Showing 45001 words to 48000 words out of 403653 words

Chapter 16 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

33

sai dai ya yi wa mutun in short a dunkule, in ka gane kai ka sani, in ma baka gane ba nan ma kai kasani, kamar wani mai ciwon baki.

"My son wai ba zaka bar wanan halin naka ba ko?". Cewar Abbie da ƙaguwa kamar ta kashe shi, yana bala'in san jin karin bayani!.

Sai a lokacin ya ɗago da kallonsa a kan Abbie. Yasan a kan me Abbie yake magana, a kan rashin maganarsa ne, dan haka sai bai wani kula shi ba, alamar ba dainawa ɗin zai yi ba kenan!.

"Bomb ne a kewaye da hall ɗin nan, wanna wayar ita ce matashin bomb ɗin, shi ne dalilin fitana yanzu". Cewar Ramish.

Kallon Abu Abdussalam a kansa ya kara zaro idanu sosai, a hanzarce ya ce.
"Bayan harin da aka kawo maka bai yi masu ba shi ne suka kewaye mu da bomb? To su wanene? Wai me ka tsarewa mutane ne?".
Cike da tashin hankali Abbie ya yi maganar.

Tamkar babu Ramish a wajen, bai sake cewa ko uppan ba.

"Yanzu kun cire bombs ɗin ne?".
Abbie ya sake jefa mashi tambaya. Wato idan baka da hakuri sosai ba zaka iya zama inuwa guda da Ramish ba, dan zai kasheka da takaici ne, sai ayi mashi magana goma bai amsa ɗaya ba, to in ba mai hakuri ba waye zai iya jure wannan walaƙanci fisabilillahi?.

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Abbie Yah Ramish wannan ai wayar Leesharh ne!".
Sharifat ta katsesu da faɗar hakan, ta yi maganar cike da tashin hankali maras misiltuwa, sannan ta yi maganar tana miƙewa tsaye haɗe da dafe saitin zuciyarta.

Ramish and Abu Abdussalam har suna rige rigen kai kallonsu a kanta.

A miliyan ita ma Leesharh ta miƙe tsaye.............. Wani irin zufa yana kara tsananta a saman face ɗinta, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi, jikinta sai wani irin kermar wahala yake yi. Da kyar ta haɗiyi wani irin azabbabben wahalallen yawu mai wuyar wuce maƙogwaranta.

Miƙewa tsaye shima Abu Abdussalam ya yi kallonsa a kan Sharifat da kwayar idanunta tamkar zasu faɗi ƙasa saboda zarosu da ta yi!.
Baiwar Allah jikinta har kerma yake yi, bata taɓa tsammanin makamancin hakan ba ko a mafarki.

Ramish kam yana zaune bai miƙe ba, idan ka kallesa in the first place zaka yi zaton Sharifat yake kallah, amma kuma Leesharh yake kallo saboda ya gano abin da yake san ganewa, dama shi tin ainahi bata kwanta mashi a ransa bane yasa ya ce kada ta sake zuwa part ɗinsu, sai ga shi an kamata red handed.

My people's me kuke tinanin zai faru a wannan waje? Akwai tashin hankali kuwa!!. Rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya

===========================🔥

••••••••••••••••JIMETA🔥••••••••••••••••

Tsawon kwanaki biyu babu Jaish babu labarinsa, tin bappa yana sa tsammanin zai waiwayesu har ya dai'na, yanzu har ya fara rage damuwansa a kan haka, bawan Allah sai dai har ƴar rama ya yi saboda damuwa.

A ɓangaren Nenne kuwa farinciki kamar ba zata mutu ba, burinta ya gama cika rayuwar Mahnoor ya lalace, ta zama karamar bazawara, bata wuce 15 years ba amma ta zama bazawara, abin ya yi wa Nenne da gwaggo mugu mugun daɗi.

