Showing 306001 words to 309000 words out of 403653 words

Chapter 103 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

19

yi maganar. Gudun kada tasa a gane halin da suke ciki yasa ya yi gaggawar janyota jikinsa ya rungumeta, muryarsa har tana kerma wajen cewa. "Please kiyi shiru, zan yi dik abin da kike so, amma please ki yi shiru kin ji?". Kin kula shi ta yi tana cigaba da kukanta. Damuwa da tashin hankali yasa ya yi gaggawar kamo hannun nata ya ɗaura a saman kirjin nasa dai'dai nipple ɗinsa, a rikice ya ce. "To ga shi nan yanzu ai kin taɓa kin rama, dan Allah ki yi.......".

Kasa iya kai karshen maganar ya yi sakamakon idanu da ta wurgo mashi, ga shi suna kusa kusa da juna, ta bushe mashi tamkar wadda aka zarewa ruhi, ƴar ƙaniya ta ji ta taɓa kirjin maza, tuni bakin nata ya mutu, kukan ma ta nemesa ta rasa. Ya ɗan tsorata ganin yadda ta kafesa da ido bata wani motsi, a rikice ya kai hannu ya fara jijjiga kumatunta yana ambatar sunanta. Ina bata motsa ba, a nan ya fahimci sume mashi a jiki ta yi, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rage tsawonsa ya ɗauketa zuwa saman bed ɗinsa, sai faman nisawa yake yi. Ya tsira daga bala'inta!!

Yana kwantar da ita aka fara knocking na door ɗin nasa, wani irin fargaba ya ji, gabansa ne ya yanke ya faɗi, murya na rawa ya tambayi wanenen? Daga waje Omaid ya amsa mashi da shi ne. Ai sake rikicewa ya yi, abin da yake gudu ne yake shirin faruwa, wato kannensa su kama shi da ita shikenan girmansa ya zube. Rasa me zai cewa Omaid ya yi, ga shi bai isa ya hana shi shigowa cikin ɗakin ba.

My people's ko kuna da wani abin cewa? Ko kuna da dabarar da zaku faɗawa guyson ya yi dan ya tsira daga Omaid ya gane suna tare da Mahreen?. To idan kuna da shawara ku yi gaggawar bashi kafin in dawo daga Black world.


🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥

Washegari da safe, sanye take cikin jelly dreass launin pink, ta yi masifar kyau, ta ɗaure haɗaɗɗen gashin kanta, da karfi da ya ji Sweetie ta koyi yawo babu ɗankwali, aka ce zama da maɗauki kanwa shi ke kawo farin Kai.

Tsaye take a tsakiyar bedroom na Ronnie, kyawawan kafafunta na sanye cikin flip floor launin white color, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai, sai wani sheki yake yana wani ɗaukar hankali, sai launin dark purple lips ɗin nata ya kara turuwa sosai, idanunta sun kara kyau tamkar ta sanya kwalli alamar tana cikin farinciki sosai kenan. Ronnie dake zaune a tsakiyar bed ɗinsa sanye da pj's dress a jikinsa ne ya harbeta da wani ɗan ƙaramin throw pillow yana faɗin. "Ba zan barki ba, sai kin faɗa mun shirinki".

Yana jefo mata pillown ta yi gaggawar juyowa haɗe da buɗe tafin hannunta, take magic ɗinta ya fita ya daki pillown, kai tsaye ya koma ya daki face ɗin Ronnien. Ƙayataccen murmushi ta saki kafin ta ce. "Alhaki cuicuyo, yanzu dai pillownka ya koma kanka". Tana magana tana kara faɗaɗa murmushinta, wlh sai ka ji ba zaka taɓa gajiya da kallanta ba matuƙar tana wannan sanyayyar murmushin nata. Shi kansa Black Tiger bai san ɗauke idanunsa daga kanta idan tana yi, shi ma dai Ronnie yana kyatsawa sosai, tana bashi a jikinsa.

