Showing 57001 words to 60000 words out of 403653 words

Chapter 20 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

135

sanye da kusan irin kayan da suka rabu da Sweetie a wannan rana da damusa ta far masu, sai dai wannan kayan milk color ne.

Ta yi shiru haɗe da buga uban tagumi, kamar dai akwai abin da take tunawa. Allah sarki har ta rame, Sweetie ta matsa mata akan ƴar dumurkurewa da ta yi a lokarin da suke a tare, har tana gayawa Kamran cewa Pretty ta fita kiɓa saboda ta fita cin abinci.

To yau ina Sweetie take? Ta zo taga Pretty ta yi rama sosai, ta canza kamar ba ita ba, wuyarta sai layin guru zaa gani alamar tsokar nama ya taɓa taruwa a wajen.

Kan nan nata ba ɗan'kwali, gashinta a watse, ko gatan tarawa a ɗaure bai samu ba, dama Sweetie take ɗaure mata, to yanzu Sweetie bata nan babu mai yi mata, ita kuma bata iya ba, sai ta barshi a watse har gadon bayanta, dik ya yi datti ma bata wanke ba.

A hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa a jikinta, tsabar ta yi nisa cikin duniyar tunanin da take yi ma bata ji alamar ruwan saman ba.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





A hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauƙa a jikinta, tsabar ta yi nisa cikin duniyar tunanin da take yi ma bata ji alamar ruwan saman ba.

Wani irin narkakken hadari bakinkirin ne yake tasowa a gajimare, sai walkiya da tsawa ake yi, amma tamkar sassaka Pretty aka yi a wannan waje, sam bata motsa daga in da take ba.

Lokacin guda ruwa ta barke kamar da bakin kwarya, amma Pretty tana zaune shiru, kamar wadda babu rai a tattare da ita.

Allah sarki abar tausayi, ga rashin uwa, ga rashin madogara, yanzu kuma ga rashin ƴar uwa, babu Kamran, abin ya yi wa kakanun shekarunta yawa wlh.

Tun farkon ruwan saman nan har karshensa a kanta ya kare, daga karshe ma haɗe kai da gwiwonta ta yi tana ruwan hawaye sosai. Ruwa sai dukanta yake yi.

Har ruwar ta dakata Pretty bata da niyar motsawa daga in sa take zaune, yadda kuka san ba mutum bace. Ko ɗago kanta taki ta yi.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Omnish". Daga bayanta ta ji wata murya an furta hakan.

Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta ɗago kai tare da juyowa ga muryar. Idanunta sun yi jajir kamar wuta saboda kuka ga ruwan da ya dakata.

Yana tsaye cikin wannan shiga tasa ta kullum, face ɗinsa a rufe da hular mayaƙa, tsayuwa cikin jarumta da nuna cikar zarra, ya ɗaura hannunsa ɗaya saman tabkekiyar takobin dake manne a waist ɗinsa, jikinsa dik yayyafin ruwan sama.

Tana ɗaura idanunta a kansa ta yi maza ta miƙe tsaye, sai a lokacin ta fara jin sanyin ruwan saman da ya jiƙata, takure jikinta waje guda ta yi, fuskarta gwanin ban tausayi, idanu cike tab da ruwan hawaye, ta kasa yin magana sai dai ido take binsa da shi.

Cikin harshen tsabtataccen larabcinsa, ga nitsuwa da kamala a tattare da voice ɗin, kamar baya san yin magana ya ce.

"Omnish meya tsayar dake cikin ruwan nan haka?".

Tamkar jira take yi a yi mata magana, ai sai kawai ta fashe da kuka mai ɗan sauti.

Cikin jarumta da zafa ya tako ya matso kusa da ita, ɗan rungumota kaɗan ya yi a jegen takobin dake waist ɗinsa, ya fara bubbuga bayanta alamar rarrashi.

