Showing 81001 words to 84000 words out of 403653 words

Chapter 28 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

133

kawai take gani a face ɗin guyson.

Sam bashi da kuzari a jikinsa ya dawo da kallonsa a kan Momma, Mahreen sai faman jan mashi hannu take yi.

"Bita muje ka ji, dik yadda aka yi a gidansu yayanka ya zauna shiyasa take janka, ga dikkan alamu kallan matsayin yayanka suke yi maka".......... Cewar Momma kenan.

Kamar zai yi kuka ya ce. "Momma jikinta dik datti fa! Kalli yadda ta zo ta taɓani ta ɓata mun jiki".

Kunsan guyson ɗan wanka ne, ga kayan jikinsa farare kal kal, irin Pakistan na maza riga da wandon nan ne, ya sha rawani a kansa, kyau iya kyau, so baya shiri da datti ko kaɗan, Allah sarki dan ma yana da saukin kai ne yasa bai yi mata faɗa ko ya mareta ba, da su Omaid ne ai da yanzu zancen sun sumar da ita ake yi.

"Yi hakuri, ɗaukin ganin yayanka yasa ta yi maka haka, idan mun koma gida sai ka cire kayan ka ji?"................ Cewar Momma.

"Momma ni Allah bana san dattin, kice kawai ta sakeni".

Momma da ta fahimci zai iya saka masu kuka a wajen, dan wlh ko da wasa baya san datti, sai ta riko hannun Mahreen da take rike da shi, cikin harshen larabci ta ce da Mahreen.

"Zo wajena kin ji?......"

Bata idasa maganar ba Mahreen ta kwace hannunta, cikin tsiwa ta ce. "Wacece ke da zaki rikeni? Ni ki barni a wajen hamma na". Tana kai karshen maganar ta sake rike hannun guyson.

Kasancewar da fillanci ta yi maganar sai momma bata gane me ta faɗa ba. Shi kuma guyson tana rikesa ya fisge hannunsa da karfi haɗe da cewa........... "Kada ki sake rikeni da hannunki dik datti".
Da larabci ya yi maganar. In baku manta ba a baya Mahreen ta fara koyar larabci kaɗan kaɗan, dan haka ta ji wannan kalmar da guyson ya ce ta sake shi.

Sai kuma a lokacin ta lura voice ɗinsa ba iri ɗaya da Jaish ba, muryarsa na yara ne, kuma ɗan siriri ne sosai. Fahimtar hakan yasa ta yi saurin ja da baya daga kusa da shi.

A tinanin momma tsawar da ya daka mata na ta sake shi ne yasa ta ja bayan, dan haka sai ta yi ƙoƙari matsawa kusa da ita ta rikota. Ai ina, a miliyan Mahreen ta juya ta bar wajen tana rushewa da kuka mai ban tausayi, Allah sarki ta gane ba Jaish bane yanzu.

Uncle Jahiz da ya tsaya yana turɓune fuska yana binsu da kallo ne ya matso kusa da momma............ "Ga gidan nan, ku shiga ku yi abin da zasu yi kin dai ji yaya ya ce kada mu kwana, yau zamu juya". ....... Ya faɗa ransa a ɗan ɓace, da alama bai so batun zuwansun nan ba sam.

Momma ta lura da baya san zuwa, dan ma saboda ita ce, wlh da mummyn Chuchu ko mama ne ba zai zo ba, dan haka sai ta wuce gaba saboda su yi sauri su je su fito.

Cikin mutunci ta gaida Arɗo, sannan ta buƙaci da ya yi mata jagoranci izuwa ciki, bodyguards zasu shige cikin su duba babu wani abin cutarwa kafin ta shiga, ta yi saurin dakatar da su, ta ce su bari zata shiga kawai.

Mairo Arɗo yasa ta tarbesu hannu bibbiyu, a lokacin da suka shigo bappa baya ɗakin, ya samu kaikayin ta sakesa saboda Arɗo ya labta mashi kashin sosai a jikinsa.

