Showing 360001 words to 363000 words out of 403653 words

Chapter 121 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

30

wanda ni dai ban gane wani irin tinani bane...............🥱

Zuciyar Big bro kamar dutse take, dik bakinka baka isa ka tsaga cikinta kaga me yake tinawa ko me yake ciki ba, dole ka hakura sai ya fito da ita fili ka gani!!

Da alama Big bro yau ya ga wani sabon al'amari daga Sweetie, to ni dai ba ruwana ato!!.

Ita kuwa tana fita ta tsaya a bakin kofar bedroom ɗin nasa, Astagfirullah ta shiga nanatawa sama da kafa 100 kafin ta nufi ƙasa zuciyarta cike da tinanin abin da take yi!!. Parlour ta sauko, tana sauka suka ci karo da Ronnie da ya nufo sama zai sake komawa bedroom na yayan nasa ya sake dubata. Yana ganinta ya nufeta da sauri yana sauke ajiyar zuciya!.
"Lovely sis ina kika shiga?". A ruÉ—e ya faÉ—i maganar. Kin kallonsa ta yi, ta É—aure fuska kafin ta ce. "Ba ko'ina mu je ka yi dropping É—ina a school". Tana kai karshen maganar ta nufi in da jacket É—inta and school bag É—inta yake. Da sauri ya bi bayanta, dik wahalar da ya sha wajen nemanta sai ta zo ta wani wucesa tana wani ciccin magani?.

Jacket ɗinta mai kama da boyfriend Jacket ta ɗauko tare da sanyawa. Tana ƙoƙarin zuge zip ɗinsa sama sai taga wani haɗaɗɗen chain a wuyanta, a hanzarce ta kai kallanta da kyau kansa. Dai'dai lokacin Ronnie ya kariso wajen yana faɗin. "I forgive you lovely sis, and why kike ɓata rai? Ko dai kun haɗu da Big bro ne ya ɓata maki rai...........". Bai ƙarisa maganar ba sakamakon sauka da idnaunsa ya yi a kan chain dake wuyarta. Ɗan zaro idanu ya yi yana faɗin. "Wow, kinga kyansa kuwa? Kinga yadda ya yi maki kyau kuwa?. Nasan Big bro ne ya baki! Amma waye ya yi maki wannan haɗaɗɗen make up ɗin da har kika fito tamkar Queen of the world?". Cike da tsantsar kaunarta ya yi maganar!.

Ɗauko school back ɗinta ta yi tare da wurga mashi ta wuce gaba tana harararsa. Capke jakar ya yi, a hanzarce ya rufa mata baya. Yana isota ya riƙo hannunta. "Yau sai ɓata rai kike yi? Na yi maki wani laifi ne?". Kin kula shi ta yi, wasa wasa har suka shiga mota, sai magana yake yi mata taki amsawa har suka isa school, motocinsu na parking a parking lot na school ɗin bata jira sun buɗe mata kofar motar ba ta ɓalle ta fito abinta. Da ido Ronnie ya bita yana mamaki, jikinsa dik ya yi sanyi, a cikin ransa ya ce ko dai Black Tiger ne ya hanata yin magana? Haƙiƙa ya shiga damuwa sosai da bata kulasa ba.

Ya yi nisa a cikin tinanin nasa, sam bai san time da ta ɗauki jakarta ba, sai ji ya yi ta manna mashi hot sumbata a kumatu tana faɗin. "So much love my lovely bro". Ta faɗa tana murmushi haɗe da juyawa ta nufi hanyar tafiya. Ai bai san time da ya saki ƙayataccen murmushi game da sauke ajiyar zuciya ba, da ya ɗauka fushi take yi da shi.

"You're the only my brother that making me happy anytime, I really love you my pleasure". Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba, tana cigaba da tafiyarta.

