Showing 384001 words to 387000 words out of 403653 words

Chapter 129 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

108

bata san nan ta shigo ta kwanta ba , dama bedroom ɗinta zata wuce sai gigin barcin ya kwasheta. Bata san ya gama gane komai ba, ya ganota. Binta da kallo ya tsaya yana yi, wai irin zata yi basajan nan, ta manta a gaban babban jami'i take!.

Ganin ya yi shiru yana kallonta yasa ta yi gaggawar yunƙurawa zata sauka ta bar gadan tana ƙoƙarin danne murmushin dake san kubce mata. ANKAMA WATA TA YI KARYA..😅

Hannunta ya capko tare da janyota ta faɗa saman kirjinsa. Sai da dattijuwar nan ta ji kirjinta ya amsa, wani irin zafi ta ji a ranta, abin ya komata sosai. Kai kallanta a kan kafar dattijuwar dake leƙowa ta gefen labule Leesharh ta yi, nan ta ga matar ta matse yatsun kafafun nata a kasa, nan Leesharh ta gane abin ya ciza mata zuciya, bata so ba!.

Cikin wani irin kasalallen murya ya ce. "Me kika zo yi bedroom ɗina?". Ya yi maganar tare da sanya hannun ya zame pil da ta kama veil da ta yi rolling a kanta......... "Ni fa Yah Ramish ban san cewa bedroom ɗinka na shigo ba, na fito daga wajensu Auta ne barci kamar zan yi hauka, shi ne na afko nan ban sani ba". Ta kai karshen maganar tare da dafa kirjinsa zata miƙe. Mayar da ita ya yi ta kwanta, veil ɗin nata ya cire ya ajiye a gefe, haɓarta ya ɗago ya zama suna fuskantar juna. Ɗan zuba mata idanu kamar na ƴan sakanni kafin ya ce. "Meyasa kike wahalar da ni ne Aesh? Meyasa ba zaki yarda mu yi aure ba?".

Satar kallon kafar dattijuwar ta yi kafin ta ɗan kalli sama, nan taga tana lekansu bata dai'na ba, dawo da kallonta a kansa ta yi, sillent talk ta yi mashi ta hanyar motsa lips ɗinta, babu wanda zai iya fahimtar me ta ce mashi sai shi ɗin, a fili ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce. "In kuwa haka ne zan kasance cikin dakon wannan rana, sannan kuma a ranar zan baki kyakkyawar kyauta da na tabbata zaki ji daɗinsa sosai". Ya kai karshen maganar tare da matsar da ɗan bakinsa dap kunnenta, ya cigaba da cewa. "A wannan rana babu shakka ba zan kyaleki ba sai na yi round two, dan kin bani wahala sosai".

Ɗago da kanta ta yi, a hankali ta kai ɗan bakinta saitin kumatunsa, zazzafar sumbata ta bashi wanda sai da ta sanya dattijuwar nan sakin labulen da ta rike ta ɗan yaye tana leƙansu, idanunta sun yi jajir sun cika da kwallah, wlh Leesharh ta iya tsiya. "Nima ina da kyakkyawar kyauta yau a gareka, amma idan na baka me zaka bani?". ME KUKE TINANIN ZATA BASHI?.

Ai bai iya bata amsa ba saboda wani irin tayar mashi da hankali wannan sumbata tata da ta yi, ji ya yi tamkar wanda aka jonawa lantarki.
Jin ya yi shiru yasa ta sake maimaita abin da ta faɗa tare da ɗan ɗago kanta da kallonta a kansa, tana ɗagowa bakinsu ya haɗe dan in baku manta ba ya kai bakinsa ya yi mata raɗa a kunne.

