Showing 288001 words to 291000 words out of 403653 words
mashi a cikin empeir ɗin, tamkar fadar sarki ne shi ma, tsarin ginin ya fi wanda yake ciki komai da komai, sai dai ya ce da zallar gold za'ayi mashi ginin, dan yana san zarce kowani sarki a mulkinsa.
Ni kam na ce mu da mun san tarihin sarkin romawa da su habashawa, a zamanin da manyan sarakunan da suka yi gidan ɗan yar gold a tarihi ma ai suna dayawa, amma yau ina suke? Sun koma ga Allah, to a zamanin nan ma mun samu King Black Tiger, ginin ɗan ƴar gold za'a zuba mashi, my people's yake kuke ayyana wannan gini a ranku? Ɗanyar gold fa? Tab Black Tiger zai tashi hankalin duniya, ai dole ne ma kowani sarki zai so kwace birnin daga hannunsa, ko dan tarin arzikin da Allah ya basu, aww ace fadarsa da komai na gold, dole hankalin duniya ya tashi, ga katafaren filin saukar jirginsa a saman ginin gabaɗaya, ginin dai ya tsaru matuƙa, a zamanin yanzu banda sarakuna da suka shuɗe kafin zuwan manzan Allah (SAW) a zamanin yanzu shi ne mutum na farko da zai yi irin wannan gini, abin dai ba'a cewa komai.
(Ni kuma na ce ya kuke tunani idan ya kammala wannan gini Sweetie ta zama Queen a ciki? Ronnie ya zama Prince? Su dake a fada su ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya suna zartar da hukunci irin na addinin musulunci, ya kuke ganin haɗuwar wannan sabon empire ɗin nasa zata kasance da waɗan nan taurari guda biyun a cikinta?.🤔)
Sai dai har yanzu bai sakawa sabuwar empire ɗin suna ba, ya ce dai su fara kaddamar da ginin sai an kammala zai faɗi sunanta a rubuta a farkon shiga.... Amma kuna tunanin wani irin suna zai bawa empeir ɗin nan?.
Yana kammala sa hannu a kan document ɗin, sai ya sanya hannu a kan wata takardar da ya umarci a biya dik mutanen birnin asarar dukiyar da aka yi masu a sanadin wannan yaki, waɗan da basu bijire mashi ba kuma suka rasa nasu a biyasu diyya na makuɗan kuɗaɗe masu zafi, sannan ya cike wasu takardu na sabbin ma'aikatan da yake san buɗewa na sarrafa abinci da abin sha wanda kowani ma'aikata ɗaya zai iya ɗaukar ma'aikata sama da 500, kunga ya ragewa mata zaman banza, kuma fa shi a ƙaidarsa maza basa aiki sai dai su tafi bakin daga, mata ke yi mashi aiki a dikka ma'aikatunsa domin su samu abin dogaro da kai tun da basu da maza da zasu wani ɗauki nauyinsu........ Yaseen Black Tiger shegen kwaro ne, wai yanzu kun yarda da batun Sweetie da ta ce tana da yakinin akwai abin da ya canza zuciyarsa daga fara zuwa baka? Kun yarda wani lokaci mutumin kirki ne shi, wani lokaci kuma bakin shaiɗani, sai ka rasa gane ina ne takamaiman alkiblarsa wlh, wani lokaci dai ga shi mutum, wani lokaci kuma kai bashi da kyan gani fagen mugunta.
Sai da ya kammala abin da yake yi tsab sannan ya nufi dining room ɗin nasa, da alama ya mance da ita a cikin bedroom ɗin. Wani robbot na tsaye a wajen yana jiran ya kariso ya yi serving ɗinsa. Sai da ta bari ya shiga room ɗin ta miƙe ta bi bayansa tana kara jinjinawa girman arzikin da Allah ya bawa birnin nan. Ba tare da neman izininsa ba ta shiga cikin room ɗin, wannan robbot na ƙoƙarin zuba mashi abinci ta yi gaggawar dakatar da shi tare da cewa. "Zan yi serving ɗinsa kada ka damu".
