Showing 351001 words to 354000 words out of 403653 words

Chapter 118 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

56

abin ya yi mugu mugun taɓa shi, sai dare yake zuwa dubata, har a yanzu yana ganin kamar idan aka ja lokaci kaɗan zata miƙa wuya ta hakura, shiyasa bai fara nadama ba, ban ji kamar bai kyauta ba, ya cigaba da tinanin dik in da aka yi one month zata mance da komai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam. Uhm akwai cakwakiya sosai!.

Shi kuma commander har aka yi jana'izar Hoorain aka binnesa ba tare da ya gana da shi na karshe ba, dan bai yarda da ya mutu ba, shi yana ganin ɗansa. Auta ta yi ta yi su kaita ta ga Smart, amma sun ki, sun ce mata baya nan, dan King yasan haɗuwarta da Smart ba zai yi mashi kyau ba, ta yi ta yi su bata waya ta yi kira nan ma abin ya ci tura, King ya gargaɗi kowannensu da kada su kuskura su baiwa Zunaira waya, su kyale ta har a samu ta samu lafiya ta mance da wani Hoorain, ya ce a barta sai ta fara sabuwar rayuwa da Abdussalam ta nisa sai a faɗa mata Hoorain ya rasu a wannan lokaci ba zata damu sosai ba. Uhm King yana ganin cewa soyayyar yarinta ce kawai Auta take yi, bai san abin ba haka bane, ya sha gaban yarinta King!!. Mu je dai zuwa, lokaci ne zai banbanta maka da cewa soyayyar yarinta Auta take yi ko kuwa na gaskiya!!!.

-----------------------------------------🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥

Fito da Leesharh suka yi da nufin su tafi da ita, tsabar rashin imani ma gashin kanta suka damko suna janta da shi. Dai'dai zasu gifta shi in da yake kwance yasa hannu ya damki kafar wanda ya riketa ɗin, da karfi ya yi wurgi da shi tare da miƙawa tsaye a kan ƙafafunsa.

A take suka saki Leesharh suna kallonsa da mamaki, ba su yi zaton zai miƙe ba. Wlh bibbiyu yake kallonsu saboda wani irin jiri dake ɗibarsa, ba karya sun buga mashi karfen sosai a kai. Haka ya daure ya rike kansa yana binsu da kallo, so yake yi ya san su waye su? Ya cire mask dake fuskokinsu ya gani.

Wanda ya rike da light ɗin ne ya ɗaure wutar a saman stair case, hakan yasa haske sosai ya baibaye wajen, suna iya ganin juna yadda yakamata........ "Ku kashesa, dik da baya daga cikin waɗan da aka bamu aiki a kansa, amma ya zame mana maciji a bakin kofar wucewarmu, dan haka ku kashesa mu samu hanyar wucewa". Ogan nasu my light ne ya yi maganar. Masu nikaf ma a yanzu basu san Ramish ne yake tare da Leesharh ba, dan suna tinanin ita kaɗai ya zo ya ɓoye a gidan sai masu tsaronta, shiyasa suka bada wannan aiki na a dauko Leesharh kawai, da sun san Ramish yana gidan zasu bada aikin a kashe shi a ɗaukota ne!!

Lokaci guda wani murmmunar faɗuwar gaba ta dira zuciyar Ramish, domin kuwa voice ɗin nan ta yi mashi kama da wanda idan shi ne lallai zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba.

Cike da karɓar umarni suka nufosa gadan gadan, dama su biyar ne. Dik da halin da yake ciki haka ya daure suka fara kokawa. Kuka sosai Leesharh take yi tana tari mai sauti saboda tashin hankali........ Suna fara faɗa ya ji wani karfi ya zo mashi, Allah ya taimakesa ya jibgesu sosai har suka fara gudu da kafafunsu. Nan fa ya bi su suka sauka ƙasa parlour kenan, suna gudu yana binsu, yana san kama mutum ɗaya ne ya cire mashi mask ya ga su wanenen.