Shi kam hamma Faisal ya kafe a kan lallai tin da Jaish ya koma in da ya fito to shikenan a mayar mashi da matarsa Mahnoor, har da cewa dama ai Jaish aljani ne ba mutum ba, dan haka tin da ya koma duniyarsu na aljanu ai ba dawowa zai yi ba, so shi yana nan a kan bakarsa na zancen Mahnoor.

Ya bi ya tayarwa da kowa hankali, shi lallai a yanke auren Mahnoor da aljani Jaish a bashi ita ya aura.

Tin bappa yana kallan hakan a matsayin shirme har ya fara yarda da hakan ce kawai mafita, in ba haka ba Mahnoor ta shiga uku a wannan ƙauye, abin ku da ƙarancin wayewa da rashin ilimi, zasu sakota ne a gaba da zage zage da kananan manganganu kamar ita ta ɗaurawa kanta, barema da abin ya haɗu da bappa ya hana nasu ya baiwa bare, to wlh ba zasu barta ta yi zaman lafiya har ta ji daɗi a ranta ba, zata kai ta kawo fita ma sai ta gagara yi.

So gudun takura mata yasa bappa ya fara tunanin Arɗo ya kashe aurenta da Jaish kawai a ɗaura aurenta da Faisal hakan zai sa ta samu sanyi da rayuwar farinciki.

A ɓangaren ita kuwa Mahnoor, kwananta biyu a gidan Arɗo wajen kakarta Inna, kullun ɓuya take yi ta yi ta zuba kuka babu kakkautawa, tana tsananin san mijinta, sai ma yanzu da ya yi mata nisa ta gane ashe shi ne farincikinta.

Wlh cikin ƙanƙanin lokaci ta yi wani irin zabgewa ta rame, harta wannan gurun wuyar tata da Jaish yake gani ya burgesa yanzu tsokar wajen ta zabge saura kashi.

Mahreen da Jaish yake ba mijinta bama ta rame saboda damuwa da kukan bappa ya dawo mata da Hammanta, kunsan ta saba da shi, bare kuma Mahnoor da ita kaɗai tasan ya take ji a ranta, ya saba da yi mata abubuwa dayawa, yanzu har kasa yin barci take yi.

Hankalin bappa ya gaza kwanciya na komawarta gidan Arɗo, dan haka yau ya shirya tsab zai je ya ɗauko. Ba zai iya yin nisa da ita ba.

Zaune take a tsakar gida ta buga uban tagumi, tana sanye da kayan fulani, ta yi wanka tsab, sai dai da ganinta zaka san bata cikin walwala, fuska babu annuri, ta buga uban tagumi.

Idan ka kalleta zaka yi zatan tana kallan Inna dake ta faman shanya masara a tsakar gidan ne, amma kuma ba haka bane, ta luluƙa duniyar tunani ne.

Sallamar bappanta ya dawo da ita cikin hayyacinta. Tana ɗaura idanu a kansa bata san lokacin da ta rushe da kuka ba.

Da gudu ta tashi ta nufesa, dik kunya irin tata yau bata san lokacin da ta ce mashi. "Bappa tare da hamma kuka zo?"

Miƙewa tsaye Inna ta yi daga duken da take tana shanyar masara, tsakanin tausayin jikar tata ce ya kara kamata. Shiru ta zuba kasu idanu yana kallonsu, ji take yi kamar ta matsa masu kwallah.

Bappa ya rasa abin faɗe, bashi da kwarin gwiwar iya sanar da Mahnoor ba tare da Jaish yake ba, dama ya zo da kwarin gwiwarsa ne zai sanar da Inna za'a mayarwa da Faisal matarsa tun yadda yaga sun ɗauki Jaish da wuya ya waiwayesu, sai kuma ya cikaro da wannan kuka da take yi na neman Jaish, anya zai iya sanar da ita wannan magana kuwa?.

Ya jefawa kansa tambayar, jikinsa dik ya yi mugun sanyi. Mahnoor ta rungume shi tana ta kuka.

Da gudu Mahreen ta fito daga ɗakin Inna, kai tsaye da gudu ta nufi bappa tana faɗin. "Bappa ina Hammanu yake?".