Tana ƙoƙarin yin gaggawar zame kanta ya ce ina baki isa ba, ai rikota ya yi ya fara rage zafin da ta haɗa mashi, hot kiss ya shiga bata tare da cusa hannunsa a cikin kyakkyawar gashin kanta da ya sha gyara. Ai tsabar takaici dattijuwa bata san time ɗin da ta furta no ba, sai dai Ramish ya yi nisan da bai jita ba, amma ita Leesharh ta ji time da ta faɗa, hakan yasa ta kyalesa yana kissing ɗinta bata hana shi ba, sai ma hannu da ta kai ta rungumesa da kyau. Haba ai kara haɗa mashi zafi ta yi, ya matseta sosai a jikinsa, yana ƙoƙarin tura hannunsa cikin rigarta cikin fitar hankali sai aka yi knowking na door ɗin wanda hakan ya ja ta yi gaggawar kwace bakinta daga nasa.

Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kaman ɗan maye, murya kamar na ɗan maye ya ce mata. "Aesh please bayan kiss ba zan yi maki komai ba, please ki barni in kara kaɗan". Out of control yake maganar, idanunsa a limshe. "Yah Ramish knowking ake yi shiyasa". Ta faɗa tare da janyo vail tana ƙoƙarin maidawa kanta. Ɗan ciza lips ɗinsa gam ya yi, sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa, sam bai so hakan ba. Miƙewa ta yi ta nufi door ɗin tana jin wani irin farinciki na musamman a ranta.

Tana buɗewa suka yi four eyes da guyson. "Aunty Aesh ke fa muke jira ki zo mu yi lunch amma shiru tun ɗazun". Yana magana kallansa a kan Ramish da ya waro eyes ɗinsa da suka rikiɗa izuwa red sosai. A natse ta ce. "Muje to". Guyson yana zargin wani abin, dan ya ganta gabaɗaya a hargitse, amma bai ce komai ba ya juya da nufin su tafi.

"Omar kuje ku yi lunch ɗin, fita zamu yi da ita". Muryar Ramish ya daki dodan kunnensu, ya yi maganar tare da miƙewa ya nufosu. Wucesu ya yi cikin sauri yana faɗin. "Aesh ki sameni a mota". Kallon juna suka yi ita da guyson kafin ta saci kallon dattijuwa, a ranta ta ce ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, yanzu masu nikaf zasu samu labarin hakarsu bai cin ma ruwa ba, sun so tagayyara rayuwarta, idan ta kammala aikinta su kasheta, idan kuma asirinta ya tonu su Ramish su kasheta, sai ga shi da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, su samu labarin soyayya ma take da Ramish ɗin, su san sonta yake yi kamar ransa, sai su mutu da haushi, rayuwarta bai tagayyara da suka yi fata ba!!.

"Yah Omar bari in je". Hararar wasa ya wurga mata kafin ya ce. "Ina da meeting dake Aunty Aesh, sannan kada ki wahalar mun da yaya, ki yi mashi dik abin da yake so dan faranta mashi, na baki amanarsa". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya tafi. Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, siririn murmushi ta saki a ranta ta ce ta yi sa'ar ƴan uwansa masu saukin kai ne kuma suna kaunarta...... Ni kuwa ya ce tab lallai kuwa mafarki kike yi, dan kuwa a yaran King Auta da guyson ɗin ne kawai masu sanyin halin, uhm kada ki yi fatan shiga kingdom of power da sunan zaman aure kina matsayin bare, inai maki fatan idan Allah ya yi aure tsakaninki da Ramish ku yi zamanku a Dubai, idan ba haka ba mama kawai ta isheku bala'i, baku zasu karɓeki matsayin sirika ba!!.

Bayansa ta bi tana cigaba da godewa Allah. A cikin mota ta iskosa zaune yana jiranta, gidan gaba ta buɗe ta shiga, kanta a kasa saboda kunyar sumbatar da ta yi mashi ɗazun, kunna motar ya yi ba tare da ya kalleta ba, kai tsaye suka nufi office ɗinsa. Suna tafiya tsohuwar nan ta yi gaggawar fitowa ta nufi bedroom ɗinta, idanunta sun yi jajir kamar wuta, har da guntun kwallah a face ɗinta, ranta ya ɓaci Leesharh ta yi mata taboooooooooooooo.

