Showing 333001 words to 336000 words out of 403653 words
biyu muke da su da zasu iya zama star, akwai Ronnie da King Lucian, amma bamu sani ba ko wani zai bayyana a gaba, sannan a masarautar Queen Zarina akwai Rishan ko kuma Ude, na gaba, a masarautar evil kingdom akwai Yusuf da Adam.🥱😅 Masarautarsu Bobo wannan kun rigada kun sani na faɗa maku cewa Bobo na daga cikin stars guda shiddan nan, a kingdom of power kuma waye kuka zaɓa a matsayin star? Wannan fa ba zaɓina bane, zaɓin ƴan special grp ne, ni tukun nan ban zaɓa maku stars ɗin ba, ku jirani bayan bikin Auta da Abdussalam akwai tada tarzoma, dan lallai kwakwalwarku zata yi caji fiye da tinaninku, muje zuwa cikin labari my people's)
----------------------------------------🔥🔥🔥
Kwanciya Bobo ya yi a saman sofa yana kallan Zash dake latsa waya, shi ma Smart Zash ɗin yake kallo, kamar suna zargin ya ɓoye masu wani abin ne. Shi kuwa hankalinsa gabaɗaya a kan wayarsa. Bobo zai yi magana phone ɗinsa ta gara ringing. Cikin natsuwa ya cirota daga aljihunsa yana ɗan lumshe Amber eyes ɗinsa kamar yana jin barci, lovely sis shi ne sunan dake yawo a saman screen ɗin, picking ya yi tare da matsar da wayar can gaba domin su ji daɗin ganin juna da kyau, video call ta kirasa. Wata kyakkyawar yarinya ce mai kama da shi sosai, idanunta starry Eyes ne masu bala'in kyau, kwayar idanunta Jade ne, suna wani walkiya kamar ruwan hawaye ne kwance a cikinsu, kuma haka suke, shi kuma Bobo phoenix Amber eyes yake da shi, shi ne ya banbanta shi da ita!, hancinta sharp nose take da shi, ga yawan eyebrows very thick dark brown.
Yana picking kuka ta saka mashi cikin shagwaɓa har sai da tasa Zash da Smart suka juyo da kallonsu a kan Bobo ɗin. Shiru ya ɗan zuba mata ido yana kallan yadda take kukan, kamar wacce aka sanya dole ta yi kuka. A tausashe sosai ya ce. "Pinkish lafiya kike kuka?".
Da sauri wata kyakkyawar yarinya kamanninsu ɗaya kamar tagwaye ta kwace wayar tare da faɗin. "Bro wai kuka take a kan kewarka". Ta faɗa tana kallansa. Juyar da kansa Smart ya yi ya cigaba da yin abin da yake yi, miƙa mashi hannu Zash ya yi a kan ya bashi wayar. Ba musu ya miƙa mashi yana kallansu da ido. "Beauty ina babyn take bata bari in faɗa mata yaushe Bobo zai dawo". Cewar Zash.
Baki beauty ta washe kafin ta ce. "Laaaa Yah Zash dama kuna tare? Shi ne baka nemanku ko? Kullun zamu kira Bro amma bama sanin kuna tare". Ta faɗa tana ɗan zaroviolet eyes ɗinta...... "Sorry aiki ne suka yi mun yawa, amma a mun afuwa, yanzu dai bawa wancan rigimammiyar da kullum idan ta kirasa sai ta yi mashi kuka".
Maman Sultan saboda ke da Aisha Jajeri na kara yawan page ɗin nan. Dan haɗani da Allah da kuka yi!!!.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
53
Miƙawa Pinkish wayar ta yi, har lokacin tana kuka hawaye bibbyu ta karɓa, idanunta a tsaitsaye, gashin idanun nata a tsaitsaye alamar bata da kunya ko kaɗan. Zuba mata idanu ya yi yana kallan yadda take kuka bilhakki da gaskiyarta, kai abin ma dariya ya so bashi, ta wani zage, taki ɗago kai ta kallesa, tana kallan ƙasa, a tinaninta Bobo ne, wai ita nan zata gwada mashi ranta a ɓace yake sosai dan ya yi maza ya dawo!. "Bana ce ki rinƙa rufe kanki kuma ki rinƙa sanya sutura masu rufe jiki ba?". Shi ne abin da Zash ya faɗa cikin sanyin murya.