Nenne kuma ta gudu gidan Arɗo, so Mairo ce kawai a cikin ɗakin tana ƙoƙarin gyara komai, ta fitar da tabarman da aka kwantar da bappa, ta juye mashi wani ruwan wankar ya shiga wanke jikinsa, da yake isaka na kaɗawa sosai ma har kashin shanun ta bushe a jikinsa.

Tabbas momma ta ji kyamar shiga cikin gidan, amma duba irin alkhari da suka yi mata, ɗanta sukutum, first born ɗinta suka kula mata da shi, sai ta danne kyamar ta shiga cikin gidan.

Guyson kam ya gudu wajen uncle Jahiz sun koma cikin mota sun zauna. Time da Mairo ta yi masu iso cikin ɗakin, Momma ta so ta ki shiga, amma kuma da ta tuna Jaish sai ta daure ta shiga ciki.

Mahnoor kuwa ganin babu Jaish a cikin tafiyar sai ta dawo cikin gida ta wuce ɗakinta ta kwanta, ita kuwa Mahreen bin momma ta yi har cikin ɗakin bappa dan taga me ya kawosu gidansu?.

Arɗo ma ya shigo cikin ɗakin dan ya ji me ya kawo su Momma?. Cikin girmamawa Mairo ta tsugunna ta ɗagawa Momma gaisuwa.

Sai dai kash babu fillanci, momma bata gane komai da suka faɗa ba, da yake Arɗo babban malami ne yana jin larabci sai ya sanar da momma gaisuwa Mairo take yi mata.

Jinjina kai kawai momma ta yi, ta ku ma ɗan ji daɗin ansamu mai jin irin larabcinta, dan haka sai ta faɗa mashi ita mahaifiyar bakon da suka rike ne, ta zo ne ta yi masu godiya bisa rike mata yaro da suka yi.

Sosai Arɗo ya yi mamaki, a wani ɓangaren kuma ya ji matuƙar daɗin hakan, ko ba komai sun nuna sun san anyi masu halarci.

"Bani na rike ɗanki ba, ɗana ne ya riƙesa, ya shiga wanka bari ya fito sai ku gaisa".......... Cewar Arɗo.

Jinjina kai momma ta yi ba tare da ta yi magana ba, dik zama a cikin ɗakin ya isheta, ji take yi kamar zata yi amai, amma haka ta daure har bappa ya fito daga wanka, yana sanye da jampa blue, ta koɗe kam sosai, jikinsa fa dik ya ji ciwo bawan Allah, bayansa ta ɗaye, kai Nenne muguwa ce, ta gana mashi azaba, wannan ma fa wai yanzu aka fara zaman kishin, anya nan gaba Nenne ba zata saka masu wuta ba kuwa.................🤔

Lokacin da su Momma suka zo bai gama dawowa cikin hayyacinsa ba, so bai san da batun zuwan nasu ba. Da ya fito yaga jirage a saman suna shawagi kuma sai ya ce bari ya je ya wanke jikinsa da sauri ya fito yaga menene yake faru? Shi ma dai da kallo jiragen sau ɗaya ya raya a ransa Jaish ɗinsa ne ya dawo garesu.

Har kamar zai fita waje da ya fito daga wanka, sai kuma ga kalli sabbin Queen cover shoes masu bala'in kyau a kofar ɗakinsa, hakan ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, shi ne ya ce bari ya shiga ya ga wacece a ciki.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga. Arɗo ne ya amsa mashi sallamar tasa. Yana ɗaura idanunsa a kan momma ya gane cewa mahaifiyar Jaish ce, wani irin farinciki ne ta lulluɓesa, Allah sarki har kasa haƙura ya yi sai da ya tambayi ina Jaish, ko zama bai yi ba.

Sai dai da fulatanci ya tambaya, ya manta da basa jin fillanci, sai da ya ji momma bata amsa shi bane yasa ya juya harshe izuwa larabci.

Mahreen tana ganinsa ta yi sauri ta zo ta rungumesa tare da saka mashi kuka tana faɗa mashi hamma bai dawo ba sai dai wani mai kama da shi ne ya zo. Guyson kenan.