Ta ƙarisa maganar idanunta cike tab da kwallah. Riƙota ya yi kawai ya runguma bai iya furta ko kala ba.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





Ta ƙarisa maganar idanunta cike tab da kwallah. Riƙota ya yi kawai ya runguma bai iya furta ko kala ba.

Inna da sun gama jikata da tausayi ne ta juya zata nufi ɗakinta dan ba zata iya ganinsu ba. Katseta bappa ya yi ta hanyar ɗaga mata gaisuwa.

A daddafe ta amsa mashi tare da wucewa cikin ɗaki da sauri. Tana shiga ta zauna bakin gado tana addu'ar Allah Ubangiji ya sa kada Mahnoor ta gajesu, dan tun tasowar Inna a cikin kalubalen rayuwa take har Allah yasa ta auri Arɗo, ta taso ne a hannun kanin mahaifinta, ta fuskanci wahala wajen matarsa, shiyasa kuka ga tana da hakuri, baiwar Allah ta wahala ne, ta sha fama a gidan.

Bayan aurenta da Arɗo ma bata huta ba, gwaggon Nenne har kusan haukatata ta yi a kan kishi a cikin wannan gidan, har yau har gobe kuma basu barta ta huta ba, suna bibiyar rayuwarta da sharri, dan ta tsaya da addu'a ne Allah yake kareta, amma ta sha bakar wahalar da ba zaku so ku ji tarihin ba, yawo a kan bola ne kawai bata yi ba, amma wlh haka kawai zata zauna ta yi ta ihu babu abin da aka yi mata, sai ta rinƙa jin namar jikinta yana wani irin masifar tauna tamkar an ɗaurata saman wuta.

Dik wannan azaba ta jure, dan gara mata gidan Arɗon a kan gidan kanin baban nata, ga shi ita marainiya ce ba uwa ba ba uba ba, dik ta shanye wannan har Allah ya bata cikin mamar Mahnoor, nan ma ta ci wahala kamar ta mutu, da kyar ta sha maman Mahnoor ta zo duniya.

Ita ma tin zuwanta duniya take shan wahala har ta koma ga Allah, aurenta da bappa kullum cikin ƙunci da kuka take, ya wahalar da ita har Allah yasa ita ma ta haifi Mahnoor.

Ita ma Mahnoor tun farkon zuwanta duniya take shan wahala har zuwan Jaish cikin rayuwarta, ta ɗan samo sassauci kuma ace zata sake komawa cikin wahala? Abin da taɓa zuciya matuƙa.

Sosai hawaye ya wanke fuskar Inna. Tsabar bakinciki da karayar zuciya har ta kusa furta saɓon Allah, saura kaɗan ta ce Allah baya sansu ne yake ta haɗasu da bala'i.

Sai ta yi saurin kame bakinta tana furta istigifari. Allah sarki Allah baya jarabtar wanda baya so, dik wanda ya tsinci kansa cikin jarabawa ya ɗaga hannu ya godewa Allah ya kuma roki Allah da ya bashi ikon cin jarabawar, shi ne kawai ya dace da mumini, idan kaga baka shiga kalubalen rayuwa ma to wlh ka binciki imaninka da saura!.

Ganin Inna ta shige ciki yasa bappa ya kama hannun ƴaƴan nasa suka nufi hanyar gida yana jin raɗaɗi a ransa.

A hanya suka ci karo da Mairo zata shiga gidansu da yake kusa da gidansu Arɗon ne.

Har kasa ta tsugunna ta ɗaga mashi gaisuwa. Cikin ba daɗi ya amsa. Sarai ta kula da babu farinciki a tattare da shi ko miskala zarratin, ga kuma su Mahnoor suna kuka, dan haka sai ta ce dan Allah in ba damuwa tana san yin magana da Mahnoor and Mahreen.

