Showing 186001 words to 189000 words out of 403653 words

Chapter 63 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

140

zai iya fahimtar ita ɗin macece mai kama kanta, wacce ta san mutumcin kanta, nitsastsiya mai sanin yakamata, dan ko a cikin barcinta ta haɗe jikinta waje guda ta yadda bata ba da kofar da komai ƙanƙantar tsiraicinta zai iya bayya idan barci ya yi nisa ba, ta haɗe kafafunta waje guda ta kuma dungule hannayenta ta turasu a tsakanin cinyoyinta ta kusa da gwiwa, idan ka ganta zaka yi zaton ta takure kanta dayawa, amma ba haka bane, saboda ne da irin kwanciyar ya ja hakan, ga kuma irin tarbiyar da ta samu tun kan kanwar shaiɗan Hauwa ta shiga rayuwarsu ta ruguje komai.

Zubawa face ɗinta idanu ya yi sosai yana kare mata kallo, hankalinsa dikka a kan lips ɗinta, Allah ya gani zuciyansa ya biya da wannan black beautyn, Zee dai a Nigeria fara ce tas, amma a gabansu baƙa ce gaskiya, shiyasa ya kirata da sunan black beauty.

Hannunsa na kerya ya kai ya ɗan janye bargon da ta lulluɓa ƙasa. Kayan barcin Aneesa riga da wando ne a jikinta, kasancewar bata sanya bra ba sai tula tulanta suna tsole idanun mai kallo. Shi dai da alama kirjinta yana ɗaya daga cikin abin da ya ja ra'ayinsa a kanta. Dawo hannunsa kusa da face ɗinta ya yi dan ya taɓa lallausan kumatunta, sai dai bai kai ga yin hakan ba ta fara motsi tana san farkawa, saboda ta ji alamar kamar ambuɗe mata jiki. Ya janye mata bargo.

Aneesa kuwa ta baje abinta sai zuba barci take yi, ta rungumi teddy a kirjinta a cewarta Yah Rizwan ta runguma,........... Kai Hasbunallahu wani'imal wakil, wlh jikokin Akka sai shirin Allah, ba matan ba ba mazan ba, da alama dik sun yi gadon jaraba, kai kun ji Aneesa da wani tsiya, wai Yah Rizwan ta runguma, kai jama'a ana abu a kingdom of power.

A hanzarce ya miƙe tsaye, ganin sosai ta fara motsawa zata farka yasa ya yi saurin juyawa zai fice daga ɗakin. Sai dai bai kai ga fita ba ta waro idanunta waje kai tsaye sai a kan bayansa yana tafiya. A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar bed ɗin tana kallansa. Bata gane wanene bane, saboda ya bata baya, sai dai zuciyarta ya zargan mata cewa shi ne, saboda shi ne kaɗai a gidan wanda gashin kansa bai yi dark black ba, ya ɗan yi brown brown haka.

A hanzarce ta dawo da kallonta a kan jikinta dan ta tabbatar da ba wani abin aka yi mata ba!. Ganin babu komai yasa ta yi saurin saukowa kasan bed ɗin, ashe gara da ta ce da Aneesa su rinƙa barin wutar ɗakin a kunne dan suga mai shigowa, to ga shi ya yi amfani.

Bayansa ta bi da sauri dan ta ga wanenen? Tana da karfin hali ita ma, a ranta take rayawa lallai lokacin barinsu gidan nan ya yi tun da dai maza ne suke shigo masu ɗaki da daddare.

Da sauri ta fito daga bedroom ɗin nasu ta nufi bin bayansa. Sai dai ko da ta fito bata gansa ba, babu shi babu alamarsa, ɗan waige waige ta tsaya yi a wajen, kamar dai a mafarki ta hango inuwar mutum ta wajen wannan kofa da Guyson ya bi ranar ya je wajen dinner Jawad, kun tuna ranar da ya haɗu da aljanar nan? Kun san ai dama ta part ɗin mama ne kofar yake ko idan baku manta ba? To ita kuma Zee kunga a part ɗin take tare da Aneesa, so tana fitowa sai taga inuwar mutum kamar dai yadda aka yi wa guyson.