Cikin zafa ya miƙe tare da dirowa kasan bed ɗin. Da gudu ta watsa ta nufi waje tana faɗin. "Idan ka isa ka kamani, in ka kamani zan baka satar amsa"....... Tsayawa ya ɗan yi tare da riko waist ɗinsa da hannayensa dikka biyu, a ɗan kule ya ce. "Is better for you da ki tsaya ki faɗa mun, in ba haka ba in na kamaki i will give you a hot punishment"...... Tana ƙoƙarin buɗe kofa ta amsa mashi da. "Fara kama ni ɗin tukunnan before you think about the hot punishment da zaka yi mun ɗin"........ "Kin rai'nani ko? Yau Allah ba zan barki ba". Ya kai karshen maganar tare da bin bayanta da gudu. Tini ta buɗe kofar ta yi waje tana dariya tana kara faɗin maza ya zo idan ya isa.

A gaggauce Black Tiger ya matsar da su daga gaban mirrornsa, dama su yake kallo, wani irin farinciki yake ji idan yana kallansu, amma kuma baya san su kama shi yana kallonsu, in dai yasan za su zo bedroom ɗinsa sai kuga ya fiske kamar bai san da su a empeir ɗin ba, alhalin munahiki ɗan air daɗin ganinsu yake ji, har da wani pretending ya yi gaggawar barin gaban mirror ya dawo tsakiyar bedroom ɗin nasa, sanye yake da bathrobe, linƙaya fa zai je yi a cikin karamar pool ɗinsa dake sama, amma da yaga suna dirama sai ya tsaya kallansu.

Da gudu Sweetie ta faɗo cikin bedroom ɗin nasa tana dariya tana kara faɗin Ronnie ya zo in ya isa. Da gudu shi ma Ronnie ya faɗo ɗakin yana faɗin Allah sai ya kamata yau, dan dole ya gwada mata akwai banbanci tsakanin mata da maza, ta ce idan bai kamata ba shi rago ne, dan haka shi ba rago bane dole ya kamata. Bayan Black Tiger ta zo ta tsaya tana haki tana faɗin. "Yi sauri ka zo, gani a bayan big bro kuma our shield".

Wani irin Black Tiger ya ji a ransa, kenan Sweetie tana yi mashi kallan shi garkuwansu ne, bango majinginansu? To in dai haka ne meyasa zai rinƙa cutar da ita? Meyasa ba zai ɗauketa kamar Ronnie ba tun da ita ma ta ɗaukesa yaya tamkar yadda Ronnie ya ɗaukesa?......... Da gudu Ronnie ya nufota, a guje ta fara kewaye Black Tiger yana binta tana tikar dariya tana kara tunzura shi a kan ya zo ya kamata. Sosai hakan ya yi wa Black Tiger daɗi, sai yake jin kamar dikka kannensa ne na jini, farincikin da suke ciki suna nishaɗi ya nishaɗantar da shi shi ma matuƙa.

Sosai ta yi gudu har ta fara gajiya, kun san kewaye take yi hakan ya haifar mata da ganin wani irin jiri mai karfi yana ƙoƙarin ɗibanta. Ronnie ya lura da haka sai ya ce. "Now is my time, zan kamaki in kuma hukuntaki".... Tana haki sama sama ta ce. "Ba zaka taɓa kamani ba saboda big bro ba zai bari ka hukuntani ba". Tana kai karshen maganar ta tafi zata kifa dai'dai lokacin ta zago ta gabansa. Cikin zafa yasa hannu ɗaya ya riko wuyar rigar jikinta, tafiya ta yi gabaɗaya ta faɗa jikinsa tana numfashi sama sama, ta sanya hannunta ɗaya a saman shoulder ɗinsa ta wajen damatsan hannunsa tana cigaba da yin haki.