Tin da ta fito idanun gabaÉ—aya student a kanta, su kansu sun shaida da ta yi fitina yau É—in nan, kalar kyanta ma na daban ne. Dik kyan mutanen birnin sun jinjinawa nata. Kasa hakura ya yi da jin kalamanta, da gudu ya fito ya bi bayanta. Sai da ya kamota ya manna mata sumbata a kumatu, sannan ya juya ya koma mota yana yi mata fatan alkhairi tare da fatan ta kula da kanta kuma ta yi karatu sosai. Da okey ta amsa tana yi mashi bye bye, ji ya yi kamar kada ya tafi ya barta, amma haka ya daure suka juyo suka dawo gida.

Dik sai ya ji gidan babu daÉ—i da bata nan, dan haka wunin cikin É—aki ya yi, ya takure kansa har zuwa lokacin tashinsu school, tin da sauran lokaci ya tsara wanka tare da shiri cikin sport wear É—insa ya nufi school É—in nasu. A lokacin da suka iso school É—in tana zaune ita da wasu Æ´an'mata kyawawa guda biyu da ita uku, zaune suke a garden na school É—in nasu suna hira, basu komai a class ne suka fito waje. Yana zuwa kuma aka buga tashi. Fitowa wajen motar ya yi tare da jingina bayansa a jikin motar yana jiranta. Tana jin an buga tashi ta yi saurin yiwa Æ´an'matan sallama tare da wucewa, dan tasan already ya zo, baya lattin zuwa É—aukarta.

A tare ƴan'matan suka ce zasu rakata, kowa son ta yake yi, suna san yin ƙawance da kyakkyawa, ita kuma very friendly take, bata da matsala. Amince masu ta yi suka rakota wajen motar, yana tsaye tin daga nesa yana kallonsu, sun nufo shi, tamkar wata a cikin taurari haka ta kasance a cikin waɗan nan ƴanmata, dik ta haskesu, ta dishashe haskensu da nata. Tin bata ƙarisa isowa ba ya buɗe mata hannu, tana zuwa ta faɗa jikinsa tana murmushi.

Kallan juna ƴan'matan suka yi, lokaci guda suka sha jinin jikinsu tare da komawa gefe suka tsaya shiru, sun gane Ronnie sarai, dik wanda yake cikin birnin dole ya sansa. Basu taɓa zatan Sweetie daga Black Tiger Empire ta fito ba, lallai yanzu ta kara samun girma da daraja a idanunsu fiye da a baya, dole su yi respecting ɗinta sosai, tab ai ta wuce class na ƙawance da su, dama tin da yake kawota baya fitowa shiyasa basu san mai kawota da kuma mai ɗaukarta ba sai yau.

"Bro this is my friends Loosi and Rose". Ta faɗa tare da raba jikinta da nasa, sannan ta ce. "Rose this is my brother". Ta yi maganar tare da nuna shi da hannu!. Cikin girmamawa suka zube gwiwowinsu a ƙasa game da yin ƙasa da kai suka fara zuba irin gaisuwar da suke yi wa manyansu a birnin, wato dik wanda ya fito daga cikin Empeir ɗin haka suke gaida shi.

Ɗan ɗaure fuska ya yi kafin ya yi masu alama da hannu a kan su miƙe ba tare da ya yi magana ba. Ba musu suka miƙe tsaye, da hannu ya yi masu alama da su tafi. Cikin hanzarin suka bar wajen suna sake waigosa, Allah ya gani Ronnie burin dik wata yarinya dake cikin wannan birnin ne, har manya kwaɗayinsa suke ji.

Riƙo hannunta ya yi, ya shige cikin mota yana janta ta shigo. Tana ƙoƙarin shiga daga bayanta sai ta ji an ce. "Omaish O Mutallab ka book ɗinki". Da sauri ta juyo, shi ma Ronnie ɗan leƙowa ya yi dan ya ga wanenen?. Wani matashi ne da a kallah zai iya kai 19 to 20 haka, uniform na seniors ne a jikinsa, a Ss3 yake, ta mance da book ɗinta ne a set ɗinsu wajen small library ɗin nasu, shi ne ya biyota da shi, dama burinsa ya samu wani abin da zai haɗa shi magana da kyakkyawar nan, shiyasa yake yawan bibiyarta, dik in da take sai ya je wajen, sai Allah ya yi yau ya samu damar yin magana da ita, ta hanyar ta kammala karatu ta bar book ɗin a wajen saboda sauri!.