Ai tana jin voice ɗinsa a miliyan ta ɗago da kanta, tana sauke kallanta a kansa bata san time da ta waro idanu waje ba, wani irin walwali Zash ya gani na idanunta kamar in an haska madubi a rana, tana ganin shi ne ta yi gaggawar miƙewa zaune, yau babu shagwaɓa sam sam, cike da mamaki ta ce. "Yah Zash dama kai ne? Amma ai kaman Yah Bobo na gani, ko dai numberka na kira ne dama? Kuma dai Yah Bobo na kira fa". A dibirbirce take maganar, tana wani kame kame. Zuba mata idanu ya yi yana kallan yadda take wani muzurai kamar maras gaskiya, tasan sun yi alkawarin zata rinƙa sanya ɗankwali da sutura ta kwarai, bata san shi ya karɓi wayar ba da ba zata taɓa yarda ya ganta a haka ba, kuma wlh tana rufe jikin nata dan cika alkawarin da ta ɗaukar mashi, yau ne kawai aka samu matsala bata rufe ba, tashinta daga barci kenan, yanzu tasan kome zata ce ba zai taɓa yarda tana rufe jikinta ba!.
"Yah Zash ina rufewa fa, kuma yau ɗin ne na manta ban rufe ba, ka tambayi Aunty beauty zata faɗa maka". A dibirbirce yanzu ma ta yi maganar, word ɗin suna sarke mata. Shiru dai bai amsa mata ba, hakan ya kara dibirbirtar da ita ya yi, tana san ya yi magana dan ta san ransa ya ɓaci ne ko bai ɓaci ba,.amma ya yi shiru. "To Yah Zash bari in ɗauko kayan in saka ka ji?". Ta faɗa tana kallan cikin idonsa zat tana jiran me zai ce, ko kunyarsa bata ji ba. Kuma fa zata kai irin 15 years haka, amma babu ko kunya, ga shi kayan barcin jikinta irin riga mai ɗan siririn hannun nan ne, ga cup na breast, ya fitar da gabaɗaya shatin nipples ɗinta, ga tudun breast ɗin nata ma dikka a waje.
"Yah Zash ka yi magana mana". Tamkar zata sanya kuka ta yi maganar. Siririn harara ya bita da shi kafin ya ce. "Sai da kika ganni ɗin ne zaki ce bari ki je ki saka kaya? Ya muka yi dake time da na zo gida last?"...... A word ɗinsa ta fahimci bai ji haushi ba, ransa bai ɓaci ba kenan, dan haka sai ta saka mashi shagwaɓa, tana turo baki ta ce. "Da gaske Yah Zash ina saka kaya manya, wai baka ga yanzu na tashi daga barci bane?". Harara ya sake binta da shi kafin ya buɗi baki da nufin magana sallamar Auta ta karaɗe kunnuwansu.
Gabaɗaya kai kallansu suka yi a kansu. Ai Smart bai san time da ya zaro idanu yana kallan Pretty ba, ta yi masifar kyau cikin English wears ɗin nan, ya ilahi kowa ya ganta sai ya sake waigawa, Auta ta kasheta da haɗuwa, madarar kyanta ya kara bayyana. A ransa ya ce kaga yarinya kamar ita ta yi kanta, ƴar karama sai shegen kyau da shegen miskilanci.
Pretty ba hankali, ko sannu bata cewa su Bobo ba, ta wuce ta yi zamanta saman sofa, ko kallan in da suke ma bata yi ba, kamar bata san da halittarsu a wajen ba. Ita kuwa Auta cike da zumuɗi ta ƙarisa wajensu, wajen Zash ta fara nufa tana faɗin. "Yah Zash tin da nazo nike tambayar Yah Omerish ina kake? Sai ya ce mun ka tafi Dubai".