Da gudu Ronnie ya zago da nufin ya kamata, tin bai ƙariso ba ya ce. "Nakamaki ai yanzu". Ya kai karshen maganar haɗe da sa hannu zai capko shoulders ɗinta. A miliyan Black Tiger ya ɗagata da hannu ɗaya ya juya da ita alamar ba zai bari Ronnie ya kamata ɗin ba kenan........... Sosai Ronnien ya yi muguwar mamakin ganin hakan, bai taɓa tinanin hakan ba ko a mafarki, kenan Black Tiger ya shigar mata faɗa? Ya jefawa kansa tambaya, lokaci guda kuma ya ji wani irin sanyi a ransa, dan hakan ma wata nasara ce a garesu, tabbas ko a iya haka big bro ya fara canzawa, Allah mai iko.
Amma saboda su cigaba da samun nasara sai bai nuna mamakinsa a fili ba, sai ma ya haɗe fuska tare da cewa. "Kenan haɗe mun kai zaku yi? Yanzu big bro kenan ka shigar mata? Wannan ojoro ne, kuma ban da ojoro, ka bari kawai in kamata". Ya kai karshen maganar tare da sake kai mata capka zai kamata, sake juyawa da ita Black Tiger ya yi, saboda sun tafi da imaninsa har bai san time da ya ce. "Ba zan bari ka kamata ɗin ba". Wlh bai ma san ya yi wannan magana ba.

Daga ita har Ronnien sai da mamaki ya daskarar da su na ƴan dakiku, kai abin al'ajabi wai ba zai bari Ronnie yakamata ba, like wow abin ya ƙayatar ba shakka, da alama yau Allah ya amsa addu'ar Sweetie yasa zuciyar big bro ta fara sauyawa, dama ta jima tana yi mashi addu'a, kullum tsakar dare sai ta tashi ta yi nafilfili ta yi mashi addu'a, har ta fara cire ran addu'arta zai amsu, ashe kuwa yana hanya. A cikin zuƙatansu gabaɗaya suka shiga faɗin alhamdulillah, alhamdulillah sun nuna godiyarsu ga Ubangiji matuƙa, yau big bro nasu ya shiga maganarsu, kai ba zasu taɓa manta wannan rana ba.

Cigaba da binta Ronnie ya yi yana san kamata mamaki kamar zai kasheta, shi kuwa Black Tiger ya cigaba da kaucar da ita yana faɗin Ronnie ba zai kamata ba, tin da ta kasance mai rauni tana da shi wanda shi kuma ba mai rauni bane. A takaice dai sai da Ronnie ya gaji lilis ba tare da ya iya kamata ba, shi kuwa Black Tiger yana tsaye waje guda ya yi nasarar wahalar da Ronnie har ya gaji ya durkushe a wajen yana haki yana faɗin. "Wannan ojoro ne, ba dan kai ba big bro Allah da na kamata, kuma ni ban yarda da wannan ojoron ba, amma ba komai zamu haɗe anjuma ne ai". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Bari in duba parents na Floris, zan je in apologies, zan ɗaukota in dawo da ita, i really missed her to much".

Lokaci guda face ɗin Black Tiger ya sauya jin kalaman kanin nasa, dan yasan me zai biyo baya idan Ronnie ya je can, ga shi bashi da hanyar dakatar da shi. Shiru ya yi bai iya dakatar da shi ba har ya fita daga bedroom ɗin har lokacin yana haki kaɗan kaɗan. Yana fita Black Tiger ya sauke Sweetie, cikin gaggawa ya wuce ya nufi wani siririn stair case dake cikin bedroom ɗin ya haura sama in da pool ɗinsa take. Da kallo Sweetie ta bi bayansa tana jin wani irin fargaba, gabanta na faɗuwa sosai.

Almost 5 mins tana tsaye a wajen, daga karshe ta yanke shawarar bin bayansa, domin tana san yin magana da shi. Ba tare da tsoro ko tinanin menene a saman ba ta yi maza ta haura ita ma...... Like wow, wani irin yanayi ta tsinci kanta a lokacin da ta haura saman nan, domin kuwa wani haɗaɗɗen waje ne wanda sai ka yi zatan ba a duniya kake ba, blue light ne a wajen, tamkar ɗaki haka aka yi shi, kazalika blue light ne a cikin kwayayen bulb dake cikin pool ɗin, hakan yasa suka sanya ruwan ya koma blue sosai, ga wani kamshin dake tashi a wajen, abin dai ba'a magana.

