikin zuciyarsa, dan har da sauke ajiyar zuciya ya yi, kuma ta ji hakan, dan haka ta shiga farinciki ita ma.

"Kana da kyau sosai our big bro, haka zalika zuciyarka ma mai kyau ce tsarkakekkiya". Yadda take magana cikin salo mai ɗaukar hankali yasa bai san lokacin da ya amsa mata da. "Amma kuma jiya kin ce zuciyata bata da kyau ai?"....... Kam bala'i ashe kalamanta na jiya sun shiga kunnuwansa, magana da ta yi mashi a tsawatance yasa ya ji ba zai iya ragawa kowa ba, da ace jiya ta yi mashi magana yadda ta yi mashi yau da tabbas za'a samu rangwame, sai dai kash, ta fusata ita ma, tabbas magana cikin natsuwa yana iya canza komai.

"Jiya ai ɓacin rai ne yasa na yi maka magana a haka, amma tabbas kai mutum ne mai farar zuciya". Ta kai karshen maganar tare da ɗaura mashi ɗan towel ɗin nasa a saman shoulder ɗinsa, sannan ta juya da nufin ta matsa daga gabansa, ta koma saman sofa ta zauna ta jirasa yasa kaya ya fito ta kara yi mashi godiya, bata san karya Ronnie ya sharara mata ba.

Tana juyawa ɗan ruwa ruwan da ya zuba a wajen daga gashin kansa yasa ta zame, baya baya ta yi ta faɗa jikinsa, buga kanta da kirjinsa ta yi a in da ta tsuke fuska kamar zata yi kuka. Tana ƙoƙarin yin ƙasa daga jikin nasa yasa hannu ɗaya ya tallabota tare da juyota garesa, face ɗinta ya zubawa idanu yana kallan yadda ta datse nata idanun tana jiran ta ji ta isa ƙasa. Yau yabon da ta yi mashi ne ya sanyaya mashi rai har yasa ya ceceta bai bari ta kai ƙasa ba, dama ransa tun jiya a ɓace na juya mashi baya da mutanensa suka yi.

Kurawa juna ido suka yi gabaɗaya kamar sun mance a wani duniya suke, sun shagala da kallan juna gangar jikinta ya gaza iya jurar tsawuyar da ta yi ɗin, dan kusan a iska take, bayan wuyarta ya tallabota da hannunsa. Kerma kafafunta suka fara yi a in da ta yi ƙoƙarin zubawa ƙasa, cikin zafa ya fisgota mai gabaɗaya ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa, yasa hannunsa ɗaya ya tallabi tsakiyar bayanta. Like wow, abin da bata taɓa expecting zai yi mata ba, wai ya taimaketa, bata taɓa zata ba, sai ga shi ya yi hakaɗin sanadiyyar daɗaɗan lafuzanta a kansa, abin fa ya yi mashi daɗi ne sosai, sai dai shi ba'a gane farincikinsa ko bakincinsa shiyasa bata wani gane sosai ba.

Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman lion chest ɗin nasa ta gefe, dan dikkanta bata gama cike rabin faɗin kirjinsa ba, ƴar karama a gabansa. So sai ta ɗaura hannunta a gefen chest ɗin nata, a hankali ta ɗago da kanta dan ta kalli face ɗinsa, ya kura mata idanu yana yi mata kallan kurillah. Habawa sarkafewa idanunsu ya yi cikin na juna kamar ɗazun. Sun ɗan jima a haka kafin ya yi gaggawar kawar da kallansa a kanta tare da saketa, kamar wani mara gaskiya ya juya da sauri ya nufi clothes set ɗinsa. Bin bayansa da kallo ta yi har ya shige cikin wajen, ajiyar zuciya ta sauke, cikin natsuwa ta taka ta isa gaban sofars ɗinsa, saman ɗaya ta zauna, tsabar laushi har lumewa da ita ya yi, tagumi ta ɗan yi tare da afkawa duniyar tinani, faɗi take yi a ranta ta fara yin nasara, ji take yi sun kusa canza zuciyarsa, amma ita dik a tinaninta yafewa mutanen birnin da Ronnie ya ce mata ya yi ne take ganin sun fara nasara ba. Uhm akwai sauran aiki a gabanki Sweetie, dan wannan mai black heart ɗin kam bai ji komai a ransa ba.

Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu..................

Dama a karshen littafin nan na yi maku alkawarin baku wasu addu'oi na mallakar zuciya ko? Da na yi niyya sai a kashen littafin, amma duba da ramadan ya gabato, a cikin Ramadan ma buƙata zata fi saurin biya yasa nace bari na baku the most important ɗin, ku yi shi a cikin watar Ramadan, ki yi shi da kyakkyawar niyya, ina uwa da ɗanta yake zinace zinace, yake yawace yawacen banza bin abokan banza da shaye shaye? Ina mata masu shan wahalar namiji? To dik dai ku matso, ku yi shi da tsarkakakken niyya sosai

Da farko dai zaki yi. Astaghfirullaha Rabbi min kulli zambin wa atubu ilayh kafa ɗari dai'dai, sannan ki yi salati ga annabi kafa goma. Amma fa sai kin yi alwala, zaki iya farawa karfe sha biyu na dare, za kuma ki iya farawa karfe 2 na dare, idan kin yi alwala kika yi sallah raka'a biyu, sai ki zauna, ki gabatar da abin da na faɗa a farko, sannan ki yi salati, ga salatin ma a rubuce ga waɗan da basu iya ba. Allahumma salli ala Muhammadin wa ala ali Muhammadin, kama sallayta ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima innaka Hamidum Majid. Bayan kin yi wannan sai ki gyara zama sosai a kan dadduma, ki ɗaga hannayenki sama ki fara addu'ar kamar haka.

Allahumma aslih zawji ( sai ki ambaci sunansa, wato suna da kike yiwa ɗin kenan) waj’alhu min as salihin, waj’alhubniyyatahu nafi’atan lid duniya wa akhirati. Da kyakkyawar niya fa, ki sanya a ranki tamkar Allah ya gama biya maki buƙata, ki ji cewa bayan Allah babu wanda zai yi maki. Sai Rabbana hablana min azwajina wa dhurriyyatina qurrata aƴunin waj’alna lil-muttaqina imama. Wannan addu'a tana da mahimmanci kowace uwa ta kasance tana yi, yana cikin Suratul Furqan. Sai Allahumma inni as’aluka an tahdi zawji ila sabilika al-mustaqim, wa an tub’idahu ‘an ma yughzibuka, wa an taj’alahu min ahlil taqwa wal istiqama. Wannan addu'oi masu tsadar gaske ne, idan kika yi sho da tawali'u zaki sha mamaki, zaki gode mun kamar babu gobe. Sai Allahumma inni a’udhu bika min jahdi al bala’ wa su’il qadha’ wa shamatati al a’da’, wa min kulli sharrin dhahirihi wa batinihi. Wannan addu'a tana matuƙar kariya daga dik wata sharri na abin halitta, wannan ba dan miji ko wani zaki yi ba, kanki zaki yi wa dan Allah ya kareki, amma zaki iya yiwa kowa yaki dan ya shiga kariya, wlh wlh wlh addu'a ce mai karfin gaske. Tsarin yin wannan addu'oi dama kwanaki 40 zaki ɗauka kina yinsu cikin dare bayan kin yi sallah raka'a biyu, kinga ga Ramadan ya zo, zali samu saukin tashi ki yisu, sai ma buƙatunki sun fi biya, shiyasa na baku a yanzu dan ku yi da ramadan, saura sai mun haɗu a karshen littafin, saura wata budurwa ta je ta yi wa sarauyinta ta zo ba aurensa zata yi ba, wlh babu ruwana, ya Allah dik wanda ba da kyakkyawar niya zata yi wannan addu'oi ba Allah kada ka amsa mata, dan ba da ni za'a cutar da wata ko wani ba!!.

