Showing 24001 words to 27000 words out of 403653 words

Chapter 9 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

23

suka fara yi mashi na lokacin da mahaifinsa yake zama a saman wanna kujera, hango babansa yake yi yana sanye da wannan the most powerful CROWN OF INJUSTICE ɗin a kansa yana jawabi.

Ba zai taɓa manta lokacin da wani bawa ya yi laifi aka kawosa gaban sarki mahaifinsa ba, yana zaune a gaban Tv a room ɗinsa yana ganin yadda babansa yake wanzar da mulki, dan baban nasa yasan shi zai gajesa, dan haka sai ya sanya yana ganin dik yadda ake mulki ta Tv, yana kuma koya mashi a zahiri idan ya koma cikin gida, hakan yasa ya iya gudanar da komai cikin tsanaki.

Yana gani babansa ya sa aka ja wanna bawa, ya ce aje a tsaresa tsawon sati biyu babu abinci babu ruwan sha, sannan a tabbatar da sauran bayi dake tsare suna cin abinci a gaban idanun wannan bawa shi kuma yana ganinsu tsabar zalincinsa.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da yin magic walk ya isa gaban wanna kujerar. Ya ɗan ɗauki tsawon lokaci yana kallonta kafin cikin nutsuwa ya zauna a samanta.

Yana zama nan take fadar ta bada wani irin duhu wanda ya samu sanadiyyar ɗaukewar dik wasu fitillu dake ciki, sanna lokaci guda suka sake kawowa da hasken gaske fiye da yadda suke.

Komai na cikin fadar sai da ya girgiza, shinfiɗun dake ƙasar wajen ne kawai basu girgiza ba.

Dik ya ga hakan, amma sai ya yi kamar bai gani ba. Ya ɗan ɗauki lokaci a cikin fadar kafin ya fice izuwa room ɗinsa, shap ya fita harkar Sweetie, yanzu abin da yake a gabansa ya sha gaban tunanin mutum, dole ya mance da wata ƴar karamar kwaruwa Sweetie.

Ta in da ya saba magana da master Devil wato ta wani ɗakin duhu, in da ko ɗan yatsanka baka iya gani, nan ya nufa tare da kiran master Devil a kan ya zo.

Yana zuwa ba ɓata lokaci ya umarcesa da ya sanar da gabaɗaya mutanen birnin Black world a kan gobe zai shiga fada, zai koma kan kujerar mahaifinsa.

Sosai master ya yi mamakin jin wanna magana, amma bashi da ta cewa da ya wuce ya isar da abin da aka umarcesa kawai, dan haka sai ya karɓi umarni ya tafi.

Ita kuma Sweetie, room ɗin Ronnie ta koma ta takure waje guda, ko tsoron komawa cikin ɗakin bata yi ba.

===========🔥🔥🔥==========

ABUJA.


Kwance suke a cikin A&E cikin katafaren hospital mafi tsada a garin Abj.

Kowannensu yana kwance saman nasa bed ɗin, jaririn Khadija yana hannun ɗaya daga cikin securitys da suka kawosu hospital ɗin, an duba shi an yi mashi dik abin da ya dace.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





Kwance suke a cikin A&E cikin katafaren hospital mafi tsada a garin Abj.

Kowannensu yana kwance saman nasa bed ɗin, jaririn Khadija yana hannun ɗaya daga cikin securitys da suka kawosu hospital ɗin, an duba shi an yi mashi dik abin da ya dace.

Sai kuka yaron yake yi yana neman abin da zai sanya a cikinsa, yunwa sosai yake ji, ga uwarsa kuma bama a san a wani hali take ciki ba, ta mutu ne ko tana raye? Allah masani.

Ko motsawa babu wanda ya yi a cikinsu, kamar babu rai a jikinsu. Sai kai komo wanna security da ya rike yaron yake yi, yana ta safa da marwa ya kasa zama, sai haɗa uban gumi yake yi, ga babyn yaki ya yi shiru saboda yunwa.