Yana tsundume a cikin ruwan, ya lume gabaɗaya jikinsa, iya kansa ne kawai a waje, ya ɗaga kan nasa sama haɗe da lumshe kyawawan shape eyes ɗin nasa tamkar mai tinanin wani abin. Tabbas ya ji motsinta, amma bai ji kamar zai buɗe idanunsa ba. Cikin natsuwa ta tako ta nufo in da yake, a gabansa ta tsugunna tare da kurawa kyakkyawan face ɗinsa idanu. Lokaci guda ta ji wani irin shock a jikinta, ko idanunsa a rufe wlh kwarjini ne da shi sosai........ "Please ka faɗa mun menene ya samu Floris?". Ta jefa mashi tambayar cike da fargabar amsar da zai bata, kirjinta har wani dukan uku uku yake yi, Allah Allah take yi kada ya ce mata wani abin mummuna sosai ne ya sameta, har yanzu dai basu bata mutuwa ba.

Shiru bai amsa ba, kuma bai motsa daga in da yake bama, saboda kwata kwata baya san tina zancen.......... "Tabbas akwai abin da kake ɓoye mana, tabbas akwai abin da ya samu ƴar uwarmu, tabbas naga hakan a cikin idanunka a lokacin da Ronnie ya ce maka zai je dubata, please ka sanar damu menene ya sameta ko zamu ji sanyi a ranmu". Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa da kwallah, saboda tabbas taga rashin jin daɗi a kwayar idanunsa a lokacin da Ronnie ya ce zai je ya duba iyayen Floris ya basu hakuri.

Nan ma dai shiru bai yi magana ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa. "Shirunka ya fi komai kona mun rai, shirunka dai'dai yake da amsar cewa Floris is not alive, shin haka ne?"...... Ai bai san lokacin da ya tsinci kansa da girgiza mata kai alamar a'a ba haka bane, kuma ya yi hakan ne gudun balain da zasu tayar mashi ita da Ronnie, yau ita ce ranarsa ta farko da ya fara yin karya a kan wani abin dan gudun samun matsala da su.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta canza murya zuwa na nuna kauna da soyayya ta ce. "Har ƙasa na ji sanyi a rai'na, to faɗa mana in take?". Ta kai karshen maganar tana kallan zara zaran eyelashes ɗinsa da suka kara tsawo sosai suka kara bayyana saboda rufe idanun nasa da ya yi. Ɗan zuba masu idanu ta yi na ƴan sakanni kafin ta mayar da kallonta izuwa saman kyakkyawan wuyansa, a hankali ta mai da kallonta izuwa kan lallausan gashin kansa da yake bakin kirin yana wani curlyn, kaɗan ya kwanto mashi ta gaban goshinsa ya manne saboda ruwan da ya jiƙasa, hakan ya kara fito da tsantsar kyansa. Kan kyawawan romance pink lips ɗinsa ta dawo da kallonta, shiru ta zuba masu idanu tana jin tamkar tasa hannu ta taɓa su saboda sun haɗu matuƙa, sun kuma tafi da ita.

........ A hankali ya waro idanunsa wajen domin ya kalli meyasa ta yi shiru a wajen. Yana buɗe idanu ta yi saurin dawo da kallanta kan idanun nasa, zubawa juna idanu suka yi babu ko kyaftawa, kamar waɗan da suka afka duniyar tinani. Cikin dabara ta kai hannunta cikin ruwan ta ɗan ɗebo, saboda tsabar shegen tsokana ya yi mata over yarinyar nan, cike da tsoron abin da zai iya aikara mata a face ɗinsa ta watsa mashi ruwan. Wani irin lumshe idanu ya yi, har cikin ransa ya ji saukar wannan ruwa, sai ya ji tamkar ba ɗaya yake da ruwan da yake ciki ba, ji ya yi wanda ta watsa mashi ɗin tamkar na daban ne. Slowly ya sake waro idanun nasa a kanta haɗe da ɗan zarosu kaɗan.