Har suka fita wajen gidan, dik bai dai'na binsu ba, gudun cetar ransu suke yi. Dai'dai zasu sha kwana ya kama ogan nasu ta baya, kokawa suka fara yi a in da Allah ya bashi nasarar cire mashi mask ɗin nasa. Yana cire mashi kuma guy ɗin ya kwace kansa yana ƙoƙarin gudu, sai dai ya juyo kafin ya gudu, kuma juyowan nasa ne yasa Ramish ya yi mutuwar tsaye yana kallansa ya kasa iya cigaba da binsu.

Wani irin zaro idanu ya yi yana kallonsu suna gudu, muryarsa na rawa ya furta. "RAJ". Girgiza kai ya shiga yi yana faɗin. "No ba Raj ba ne, wlh ba shi bane, kawai idona ne, tabbas bana gani da kyau". Wani irin jiri da ya ɗebesa ne yasa ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen yana cigaba da sambatun cewa wannan ba Dr Raj kaninsa bane!!!!. Tabbas Dr Raj ya gani, haƙiƙa ba karya idanunsa suke yi mashi ba!! Innalilahi wa inna ilahir rajiun

Tashin hankali!! Wai ni Teema mafarki nike yi ne ko gaskiya? Da sanya hannu Dr Raj a masu san ganin bayansa ko kuma dai wani dalilin yasa yake tare da sh?. Kai kaninsa ne fa! Kenan da Dr Raj da Bilal tafiyarsu ɗaya? How? Ko dai Dr Raj ba ɗan mama bane? Kai akwai rikitarwa wannan lamari, ya Ramish zai yi ransa? Innalilahi wa inna ilahir rajiun!!! Wannan shi ne ainahin tashin hankali.

Special na ce yau zan baku page mai sauki sauki ko? To ga shi nan da sauki saukinsa 🥱😅 ku karanta ƙwaƙwalwa ta ƙara ɗaukar wuta, ina ga page na yau ma ya fi na jiya tsanani 😥😅 to ina masu chorry🤓

Kada ku damu, zan baku update da zan ɗan saukaka maku a cikin satin nan.🥱 Mun iso INTERMISSION ne, dole komai ya ɗauki zafi, akwai kwayayen da zasu fashe soon!! Ku dai ku cigaba da bibiya, kun san bana yin abu sai da kwakkwarar dalili ko? To zaku ji dalilin soon. By much love 💘 🔥


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S



55



Ramish ya jima a wajen sosai kafin ya iya yunƙurawa ya miƙe tsaye, jiri yana cigaba da ɗibansa. Kasa iya juyawa ya koma ya yi, sai ya tsaya cak yana tinani, kansa ya kulle, abubuwa sun cakuɗe mashi. Shessheƙar kuka da ya ji daga bayansa ne ya sanya shi yin gaggawar juyowa. Tsaye take tana haki tana kuma shessheƙar kuka mai ratsa zuciya, kasa hakuri ta zauna a cikin gidan ta yi, shi ne ta fito da gudu ta bi bayansa, hankalinta a tsananin tashe, fargabarta ɗaya shi ne kada su ci galaba a kansa.

Ajiyar zuciya ya sauke a lokacin da ya ganta, ta ɗan duƙa tana haki sama sama. Hannayensa ya buɗe mata alamar ta zo, babu musu ta ruga da gudu ta faɗa jikinsa tana sake fashewa da kuka, tsananin tsoro ne kwance a cikin idanunta, ya lura da hakan shiyasa ya ce ta zo garesa ko zata ɗan sassauta.

Tattara dik sauran karfin da suka rage mashi ya yi ya ɗauketa cak, dan tsayuwarsu a waje babban haɗari ne, they have to be enter in. Ta fahimci yana cikin tsananin damuwa, dan haka sai ta ɗago da kansa daga saman kirjinsa, ɗan zuba mashi idanu ta yi yana tafiya kafin tasa hannunta dake ta faman kerma ta ɗan shafi face ɗinsa. "Yah Ramish sun ji maka ciwo ne?". A ruɗe ta yi maganar. Hakan yasa ya dawo da kallonsa a kanta. Kai ya ɗan girgiza mata alamar a'a ba tare da ya yi magana ba!! Wani irin yawu mai wuyar wucewa ta haɗiya game da sauke ajiyar zuciya.
Da kyar ya iya nufar ciki da ita. Unguwar so sillent sosai.