To kun san abubuwan nasa idan ya rigada ya basu umarni kawai zasu aikata abin da ya ce ne, dan haka wannan robbot ya riga ya karɓi umarnin yin serving ɗinsa, sai ya hanata ya cigaba da yin aikinsa, ba ta isa jayayya da Robbot ba, dan idan ta yi ma ita ce zata sha wahala shi babu ruwansa, dan haka sai ta ja chair dake kusa da shi ta zauna tana kallan face ɗinsa, ya ɗaure fuskar nan tamau yana tinanin gina katafaren football stadium saboda Ronnie, kun san yana sha'awar wasannin.
Kammala zuba mashi abin da ya buƙata wannan robbot ɗin ya yi tare da matsar mashi da plate ɗin gabansa. Chopping stick ya ɗauko guda biyu, zubawa abincin idanu Sweetie ta yi tana mamakin wannan wani irin abinci ne? Bata taɓa gani ba, a hankali ta fara bin sauran cimar da kallo, dik launikan abinci ne da bata san ma da me ake yinsu ba, ga wasu dai kamar nikakkun nama da kwai, wasu kuma kamar damammen shinkafa da yoghurt, abubuwa dai kala kala, baki ta taɓe tana jin ko kasheta za'ayi ba zata iya cin abincin Black Tiger ba, gara ma nasu Ronnie wanda ta sani ne.
Abin da bata sani ba anan shi ne, ta sha cin irin wannan abinci a hannun Kamran, kun san a lokacin bata gani shiyasa bata san irin abincin da yake bata tana ci ba, wlh babu wani banbanci tsakanin cimar mammar Kamran da na Black Tiger, dik irin ɗaya ne, sai dai nata local ne na talakawa, nasa kuma na manyan kai, amma dik iri ɗaya ne, amma har da cewa sun yi mata wani irin ba zata iya ci ba, bayan su ta ci ta girma har ta ƙosa ta yi kumatun da in ta yi murmushi suke birge big bro, eh manaaaaaaaaaaaa.😅
Ɗibar abincin ya yi da chopping stick, abincin wani ball ball haka ash colar, yana ƙoƙarin kaiwa ɗan bakisna cool voice ɗinta ya daki dodan kunnnesa in da take cewa. "Ka yi bismillah kafin ka ci". Ta yi maganar tana kallansa. Tamkar bai jita ba, kamar bai san da halittarta a wajen ba ya cigaba da ƙoƙarin sanya abincin a bakinsa. Cike da tsoro a gaggauce ta kai hannu ta rike hannunsa, kirjinta na bugawa da karfi ta ce. "Please say Bismillah before you eat.........".
Bata gama rufe baki ba robbot dake tsaye ya yi gaggawar kai hannu ya damki wuyarta ta baya tare da capke hannunta da ta rike hannun Black Tiger, dan dolenta ta saki hannun big bro, da hannu ɗaya wannan robbot ya ɗagata daga saman chair ɗin, kai tsaye ya yi wurgi da ita izuwa saman wani kyakkyawan sofa two seater dake wajen wanda an ajiye shi ne dan ɗan hutawa idan ka kammala cin abinci, dama ana san idan ka ci abinci ka ɗan miƙe kafafunka ka huta ko da na 30 mins ne, a nan ne abincin zai shiga cikinka da kyau.
Bata san ba'a kusantar Black Tiger ba idan ma'aikatansa suna nan kusa, yanzu mutum zai bakunci lahira, ita ta samu har ta zauna a kusa da shi shi ne zata kama hannunsa, a tinanin robbot ɗin riko hannunsa da ta yi ta hana shi cin abinci cutar da shi zata yi shiyasa ya yi mata abin da ya yi mata. Kai tsaye ya nufi kanta domin ya zartar da hukuncin da suke yiwa dik wanda ya kusanci Black Tiger. Wuyarta ya rike tare da sanya ɗayan hannunsa zai ɓalle mata makogoron wuya shikenan ya kasheta, yana ƙoƙarin yin hakan Black Tiger ya dakatar da shi tare da ce mashi ya barta ya koma bakin aikinsa, daga haka ya cigaba da cin abincinsa babu wani bismilla da ya yi. Ita kuwa ta sha shakar robbot sai da ta ji kamshin mutuwa, ta zaro ido tana numfashi sama sama.