Ya rasa ya zai yi da shi, ga shi shi ba iya reno ya yi ba, haka dai suke ta fama, idan ya gaji sai ya miƙawa wani daga cikin securitys ɗin, shi ma in ya gaji sai ya miƙawa wani.

A haka har gari ya waye, babu wanda ya nufosu domin ya taimaka masu ya sa yaron ya yi shiru, saboda kowa a cikin hospital ɗin tsoronsu yake ji, sun ga jiga jigan jami'ai ai dole su tsorata kowa ya kama kansa, so kwanan tsaye waɗan nan securitys suka yi. Ba halin su koma hotel da suka sauƙa, dan kafin tafiyar Ramish ya ce su kula da case ɗin har komai ya warware, ma'ana su kula da waɗan da aka buge har su sami lafiya.

Washegari da safe haka babyn nan ya rinƙa kuka, Allah sarki bawan Allah yunwa yake ji sosai. Waɗan nan securitys ɗin dikkansu har sai da suka ji sun tsani yara saboda kukansa, sai dai kuma wanna baby na Khadija fa ya shiga ransu ba kaɗan ba.

Sai misalin karfe 12 uncle Jahiz da wasu securitys ɗin suka nufo hospital ɗin, so yake su wuce Tunisia, shi ne ya biyo sahunsu ya ga shin zasu iya tafiya ne ko yaya?.

Har yanzu Jaish yana sume bai farka ba, Ramish ya ce su barshi ya farka da kansa.

Tun daga nesa da securitys ɗin nan suka hango uncle Jahiz suka yi saurin nufarsa, har lokacin baby bai yi shiru ba.

Tun da suka doso in da yake idanunsa na'a kan babyn hannunsu, mamaki yake yi a in da suka samo baby, dan shi a daren jiya bai ga wani baby ba.

Suna ƙarisawa wajen suka fara yi mashi sannu da zuwa haɗe da barka da safiya.

Bai iya amsa masu ba, idanunsa na'a kan babyn. Sai da ɗaya daga cikin securitys ɗin ya ce.
"Sir mu ƙarisa ko?"

Jinjina kai ya yi, sannan ya wuce gaba, har ya yi taku step biyu sai kuma ya juyo, ga mamakinsu sai suka ga ya miƙa hannu a kan su bashi babyn.

A hanzarce securityn ya miƙa mashi, basu taɓa ganinsa rike da yaro ba, bama su yi zaton ya iya riƙewa ba. Ga mamakinsu kuma sai suka ga ya iya riƙe jariri ɗanyan haihuwa da kyau.

Yana karɓar yaron kuma ya yi shiru kamar wanda ya ji ɗumin jikin uwarsa ko ubansa. A saman kaffaɗar kirjinsa da ya ji training saboda football ya ɗaura yaron, ya janyo towel da suke riƙe shu da shi dama ya ɗan lulluɓe shi da shi, ya zubawa babyn idanu sosai yana ta kallonsa, haka kawai ya ji kaunar yaron tana ratsa shi.

Gaba ya wuce securitys cike da mamaki suka rufa mashi baya, a maimakon ya kalli hanya sai gabaɗaya idanunsa suna a kan babyn har suka ƙarisa ɗakin da su Khadija suke kwance.

Dr ya buƙaci gani domin yasan me yake damunsu, saboda yana san yau zai wuce kasar Tunisia, ya ƙosa ya mayarwa da King Jaish ɗinsa su ga juna, rashin sanin ya fi dare duhu, bai san yanzu ne ma zasu shiga ainahin tashin hankalin na mutuwa da kuma ɓacewar gawar Gimbiya Zunaira ba, ko shi kansa Jaish ɗin sai ya ji a jikinsa.

Buƙatar su haɗu a office babban Dr ya yi, bai ja ko ya yi wata magana ba, yana rungume da baby kamar wani ɗansa ya bi Dr izuwa cikin office ɗinsa.

Su kuma securitys suna ta going up and down a cikin ɗakin. Ya ɗauki a kallah 30 mins suna tattaunawa da Dr kafin ya fito fuskar nan tasa babu annuri sam, kamar Dr ya gaya mashi wata magana mara daɗin ji.