Hannu ya miƙa mata ta bashi nata tana murmushi, zaunar da ita kusa da shi ya yi kafin ya amsa mata da. "E jiya na dawo, na yi kewarki sosai my sweetheart"..... "Nima na yi kewarka sosai, kullum sai na tinaka". A shagwaɓe ta faɗa. Cike da zolaya ya ce. "Da gaske anyi kewata ɗin nan kuwa?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e da gaske. Wani irin kallo ya wurga mata mai kama da hararar wasa yana faɗin. "To meyasa ba'a kirani ba tin da an yi kewata?". Zata yi magana ta ji murya cikin harsh voice ance. "Yah Zash wacece kuma wannan?!". Bawan Allah shi ya ɗan manta ma waya yake yi!.
Dawo da kallonsa a kan wayar ya yi kafin ya amsa masu da. "She's my sweetheart". Ya faɗa yana ɗan riko shoulder ɗinta, ya matsar da ita jikinsa kafin ya ɗan sauko da wayar dan su samu damar ganinta sosai. Cool murmushi ta sakarwa Pinkish kafin ta ce. "Sannunki".
Ɗaure fuska sosai Pinkish ta yi, sai ma da ta ɓalla mata harara kafin ta amsa da. "Yauwa". Saura kaɗan su saka Zash murmushi, Pinkish bata da hali mai kyau, ita sam sam bata san mutane, ji yadda ta haɗe rai fa, amma fa a ganin Zash ne bata san mutane shiyasa ta ɗaure fuska dan taga Auta, ku fa a ganinku me yasa ta yi hakan?.
"Yah Zash she looks like Yah Bobo". Cewar Auta kenan. Jinjina mata kai ya yi kafin ya sanar da ita kannen Bobo ne, kara faɗaɗa murmushinta ta yi baiwar Allah, sannan ta kara ce masu sannu. Fuska a ɗaure tamau ta ce. "Wacece ke kuma?".
Tana ta fara'a ta amsa da. "Sister Yah Omerish ce ni". Bata ƙarisa maganar ba beauty ta leƙo da kanta ta cikin wayar, wani irin haɗaɗɗen murmushi ta sakarwa Auta kafin ta ce. "Wow they looks alikes, you're so cute, pretty and beauty like him, i like you!".
Sosai Auta ta ji daɗin kalamanta, tana murmushi sosai ta ce. "Same, I like more, and you're very beauty more than me". Girgiza kai ta ɗan yi. "Not more than your, lest than your okey?"........ Zata yi magana harsh voice ɗin baby ya katsesu da cewa. "Then so what if she's beauty? Am also beauty more than........".
Zash ne ya katse mata maganar bata karisa ba ta hanyar zaro almond eyes ɗinsa, ya yi mamakin jin yadda take faɗa, dik da yasan dama mafaɗaciya ce kamar mom ɗinsu, ba'a taɓata ta yi shiru, to amma me Auta ta yi mata da zata fara faɗa da ita kawai ba gaira babu dalili?.
"Pinkish are you hard what you're saying?". Cewar Zash. Shi dai Smart ya koma kan aikin da yake yi, yana yi yana satar kallan Pretty da ta kwanta tana kallan sama kamar mai motsi a kai, ta yi shiru kamar dai bata tare da su haka. While shi kuma Bobo hankalinsa na'a kan tiger dake kwance a can kusa da pool dake wajen. Pretty bata san da tiger a wajen ba.
Ganin Pinkish bata nuna mata so ba yasa ta tashi daga wajen, dan bata san mutum ya nuna mata kiyayya. Kusa da Smart ta zauna hankalinta a kan Bobo ta ce. "Yah Bobo sannu da zuwa". Hararar ya wurga mata kafin ya ce. "Sai yanzu kika ganni?". "Sorry Yah Bobo waya nike yi fa". Dawo da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "A'a kin dai'na san Yah Bobo yanzu, Yah Zash ya fini"....... "Yah Omerish ka faɗawa Yah Bobo ban fi san kowa ba, dikkanku ina sanku kamar rai'na". Ta faɗa kamar zata yi kuka.