Ƙarisowa ya yi in da take, miƙa mashi hannu ta yi ya miƙe mata book ɗin. "Thank you". Ta faɗa tare da juyawa. "Am baki ji ba Omaish". Ya faɗa cikin sanyin murya. Juyowa ta yi tare da ɗaga mashi gera irin alamar lafiya?.

"Seriously you're so cute and pretty". Ya faɗa yana ɗan shafa kansa. Ɗan sake face ɗinta ta yi kafin ta ce. "Thanks". Ta faɗa zata sake juyawa sai ya katseta da cewa. "My name is Michael, can we be a friend?". Ya yi maganar tare da miƙo mata hannu wai su yi musabaha, daga haka sai sun zama abokai, dik abin da yake yi bai lura da Ronnie dake kusa da su a cikin mota yana kallonsu ba.

Yana miƙo mata hannu Ronnie ya zuro nasa hannun ya capki nasa tare da fitowa waje daga cikin motar. Ai yana ganin Ronnie a zabure ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta tare da buga hannunsa a kirji, sannan ya risinar da kai kasa alamar girmamawa. Ɗaure fuska sosai Ronnie ya yi, yanzu yasan darajar mata, saboda musulunci ta ratsa shi matuƙa.

"Michael I don't want to see you close to my sister again!!". Ya faɗa with harsh voice, cikin bada umarni, babu wasa a tattare da shi, da alama ya san kishi a yanzu!!. Da ido ya yi mata alama da ta shiga mota, da sauri ta faɗa ciki tana ɓoye murmushin dake san kwace mata bayan taga yadda ya ɗaure fuska. Bata san me da me ya faɗawa Michael ba tana daga ciki ya shigo ya sameta bayan ya gama kenan, ta so jin yadda zasu kare, sai dai ina, tana ciki! Haka ya shigo ya sameta suka nufi gida, a hanya ya daka mata zazzafar warning a kan kula maza, ya ce babu ruwanta da su, ko matan ma bai ce ta saki jiki da kowa ba, bai dai hanata ƙawance da mutane ba, amma nesa nesa, dan matsayinsu ba ɗaya ba!!.

Okey ta amsa mashi da shi, yarinya mai jin magana, (Ba irin Pretty abokiyar faÉ—an Smart ba, wai ke ka ce ba Pretty ba, kai Pretty duniya!!)

Sai ta ce mashi harta matan ma bata buƙatar kowa a kusa da ita, shi kaɗai ya isheta. Ya matuƙar jin daɗin kalamanta a in da ya manna mata sumbata a goshi. Haka suka isa gida. A tare suka fito daga cikin motar suka nufi cikin gida, kai tsaye bedroom ɗinsa suka nufa tana faɗa mashi ya zo ya yi mata home work, da okey ya amsa mata suka wuce ciki.

Abinci yasa aka kawo masu kamar kullum, a tare suka yin lunch bayan ya jirata ta yi wanka, ta tsantsara kyau cikin wandon jeans baki mai kwalliyar pink a jikinsa, and pink long sleeve shirt, ta yi matuƙar kyau, ta sanya headband baki a kanta, wannan sarka da Big bro ya bata yana nan a wuyanta sai kyalli yake yi, a school ɗinsu babu wanda bai yi magana a kan sarkar nan ba, uncles ɗinsu ma sai da suka yi magana, saboda haɗuwarsa, dik wanda yasan abu mai tsada dole ya jinjinawa wannan sarka, dan dubabbannin miliyoyi ake magana a wajen. Wato Big bro wuyarta tana burgesa, shi ne ya kara kawata mata shi yadda zai ji daɗin kallo, wlh Black Tiger ɗan duniya ne!!.