Motarsa ya nufa ɗauke da baby, bayansa securitys uku daga cikin waɗan da ke gadinsu Khadija suka bi. A tunaninsu tun da zai tafi zai basu babyn, sai suka ga akasin haka, dan kuwa ya manne babyn nan da jikinsa kam, babu alamar zai iya ɓanɓarosa ya basu shi.

Yaronma da gulma ji kake yi tsit kamar wanda aka mukkawa nono uwa, har barci ya fara yi.

Magana ya yi da securitys ɗin na tsawon 10 mins, bai bawa kowa damar jin maganar da suka tattauna ba, daga karshe ya rufe masu zancen da yau zai wuce Tunisia.

Yana gama magana suka amsa umarninsa cikin girmamawa, suna ta jiran ya miƙa masu baby sai suka ga akasin haka, dan kuwa yana gama magana ya sanya aka rufe mashi kofar mota, basu yi gangancin cewa ya basu babyn ba, saboda sun san ba mancewa ya yi da shi a hannunsa ba, saboda dik maganganun da ya yi da su ma idanunsa a kan babyn, so yana sane da shi.

Wucewa suka yi suka koma cikin hospital ɗin, shi kuma ya kama hanyar tafiya izuwa hotel ɗin da suka sauƙa.

Yana sako kafarsa a cikin room ɗinsu ɗauke da babyn nan Jaish yana farkawa daga doguwar sumar da ya yi tin jiya da rana.

A hankali ya fara motsawa yana ɗan kwaɓe fuska, tsayuwa a tsakiyar ɗakin uncle Jahiz ya yi yana kallonsa.

Ganin da gaske farkawa yake son yi yasa ya zaga ta ɗayan gefen bed ɗin domin ya kwantar da babyn ya dawo wajen Jaish.

Sai dai ina, yana kwantar da babyn ya fara ihu wanda sanadiyar hakan yasa Jaish ya waro idanunsa waje babu shiri. A hanzarce uncle Jahiz ya ɗauki babyn ya rungume haɗe da fara ɗan jijjiga shi ya dawo ta kusa da Jaish da ya gama waro idanunsa waje yana bin saman p.o.p da kallo.

A hankali Jaish ya juyo da kallonsa a kan uncle Jahiz dake ta faman ɗan bubbuga jikin baby.

Kara zaro idanunsa waje ya yi, bai iya motsa bakinsa ba, dan ko'ina na jikinsa ya yi mashi nauyi, tongue ɗinsa ta yi mashi nauyin da ba zata iya yin magana ba, amma tabbas yana son yin magana, kuma ga dikkan alamu ya dawo cikin hankalinsa, kallon sanayya yake yi wa uncle Jahiz ba kallon bakunta ba.

"My son brk da tashi". Uncle Jahiz ya faɗa yana kallonsa shi ma.

Bai yi wani motsi ba, bai kuma yi wani yunkuri ba, shiru kamar wanda ruwa ta cinye.

"Kana san wani abin ne?". Uncle Jahiz ya sake jefa mashi tambaya.

Ido kawai ya kafe shi da shi babu ko kyaftawa. Ganin hakan yasa uncle Jahiz ya ɗan matsa daga in da yake tsaye dan ya ga da gaske Jaish ya farfaɗo ne ko dai ya sake suma idanunsa a buɗe ne, yaga irin kallon da yake yi mashi babu ko kyafawa tamkar in aka zare ran mutum yana kallon wani wajen.

Yana matsawa Jaish ya bishi da ido, wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da yin hamdala ga Allah, sannan ya matso ya zauna kusa da jaish ɗin.

"Akwai abin da kake so ne my son?".

Da kyar ya iya girgiza kai, a hankali ya fara ƙoƙarin motsa laɓɓansa dan ya yi magana. Idanun uncle Jahiz a kansa.

Rigasa uncle Jahiz ya yi da cewa. "Zaka yi wanka ne?".