Hannunsa Smart yasa ya janyota jikinsa, can ƙasa cikin sigar rarrashi ya ce. "Kyale Bobo, yana cikin damuwa ne zai sauke mana a kanki, bashi hai"..... Take ta ji tausayin Bobo ya mamaye zuciyarta, cike da alhini ta ce. "Yah Omerish meyasa me shi?". "Matsala ce ta gida shi da mom".
Kamar zata yi kuka ta dawo da kallonta a kansa. "Sorry Yah Bobo ka ji? Believe Allah Everything it will come to and end". Jinjina kai ya yi kafin ya ce. "In Sha Allah our sweetheart"..... Shi kuwa Zash ya zage sai bawa Pinkish hakuri yake yi, ita kuma ta kafe a kan bafa zata hakura ba, dan ranta ya ɓaci, daga karshe ma kashe wayar ta yi tana kuka, ya rasa me ya yi mata ya bakanta mata rai har haka. Pinkish manyan ƙasa!.
"Yah Omerish mu tafi to". Cewar Auta. "No my sweetheart, baki ga su Bobo sun zo ba, mun fasa fita, sai gobe". Take fuskarta ta nuna rashin jin daɗin hakan, ta so yau tun da sun samu dama su fita, amma kash hakan ba zai yiwu ba, miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi barin wajen. Har cikin ransa ya ji cewan bata ji daɗi ba, amma ya yi kamar bai gane ba, hannun Pretty ta riƙo tare da cewa. "Pretty zomu je bedroom ɗinmu mu kwanta mu yi hira". A miliyan Pretty ta ɗago da kanta. "Fitar fa?". Ta jefa mata tambayar tana kallanta, yarinyar nan tamkar bata san da halittar mutane a wajen ba, wlh da a gidan sarauta cikin gata Pretty ta tashi za'ayi bala'i, wato dik miskilanci mutum sai ya sarara mata, wannan ma ba wayewa ne da ita ba, da yake dai a jininsu abin yake ne sai gata tana dakonsa.
"Yah Omerish ya ce ba zamu fita yau ba sai dai gobe". Auta ta bata amsa tamkar zata yi kuka. Girgiza kai Pretty ta fara yi kafin ta ce. "A'a ni ba zan yarda da hakan ba, tin da ya ce zai kaimu yawo to sai ya kaimu!". Cike da gadara ta yi maganar, sak dai yadda shi yake magana da gadara kamar kowa mallakinsa ne a karkashinsa yake, ashe ba laifinsa bane, sarauta ke ɗawainiya da shi, to yau dai ya samu dai'dai da shi.........😅
Da mamaki gabaɗayayansu suka ɗago da kallonsu a kanta, sai a yanzu Zash ya san da ita a wajen, shi ma Bobo dik da ta zo ta wucesa bai ɗago ya kalleta ba, hankalinsa a can duniyar tinani, sai a yanzu ya ganta. Shi kan Smart wlh burgesa take yi, sai ma idan tana magana, a yanayin yadda yake kallan abin nata kamar yarinya irin ce mai cike da class da ji da kanta, zaku iya zama da Pretty tsawon wuni a waje guda word ɗaya bai haɗaku ba, in baka mata magana bata yi wa mutum, idan ma ka yi mata ɗin ma sai ta yi niyya zata amsa, kamar wata mai aljanu.