Nan take bappa ya ji jikinsa ta yi sanyi, gabansa har sai da ta faɗi, dik tinaninsa Jaish ya dawo garesu ne. Arɗo ne ya ce mashi ya nemi waje ya zauna momma wajensa ta zo.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya samu waje ya zauna yana tinanin Jaish. Cikin mutunci da girmamawa ya ɗagawa momma gaisuwa da larabci.

A ɗan dake ta amsa mashi kafin ta ɗan yi shiru na ƴan mintuna. Sannan ta gabatar mashi da wacece ita da kuma abin da ya kawota.

Sosai bappa ya sake jin zuciyarsa ya karaya, wato godiya suka zo yi mashi ma ba wai sun kawo Jaish bane, sam abin bai yi mashi daɗi ba, ba haka ya so ba, shi bai yi dan ayi mashi godiya ba, saboda Allah da kuma kaunar da yake yi wa Jaish ya yi.

Ganin ya yi shiru kaman ya shiga damuwa ne yasa Momma ta buƙaci da ya bata tarihin a ina ya ga Jaish da har ya rikesa na tsawon watanni haka?.

Jiki ba kwari ya zayyana mata komai daga farko har karshe, bai ɓoye mata komai ba har da gudun Jaish da ƴan kauyen suka rinƙa yi suna ce mashi aljani, dik ya zayyane mata.

A gabaɗaya maganganunsa da ya faɗa abu ɗaya ne ya yi mata daɗi shi ne Jaish ya yi aure, wannan magana ta yi mata daɗi sosai, har sai da ta ɗan murmusa, cike da farinciki a ranta ta buƙaci da a nuna mata matan ɗanta.

Bappa ya yi mamakin ganin bayyanar farinciki a tattare da ita daga jin Jaish yana da mata, ya yi zaton zata ki batun auren, ashe ba haka bane baiwar Allah. Tabbas momma har cikin ranta ta ji daɗi, saboda ko ba komai ta kara samun ɗiya mace, sannan kuma zata rama masu alkhairi da suka yi mata, sun cancanci hakan, sun cancanci a rike masu ƴa da amana, dik ɗan halak ba zai manta halacci ba, dan haka tana maraba da Mahnoor from the button of her heart. Kuma ni da ku mun san bappa ya yi matuƙar ƙoƙari a kan Jaish, kada ku manta fa farko ko irin abincinsu Jaish baya iya ci, amma haka bappa ya rinƙa yanka mashi nama yana ci, dik kaunar ƴan kauye da dabobinsu haka bappa ya sadaukar da nasa dabbobin wa Jaish, ai ya yi namijin kokari.

Allah sarki ni Princess Teema na ji matuƙar tausayin Fanan, tana murna Jaish ɗinta ya dawo sai aure, ashe mata garesa, heart breaked!!.

"Mahreen jeki ki kira Mahnoor a ɗakinta". Cewar Bappa.

Cikin kunci, tana guntun kuka ga hawaye a saman face ɗinta ta miƙe ta fita, sai gunjin kuka take yi. Godiya momma ta yi wa bappa sosai tare da nuna mashi jin daɗinta a kan wannan aure, ta kara mashi wani godiya na daban a kan bawa ɗanta mata da ya yi, daga karshe ta rufe mashi da zata tafi da Mahnoor.

Tashin hankali, nan fa matsalar take, dan kuwa bappa bai shirya rabuwa da Mahnoor ba, a tinaninsa wai sai dai Jaish ya zo su yi zaman aure da ita a cikin kauyen, shi bai yarda a ɗauketa ba, ita kuwa Momma ta ce mashi ina hakan ba zai yiwu ba, Mahnoor matar Prince ce fa ba wai matan mutum gama gari ba, ai kuskure ne ma su bari wani yaga face ɗinta, nan fa momma ta shiga zayyana mashi dokikin gidan sarauta da tsarukanta da yadda matansu suke kasancewa cikin tsaro da lulluɓe kai, daga karshe ta ce tafiya da Mahnoor dole ne!!! Idan suna da ra'ayi su tashi mutanen da zasu bisu su ga in da suke, amma tafiya kam babu fashi............ Babbar magana.