Kafin ta gama wanka ya shirya masu komai, tana fitowa ta yi sallah suka yi lunch, sai suka yi karatu na awa biyu a in da ya koya mata Home work ɗin nata da aka bata, ta ji matuƙar daɗi sosai da sosai, sai murna take yi. Hira suka zauna yi har la'asar ta kawo kai, sannan ne suka miƙe, a lokacin Black Tiger baya nan, yana fada, hakan yasa suka wuce bedroom ɗinsa suka yi sallarsu a can, sannan suka zauna ta ɗan koyawa Ronnie karatun addini dai'dai gwargwado, bayan sun kammala around 4:30, sai ya ce su je trainin, su ɗan motsa jiki kaɗan kafin su shirya zuwa church kamar yadda ya yi mata alkawari.

Cike da murna ta ce. "Muje amma zuwa church ka bari sai zuwa gobe". Cike da mamaki ya ce. "Why?". Kashe mashi ido É—aya ta yi kafin ta ce. "Akwai dalili, akwai abin da nike san kammalawa ne". "Sisterrrrrrrr". Ya faÉ—a yana É—an jan sunan alamar kamar warning yake yi mata. "Don't worry ba zan yi abin da zai kawo mana problem ba". "Are you sure?". Sure ta bashi amsa tana wucewa gaba!. "To please kada ki yi magana sosai, and komai zaki gani ki yi shiru kin ji?". Jinjina kai ta yi alamar ta yarda.

ÆŠan gudu ya yi ya kamota tare da rike hannunta suka wuce suka nufi gym É—insu. Yana zuwa ya hau motsa jiki, a hankali ya fara cigaba da koya mata, push up ya fara yi, a nan Black Tiger ya zo ya samesu suna yi, bai bi ta kansu ba ya fara nasa gym É—in, tin da ya shigo wajen ta tsaresa da kallo, ya yi masifar kyau cikin wasu shegu kuma tsadaddun gym wears, shi kuma sam bai kalli in da take ba ya fara aikinsa.

After some minutes Ronnie ya ce mata ta zo su fara faɗar takobi da ya fara koya mata last week, cike da murna ta fara tsalle tare da tasowa ta nufesa. Wani keɓanɓɓen waje suka shiga can ɗan gefe da gym ɗin, wajen tamkar duniyar mafarki yake, ga ruwa yana zuba ta sama kaɗan kaɗan kamar shower haka. Dai'dai tsakiyar da ruwan yake zuwa ta zo ta tsaya yana jiƙata, shi kuma zaro takobi marasa tsawo da nauyi sosai guda biyu ya yi, ya miƙa mata guda ɗaya ya riki ɗaya a hannunsa, sannan ya ciro hulunar faɗa masu kariya ga kan mutum, ya bata ɗaya ya ɗauki ɗaya, gabaɗaya wajen shake yake da kayan yaki kala kala.

Faɗar wuƙa suka fara yi ruwan nan na zubowa a kansu yana cigaba da jiƙasu, yanzu ta ɗan fara iyawa ya fara yi mata manya manya, da a hankali hankali yake yi mata. Ita ma ta zage tana san ta ko yi abubuwan, dan suna burgeta, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa take san Ronnie, saboda iya faɗarsa ga shi ɗan wrestling, bugu da kari yana da horon mayaƙa, abin ƙayatarwa kuma ɗan wasa ne, kwallon kafa, basket ball, kai dik wasanni yana bugawa har snooker bai bari ba, ga su skater dikka, shiyasa ta ce ya koya mata ita ma ta zama kamarsa.

Cigaba da wasan takobinsu suka yi gwanin birgewa, tana ɗan tsoro tsoro sai da ya ce mata kada ta damu, ta kawo mashi kowani irin hari ne ba zai ji ciwo ba, zai iya tarewa, ita kuma ta ce kada ya zo bai tare ba ya ji ciwo, kai ya girgiza mata alamar kada ta damu, shi fa da yayansa yake wannan training ɗin, dan haka zai iya tarewa, kuma idan har bata kawo hari kowacce iriya ce ai ba zata taɓa iya yaki ba, dan haka dole ta kawo hari. Jin abin da ya ce yasa ta ɗaga takobin hannunta da karfi ta nufesa zata sara mashi a wuya.