A hankali ya gyaɗa kansa sama alamar e, dama abin da yake ƙoƙarin ya gayawa uncle ɗin nasa kenan, amma tongue ɗinsa taki motsawa.

Miƙewa tsaye uncle Jahiz ya yi ya nufi cikin toilet, babynsa dai yaki ya kwanta, rike da shi ya shiga cikin toilet ɗin.

Ga shi dai katafaren hotel mafi tsada suka kama, amma sai gabaɗaya uncle Jahiz ya raina hotel ɗin, toilet nasu ko na bedroom ɗin Sarina bai kai ba, sam basu ji daɗin sauƙa a wajen ba, amma da yake a kan hanya suke sai ba su wani tashi hankulansu ba.

Shiga ya yi ya haɗa mashi ruwan wanka mai ɗan ɗumi, sannan ya fito, a lokacin babyn nasa ya yi barci, cikin dabara ya kwantar da shi a saman bed ɗin, tamkar ya iya reno, sannan ya matso domin taimakawa Jaish ya miƙe tsaye.

Ga dikkan alamu Jaish ya dawo dai'dai sosai, dan tambayoyi uku ne yanzu a cikin ransa, ina Momma da dad? Ina Jawad? Ina Auta? Waɗan nan su ne kawai damuwarsa, ya yi kewarsu.

Taimaka mashi uncle Jahiz ya yi, da kyar ya iya tashi zaune, har yanzu yana ganin jiri jiri, sanna kansa yana ɗan sara mashi kaɗan kaɗan.

Hakika ya sha madarar mamaki na ganin irin yanayin kayan da yake a jikinsa, ko a mafarki bai taɓa ganin irin kayan ba, domin kaya ne na gargajiya wato shadda jampa da wando, shi dai yasan ba irin kayansu bane wannan, bai ma taɓa ganin irin kayan a zahiri ba sai dai idan a waya ya ci karo da videos na Hausawa, amma yau shi ne sanye da irin wannan kaya, to a ina ya samo su? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsa, kuma bai iya magana bare ya tambayi uncle Jahiz.

Taimaka mashi uncle ɗin nasa ya yi izuwa cikin toilet, ya fito ya bashi waje, ya dawo cikin ɗakin domin haɗa masu kayansu jirginsu ya kusa ɗagawa, dik abin da yake yi idanunsa na'a kan babyn nan na Khadija, da alamu ya kamu da kaunar yaron sosai sosai, kun san fa kyawawan koreans akwai madarar kyau ba kaɗan ba, dole su shi ga ran mutum ko baya so.

After some minutes. Like wow Jaish ya fito da kafafunsa ɗaure da towel a kunkuminsa, ya samu kwarin jiki na wanka da ya yi, a take har ya fara komawa yaron mommarsa, dama ya ɗan yi duhu zamansa a Yola.

Kayansa uncle Jahiz ya fitar three-piece suit ya miƙa mashi, sannan ya janyo zip ɗin echolac ɗin nasu ya rufeta.

Ba musu Jaish ya karɓi kayan domin ya shirya, uncle Jahiz ya fito waje dan ya sanar da securitys ɗinsu su juya kan motocin zasu wuce airport dan su koma ƙasar Tunisia yanzu.

Kafin ya dawo cikin ɗakin Jaish ya kammala shiryawa, like wow ya yi masifar kyau sosai, sai dai gashin kansa a jiƙe yake, bai busar da ita ba, ya zubawa babyn Khadija idanu yana mamakin a ina uncle ɗinsu ya samo wannan kyakkyawan yaro haka?.

"Jaish yaron ya yi maka kyau ko?". Uncle Jahiz da ya shigo a yanzu ne ya jefa mashi wanna tambaya.

To kun dai san halin yaron Mommarsa, ba sai na sake faɗa ba, dan haka yana jin uncle Jahiz amma bai amsa ba, ya yi banza da shi, sai ma ya wuce ya zauna a bakin bed tare da yin kasa da kai kamar mai nazarin wani abin, da alama kunyarsa da ya rasa a garin Jimeta yau ta dawo, halinsa dai sak ya dawo, an koma gidan jiya malam.