Suna shiga ciki ya fito da wayarsa bayan ya sauketa a tsakiyar bedroom ɗinsa, kunna wayar ya yi, emagemcy number na masu gyaran wuta ya kira tare da sanar da su buƙatarsa, sannan ya katse kiran. Wani zuciya ce ta ce mashi ya kira Smart ya sanar da shi halin da yake ciki ko zai samu sauki a ransa, dan gabaɗaya zuciyarsa ta zanto tamkar an ɗaura garwashin wuta a kai. Idan har da gaske ya san Dr Raj, to ba shakka shi ne wanda ya gani a yanzu!! Kamar zai kira Dr Raj ɗin ma, sai kuma ya fasa, tinanika kala kala ne sosai a ransa. Ita kuma tana tsaye a kusa da shi, a dai'dai wannan lokaci aka dawo da wutar gidan, masu gyaran wuta har sun iso sun gyara.

Gaban mirror ya nufa, face ɗinsa ya zubawa idanu yana kallan kansa. Lokaci guda gabansa ya yi wani irin mummunar faɗuwa sakamakon wani tinani da ya yi, wayarsa ya kawo face ɗinsa, number mamansa ya fara kira ba tare da ya duba time ba. Bugu ɗaya ta ɗaga, ɗan gyaran murya ya ɗan yi kafin ya yi mata sallama.

Tana daga kwance a saman katafaren bed ɗinta bata san time da ta miƙe ba jin muryarsa wani irin, cike da tsananin tsoron kada ace wani abin ne ya same shi ta amsa sallamar tare da tambayarsa ko lafiya yake?. Nisawa ya yi kafin ya ce. "Lafiya lou mama, aiki na sha na gaji". Wani irin ajiyar zuciya da ta sauke sai da ya jiyota, alhamdulillah ta furta sau uku a jere tana ɗan rintse idanu.

"Mama menene ratar dake a tsakaninmu da Raj? And Mama kada ki ɗauki tambayata da wata manufa please ke kika haifeni da gaske?".......... Ai bata san lokacin da numfashinta ya ɗan dakata na ƴan dakiku ba, zaro idanu sosai ta yi, lokaci guda ta rikice. "Ramish wani irin tambaya ce wannan kuma?". Ta yi maganar word ɗinta suna harhaɗewa........... "Mama ai dama na ce kada ki ɗauki tambayata da wata manufa, kawai na yi ta ne ba dan wani abin ba sai dai ina san sani".

"Wallahi billahi ni na haifeka Ramish, meyasa kake tantama?!!". Daga yadda ta yi maganar ya fahimci da iya gaskiyarta ta yi, dan haka ita ta haifesa, sai dai idan Dr Raj ne ba ɗanta ba, dole akwai wata a ƙasa. "To mama Raj..........." Ƙasa ƙarisa tambayar ya yi, dama zai tambayeta ita ta haifi Dr Raj ne, sai kuma ya tina yanzu zata iya zargan wani abu, shi kuma bayan Smart baya san kowa yasan abin da yake faruwa bare har su ɗaga hankalinsu haka, ta haka ne kawai zai iya cin nasara a aikinsa, rufe sirrinka shi ke kaika ga nasara, and kuma ya tina yana da jinin Dr Raj a bedroom ɗinsa a gidan Abu Abdussalam, yana nan a ma'adanarsu na gwaje-gwajen lafiya, ya taɓa gwada shi a lokacin da ya yi wani ciwo, a lokacin sun tsorata sosai, sai suke ga kamar yana shan miyagun kwayoyi shiyasa suka yi mashi gwaje-gwaje sosai shi da Bilal.