Tsorata ta yi, a tinaninta hukuntata zai yi, dan haka sai ta yunkura ta miƙe da gudu zata bar wajen. Cikin zafa ya sanya hannunsa ya capki dogon gashin kanta ba tare da yasan ya yi hakan ba, ai tafiya ta yi gabaɗaya ta afka cikin ruwan ta faɗi saman lion chest ɗinsa. Lokaci guda ya ji wani iri a jikinsa, while ita kuma tsorata ta yi sosai, da kyar ta iya janyo numfashinta ta cigaba da tafiya daidai, murya na kerma ta fara faɗin. "Wayyo na shiga uku, am so so sorry big bro, na tuba ba zan sake ba". Tana magana tana zazzare idanu haɗe da ƴan kame kame, take ta yi kasa da hannunta izuwa cikin ruwan ta ɗaura saman flat tummynsa.

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, slowly ya ɗan yi blinking eyes ɗinsa ya sake tsaidasu a kanta, while ita ma shi take kallah, a yanzu ma sake tsare juna da kallo suka yi, take ya fara hasko wasu sirrika na musamman dake tattare da kwayar idanunta, kamar dai akwai wani buri da take san cinmawa a rayuwarta. Ita ma kuma karanta kwayar idanun nasa take yi, saboda taga alamar akwai abin da yake hidden masu.

Tsit wajen ya yi, sun mace da kallan juna, cikin salo ya ɗan motsa romance lips ɗinsa da nufin ya yi mata magana ba tare da ya kawar da kallansa daga kanta ba, sai ta rigasa da cewa. "Please our big bro ka faɗa mun ina Floris take?". Ta yi maganar tana ɗan hauro da hannunsa izuwa saman lion chest ɗinsa ta cikin ruwan kenan. Babu riga a jikinsa fa, daga shi sai Swimming short, ya cire bathrobe ɗin.

Tamkar wanda bakinsa yake yi mashi ciwo, baya san motsasu haka ya ɗan motsasu wajen cewa. "She died". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar....... A razane ta wani irin zaro mashi eyesball ɗinta tamkar kwayar zasu firfito su faɗi ƙasa, tana ƙoƙarin yin magana cike da tashin hankali ya yi saurin sanya hannunsa ya rufe mata baki, a hankali ya girgiza mata kai alamar a'a ta yi shiru. With his lion voice ya fara yi mata bayani wanda bai bawa kowa damar sauraron abin da yake faɗa ba, sai da ya kai karshe daga nan ga rufe maganar nasa da cewa ta san yadda zata yi da Ronnie kada ta bari ya birkice sosai, ta taya shi ɓoye mutuwar Floris har zuwa wani ɗan lokaci, kada su sanar da Ronnie.

Ai yadda kuka san ruwa ya cinye Sweetie, ta kasa motsawa daga in da take, tamkar wadda ta sume, idanunta a kansa kuma babu ko kyaftawa.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️









51




🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Kurawa face ɗinta idanu ya yi, sai yau ya tabbatarwa da kansa cewa Sweetie kyakkyawar gaske ce, ta sume mashi amma idanunta a buɗe, ɗan lumshe idanunsa kaɗan ya yi tare da sake buɗesu a kanta, hannunsa ya ɗago, tafukan hannun nasa ya ware tare da shafa face ɗinta da shi, take ta ja doguwar numfashi, da alama magic ya yi mata ta farfaɗo. Kamar mai raɗa haka ya fara raɗa mata cewa kada ta bar Ronnie ya fahimci abin da ya faru, ta yi mashi dabara, daurewa ta yi ta yi ta mazan cewa sai dai idan shi ma zai yi mata wani

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login