A ɗan rikice Auta ta ce. "Pretty Yah Omerish ne fa, meyasa zaki ce haka? Shin ba yayanki bane shi?". Ɗan turo baki ta yi, kuma dik maganar da take yi kallanta a ƙasa, bata ɗago kai ba bare ta haɗa ido da kowa. "To shi Yah Omerish ɗin ba shi ya yi mana alkawarin zai kai mu ya wo ba? Waye ya ce mashi ana saɓa alkawari? Ko bashi da ilimi ne? Kuma shi ɗin waye ne shi da ba za'a faɗa mashi gaskiya ba? Dole ya cika alkawari ya fita da mu!". Babbar magana, mai ilimi tana magana, wai Pretty ce zata cewa wani bai da ilimi, ita da lokacin da mamansu ke karantar da su tana karkashin korama tana shakar iska mai ni'ima, Sweetie na kwasan ilimi, amma da ɗan guntun karatunta da bai wuce primary 3 ɗin bane zata ce wai wani bai da ilimi, kai Pretty ƴar duniya ce wlh.
Zash da Bobo kallan Smart suka yi, har suna haɗa baki wajen tambayarsa wacece Pretty. Mayar da kansa a kan laptop ɗinsa ya yi, bashi da amsar da zai basu, dan shi ma bai san wacece ita ba. A karo na biyu suka sake tambayarsa, kawai sai ya ce masu sistersa ce. Da mamaki suka sake binta da kallo, kwata kwata bata yi kala da ƴan gidansu ba, kalarta daban, ko iya kyakkyawan eyesball ɗinta kawai ya isa ya fahimtar da mutane ba zubin larabawa gareta ba, amma sai basu yi wani dogon tinani a kan komai ba, suka yi shiru kawai.
Auta na kokarin yi mata magana ta wuce izuwa in da Smart yake zaune, ƴar rainin wayo bata ganin mutane ashe tasan in da kowa yake zaune. A kusa da shi ta tsaya, tana zuwa ta riko hannunsa a cikin nata, cikin shagwaɓar da take yi wa Kamran, without respect ta ce. "Ka tashi ka kaimu yawo ka cika alkawarinka!". Kamar Momma ke bashi umarni, ba abin ya maketa ta mutum mashi a wajen ya yi kisan kai ba............ Shi yanzu ya fara yi mata kallan mai matsala a ƙwaƙwalwa, har ya fara tinanin yin scanning na brain ɗinta.
Tsawa Auta ta daka mata a kan bata da hankali ne? Ita bata san babba bane?. Kuka ta saka tare da faɗawa jikinsa, ita ba ruwanta da wani babba, bata ma nemi sanin ko waye shi ba ato, kawai tin da ya yi alkawari bai isa ya karya ba, dole ya cika mata. Babbar magana, ai rasa abin faɗe ya yi, su Zash sun tsaresa da ido kawai suna binsu da kallon mamaki, yau sun ga wadda Smart yake ragawa,.abin wlh ya yi mugu mugun basu mamaki.
Shi kuwa banza da ita ya yi, kamar bai san tana yi ba, ta rinƙa kuka kamar wadda aka saukarwa da wahayin yinsa, Auta dai sake baki ta yi ta rasa abin faɗe. Cigaba da aikinsa ya yi yana tinanin tafiyarsu kingdom of power jibi da za su yi, zasu je su amsa kiran King. Ya yi nisa cikin tinanin da yake yi sai ji ya yi tamkar wanda aka tsayarwa da gabaɗaya jinin jikinsa, cak ya ji kowani kofa na jininsa ya dakata da yin aiki, lokaci guda ya jisa a duniyar mercury. Slowly ya dawo da kallonsa a kanta. Tana kuka tana yi mashi wasa da cibiyarsa kamar ya sakata, sam bai ji lokacin da ta ɗaga mashi riga ba, sai jin ɗan yatsarta ya yi a cikin cibiyarsa.
Ai wani irin shocked da ya yi sai da yasa su Zash hankalinsu ya dawo kansa, amma basu fahimci dalilin shocked ɗin ba, saboda basu iya ganin me Pretty ɗin take mashi ba, dik da haka sai suka tambayi dalili. Kai kawai ya iya girgiza masu, Pretty na nema kiran ruwa, dama yaya, su da suka yi gadan abin, lallaɓa rayuwarsa yake yi amma yarinyar nan zata jefa shi cikin bala'i. Da kyar ya iya riƙo hannunta a cikin nasa, a take ya ɗaure fuska wai irin ta zaci ba