Ɗan tsorata ta yi, sai kuma ta tina abin da mamarsu take yawan faɗa masu a kan kada su ji tsoron kowa face Allah da ya haliccesu. Tuna hakan yasa ta ce bari ta je ta leƙa kila inuwar wanda ya shigo masu ɗaki ne, yau so take taga wanenen?. Ba tare da tina abin da zata iya gani ba ta nufi kofar, tana taɓa kofar kuma sai ta jita a buɗe.

Wai nace ba, meyasa wannan kofar a dik lokacin da wannan inuwa ta gifta kofar yake buɗe kansa da kansa ne? Kun san fa ba'a buɗe wannan kofa kwata kwata, ko da rana a rufe yake, so meyasa in dai inuwa ta gifta kofar zai buɗe? Muje dai zuwa.

Jan kofar a hankali Zee ta yi da nufin ta fita waje, daga bayanta ta ji muryarsa ya ce. "Ina zaki je a daren nan, sannan kofar nan ai ba'a buɗeta". A hanzarce ta juyo da kallonta a kansa, uncle Jahiz ɗin ne dai, yana tsaye yana kallanta.

Ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin juyo da jikinta a garesa dan ta bashi amsa ta wuce ciki, unexpext idanunta suka kallo mata fuskar mace mai kama da aljana ga wasu kahohhuna dogaye a hancinta har zuwa bakinta, jini na bin jikin kahon, sannan idanunta manya manyan jajir kamar wuta, gwanin ban tsoro.

Ai Zee bata san time ɗin da ta zunduma wani irin ihu mai doɗe kunne ba, kwata kwata bama ta san ya akayi ba sai ganin kanta ta yi a kirjin uncle Jahiz, shi kuma fa babu abin da ya gani, ita kaɗai aka tsorata, kada ku manta uncle Jahiz fa na Aliyah ce, Aliyah kanwar Mammie shugaban mashirikai ita mammie ta ce zata auresa in baku manta ba, to ni dai ina ga kila saboda uncle Jahiz ya nuna ra'ayinsa a kan Zee yasa Mammie ta fara ɗaukar mataki, amma ku ya kuke gani?.

Kankame shi ta yi tana ihu. Gudun kada ta tashi family yasa uncle Jahiz ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa yana kai kallansa a wajen da ta baro take ihun. Shi dai bai ga komai ba face kofa kawai, to meyasakata ihu har haka? Ya jefawa kansa tambaya.

Motsi ya ji a bayansu ta wajen part ɗin momma, hakan yasa ya yi saurin janta baya dan ma kada wani ya gansu, ganin kamar razana sosai ta yi yasa ya fara tofa mata addu'oi har lokacin bai zame hannunsa daga bakinta ba. Ita kuma tana ƙanƙame da shi.

Addu'oin da yake tofa mata ne yasa ta fara samun nitsuwa hankalinta yana dawowa jikinta, tsoratar da ta yi yasa har ta fita a hayyacinta.

Ganin ta ɗan fara nitsuwa yasa ya jata suka karisa shiga bedroom ɗin Aneesa, a saman sofa ya zaunar da ita tare da zame hannunsa daga bakinta, ya kurawa face ɗinta idanu yana kallanta. Ta ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ta iya dawowa dai'dai, hankali a tashe take kallansa, sai kuma ta kasa yin magana.

Cikin nitsuwa ya tambayeta dalilin ihun da ta yi, ta kasa bashi amsa, tamkar an ɗaure mata tongue ɗinta, ganin hakan yasa ya ce ta je ta kwanta da safe zasu yi magana kuma kada ta sake fitowa. Ba musu ta miƙe ta isa bakin bed ɗinsu, hayewa ta yi ta kwanta har wa lokacin tongue ɗinta a ɗaure ta kasa iya yin magana.

Miƙewa ya yi ya koma kusa da ita, addu'oi sosai ya tofa mata, tin tana satar kallan face ɗinsa har ta lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya alamar hankalinta ya kwanta. Jin saukar ajiyar zuciyarta yasa ya fahimci ta samu natsuwa, bargo ya ja ya lulluɓeta tare da karisawa gaban switch ya kashe masu wutar, sannan ya fita ya janyo kofar ya rufe masu.