Bappa ya yi shiru cikin ransa yana tunanin yadda zai fara rabuwa da yarsa. Dik tattaunawar da suke yi Ibrahim kawunta yana jinsu, dan yana zaune a tsakar gida, ba ƙaramin daɗi ya ji ba na jin matsayin da Mahnoor ta samu, abin da basu taɓa tsammani ba, ya ji daɗi da suka ce zasu tafi da ita, kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha.

A tare Mahreen da Mahnoor suka shigo cikin ɗakin, Allah sarki ashe da ta koma cikin ɗakinta kuka ta je ta rinƙa yi, idanunta har suka kumbura. Suna shigowa bappa ya ce da momma ga matar Jaish ɗin, ya kuma cewa Mahnoor wannan mahaifiyar mijinta ne ta je ta gaisheta.

Matsawa ta yi kusa da momma, kanta a kasa ta tsugunna zata gaisheta. Jawota momma ta yi ta runguma tana tsananin farinciki, dan kuwa tamkar an shiga ranta anyi bincike kafin a bashi wannan mata, tabbas irin matar da take mashi fata take kuma yi mashi addu'ar samu kenan, kyakkyawa san kowa kin wanda ya rasa, abin ya yi mugun yi mata daɗi, dik wani bakincinkinta sai ta ji ya kau, tamkar zata mayar da Mahnoor cikin cikinta saboda so da kuma murna.

Shi dai bappa dik wannan bashi bane damuwarsa ba, ya za'ayi momma ta ce, zasu tafi da Mahnoor? Gaskiya ba dan su gidan sarauta ba a ja in ja da su ba wlh da shi dai ba zai yarda ba, amma ba yadda ya iya.

Dai'dai lokacin Jaish ya kira Momma ta Whatsapp, voice call kuma ya kirata, dan ya gwada number kai tsaye taki shiga.

Ganin shi ne yasa ta yi saurin ɗauka, cikin nitsuwa suka gaisa ya tambayeta ya hanya?. Murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha ta ce mashi ai gata a cikin gidansu tare ma da matarsa.

Ya ɗauka wasa take yi sai ya ce. "Momma kada ki ɓata lokaci please, ku dawo da wuri dan har na damu na fara kewarki".

Ita kuwa sai ta ce mashi ga matarsa nan su gaisa.

A ɗan dakile ya ce. "Mata kuma?!".

Jinjina mashi kai ta yi haɗe da tabbatar mashi, bada ban ita ta ce matarsa ba da ya ja tsaki kuma ya kashe wayarsa, amma ita ce ya zai yi? Sai ya ce.......... "Please momma kada ki fara wannan zancen auren naki, ni kada ki ce ma zaki ga ƴar mutane ki saka mata ran aurena, bani da lokaci a yanzu, please kada ki mun irin abin da kika yi wa uncle Abbas, zan tabbata cikin kunci". Yana maganar fuska a ɗaure tamau kamar hadari, alamar bada wasa yake yi ba!!.

Kunsan momma ita ta haɗa auren uncle Abbas da maman su Yah Jawad, kawai daga ziyara ta haɗa wannan aure, to shi Jaish a tunaninsa irin taga mace kyakkyawa ne ta ce zata zaɓa mashi, kwata kwata bai taɓa kawowa ransa matar ta gaske ce kuma mallakinsa ce ba.

Momma da ta rasa me zata ce mashi saboda bata san tsayawa yi mashi dogon bayani ta waya, sai ta ce mashi zasu yi waya anjuma, yanzu bari ta samu ta bar wannan kauyen su kamo hanyar kasarsu shi zai fi.

Da okey ya amsa mata, har zai katse kiran kuma sai ya sake ce mata dan girman Allah shi kada ta jajuɓo mashi bala'i yana zaune lafiyarsa. Bata amsa mashi ba ta katse kiran, dan bata san biye mashi yanzu.

Bappa dik da bai san da waye take waya ba sai ya ji yana san yin magana da na cikin wayar, dan zuciyarsa na faɗa mashi da Jaish take waya.

In short haka momma ta gama dik abin da zata yi, ta kawo makudan kuɗin da suka canza nasu izuwa na Nigeria, miliyoyi ta bawa bappa, suka kara yi masu godiya sosai, sannan ta ce yakamata su tafi da wani ya bisu ya ga ƙasarsu.