Ɗan juyawa gefe ya yi a in da ta wuce ita da takobin nata gabaɗaya ta tafi zata kifa, hannunsa ɗaya da bai rike takobi ba yasa ya tallabo flat tummynta, dama tafiya ta yi zata kifa, sai ya tarota ta gaba gaba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗagowa cikin zafa, wai irin ita ma yanzu zata fara yi mashi da zafa tin da ta ga yana tarewa, ashe da gaske zai iya tarewa ba zai ji komai ba!!. KAI SWEETIE WANI LOKACI AKWAI SHIRIRITA, TO MEMA TA IYA DA HAR TAKE GANIN IDAN TA KAWO MASHI HARI BA ZAI IYA KAREWA BA?! WAI ITA A TINANINTA TA ƊAN IYA WANI ABIN.......😅

Yunkurin sake kai mashi sara ta yi, ina ai sai ya fara wasa da ita tamkar wata ƴar tsana, ya cigaba da bata wahala har sai da ta gaji ta ce. "Lovely bro am tied, ka barni haka, ko sau ɗaya ban yi nasara ba fa". Jefar da takobin ya yi tare da jawota jikinsa yana faɗin. "Ai in dai a kai'na ne ba zaki taɓa yin nasara ba, muje ki yi wanka". Turo baki ta yi. "Soon zan yi nasara". Jinjina kai ya yi. "Zan yi fatan hakan, zan so gani lovely sis ɗita ta yi nasara". Raba jikinta da nasa ta yi tana jefar da takobin kasa kafin su nufi cikin gida. Wanka ta fara yi kafin ta bashi waje ya shiga, shi ma wanka ya yi.

Shiryawa ta yi cikin wani haɗaɗɗen gown fari irin mai breast cuf ɗin nan, so kana iya ganin tudun matasan tula tulanta da suke gwanin birgewa, ta yi masifar kyau matuƙa, ga kayan ya fitar mata da coca cola shape ɗin jikinta sosai, dan irin malesian gown ɗin nan ne, ya bi surar jikinta and rigar bai kai mata har ƙasa ba, da kaɗan ya rufe mata cinyoyinta, ta sanya wani high heel, yadda kuka san wacce zata tafi club party, ta zuba chewing gum masu balai'n kamshi a bakinta tana wani tauna, da alama yau da rashin mutumci take ji. Fitowa ta yi ta nufi sama kololuwa tana gyara headband ɗin kanta, wai hoto zata je ɗauka a saman, ɗazun taga wayar Ronnie a wajen.

Tana haurowa shi kuma yana saukowa sanye da pj's dress a jikinsa, ya yi fitina a cikin kayan. Wuceta ya yi tamkar bai ganta ba, ita ma wucewa ta yi kamar bata gansa ba. Har ta É—an yi nisa sai kuma ta É—an É—aga hannunta sama kamar mai neman wani abin a sama, a hankali ta juyo tare da cewa oh irin ta gane magana take san yin mashi É—in nan. Gently ta ce. "Hi big bro! One minute please!". Ta faÉ—a tana sauke hannunta izuwa saman waist É—inta.

Dakatawa ya yi da tafiyar ba tare da ya juyo ba, alamar dai ya bada one minute da aka tambayar. Cike da yanga ta tako ta nufosa, dik Ronnie ya koya mata wannan iskanci, shi ya yi mata wayo ya ce ta rinƙa yiwa Black Tiger haka zasu yi nasara, bata san wayo ya yi mata dan yasa su rufta da san juna ba, shi a nasa tinanin idan ba soyayya ba akwai matuƙar wahala Black Tiger ya iya canzawa, sannan ba zai taɓa musulunta ba idan ba ya kamu da soyayyar musulma ba, Sweetie ta faɗa mashi babu aure a tsakanin namiji krista da mace musulma, to shi ne yake san Black Tiger ya rufta kogin sonta, idan ya yi zurfi sai ace ba zai mallaketa ba sai ya musulunta, wannan ne shirin Ronnie, amma bai sanar da kowa ba, ko ita Sweetie

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login