Tina yana da jinin yasa ya fasa yi mata tambayar tare da kawar da zancen zuwa zancen gidan da abubuwan da suke faruwa, a zuwan zai je gobe ya ɗauko jinin ya zo ya gwada ya gwada nasa sai ya tabbatar, ya so ma da ya samu jinin mamar tasu, dan ya kara samun tabbaci, lallai da wuya ne idan Dr Raj ɗanta ne, akwai dai wata a ƙasa.

Zama a gefen bed Leesharh ta yi tana ta kallansa yadda yake waya da mamarsa a natse. Bayan ya kammala ya katse kiran, zubawa kansa ido ya yi yana tinanin kalaman yayansu, wato Smart, a kullum yana faɗa mashi kada ya yi saurin yanke hukunci a aiki, ya koyi hakuri da danne abubuwa game da zurfafa bincike, ya zamana mai tsananta bincike da rufe sirrin dik abin da yake yi, shiru ita ce babban makaminsu a matsayinsu na jami'ai, idan yana zargin na kusa da shi, kada ya kuskura ya bari su iya gane yana zarginsu, ya yi masu sillent walk wajen kamasu, ya barsu su cigaba da rayuwa da shi kamar yadda suke a baya, amma shi yasan irin takunsa a kansu, yana lallaɓawa wajen bincike a natse ta yadda zai haɗa hujjojin da idan ya yi masu kamu ɗaya ba zasu sake dawowa ba!!.

Tuna waɗan nan kalamai na Smart yasa shi sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da furta alhamdulillah. Yana furta hakan ya ji sanyi ta ratsa zuciyarsa, a hankali ya ɗago da kallansa a kanta ta cikin mirror, while ita ma shi take kallah, zubawa juna idanu na ƴan mintuna suka yi, ta shagala da kallan kyansa sai jin sexy voice ɗinsa ta yi ya ce. "Zaki iya bani haɗin kai a yanzu dan mu iya kamasu?".

Kai ta gyaɗa mashi alamar e, dan yanzu ta fara tsorata da al'amarin mutanen nan, kuma ita suke hari sosai, dan sun san ta iya ganesu, idan basu gaggauta kawar da ita ba zata tona asirinsu, ai kun san da suna ganin kamar bata da hujjar nunasu ko da an kamata ne, shiyasa suka saki jiki, amma sai suka ga ba haka bane, kuma ita ma Leesharh ta yi babban kuskure! Domin ba'a nunawa mutane irin wannan cewa ansan wani abu a kansu ko kuma za'a iya fito na fito da su, kun tuna lokacin da suka kirata tana gidan Abbie?. Ba ta ce masu tana da hujoji a kansu har da recoding ba? To wannan shi ne babban kuskuren da ta tabka, da ta yi shiru bata sanar da su cewa tasan wani abin ba, da wlh ba zasu nemi rayuwarta har haka ba....... Ku ɗauki darasi a nan, kuskure ne faɗawa wani abokin faɗa naka cewa kasan wani abin a tattare da shi wai dan ka yi mashi barazana, idan har baya san wannan abin ya fita a duniya to tabbas zai iya cutar da kai koma ya yi ƙoƙarin kawar da kai wa duniya, ba a iya labari ba, a gaske ma ya fi faruwa! Kowa ya iya harshensa, sai dai a ga komai a aikace kamar yadda Smart ya bawa Ramish shawara! Kuma kamar yadda Smart ɗin yake yi! Kun taɓa jin ya faɗi shirinsa wa wani ne? Ai sai dai ku gansa a aikace kawai!!.

"Bari in yi wanka in zo sai mu fara aiki ko?". Ya faɗa yana kallanta. Jinjina mashi kai ta yi. Toilet ya nufa, har zai shiga kuma sai ya tina da dattijuwar dake gidan, wani zuciya ce ya ce mashi ya je ya dubata, wani kuma ya ce to ya bari sai ya yi wanka, hakan kuwa aka yi, ya ce bari ya yi wanka ya fito. Yana shiga toilet Leesharh ta miƙe ita ma, dik da a tsananin tsorace da gidan take hakan bai hana ta daure ta nufi toilet ɗinta ba, dan ita ma ta yi wanka.