Yauwa ina da wata ƴar rokan alfarma a gareku my people's, kunga dai azumi ya zo, Please a taimaka a sakani a addu'a, wlh addu'a in dai ta alkhairi ce a gareni kowacce iriya ce ina so, please my people's, ina kannena da suke gida, ƴan yaran nan da basu wuce 10 ya yi ƙasa ba, please a sanyasu su yi wa princess taku ta amana addu'a, kun san addu'ar yara da karɓuwa yake, to a taimaka a mun wannan alfarma, dik wadda ta je ta hajju ta jefani cikin addu'arta, ina godiya Allah ya bar kauna 💘 🔥 💘 🤍 much love my people's, sai mun haɗe gobe.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

48


Zaman good 10 mins ta yi a wajen kafin ya fito shirye cikin sleeping dress ɗinsa, yana fitowa ta miƙe tsaye tana kallan irin kyan da ya yi cikin wannan kaya, dai'dai lokacin kuma aka turo kofar ɗakin aka shigo..... A hanzarce ta kai kallanta wajen kofar nasa dan ganin wanene?. Wasu kyawawan robbot ne gungu guda da a kallah zasu kai su 8, gabaɗayansu kowanne ɗauke yake da katan tray mai shake da kayan abinci kala kala, ga wasu irin abin rufe abinci wato food cover masu shegen kyau da tsada launin golden suna ɗaukar idanu aka rufe abincin da su, kai tin daga kan masu ɗauko abincin zaka fahimci robbot ne na musamman da zasu kaiwa mutum na musamman abinci, harta tafiyar da suke yi cikin tsari suke yinsa, a tare suke ɗaga kafafu su sauke.

Ai zuba masu idanu Sweetie ta yi tana kallan yadda suke taku gwanin birgewa, kai tsaye suka nufi can wani ɓangare na ɗakin, kun san ɗakin da shegen girma yake, wajen da yake cin abincin zaka yi zatan ba'a ɗakin yake ba saboda girmansa. Sweetie bata kara tsurewa ba har sai da suka yaye white curtains dake wajen, ai wani irin zaro idanu ta yi tana kallan tsaruwar dining room ɗin, kun san a baya Black Tiger baya fita, hakan yasa yake da haɗaɗɗen dining room a cikin bedroom ɗinsa bayan na parlournsa. Sweetie ta sha madarar mamakin ganin set na table ɗin dake ciki, haɗaɗɗun chairs har guda 24 ne a wajen, ko shi da waye yake zaman cin abinci yawan chairs har haka? Ta jefawa kanta tambaya, my people's dining room ɗin nan ya haɗu, ga wasu decorations masu ɗaukar hankali, manya manyan flowers da kayan more rayuwa, sai dai kuma kusan dik da ɗanyan gold aka yi su, yo Black Tiger da WC ɗinsa ma na gold ne me ba zaku gani na gold ba?..... Shi dai wannan sarki wlh sai shirin Allah.

Glass wall ne wajen, haka zalika glass door ne, tura kofar suka yi suka shiga ciki, shi kansa table ɗin abin kallo ne, ya tsaru matiƙa, samansa suka hau shirya mashi abinci kamar yadda suka saba. Suna kammala shirya komai suka kunna ligh launika daban daban dake wajen bayan sun kashe white light ɗin, take wajen ya ɗauki wani irin launi mai ɗaukar hankali, sai ma da suka kunna kenduran dake saman table ɗin, ya ilahi ya lilliahi, haɗuwa iya haɗuwa. Sweetie kam dai sumar zaune ta yi, sai taga tamkar ba a duniya wannan dining room ɗin yake ba.

Fitowa suka yi su 7 sun bar ɗaya a ciki, suka nufi waje ba tare da sun yi komai ƙanƙantar magana ba, da kallo Sweetie ta bisu tana mamakinsu, ita dai yau taga abin da ya goge mata hadda, tambayar kanta ma take yi ashe Black Tiger yana cin abinci? Abin like wow, ya ƙayatar.

Shi kuwa gaban mirror ya wuce, wasu document ya ɗauka yasa hannu, takardu ne na katafaren ginin da za'ayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login