Showing 309001 words to 312000 words out of 403653 words

Chapter 104 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

70

alkawari, in ya yi mata hakan ita kuma ta yi mashi alkawarin Ronnie ba zai taɓa shiga wata damuwa ba izinin Allah.

Jama'a ku tafawa addu'a, lallai ne addu'a bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, da izinin Allah addu'ar Sweetie a kansa ta karɓu, black heart ɗin ta fara sassautawa!.

Jinjina mata kai ya yi alamar ya yarda da batunta tin ma bai ji wani irin alkawari bane, Ronnie amanarsa ne, kun san da cewa amana mahaifinsa ya bar mashi Ronnie? Kun san da cewa sai da ya rokesa da kada ya bar hawayen Ronnie ya zuba a banza?. Kun san da cewa kafin mahaifinsu ya rasu ya yi wa baban nasu alkawarin in dai yana numfashi to ba zai taɓa barin hawayen kanin nasa ya zuba ba? Shiyasa kuke ga zai iya aikata komai a kan kanin nasa, kuma yana bala'in sansa na haƙiƙa shi ma, ba wai dan iya alkawarin da ya ɗauka bane yasa yake kula da shi, yana kaunarsa sosai.

Ɗaga ƴan kafafunta ta yi tana san kai tsawonsa dan ta yi mashi raɗa a kunne, sai dai ina, bata iya kaiwa tsawonsa ba, ya fita nesa ba kusa ba, yana da tsawo sosai. Ganin hakan yasa ya rage tsanwonsa ya ɗan rankwafo kanta, hannu tasa ta saƙalo wuyansa kafin ta gwada sake ɗaga kafa ko zata kai. Sai dai kash bata kai ba, hakan yasa ya ɗagata cak sai saman lion chest ɗinsa, hakan ya bata damar kwanto kanta a saman shoulder ɗinsa, ta kai ɗan bakinta saitin kunnnesa, nan ta fara yi mashi raɗan yarjejeniyar da zasu yi kafin ta yi mashi aikin kula da Ronnie, idan ya aminta tabbas zata kula da Ronnie sosai wajen sanya shi farinciki.

Hakika maganganunta sun zo da tsauri, sai dai kuma farincikin Ronnie ya fi mashi komai, kuma babu in da Ronnie ɗin yake samun farinciki na wuce misali face a wajenta, dan haka yazamar mashi dole ya aminta da wannan yarjejeniya in ba haka ba akwai matsala. Shiru ya yi yana tinanin ya amince ko kuwa ya daure ya juri tashin hankalin da Ronnie zai shiga?. A wannan hali Ronnie ya shigo wajen ya samesu, fuskarsa ɗauke da damuwa matuƙa ya ƙariso in da suke.

Ai yana sauke kallansa a kan yayan nasa da Sweetie bai san time da ya saki cool murmushi ba, sun yi matuƙar burgesa, da sauri ya tsugunna a gaban pool ɗin, cikin sanyin murya ya ce. "Wow you guy's looks so very cute and amazing"....... Maganarsa ya fargar da Black Tiger har ya yi saurin zare kallansa daga kanta, kamar wani maras gaskiya ya yi saurin saketa ya kuma ɗan yi ƙasa kaɗan ya kara lumewa a cikin ruwan kaman mai san ɓoye wani abin. Ita kuwa, da tsantsar tashin hankalin da take ciki yaki ɓoyuwa a kan face ɗinta ne ta juyo da kallanta ga Ronnie, tamkar zata yi kuka, ta ƙasa yin magana, dan yanzu ganinsa yasa wani irin tausayinsa ya kamata.
Take yanayin face ɗin Ronnie ya canza, dan ganinta cikin damuwa bai yi mashi ba, kamar mai tsoronta ya ce. "Lovely sis big bro ya yi maki wani abin ne?". Ya yi maganar yana satar kallan Black Tiger ta wutsiyar ido.

Kai kawai ta iya girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba. "Big bro me ka yi wa lovely sis ɗita?". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar. Banza da shi Black Tiger ya yi, sai ma ya kara lumewa cikin ruwan, tamkar bai san da su a wajen ba, da alama kuma akwai abin da baya san su gani a jikinsa shiyasa ya yi ƙasa a cikin ruwan........ Ronnie fa ya zo da kokensa ne a kan bai ga iyayen Floris ba, ya tambayi mutanen birnin kuma kowa ya ce mashi bai gansu ba, shi ne ya dawo wajen yayansa da kokensa dan ya nemo mashi su, amma yana tarar da su cikin wannan yanayi ya tsinci kansa a cikin farinciki maras misaltawa.