Bai musa mata ba ya sake hannunsu ya ce su je wajenta. Da yake Mahnoor kam ta saba da ita kanwar mahaifiyarta ce sai bata yi gardama ba, tana zuwa ma ta rike hannunta tana cigaba da kuka.

Cikin gida Mairo ta wuce da su, shi kuma bappa ya samu waje a karkashin wata bishiyar kuka ya zauna yana jiransu.

Sun shafi good 30 mins a cikin gidan ka fin su fito, dikkaninsu sun daina kuka, fuska ba yabo ba fallasa, da alama Mairo ta iya kula da yara, tuni ta yi masu dabara sun yi shiru.

Ba karamin daɗi bappa ya ji ba, bawan Allah har da sauke nannauyar ajiyar zuciya, ya ji ya kara samun kwarin gwiwa a kan aurenta, sai ya ji ma bai ga abin ɓata lokaci ba, gobe dole ya kamo shanu ɗaya ya kawowa Arɗo a kai gidansu matsayin sadaki, tin da ta sanya mashi yar marainiyarsa farinciki ai dole ta sanyaya mashi rai.

Dole ayi wanna aure da wuri ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji.

Ita ma ta lura da tabbas ya ji daɗi, sosai ta ji ta yi farinciki da Allah yasa ta sanya shi jin daɗi, da alama ita ma tana son shi sosai.

Sallama suka yi mata ya riko hannun su Mahnoor suka wuce gida. Ya so su tsaya hira da Mairo ko shi ma zai samu sassaucin zogin da zuciyarsa take yi mashi, amma kash, saboda su Mahnoor da suke a tare da shi yasa ya ce mata sai dare yana zuwa.

Daga haka suka wuce gida.

Nenne na zaune a tsakar gida ta baje tana cin ɗinya da addu'a suka iskota, ta yi zaman ƴan bori a kasa tana wani cika tana batsewa.

Ko ci kanki bappa bai ce mata ba ya wuce zai shiga cikin ɗakinsa rike da hannun ƴaƴan nasa.

"Kwairaga magana nike san yi da kai!". Cike da isa da gadara ta yi maganar, yau babu bappan Mahreen da ake cewa, rashin mutuncin ta motso kwairaga kai tsaye aka kira.

Ko a gefen takalmarsa, tamkar bai san da wata halitta a wajen ba ya wuce zai shi ga ɗaki, shi fa namiji kunsan dik in da yake hakan nan dai yake hali baya canzawa, to shi ma fa bappa namiji ne, kun san idan maza zasu kara aure har wani sabon iskanci da waƙalanci ƙwaƙwalensu take karowa, su rinƙa jin kansu a saman iska, sai su ji zasu iya yin komai a kan wanna aure nasu, kamar basu taɓa yi ba, ayi ta rawar kafa ana wani kauɗi kamar angon kare, to yaseen haka suke, a jininsu abin yake.

Idan baki da wayau kika biye masu kika kulasu takaici ya sa zuciyarki ta buga, idan kuma kina da wayo kin san in Allah ya kaddara sai an yi sai ki bawa iska ajiyar ɗan albarka, yana kauɗinsa ki yi kamar baki san da halittarsa a cikin gidan ba, wlh da kansa zai damu sosai, ya yi ta jin kamar ya fasa aure, zai ji kamar ba shi ba, dik wani kauɗi zaki ga ta ragu.

Amma in kika nuna ɓacin rai yaseen kara wa zai yi dan ya shaƙa maki takaici. To kun dai ga bappa ya karo sabon walaƙanci, da dik iskancin da Nenne take yi mashi yana daurewa baya kin yi mata magana, amma yanzu ina ai banza yake bawa ajiyarta, bata isheshi ya ɗaura idanunsa a kanta ba, ango na Mairo bada kanka a sare ba............😅

Mu dai ba abin da zai hana mu zuwa wanna biki, ai ko dan mu je a kayar mana da shanu a yanka, mu ci nama mu kora fura da nono mu godewa Allah dole fa mu je.......... Nenne sai dai a mutu idan za'a mutu.