Shi kuwa Black Tiger a cewarsa ya sa a barta ne saboda ba zai iya ɗaukar haukar da Ronnie zai yi mashi ba, kun san yasan Floris ta mutu ai? To ace Sweetie ma ta mutu, ai wlh Ronnie zai yi mashi hauka mai zigidir mai lasisi, yanzu ma bai san taya zai iya shawo kansa ba idan ya gane Floris ta mutu, saboda har ga Allah Ronnie yana kaunar Floris fiye da tinaninku, akwai soyayyarta ma a kasar zuciyarsa wanda bai san da ita ba, kun ga kuwa babu zaman lafiya idan ya gano meke faruwa, ina ga wlh irin hukuncin da zai yi wa master kare ba zai shinshina ba.
Tana ƙoƙarin miƙewa zaune domin ta samu damar shaƙar numfashi da kyau sai ga Ronnie ya shigo wajen, ko excuse babu, hankalinsa a tashe ya ce. "Big bro please ka tayani neman Floris, dik in da nike zatan zan ganta a cikin empeir ɗin nan babu ita, na tambayi Angela ta ce mun tun shekaran jiya bata kara ganinta ba". Cikin ruɗu yake maganar, har word ɗinsa suna harhaɗewa.
Miƙewa tsaye Sweetie ta yi, take ta ji faɗuwar gaba, a kiɗime ta ce. "Ina ta shiga to? Karfa ace wani abin ya sameta a wajen yakin da aka yi....... ". Cikin zafa Ronnie ya katseta da cewa. "No lovely sis, babu abin da ya sameta, nasan dai fushi take yi da ni shiyasa kila take san bani wahala ta ɓuya, kila ma ta gudu wajen parents ɗinta ne"..... Shi kansa faɗuwar gaban nan yake ji, amma yana ƙoƙarin dole dole sai ya karyata zuciyarsa a kan wani abin ya sameta.
Shiru Sweetie ta ɗan yi kamar mai tinanin wani abin, can kuma sai ta ce. "Muje wajen parents ɗin nata mana mu dubata". .... A gaggauce ya amsa da. "Good idea, lest go". Ya faɗa tare da juyawa da sauri. Cikin kakkausar murya Black Tiger ya dakatar da shi ta hanyar ce mashi kada ya kuskura ya fita bedroom ɗin nan nasa a wannan daren. Turus Ronnie ya tsaya, lokaci guda zuciyarsa ta tilasta mashi dole ya yarda wani abin ya sameta, dan Black Tiger bai taɓa hana shi yin komai ba idan ya sa a gaba, tun da kuwa ya hanasa zuwa nemanta dole akwai abin da ya saɓa, to me kenan? Tashin hankali da fargabarsa ɗaya kada ace mashi ta ji mummunar rauni ko wani abin makamancin haka, shi kwata kwata ma bai kaita ga batun mutuwa ba tukun nan. tashin hankali. Bai ma san har iyayen nata dik babu su ba.
Kallan yayan nasa ya yi, faɗuwar gabansa tsananta ya yi sosai, saboda yasan yayansa na ganin komai dake faruwa a birnin, tabbas yaga abin da ya samu Floris, amma yasan ko ya tambayesa ba zai sanar da shi ba. Dan dolensa ya dawo cikin room ɗin, saman chair ya zauna tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, murya a raunace ya ce. "To big bro da safe zan iya zuwa nemanta?"...... Jinjina mashi kai Black Tiger ya yi alamar e, sannan ya cigaba da cin abincinsa. Umartar robbot ɗin shi ma Ronnien ya yi da ya yi serving ɗinsa. Cikin gaggawa kuwa ya yi, hankalinsa ya ɗan kwanta tun da yayan nasa ya ce da safe ya je nemanta.