A nan ne Arɗo ya ce su tafi da kawu Ibrahim. Bappa ma ya aminta da hakan. Sai kuma me?.

Momma tana rike da hannun Mahnoor taki saketa, sai da suka je zasu shiga motocinsu Mahreen ta ce wlh basu isa ba, bata ga uban da zai rabata da ƴar uwarta ba. Ita ma Mahnoor ɗin kuka ta saka masu, ta ce wlh ba zata iya rabuwa da Mahreen ba, infact sai cewa ma ta yi da a rabata da Mahreen gara ta hakura da Jaish ɗin har abada.

Ganin haka yasa momma ta ce zata tafi da su dikkansu biyu kuma ta yi alkawarin zata rikesu amana, dan ba zata iya barin Mahnoor ba, ai ita taga wa ɗanta matar da babu rabuwa.

Nan fa bappa kuma ya ce gaskiya bai aminta a tafi da Mahreen ba, to shi wa za'a bar mashi?. Sai da Arɗo yasa baki ya roƙesa a kan ya dubi girman Allah kada ya raba ƴan uwan nan guda biyu, tare suka taso, tare suke komai, suna bala'in kaunar junansu, idan ya rabasu wlh zai cutar da su ne, ya yi hakuri ya kyalesu su tafi ɗin kawai.

Kun san abin isn't easy wlh, rabuwa da yara biyu lokaci guda, yaran ma su kaɗai ka mallaka, a rabaka da su kai akwai wuyar iya ɗauka fa. Da kyar da suɗin goshi bappa ya aminta da su tafi a tare. Kawu Ibrahim ya yi masu rakiya suka tafi.

Nenne tana gidan Arɗo bata san abin da yake faruwa ba, daga baya ta ji maganar daga sama, tuni ta rugo tazo dan ta ganewa idanunta, sai dai kash, suna tafiya tana isowa, dan haka bata samu damar ganinsu ba. A lokacin kuma bata san da Mahreen aka tafi ba, da za'ayi bala'i kam.

To our Mahnoor safe journey, daga Jimeta sai Abuja, daga Abj sai Tunisia, Allah ya kaiku lafiya.

9:30pm. Su momma suka isa Tunisia, su Mahnoor sai kauyanci suke ta bugawa, da yake Mahnoor tana da kunya, ta san momma surkuwarta ce, sai tana danne kauyancinta.

Ita kuwa Mahreen da suka zo shiga cikin kingdom of power, idan baku manta ba dama akwai wasu gumaka na zakuna a bakin gate ɗin, sannan akwai kungin Aunty MieMie. Ai kuwa tana ganinsu ta fara yi wa su Momma hauka wai taga mugun abu.

Da kyar Ibrahim ya rarrasheta, haka a wajen shiga jirgi ma ta rinƙa yi masu hauka, ta ki hawa sai da Ibrahim ya ɗagata, Mahnoor dai dik da a tsorace take ta danne bata fito fili ta yi haukar ba, sai dai zuciyarta cike yake tab da tashin hankali, ta gama tsorata. Dama da pr jet ɗin King Zuhair suka zo.

Ai Mahreen bata gama yi masu hauka bama sai dai suka nufi family part, a lokacin ne suka ga hauka, ta rinƙa yi masu kuka a kan ita a mayar da ita wajen bappanta, ai nan ba duniya aka kawota ba, kasheta za'ayi. Ta ƙanƙame Ibrahim tana ihu.

Ita ma Mahnoor kukan nan take san yi, amma ta danne, idanunta sun ciko da kwallah sun yi jajir. Ta kofar baya motocin su momma suka tsaya, dik da dare ne basu tsaya ta gaba ba, dan in baku manta ba doka ce ba'a ganin matan sarki.

Momma tana rike da hannun Mahnoor gam suka nufi cikin gidan, sai ta ce Ibrahim ya jirata a wajen zata turo wanda zai kaisa masaukinsa. To shi Ibrahim ya saba yawace yawace bai wani tsorata sosai ba, amma dai ya ɗan tsorata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login