Dik wannan bidiri da ake yi Aneesa tana can duniyar mafarkin ita da Yah Rizwan, bata farka ba, amma abin mamaki kuma zata iya wayan gari ta bada labarin abin da ya faru daren jiya ɗin, anya Aneesa mutum ce kuwa? Ta fara bani tsoro sosai gaskiya, amma mu je zuwa, ita ma labari zai biyo ta kanta ne, lokacin na nan tafe.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A tare Jawad and Jaish suka jera har izuwa takiyar main parlour, a nan ne suka rungumi juna tare da yi wa juna good night, a daidai lokacin Chuchu da Mahnoor suka iso wajen.

Wucewa gaba Jaish ya yi ya nufi part ɗinsa ba tare da ya kalli in da Mahnoor take ba, shi kuma Jawad ya rike hannun Chuchu yana janyota jikinsa suka wuce nasu part ɗin suna yi wa Mahnoor good night.

Shiru ta ɗan tsaya a wajen tana tinanin yadda zata kwana da shi ɗaki ɗaya yau. Ganin tsayuwa ba zai haifar mata da mafita bane yasa a nitse ta taka ta bi bayansa.

Tana sako kafafunta a cikin parlonsa ta ji kamshi na daban ba kamar wanda ta ji da rana ba, kenan ancanza mashi perfume, shakar kamshin ta yi ta lumshe idanunta, cikin natsuwa ta ƙarisa shiga cikin parlourn.

Mama Haulat ta isko zaune saman sofa tana dudduba wasu sexy sleeping dress dake cikin kwalayensu. Cikin girmamawa ta ce. "Barka da dare mama Haulat".

Fuska ɗauke da fara'a mama Haulat ta amsa da. "Yauwa barka dai amarya kuma sarauniyarmu, zo nan ki ɗauki kayanki ki wuce ɗakin mijinki". Ɗan siririn murmushi ta saki kafin ta karisa kusa da mama Haulat, sannan ta ce. "Mama kaya kuma?".

Jinjina kai ta yi tare da amsa mata. "E kaya, momma ce ta ce abaki wannan kayan su zaki saka, kuma ta ce karfe tara kije ki ɗaukawa mijin naki cappuccino". Kasa da kai Mahnoor ta yi alamar ta ji kunya ance mijinta. Miƙo mata kayan mama Haulat ta yi ta karɓa tana wani sunkuyar da kanta ƙasa.

"Kada ki nuna jin kunya a wannan ɓangaren, domin kunya bata da wani amfani, ki tsaya tsayin daka ki faranta ran mijinki shi ne dai'dai, ki sani yanzu kin shiga layin da Mala'iku zasu yi rubutu a kanki a kan aure, so yana da kyau ki kula sosai, ki sanya shi farinciki domin ki samu rahamar Allah, na ɗaukeki ne tamkar yata, dan haka a matsayina na uwa shawarata a gareki shi ne ki ajiye wannan kunya a gefe"

Ƙasa ta yi da kanta wajen amsa cewa ta gode sosai kuma In Sha Allah zata yi amfani da shawarinsu ita da momma, fatan alkhairi da fatan nasara mama Haulat ta yi mata sannan ta ɗaura da cewa sai da safe.

Bedroom ɗin ta nufa cikin natsuwa. Baki ɗauke da sallama ta shiga ciki, babu kowa a ɗakin sai tashin daddaɗar kamshi da yake. Shiru ta tsaya tana bin ko'ina da kallo, tinani ta shiga yi a kan ina yake ne? Ko dai bai shigo ɗakin ba ne?. Ta kai almost 5 mins a ɗaya a wajen kafin ta iya fahimtar yana toilet yana wanka ne.