TO! Ina mai farincikin sanar da ku cewa book ɗina mai suna MACE MAI DARAJACE, zai saukan maku da zafizafinsa very soon, wannan book ɗin na yisa ne kawai dan matan aure da kuma waɗan da suke gab da yin aure, ko zawarawa wanda ba aure zasu yi ba ban yarda su karanta mun littafi ba, ba novel bane, littafi ne da dan ma'aurata na yi shi, na jima ina tsara shi ina kuma tattara dik wasu muhimman abubuwa a cikinsa, book ne da ya haɗa komai da komai na rayuwar aure da sauransu, kada wata budurwa ta buɗe mun book tam!!! 2k yake, akwai sirrika kala daban daban a cikinsa, akwai kayan gyare gyaren abubuwa daban daban, kai baki ba zai iya faɗar abin dake cikin book ɗin nan ba, in kina buƙata kai tsaye ki mun magana, amma ba yanzu zan sake shi ba, saura kaɗan, idan na tashi sakansa zan sanar da ku!!. Amma dik mai so tin yanzu ta mun magana in san da ita, an zuba abubuwa a ciki, akwai salo kala kala sai wanda ya karanta zai gane, bana san buɗe me a ciki saboda kada na baku satar amsa, amma fa akwai abubuwa a ciki ba karya!!. IN SHA ALLAH RAYUWARKI ZATA CANZA KAMAR HAKA IDAN KIKA SAMU DAMAR MALLAKAR WANNAN LITTAFI KUMA KIKA YI AMFANI DA ABIN DAKE A CIKI!.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️


60




Auta da guyson kuwa a tare suka yi lunch ɗinsu, Auta taki ci da farko, sai da guyson ya yi ta lallaɓata sannan ne ta ci.

Shi kuwa Ramish yana yin parking motarsa a parking lot na h-c ɗinsu kan kace me wasu jiga jigan jami'ai sun kewaye motar, sosai Leesharh ta tsorata daga ciki, dan a tinaninta tin da taki tayasa aiki shi ne ya kawota su lallasata irin na wancan karan!. Zuba mashi idanu ta yi tana kallan yadda ya ɗaure fuska tamau tamkar hadari, abin sai ya yi mugun bata tsoro.

Buɗe mashi door ɗin aka yi, ba tare da ya sake kallan in da take ba ya fito waje abinsa. Shiru ta yi a ranta tana tinanin ya zata yi? Sai gani ta yi an buɗe mata door na side ɗinta, kallon jami'in da ya buɗe mata ɗin ta yi, wani shirgegen balarabe ne mai tsawo da cikar halitta. Fitowa ta yi jiki ba kwari, tinanin irin azaban da jami'an nan suka bata a farkon karonta da su ne kawai ya faɗo mata a rai, tin da ta zo duniya bata taɓa shan azaba irin wanda suka gana mata ba, a lokacin har ji ta yi da sun bata wata dama kaɗan tsab zata kashe kanta ta huta!.

Ta yi nisa a cikin tinaninta sai ji ta yi anja hannunta, almost 3 times yanayi mata magana bata ji shi ba, shi ne yasa ya kama hannunta kawai. Zaro idanu ta yi tana kallonsa tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, da ta san nan zai zo ba zata rakosa ba. Binsa kawai take yi tana karanta lailahaillah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, gabaɗaya jikinta kerma yake yi. Ya lura da ta tsorata sosai, hakan yasa ya yi ƙasa da murya sosai wajen cewa. "Aesh babu abin da za su yi maki fa, a yanzu wannan zuwan na daban ne, ba irin wanda kika yi a baya bane!".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta amsa mashi da to, manya-manyan jami'ai guda shidda ne suke take masu baya har izuwa cikin office ɗinsa. Already mai zane yana zaune yana jiransu. Saman wani lallausan seat ya ce mata ta zauna. Ba musu ta zauna tana kallon office ɗin, ɗauko mashi wata chair dake kusa da table ɗinsa yasa aka yi aka kawo mashi kusa da ita, zama ya yi suna fuskantar juna, sannan ne ya ce. "Ki faɗa mashi fuskokin waɗan da kika sani daga cikinsu, dan gabaɗaya waɗan da kika ambata na bincikasu a gidan Abbie babu su".