"Sweetie ki zo ki ci abinci". Ya faɗa yana ɗaukar chopping stick, cikin natsuwa ya yi bismillah can cikin zuciyarsa kafin ya fara cin abinci. Kai ta girgiza mashi alamar ita ba zata ci ba, sannan ta miƙe ta dawo saman chair ɗin zuciyarta cike da tinanin ina Floris take? Tabbas akwai abin da ya saɓa haka take ji a ranta. Zama ta yi suka sanya Black Tiger a tsakiyansu, shi da Ronnie suna cin abinci ita kuma ta buga uban tagumi tana binsu da kallo.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
Washegari da misalin karfe 9, shirye cikin ƙananan kaya masu kyau ya fito daga cikin bedroom ɗinsa, wata irin trouser ce mai kama da army one, sai shirt milk color ya sanya daga ta sama, yau har da black glass and p-cap milk color ya sanya a kansa, sannan ya sanya ankle boots masu shegen kyau da tsada suma milk color, ya yi kyau matiƙa.
Hannunsa rike da wayarsa. Kai tsaye bedroom ɗinta ya nufa, yana tafiya cikin natsuwa da kamala. Bakinsa a ɗauke da siririyar sallama ya tura kofar bedroom ɗin ya shiga ba tare da ya jira izininta ba. A wani irin miliyan ta juyo da kallanta a kan kofar, tana ɗaure da towel a kirji ta fito daga wanka, gabaɗaya jikinta ruwa. A maimakon ya juya ya bata waje, sai ya ɗan shagala da kallanta irin kallan kasan ido ɗin nan, ita kuwa tana ganin shi ne da gudu ta bar wajen ta shiga dressing room na ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke yana mai ɗago kansa sama kaɗan, kamar wanda yake magana da wani ya ɗan jinjina kansa kafin ya ƙarisa shigewa cikin ɗakin. A saman side bed ya zauna yana bin ɗakin da kallo, a ransa ya hayyana yaushe ta tashi daga barci har ta yi wannan gyara, ta ko'ina kamshi ne yake tashi, yarinya mai tsabta kamar dai shi.
Can a cikin tinanin nasa surar jikinta ya ratso mashi ta cikin kwakwalwarsa, ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda ya gamsu da abu, sannan ya ciro wayarsa domin ta ɗebe mashi kewa kafin ta fito, dan baya san yawan tunane tunanen nan da yake yi, ƙwaƙwalwarsa tana da abin ɗauka mai mahimmancin da ya fi wasu tinane tinanen. Almost 10 mins yana zaune a haka kafin ta fito sanye cikin ɗaya daga cikin abayas da ya saya mata, ta yi matuƙar kyau kasancewar abayar milk color ita kuma chocolate color, ta fita sosai, yadda ta yi rolling veil ɗin sai ya baka sha'awa, ga wani kyakkyawan fashion flat shoe a kafafunta, launin kayan jikinta, sai tashin kamshi take yi sosai. Wucesa ta zo ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba ta nufi waje, sai satar kallansa ta witsiyar ido take yi.
Cikin sanyin murya ya ce. "Aesh come here, wajenki na zo"........... Kamar ba zata tsaya ba, sai ta tina dik in da ta je a cikin gidan ma yana iya biyota, so is better for her to stay with him hare. Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo garesa ba, ta yi ƙasa da kanta dan ita kunyar haɗa idanu da shi ma take yi. Miƙewa tsaye ya yi, cikin kamala ya kariso in da take tsaye. "Wani waje nike san mu je". Ya faɗa idanunsa a kan face ɗinta. Bata da bakin tsayawa yi mashi gardama ko ja in ja da shi, dan haka sai ta jinjina mashi kai kawa ba tare da yin magana ba.