After some minutes ta fito shirye cikin kayan barci riga da wando masu covering jiki yadda yakamata, ta ɗaura Arabian hijab a saman kanta, kwata kwata hijabin bai wuci zuwa kirjinta ba. Kitchen ta nufa ta ɗauko cappuccino cup ɗaya da plate na small chop, sai tashin kamshi take yi ta nufi stair case ɗin, tana tafiya tana waige waige, tsabar tsoro sai ji take yi mamar ana bin bayanta. Dai'dai zata wuce bedroom na wannan dattijuwa ta nufi nasa sai ta ji kamar motsi a ciki. Dakatawa da tafiyar ta yi, a hankali ta lallaɓa ta matsa jikin kofar. Ajiye cup and plate ɗin hannunta a kasa ta yi, kamar wata ɓarauniya ta sanya hannu ta ɗan tura kofar bedroom ɗin kaɗan ta buɗe!!.

Ai bata san lokacin da ta zaro ido saura kaɗan ta zunduma ihu ba. Matashiyar mace da bata haura 23 years ba ta gani tsaye a tsakiyar ɗakin, tana sanye da irin fighter wears ɗin nan a jikinta, rike take da waya tana magana ƙasa ƙasa alamar munafurci take kullawa. A hanzarce Leesharh ta juya kallanta izuwa kan gado, nan ta hango kayan dattijuwan, wato kenan matashiyar yarinya ce ta yi shigar dattijai ta shigo cikin rayuwarsu ita da Ramish? Sai a yanzu Leesharh ta tina wannan dattijuwa ai sun jima tare da ita a gidan Abu Abdussalam, kenan dama ashe ba dattijuwa bace?. No wonder take iya aiki lafiya lou ba tare da ta nuna gajiya na tsufa ba, babbar magana, yarinya ce kenan ashe, kam bala'i lallai masu nikaf basu fitowa ba sai da suka shirya, ashe suna da gaskiya da suka ce suna da mutane dayawa a gidan Abbie. Shi Ramish ya kalli dattijuwa ce shiyasa ya ɗaukota ta kula da Leesharh, a tinaninsa tin da tsohuwa ce ba zata yi wani mugunta ba, bai san ya tabka babban kuskure ba!!.

Zuba mata idanu Leesharh ta yi tana karantar bakinta abin da take faɗe....... "Dikkansu suna cikin koshin lafiya fa, babu abin da ya samesu, sai kun kara zazzafar shiri a kansu!!". Shi ne abin da Leesharh ta iya karanta daga bakinta na abin da take faɗe. Saura kaɗan ta zunduma ihu saboda tashin hankali, mamakinta ma ɗaya shi ne yadda wannan matashiya ta yi shigar tsofaffi, ba zaka taɓa cewa ba tsohuwa bace, har da wani ɗan duƙawa idan tana tafiya, wato idan mutane suna san abinka sun fika dabara, ji zukekiyar budurwan nan fa, amma suka mai da ita tsohuwa, har da tamu tamun fata suka saka mata, kai mutum abin tsoro ne, babu mai iyawa ɗan adam sai ALLAHN da ya haliccesa.

Ta shagala da tinane-tinanen da take yi sai gani ta yi dattijuwa zamu ce ko matashiya yanzu kuma?. To oho dai, sai ganinta ta yi ta katse kiran ta nufi wajen bed ɗin, nan ta ɗauki kayanta na dattijuwan ta fara maidawa jikinta, da alama wanka ta yi, shiyasa ta cire kayan. Wani irin zaro idanu Leesharh ta yi tana ganin yadda budurwa take rikiɗewa izuwa tsohuwa cikin ƙanƙanin lokaci, amma sun iya shiri, harta fatarta mai tamu tamun ma ashe ba fatar gaske bace, ashe sakawa aka yi, yanzu ga shi ta ɗauko shi tana mayarwa, har farin gashin kanta ashe attachment ne, shi ma ta mayar. Take ta koma ainahin tsohuwa. Tsabar tashin hankali Leesharh bata san lokacin da ta saki kofar ta dafe kirjinta ba, da karfi yake buga mata ne. Baya baya ta fara komawa har ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login