In baku manta ba dattijuwa tasa sun ɓoye shaidar da za'a iya kamasu da shi, so ya bincika bai iya kamasu ba, dan haka dole su kasance suna da zanensu. Ganaɗaya jami'ansa tsayuwa suka yi a bayansa suka binta da kallo suna jiran ta fara zayyano bayanai. Lokaci guda ya ji hakan ya kona mashi rai, a ɗan dakile ya ce da jami'an dik su fice mashi daga office, dan bai ga amfanin su tsaya suna kalle mashi ita ba, shi kaɗai zai ganta kuma ya ga zanen da za'a zana.

Abin har murmushi yaso ya sakata, sai ta danne tare da cewa. "Yah Ramish ina tsoro sosai". ......... Hannunsa ya miƙa ya riƙo nata, cikin natsuwa ya ce. "Babu abin da zai faru kin ji? Please ki daure". Jinjina mashi kai ta yi tare da juyo da kallonta a kan mai zanen, cikin natsuwa ta fara bashi bayanan yadda suke a zahirance. Zanasu ya fara yi har da face mask na fuskokinsu, tana cigaba da yi mashi bayani yadda yakamata har suka kammala, bata yi kuskure ba sam sam, zanen ya fita sosai.

Ana kammalawa kallo ɗaya Ramish ya yi wa zanen ya gano su wanenen daga cikin securitys ɗinsu, ya girgiza sosai da ganinsu, zubawa hoton zanen idanu ya yi yana kara tambayarta ta tabbata sune babu kuskure, kai ta gyaɗa mashi alamar ta tabbata. Nisawa ya yi kafin ya karɓi zanen, sannan ya cewa mai zanen ya haɗa kayansa ya je, already dama ya biyasa hakkinsa.

Mai zanen yana fita Leesharh ta matsa kusa da shi. "Yah Ramish akwai abin da nike san faɗa maka fa, ko in ce akwai abin da nike san baka, amma dan Allah idan na baka kada ka tambayeni daga ina na samu ka ji?". Dawo da kallonsa tsam a kanta ya yi. "In Sha ALLAH ba zan tambaya ba". Ya faɗa yana sake riko hannunta cikin nasa.

Wayarta ta fitar daga aljihun rigarta da ɗayar hannunta, kai tsaye ta shiga picks, hotunan da ta ɗauka a ɗazun bedroom na dattijuwa ta fitar, miƙa mashi wayar ta yi tana faɗin. "Dik waɗan nan suna da sa hannun a abubuwan da suke faru, and ka nemosu zaka samu dik abin da kake so daga bakunansu".

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a ransa ya furta alhamdulillah almost 3 times, kai amma ya ji matuƙar daɗi, koba komai yanzu ya sami wasu da face ɗinsu yake a buɗe, a gaskiya Leesharh ta taimaka mashi, ya kuma ji daɗi, dole su nemo waɗan nan fuskokin.

Cigaba ya yi da duba hotunan a tinaninsa zai ga wasu, sai kawai ya fara ganin hotunansa kala daban daban a cikin wayar, dik kuma bai sani ba ta yi ta ɗaukarsa, sun yi fitina hotunan ba kaɗan ba, saboda yadda ta ɗaukesu bai sani ba, kun san hoto idan baka sani ba aka ɗauketa wlh ya fi kyau, ba karamun daɗi ya ji ba, ɗago idanu ya yi ya kallenta, while ita ma shi take kallo. Suna haɗa ido ta yi gaggawar sunkuyar da kanta ƙasa. Matsar da kujerarsa dab da ita sosai ya yi tare da ɗaura hannunsa a saman shoulder ɗinta, ya kashe masu selfish mai bala'in kyau, murmushi ne ya subce mata tasa tafukan hannayenta ta rufe face ɗinta tana yin ƙasa da kai!.