A hankali ta taka ta ƙarisa cikin ɗakin, zata zauna a ƙasa sai ta tuna kaman momma da mama Haulat, momma ta ce ta mayar da gadansa wajen zamanta kamar yadda zata mayar da jikinsa gadanta. Tina hakan yasa ta ƙarisa bakin bed ɗin nasa a hankali ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

Shiru ta yi tana bin ɗakin da kallo tana ɗan shafa kwalin kayan dake ƙasar hannunta, bata ga lokacin da ya fito daga wanka ya shiga dressing room ba, amma shi ya ganta a cikin dakin, sai ya kawar da kansa kamar bai ganta ba.

After some minutes ya fito sanye da kayan barcisa masu kyau da tsada, kao tsaye bed ɗinsa ya nufo, sai da ya matso kusa da ita ne ta iya gane ya fito, a cikin hanzarce ta ɗago da kallanta a kansa. Unexpectly suka yio four eyes, domin kuwa shi ma ita yake kallah yana jin kamar ya je ya ɗauki lallen hannunta hoto.

Kwayar idanunsa ne suka rikitar da ita, a ruɗe ta miƙe daga saman bed ɗin, tsabar ta tsorata har ta ce mashi ina kwana ba tare da ta sam t faɗa ba. Kawar da kallansa daga kanta ya yi ya haye saman bed ɗinsa ba tare da ya amsa mata ba. Lokacin guda ta ji jikinta ya mutu na banza da ita da ya yi, sai ya tsaya kamar wata doluwa.

Gabaɗaya ta ji ta karaya da wannan al'amari, sai dai lokaci guda zancen momma ya dawo ranta a in da take ce mata kada ta karaya, ta jajirce kome zai yi mata, tina hanan yasa ta ji kwarin gwiwa ya dawo mata, a hankali ta fara takawa ta nufi toilet ɗinsa dan ta yi wanka.

Ta wutsiyar idanunsa ya bita da kallo, yarasa me yake damunsa, in dai ya ganta sai ya ji yana sha'awar ya cigaba da kallonta, ni kam nace saboda ita ɗin mallakinka ce ba tun yau ba, shiyasa kake kasa control na kanka a dik time da ka ganta. Sam bai yi ƙoƙarin hanata shiga toilet ɗinsa ba, saboda marainiya ce, kuma momma ta ce kada ya cutar da ita, dan tana kaunarta, ko dan momma ba zai tsawata mata ba.......... Ni kuwa nace anya Jaish yana da gaskiya kuwa? Wai ko dan momma, munafiki ko dai dan ya ga madarar kyau ba, bani dan momma kawai dai tin ganin da ya yi mata ɗazun ne zuciyarsa ta buga da sunanta, shi ne zai fake da momma, wlh maza aji tsoron Allah, amma dai ba koma zaka zo hannun ne, a lokacin ba wanda zai matse bakinka, da kanka zaka faɗi dan me kake tausaya mata, dan gulma da iskanci irin na jikokin Akka har da wani saboda ita marainiya ce, oh ni Princess Teema, mun dai san kun yi gadan abin, dan haka ba wata marainiya, ka dai ga kaya hankali ya tashi.......😅

(Ba ruwana bani na faɗa ba🥱 jarababbu kawai 🏃)

Wayarsa ya laluɓo ya hau latsawa dan ya rage lokacin kafin time na shan cappuccinon ɗinsa ya yi. Ita kuwa wanka a tsara, sannan ta ɗauki towel ɗinsa ta goge jikinta, kayan da ta ajiye a wajen wash hand base ta ɗauko, fito da su daga cikin kwalin ta yi. Cikin natsuwa ta ware kayan. Nan fa ta zaro idanu tana kallansu, wasu irin shegun sexy sleeping dress ne wanda gabaɗaya net ne jikinsu, riga mai siririyar hannu ce zuwa gwiwa da ƴar pant ɗinta wanda ita ma net ce.

Shiru ta yi tana tinanin yadda zata yi da wannan kaya. Wani zuciya ne ya ce mata wai shin ba mijinki zaki sakawa bane? Ko dai kin daina san shi ne?. A fili ta girgiza kai haɗe da cewa a'a bata daina san shi ba.