Yadda suke tsaye a wajen sai sun yi maku wani iri idan kuka gansu, in baku manta ba na ce maku wannan sadauki idanunsa iri ɗaya da Pretty, kamar an tsaga kara, dik da fuskarsa a rufe take, in kaga idanunsa da nata sai ka yi zaton kanwarsa ce ita ko yarsa dik da bamu san babban mutum ne ko yaro ba, tin da bamu taɓa ganin face ɗinsa ba.

Hannunsa dake cikin wani irin hands gloves mai karfi ya ɗaura saman lallausan kumatunta yana goge mata hawaye, tamkar kara ingizasu yake yi, yana gogewa wasu suna fasowa.

Juyo da ita ya yi suna fuskantar juna, ya ɗan rage tsawonsa dan ya dai'daita kansa da tata.

"Omnish menene ya faru kuma? Kin manta jiya kin mun alkawarin ba zaki sake yin kuka bane?".

Shiru bata amsa mashi ba, bata ma da niyar amsa mashi ɗin.

"Omnish ya isa haka kukan, yi shiru ki faɗa mun me ya sameki kuma?".

Still shiru bata amsa mashi ba. Dik sai ya ji babu daɗi, ga dikkan alamu ya ji jikinsa ya yi mugun sanyi, da alama tausayinta ya kara ratsa heart ɗinsa ne.

"Yau kuma ba za'ayi magana dani bane Omnish?".
Cike da tausayawa ya yi maganar, yana jin tausayinta matuƙa.

Kai ta girgiza mashi alamar a'a, a take ta tsuke fuska zata fara yi mashi shagwaɓar da ta saba, ashe dai har yanzu halin nan nata na shagwaɓa yana nan.

Cigaba da goge mata hawaye ya yi yana kara rarrashinta. Da kyar ya samu ta yi shiru, amma taki ta yi mashi magana. Hakan yasa ya miƙe tsawonsa ya riko hannunta suka kutsa cikin daji a tare yana mai kara rarrashinta.

Wanenen kuke tunani zai kasance wannan sadaukin? Meyasa kuma sai dai ya taimaka masu a daji ba zai ɗaukesu ya fitar da su ya kaisu cikin gari ba? Meyasa baya san su bar wannan dajin? Menene alakarshi da su? Ina mom ɗinsu? Ina ne tushensu? Ina dad ɗinsu?.

Dik cikin nutswa amsoshinku zasu bayyana, yanzu dai muje zuwa!!.

•••••••••KINGDOM OF POWER••••••••🔥

Sai misalin karfe 1 da rabi na dare aka tashi taron dinner. Har lokacin guyson bai rintsa ba, yana ta bin part part na kowa yana neman Auta.

Daga karshe ya dawo ɗakin momma dan ya ɗauki wayarsa ya kira numberta, a lokacin momma tana sallah, wayar kawai ya ɗauka ya fito waje.

Ya kirata ya fi miss call talatin, amma ina bata ɗauka na.

Idanun Hoorain biyu bai rintsa ba, yana ganin call ɗin guyson amma bai ɗauka ba, ya kasa iya yin barci, yana zaune saman bed ɗinsa kamar mai nazarin wani abin, gabaɗaya ji yake kamar jikinsa ba mallakinsa bane ba.

Idan hankalin guyson ya kai miliyan to fa ya tashi a wannan dare, ya shiga damuwa na wuce misali.

Baya shiri da Mammiensu Sarina amma a cikin wannan dare sai da ya je part ɗinsu ya buga mata kofa, dan dole yasa ta fito ya tambayeta Auta, ta ce mashi bata a part ɗin nan, hankalinsa ne ya kara ɗugunzuma ya tashi.

Wajen mommarsa ya dawo dan ya sanar da ita, tana sallah har lokacin, dan haka sai ya samu waje saman bakin bed ya zauna yana jiranta.

Ita kanta ganin shege da fice da yake yi mata a ɗaki yasa ta ji ta kagu da ta sallame sallar dan ta ji me damuwarsa da yasa bai yi barci ba har karfe ɗaya da rabi.