"Waye ya ce a saci mun hotunana ba tare da izinina ba?!". Ya faɗa yana janyota jikinsa. "Kai Yah Ramish ni da hotunan yayana kuma ka ce meyasa na sata? Yayana ne fa!". Ta faɗa tana cigaba da rufe fuska. Haɓarta ya ɗago. "Ni ban yarda da wannan wayan ba, kawai a bani amsar me ake yi da hotona". Ya kai karshen maganar tare da matsar da bakinsa saitin kunnuwanta. "Ko dan kinga kyakkyawan guy yaron mamarsa shi ne kika kyatsa kika kware mun e ƴan'mata?".

Ɗan turo baki ta yi. "Ni ba wani kyatsawar da na yi". "Da gaske?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "To me kike yi da hotunana? Faɗa mun in ji!". "Ni babu abin da nike yi da su". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Masu sunanki suna mai daraja basa karya fa, faɗa mun gaskiyar me kike yi da su?!". Kara rufe face ɗinta da kyau sosai ta yi kafin ta ce. "Zuwa dare zan faɗa maka, amma yanzu please ka barci". Ɗan lumshe idanu ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya. "Mu je gida ko mu je yawo?".

Shiru ta ɗan yi, can sai ta ce. "Yah Ramish yaushe zaka kai ni gidan Abbie in ga ƴar uwata?". Take mood ɗinsa ta ɗan canza, alamar bai ji daɗin maganar bama, amma sai ya ce. "Ba yanzu ba, sai mun kammala binciken da muke yi, zuwanki gidan a yanzu babban haɗari ne sosai". Da zata ce ya kaita a yanzu, amma ganin ya nuna alamar rashin jin daɗi yasa ta hakura, sai ta ce su wuce gida kawai dan tana san kasancewa da guyson and Auta. Bai musa mata ba ya ɗauketa suka wuce wajen cin abinci mai kyau da tsada game da tsaro, daga haka suka wuce gida ya mayar da ita ya sake dawowa h-c ɗinsu dan su cigaba da bincike a kan wannan zane da ta basu game da hotunan waɗan can fuskokin!.

🔥🔥🔥🔥JIMETA🔥🔥🔥🔥

Ai tijara Nenne ta tsayar masu a kan ko sama zata haɗe da kasa yau sai bappa ya fitar mata da Mahreen, idan kuma ba haka ba zai ga jajjagen bala'i, banza da ita ya yi tare da wucewa ya shiga cikin gida abinsa, ransa fes tin da Mahnoor dai ta koma ga mijinta, yanzu damuwarsa a nan shi ne kewarsu da ya addaba mashi.

Ɗakin Diddi Mairo ya wuce ya je ya kwanta a zuwan anjuma zai koma wajen kiwonsa. Yana cikin kwanciyar ne ya ji mutum a kansa, ɗago kai da zai yi sai ganin Nenne a tsaye da zabgegen wuƙa tana kaɗa ƙugu kamar sandar snooker a kan lallai ya fitar mata da Mahreen, cikin sauri ya miƙe zaune yana kallonta, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce. "Amma baki da hankali ko? Ko dai wani abin ne kika sha a yau?".

Wata uwar harara ta dalla mashi kafin ta ce. "Gaka babban mahaukaci kuma azzalumi! Ka sayar da ƴarka ga masu kuɗi, wlh sai ka fitar mun da Mahreen ko kuma in kasheka a cikin ɗakin nan, bakin shaiɗani kawai"....... Ransa ne ya yi mummunar ɓaci jin kalaman da take dangantasa da su, wai baƙin shaiɗani, cikin fushi ya miƙe tsaye suna fuskantar juna. Yau ya koma ainahin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login