Shi kuwa yana ta aikin latsa wayarsa idanunsa suna yi mashi gizo ma lallenta. Kamar ance mashi ya ɗago idanu unexpect ya sauke kakansa a kanta, ta fito daga toilet cikin ɗakin wannan shiga, sai wani kame kame take yi ta kasa sake jikinta, ta takure waje guda tana tafi kamar wadda aka yi wa kaciya. Hannunta yana rike da kayan da ta cire a cikin.

Ya ilahi ya lilliahi, ai Jaish bai san time da ya waro idanunta waje ba, abar tasu ta motsa, sai kuma ko me ya tina? A hanzarce ya kawar da kallansa daga kanta kamar wani maras gaskiya.

Ita kuwa ƙarisowa ta yi kusa da bed ɗin, kirjinta sai dukan uku uku take yi, kamar wata ɓarauniya haka ta lallaɓa ta zauna a gefen bed ɗinsa. Ai a miliyan ya dawo da kallonsa a kanta, razana ta yi ganin yadda ya watso mata kallo, har kamar zata miƙe ta fasa zama, sai kuma ta daure ta yi zamanta tana tinanin me zai iya ce mata.

Nan take ya ji tongue ɗinsa tamkar an ɗaureta, ya kasa yin magana, sai kawai ya kawar da kallonsa daga kanta. Ganin hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya, cikin nitsuwa ta gyara ta kwanta a wajen tare da jan bargo ta rufe jikinta, sai kuma ta juyo tana fuskantar face ɗinsa, dan tana san ganinsa sosai, bata gajiya da kallonsa.

My people's me kuke tinanin zai faru, da alama fa abar ta motsawa Jaish, to su dai suka sani, ni bari in leƙa wani ɓangaren ma dawo anjuma muga me zai faru, zai koreta ne ko dai zai yarda su kwana a tare?.

🔥🔥🔥🔥BABYN BABY.🔥🔥🔥🔥

Ɗaure take da white towel mai shegen laushi da kyau a kirjinta, daga wanka ta fito, skin ɗinta sai glowing yake ta yi, tana sanye da hular wanka a kanta.

Gaban mirror ɗinta ta tsaya tana ɗan turo baki, santala santalan cinyoyintan nan sai sheki suke yi suna wani glowing, kamar dai jikin Sarina tamu ta kingdom of power, kun san Sarina da shegen san gyaran jiki, to haka jikin baby ma yake.

Wayarta dake saman mirror drawer ta ɗauko, kamar zata yi kuka ta shiga contacts ɗinta. Number baby ta nemo, kai tsaye ta danna mashi kira. Wayar ta yi ringing har ta katse bai ɗaga ba. Juyawa ta yi tana kallan kanta a madubin, murya a shagwaɓe ta ce. "Baby, where did you disappear to today? You promised to come at night and comfort me, but now it's already 9 PM, and you haven’t shown up. I’ve been calling your phone even before I took a bath, but you refused to answer. Now tell me, how do you expect me to deal with missing you when you are my heart?". Tana magana tana tura baki.

Shiru ta ɗan yi tana kallan kanta a mirror, ita kanta tasan kyakkyawa ce ita. Kamar walkiya lokaci guda unexpect taga wutar ɗakinta ya ɗauke gabaɗaya, lokaci guda duhu ya mamaye ko'ina, wani irin tsorata ta yi, nan take ta fashe da kuka tana kiran sunan Ammo da ɗan ɗaga murya.

A hankali ta juyo cike da tsoro tana san laluɓawa ta fito waje, ga kuma wayarta a hannunta amma tsoro yasa ta mance da wayar bare ta kunna haske. Juyowa da zata yi sai ji ta yi ta bugi kirjin mutum. Wani irin razana ta yi da karfi ta waje baki zata yi ihu.

Ɗip kake ji an toshe mata baki, ta baya baya ya janyota ya mannata da jikinsa, a hankali ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, sannan ya zuro hannunsa ɗaya a saman flat tummynta.

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne kalmar da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta, haƙiƙa ta tsorata, tsoratar ma yasa sam sam bata ji kamshin perfume ɗinsa ba, ƙoƙarin kwace kanta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login