A ɓangaren ƴan dinner kuwa, Fanan ta ja hannun Chuchu a kan ta zo su wuce wannan ɗaki da yake mallakin amare dan gyarasu, a ka'ida amarya ba zata fita daga cikin wannan ɗaki ba har sai lokacin da za'a kaita ɗakin mijinta, ko dinner aka je nan zata dawo.

So ana tashi Fanan ta kama hannunta a kan su tafi can.

Wani irin hararar da Jawad ya wurga mata ne yasa Fanan ta yi gaggawar sakin hannun nata tana ɗan sunkuyar da kai.

Abdussalam yana ganinsu dik abin da suke yi, dariya suka so ɗan bashi, wato dai Jawad rashin kunyarsa a fili zai nuna? Abdussalam ya tambayi kansa yana kunshe murmushi.

Ita kuwa Fanan kasa ta ɗan yi da kai tare da cewa. "Yah Jawad zamu koma ciki ne fa!".

Tamkar bai ji me ta ce ba ya yi shiru yana kallon Chuchu dake tsaye kusa da shi.

A karo na biyu Fanan ta sake maimaita mashi abin da ta faɗa ɗazun.

Kallo mai kama da harara ya wurga mata, cikin sanyin murya ya ce. "Ke kika kawo mun ita ne dama?".

Kamar zata gyaɗa mashi kai alamar e, saboda ita ta kawota kam, amma sai taga rashin dacewar ta yi mashi hakan tun da yayanta ne, kuma tana tsoron ya hukuntata, dan haka sai ta girgiza mashi kai alamar a'a ba ita ta kawo ta ba.

Hannu yasa ya nuna mata hanya. "Jeki zan dawo da ita da kaina".........Ya faɗa idanunsa a kan Chuchu da ta sunkuyar da kai tamkar bata a wajen, tinanin Auta ce kawai a cikin kwakwalwarta.

"Kai malam kamar ya zaka mayar da ita da kanka? Ban gane ba?"...........Cewar Abdussalam, ya yi maganar cike da tsiya da iyashege.

"E zan mayar da ita time da na yi ra'ayi"....... With his full confidence Jawad ya mayar mashi da amsa.

"Kai ka kawota ne daman? Ji mun wani karfin hali, kinga Fanan kama hannunta ku tafi hai"........... Cewar Abdussalam, yana magana yana ɗaure fuska irin shi fa da gaske yake yi.

Gum kamar gunki Fanan ta tsaya ta kasa kama hannun Chuchu saboda tana tsoro, jama'a dik sun watse sun barsu tsaye a wajen.

"Fanan kama hannunta na ce ku tafi ko.........".......... Cewar Abdussalam. Bai ƙarisa maganar ba ya dakata saboda wani irin harara da Jawad ya wurga mashi.

Murmushi Abdussalam ya ɗan saki tare da riko hannun Fanan yana faɗin. "Zo mu tafi hai sister, kada ya fara saka mana duka".

Ba musu ta bishi suka tafi, wajen ya rage daga Jawad sai Chuchun.

A hankali ya kai hannunsa ya riko hannayenta, kamar mai raɗa ya ce. "Menene kuma?".

Kamar jira take yi ya yi mata magana ta fara kuka, nan take hawaye suka fara ƴar tsere a saman face ɗinta.

A ɗan rikice ya ce. "Jannat lafiya kuwa?".

Da ɗan daga murya ta ce. "Yah Jawad Auta, ban ga Auta ba, tun da yamma nike nemanta ban ganta ba, tun da rana rabona da ita, ina kiran numberta baya shiga, ya zan yi da rai'na?".

Ɗan jawota jikinsa ya yi, shi kansa yana cikin damuwar rashin Autar nan, amma bai taɓa kawo mummunar abu a ransa ba, ya fi zaton tana wajen bakin Dubai tun da ta yi sabo da su sosai.

"Auta tana nan a ciki gida, muje zuwa da safe da kai'na zan ɗauko maki ita".