Ganin bai kulata ba yasa ranta ya yi matuƙar ɓaci, kamar wata aljanar ruwa ta miƙe fuuuuuuu kafafu kamar na shamuwa sai cikin ɗakin nasa.

Daidai lokacin ya ciro kayan Jaish dake maƙale a bayan kofa ya miƙawa Mahnoor yana ce mata ta ajiye wannan kaya a ɗakinta na mijinta ne.

Kamar wata walkiya sai ganin Nenne suka yi a tsakaninsu. Sai da Mahnoor ta tsorata ta miƙe zata gudu, baiwar Allah ta saba shan ukubar Nenne, to a tinanina dukanta Nenne ta zo yi shi ne zata gudu.

Wuyar rigar bappa Nemne ta riƙo, ko tsoron Allah babu bare kunya, a gaban ƴaƴansa ta fara jajjaga mashi jajjagen masifa da bala'i kwando kwando kamar wanda ake yi mata wahayinsu daga duniyar shaiɗanu.

Riko hannun Mahreen Mahnoor ta yi tare da ɗan cewa. "Zo mu je gidan Inna Rabi". Mahnoor yarinya mai hankali da sanin yakamata!.

Mahreen da faɗa a jininta yake ga kuruciya a kai ne ta ce. "Ke ni babu in sa zanje Adda Mahnoor, ki bari in taya bappa faɗa mu ci uban Nenne".

Ai daga bappan har Nenne basu san lokacin da suka dawo da kallonsu a kanta ba. Mahnoor da tsabar zaro ido tamkar kwayar idanunta zasu faɗo kasa ne da kyar ta ce.

"Mahreen kina da hankali kuwa? Kin san me kike faɗa kuwa?".

"Nasani mana, baki ganin Nenne ta kama bappana da faɗa ne? Ni zan taya shi mu mata shegen duka, ni kaɗai ma na isheta ba sai bappa yasa hannu ba".

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun". Shi ne kawai abin da Mahnoor ta iya sake faɗa. Shi kam bappa ya rasa abin faɗe, wannan wace iriyar tarbiya Nenne ta bawa ƴarta? Ko da yake maganinta kenan ai, ba ita ta lallata Mahreen ɗin da faɗa ba, tun tana yarinya take yi mata huɗubar dik wanda ya daketa ta dage ta rama, ai ga shi yanzu za'a daki bappanta zata rama mashi, harda uban wanda zata dake shi ɗin za'a ci wato Arɗo kenan.

Sai yanzu Nenne ta gane Mahreen da take kauna take fifitawa fiye da komai ta fi kaunar ubanta a kan ita. Mata kalubale gareku, ku so ƴaƴanku duniya ta kisu, kai har Allah da manzonsa ba zasu yi alfahari da su ba, idan kika daure kika kawar da kai kika danne kika basu tarbiya mai kyau kika kisu sai duniya ta sosu Allah da manzonsa su so su.

Da karfi Mahnoor ta ja hannunta tare da tsawatar mata a kan ta zo su tafi. Tana kwaɓe fuska ta bi yar uwar tata, sai mita take yi a kan ita a kyaleta su kwashi ƴan kallo da Nenne a kan bappanta. Sai kwaɓar bakinta Mahnoor take ya faman yi har suka fita.

Suna fita bappa ya dawo da kallonsa a kan Nenne da ta saki baki tana ganin ikon god, waye ya ce maki Allah wasa ne, hmmmmm kaɗan ma kika gani.

"Zaki iya sakeni? Dan ina da abin yi ne!". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga kanta, sam yanzu baya san tashin hankali, dan baya san abin da zai mayar da shi ruwa wajen dukan mata kamar a baya kan maman Mahnoor.

Nenne da jikinta ya yi mugun sanyi ta kasa ko motsawa ne ta tsare shi da ido ba tare da ta sake shi ɗin ba.

Hannunsa yasa ya kwace wuyar rigar yasa, ba tare da ya sake furta uppan ba ya sa kai ya fice waje ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login