Da yake uncle Jahiz ya san halinsa sai bai wani damu dan bai amsa shi ba, ya ce. "Zamu iya tafiya a yanzu ko akwai wani abin da kake son yi?".

Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya iya gamana ba, alamar zasu iya tafiya kenan, maganar ce kawai ba zai yi ba, yana son tambayar uncle ɗin nasa a ina suke kuma me ya kawosu nan? Amma ina baya son yin magana yasa ya yi biris da zancen, da alama ma ya karo walaƙanci kaman ba shi ne ya gama shanyewa Mahnoor baki jiya ba, dik ya mance wanna!. Tashin sense, me kuke tunanin zai faru?.

Ɗaukan baby uncle Jahiz ya yi ya nufi waje, yana fita yasa securitys da su shigo su kwasan masu echolacs ɗinsu, zasu fara zuwa asibiti su mayar da babyn Khadija sannan su jandadawa Dr da ya kula da su kafin su tafi.

Haka kuwa aka yi, karfe ɗaya na rana dai'dai jirginsu ya ɗaga sai kasar Tunisia cikin amincin........ Safe journey our Jaish and uncle Jahiz.


=====KINGDOM OF POWER======

Zaune take a saman sofa a part ɗin Mammienta, daga ita sai wani figaggiyr simi, wani riga ne mai siririn hannu wanda ya tsaya mata a iya gwiwowinta, fararen kafafunta suna cikin wani katan bowl mai ɗauke da ruwa launin orange color, skin ɗin Sarina kullum cikin samun gyara yake, ta iya kula da shi matuƙa.

Wata kuyanga ce durkushe a saman gwiwowinta a gaban Sarina tana aikin wanke mata kafafunta dake cikin ruwan.

Mammie na zaune a saman sofa kusa da ita, Sarina tana riƙe da wasu hotuna tana kallo tana sakin ƙayatattcen murmushi, da alama yau suna cikin matsanancin farinciki daga ita har Mammie ɗin tata, sai hira suke zubawa suna fara'a.

Ita kuwa wannan kuyanga kanta a kasa tana aikinta cikin girmamawa, ga dikkan alamu tana bala'in tsoron Sarina.

Fanan ce ta shigo cikin ɗakin bakinta a ɗauke da sallama. Babu wanda ya amsa sallamar a cikinsu face kuyangar nan, ita ma a cikin zuciya ta amsa, saboda tana tsoron Sarina ta hukuntata, zasu ce ai ba ita aka yi wa sallamar ba.

Wata kuyanga ce ta sake shigowa baki ɗauke da ladabebben sallama.

Kusan a tare suka kariso ciki ita da Fanan, ita tana zuwa ta fara aikin shafawa Sarina kayan gyaran jiki a dik wasu sassa na jikinta, ita kuma Fanan saman sofa ta zauna tana haɗe rai kamar hadari.

"Lafiya kike wani kwaɓe fuska haka?". Cewar Sarina, ta yi maganar tana wani bin Fanan da kallo mai kama da harara.

"Ke Aunty Sarina baki san me yake faruwa ba ko?".

Ɗan taɓe baki ta yi kafin ta ce. "Me kuma yake faruwa?".

Mammie ma kasa kunne ta yi dan ta ji me yake faruwa.

Kara haɗe rai Fanan ta yi haɗe da alamar tausayawa a saman face ɗinta ta fara magana.
"Baki san Yah Jawad yana can kamar zai mutu saboda an aurawa Yah Rizwan Chuchu ba ko?".

Siririn tsaki ta ja. "To ni me ya dameni da su?".

"Kai Aunty Sarina kin san fa Yah Jawad ne yake son Chuchu ba Yah Rizwan ba, ke baki ji tausayinsu bane?".

Yamutse fuska ta yi tare da haɗe rai. "Su mutu ma dikkansu idan suka ga dama, ni

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login