Bata san yin ja in ja da shi ne kawai yasa ta yarda da abin da ya ce, ta kuma miƙa wuya a garesa, cak ya ɗauketa suka fito daga cikin hall ɗin.

Bai zame ko'ina da ita ba sai cikin bedroom ɗinsa, shi tun ba'a kai mashi ita ba ya kaiwa kansa ita.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Momma tana sallame sallah ko numfashin guyson bai bari ta ja ba ya yi sauri wurga mata tambayar ina Autarsa?

Wani irin dum dum Momma ta ji kirjinta ya buga, sai dai bata yi wani mummunar tunani ba, cikin nutswa ta ce.

"Ina jin tana tare da Jannat a wajen dinner.........."

Tun bata dasa aya a maganar ba ya tari numfashinta da cewa. "Naje wajen bata nan, Yah Jawad ma ya ce rabonsu da ita tun da rana.........."

Bai ƙarisa maganar ba momma ta zabura kamar wadda aka kwalawa guduma a kai ta miƙe tsaye, dan ita ma rabonta da Auta tun da rana, dik tinaninta tana a tare da su Chuchu ne yasa bata wani damu ba, sai yanzu ta tuna yadda ta rinƙa ganin giftawarsu Fanan and Chuchun ba a tare da ita ba, kwata kwata bata ga giftawarta ko kaɗan ba, to ina take kenan? Ta jefawa kanta tambaya.

Shi ma guyson miƙewa tsaye ya yi yana jiran amsa. Cikin ƙanƙanin lokaci face ɗin momma ta rikiɗa izuwa na tashin hankali.

Wayarta dake gefen bed ta ɗauko domin ta gwada kiran number Auta.

"Momma don't west your time, her number isn't going now, before i called her more than 30 times she didn't pick the call, yanzu kuma the number was not going, switch off".

Momma bata daka ta tashi ba sai da ta gwada kiran number, a kashe suka sanar da ita, hankalinta ne ya kara tashi sosai.

A hanzarce ta nufi kofar fita, kamar ta mance da guyson a tsaye a wajen. Ganin haka yasa ya yi saurin rufa mata baya.

Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King. A lokacin har barci ta fara ɗaukarsa, jin motsin taɓa kofa yasa ya farka.

Ganin sune yasa ya yi saurin miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin. Wajen switch momma ta nufa, dama iya lamp ne kunne a ɗakin, so sai ya kunna wutar gabaɗaya.

King he was very shocked na ganinsu a tare da kuma ganin yadda suka shigo momma a hargitse, da Momma ita kaɗai ce ba zai ji komai ba, amma a tare da guyson sai ya zaci ba lafiya ba, dik tinaninsa ta ta'allaka a kan ciwon guyson ɗin ne ya hanasu rintsawa.

A ƙage da son jin cikakken bayanin meyake faruwa yake binsu da kallo. Ita ma Momma kallonsa take yi ta rasa ta ina zata fara, dik yadda take ji a ranta take kuma tsananin tsorace a kan me ya sami yarta, hankalinta yake tashe ganin face ɗin King yasa ta ji nata tashin hankalin wasa ne a kan wanda shi zai shiga idan ya ji me ya kawosu.

Guyson ne ya katse masu kallon juna da suke yi ta hanyar ƙarisawa gaban bed ɗin, tamkar zai rushe da kuka ya ce. "Daddy Auta bata nan, mun duba ko'ina amma bamu gan.........."

Wani irin birki ya ci tare da haɗiye sauran maganganun a cikinsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face idanu da King ya zaro mashi tare da zabura ya yaye bargon dake jikinsa. Ai bai san time da ya sauko ƙasa daga saman bed ɗin ba.

Idanunsa a kan momma ya ce. "Da gaske ne abin da Omar ya faɗa?".

Kai kawai ta iya jinjina mashi ta kasa yin magana.

"To ina ta je? Kun duba dik part's na cikin gidan nan?".

Guyson ne ya tabbatar mashi da tabbas ya duba ko'ina bata ciki.

Innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ne abin da King ya furta kafin ya nufi waje da sauri.