"Zamu iya tafiya?". Ya tambaya yana mai da kallansa kan yatsun hannunta da ta haɗesu waje guda. Jinjina mashi kai ta yi alamar e zasu iya tafiya. Nuni ya yi mata da hannu a kan ta wuce su je. Ba musu ta yi gaba ya rufa mata baya cike da tausayi da kulawa. Kai tsaye harabar gidan zuka nufa, mai gardi guda ɗaya ne a wannan gidan, dan haka ya umarcesa da ya buɗe masu gate bari su je unguwa, dik tinanin mai gadin Leesharh matarsa ce, ya yi aure kenan, amma abin da ya bashi mamaki shi ne ya aka yi ogan nasu ya yi aure maganar bata fita ba? Sam bai ji zancen a hukumansu ba. Wani zuciya ce ta amsa mashi da ai auren sirri ya yi tun da ga shi ya ce ko su Bilal sun zo gateman ɗin ya ce masu babu kowa a gidan, dik yadda aka yi auren sirri aka yi, saboda bai taɓa sanyawa ransa Ramish zai kawo mace haka nan ya ajiye a gidansa ba, ya kullaceta ba tare da suna da aure ba, saboda kowa dai yasan Ramish ɗan wani family ne, ba zai yi wannan shashancin ba.
Sosai gateman ɗin nan yake ƙara shan mamaki a dik lokacin da ya kalli Leesharh, saboda yadda take chocolate color, abin yana bashi mamaki yadda aka yi Ramish ya aminta ya aureta, sai dai kuma sun yi matuƙar dacewa da juna sosai. Gate ya wangale masu, cikin natsuwa ya umarceta da ta shiga gaban motarsa, babu musu ta shiga ta zauna kanta a ƙasa bata san meyake yi mata ciwo ba ita da kanta.
Cikin motar ya shigo shi ma, a natse ya tada ita ya danna waje. Suna fita can ƙasa ƙasa cikin natsuwa ta ce. "Meyasa kake san fita kai kaɗai ba tare da tsaro ba bayan kasan aikin da ya kawoni gidanku a kanka? Kasan masu farautar rayuwar kusan sun fi masu kaunarka yawa". Tana damuwa sosai a dik lokacin da ya fita shi kaɗai, sai taga kamar ba zai dawo ba, kamar za'a kashe shi a hanya, dan tasan haɗarin masu nikaf. Yana driving a natse ya ce. "Kin damu da ni ne?"....... Shiru ta yi bata amsa mashi ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin.
"Aesh meyasa kike shiga damuwa a kan rayuwata?". Ya sake jefa mata tambaya. Dogon numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta amsa mashi da. "Babu komai, kawai dai dan nasan ana farautanka ne, and masu nemanka ɗin da alama sun fi yawa a kewaye da kai"......... "Ba gaskiya bane Aesh, dole kina da dalilin damuwa da rayuwata, meyasa zaki ɓoye mun?".......... Ya yi maganar dai'dai zai fita daga ainahin main gate na arear tsadaddiyar unguwar tasu ya sake ce mata. "Allah kuma yana kewaye da mu gabaɗaya daga ni har masu farautar rayuwar tawa".
Lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya, ai shikenan ya gama magana tin da ya ce Allah kuma babu wani sauran gyara ko ja in ja, dole a yi shiru. Securitys dake tsaran main gate ɗin nasu ne suka dakatar da motarsa, saboda basu san motar ba, sabuwa ce ba normal motocinsu da ya saba shiga unguwar da su ba, sannan basu ga face ɗinsa ba, sai suka dakatar da shi dan bincikarsa, sai da ya saukar da glass ɗin motar sannan suka gansa. Cikin girmamawa suka sara mashi haɗe da tambayar dama shi ne?. Kai ya jinjina masu tare da mayar da glass ɗin ya rufe, dama tinted ce, ya ja motarsa kawai suka cigaba da tafiya yana dannawa securitys ɗin horn alamar gaisuwa kenan.
Sai satar kallan juna ta kasan idanu suke yi dikkansu biyu, gabaɗayansu suna yunwar san kallan juna, saboda su kansu sun san sun yi kyau matuƙa, suna san bawa idanunsu abinci amma kamar suna tsoron haɗa idanu da juna.
"Aesh