Bayansa suka bi, a parlour ya tsaya tare da harɗe hannayensa saman kirjinsa, tunani ya fara yi a kan ina Auta ta tafi? In dai bata cikin kingdom ɗin nan to tabbas hanune ya ɗauketa, saboda ba ta yadda za'ayi wata halitta ta iya ketare gates ɗin nan gabaɗaya ta fita ba tare da saninsa ba! To ina take kenan?. Ya jefawa kansa tambayar da bai san amsarta ba. Zuciyarsa ta cika tab da tunani haɗe da ruɗani mai tarin yawa.

A nan momma ta isko shi, cike da tashin hankali ta ce. "Yanzu me abin yi?".

Guyson dake tsaye a kusa da momma idanunsa sun ciko da kwallah King ya ɗaura idanunsa a kansa. "Ɗauko mun wayata Omar"........... Ya faɗa tamkar wanda yake koyan yin magana, a hankali.

Cikin zafa guyson ya juya ya koma cikin master room ɗin. Kallon juna King da momma kawai suke yi babu wanda ya iya furtawa ɗan uwansa word.

A haka guyson ya dawo ya samesu, wayar ya miƙawa King, da sauri ya karɓa ya shiga latsawa.

Karata ya yi a kunnensa tare da matsawa gaba kaɗan.
Binsa da kallo kawai suke yi momma kamar zata ɗaura hannu bisa kai ta zunduma ihu, wannan bala'i dame ta yi kama? Abin ya yi mata yawa, Jaish ya ɓace shiru shiru tsawon watanni babu shi babu labarinsa, ta danne sai dai ta yi kuka a ɓoye, a fili tana nuna kamar bata damu ba, ta jajirce wajen shanye madarar bakincikin, yanzu kuma ace Auta ta sake ɓacewa basu san ina take ba? Ai gara mata Jaish namiji ne kuma babba ne, Auta fa? Mace kuma yarinyar da ko 14 years bata cika ba, dole hankula su ɗugunzuma su tashi.

"Abbas ka bincika mun Zunaira tana ɓangarenka ne!"........... Cewar King da ya kara waya a kunne.

Da sauri su momma suka kara nitsuwa haɗe da kara tsaresa da idanu da kyau.

Uncle Abbas da yake zaune saman dadduma yana gabatar da nafilfilin dare ne ya yi saurin miƙewa tsaye, dama ya idar yana addu'oi ne.

Mammie tana kwance saman bed tana barcin asara, kun san ita fa yanzu ba sallah take yi ba, sai shirka.

Uncle Abbas tin ba'a gaya mashi ta ɓata ba ya shiga tashin hankali, yanzu ai suna nemanta ne, a tinanin kowannensu tana cikin gidan, sai da King ya kira kowannensu har uncle Taheer ya ce su dubata, sai a sannan ne idanunsu ya fara rena fata, dan dik in da suke tinanin tana wajen babu ita, a yanzu kwata kwata basu sa a ransu kasheta ma aka yi ba, tun da ba'a ga gawarta ba, sun fi sawa a ransu saceta aka yi.

Shi King kam ma kai tsaye King Al-Mustapah ya ɗaurawa zargin yin hakan, dan in baku manta ba ya kawo masu jiyara yau da rana, kuma shi abokin gaba ne, so dole a zargesa.

King yana zargin shi ya saceta dan su cinwa wani buri nasu a kan kingdom of power.

Shi kuma uncle Abbas yana zargin Queen Zarina ce ta turo mutanenta suka saje da ƴan biki suka shigo suka ɗauke Auta, kowa da abin da yake zargi yake kuma hasashe, sai dai babu wanda ya yi hasashen ta mutu mai gabaɗaya ta bar duniya.

Dik tsananin taurin zuciya da jarumta haɗe da dakiya irin na King sai da ya shiga tsananin tashin hankalin da yake ƙoƙarin fita hayyacinsa a lokacin da suka tabbatar da bata a cikin Kingdom ɗin, dan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login