Rarrashin Sweetie ya hau yi yana ce mata ta yi hakuri zai rama mata idan ma yayansa ne ya yi mata wani abin, ita dai da okey kawai ta amsa mashi, amma na ciki kam yana ciki. Sai da ya tabbatar ya sanyata ta yi murmushi, sannan ya juya ya ce da Black Tiger. "Big bro ina iyayen Floris?". Ai Sweetie bata san lokacin da ta ce mashi. "Sun gudu sun bar birnin nan wai saboda big bro ya kona masu ƴan uwa".

Ɗan zaro idanu Black Tiger ya yi jin ta fitar masu da hanyar da bai zata ba, dama yana tinanin abin faɗawa Ronnie, gaskiya Sweetie she was very smart, ya jinjinawa ƙwaƙwalwarta wajen iya fito da mafita cikin ƙanƙanin lokaci, sannan ransa ta sanyaya matuƙa da samun mafitarsu. Shi kuwa Ronnie ido ya zaro, kamar zai ɗaga murya, sai kuma yasa kukan shagwaɓa tare da cewa shi lallai bai yarda ba! Dole big bro ya nemo mashi in da suke, dan shi yana kaunar Floris, yana san ta dawo su cigaba da rayuwa kamar da. Nan ne fa Black Tiger ya samu damar ce mashi zai nemo mashi su soon ya kwantar da hankalinsa, yana magana yana satar kallan Sweetie da ta tsare lip's ɗinsa da kallo.

Ajiyar zuciya Ronnie ya sauke, ya ji sanyi a ransa za'a nemo mashi su. Sweetie ce ta riko hannunsa ɗaya cikin nata, kamar mai raɗa ta ce matso ka ji wani abu lovely bro. Matsar mata da face ɗinsa ya yi yana ɗan murmusawa. Matsowa ta yi dab kunnensa, raɗa ta fara yi mashi tana sakin murmushi,. A hankali hankali murmushin dake saman face ɗinsa ta fara faɗaɗa alamar kalamanta akwai sugar, suna shigarsa yadda yakamata. Satar kallansu Black Tiger ya fara yi yana mamakin irin shakuwar dake a tsakaninsu, a yanzu fa Ronnie ya fi farinciki idan yana tare da ita sama da idan yana tare da shi, abin akwai mamaki. Tsabar daɗi da murnar jin kalamanta bai san lokacin da ya afka cikin ruwan ba shi ma, a jikinta ya faɗa hakan yasa suka yi kasan ruwan, dan bata da karfin ɗaukarsa. Shi dai Black Tiger abin ya birgesa matuƙa, suna kashe shi idan suna tare!.

Juyawa Ronnie ya yi cikin sauri ta dawo saman jikinsa, sannan suka ɗago saman ruwa, take ta fara jan numfashi da karfi karfi, saboda ta dannu kam. Riketa Ronnie ya yi yana faɗin ta tsaya ya hura mata numfashinsa dan nata ya daidaitu. Sai dai bai kai ga yin hakan ba take ta dawo daidai tamkar wadda aka yi wa magic, runguneta Ronnie ya yi yana faɗin sorry a gareta. Ɗan rungunesa ita ma ta yi kafin ta amsa mashi da ba komai. Cikin wasa ya ce. "Let play a game". Ɗan zaro idanu ta yi, game kuma a cikin ruwa, ta jefawa kanta tambaya a cikin zuciya.
Tana can tana tinani Ronnie ya zaro hanki (handkerchief) daga aljahinsu, dik ta jiƙe da ruwa, ɗaure mata idanu ya yi kafin ya saketa, ya sumbaci lallausan kumatunta sannan ya ce to ta kama shi a cikin ruwan idan ya kirga one to ten. A cikin ranta ta ji da biyu Ronnie ya ce su yi wannan wasa, amma ba zata ki yi ba ko dan alkawarin da ta ɗaukawa yayansa na sanya shi farinciki na musamman, so zata yi dik abin da yake so matsawar bai saɓawa shari'a ba.

Cauting from one to ten ya yi kafin ya lallaɓa ya gudu bayan Black Tiger ya ɓuya, sannan ya ce mata let's go. Lalluɓarsa ta fara yi tana tafiya a hankali. Shi ma a hankali hankali ya baro bayan Black Tiger ya matsa ya dawo ta bayanta, ya zamana tana tafiya yana biye da ita a baya, sam bata jisa ba, gabaɗaya hankalinsa a kan Black Tiger, ya tsare yayan nasa da kallo kamar mai nazarin wani abin. Sai nemansa Sweetie take yi tana zagaye cikin ruwan, ga shi ruwan ya fi karfinta, dan har wuya ya kai mata, dan dai ba ruwan gudu bane, da ba zata tsira ba. Ta sha kewaye a wajen bata ji alamarsa ba, dab kusa da Black Tiger ta tsaya, suna fuskantar juna ba tare da ta sani ba, Ronnie na bayansu, a shagwaɓe sosai ta saka kuka tana faɗin. "Ni lovely bro ka zo ka kwance mun wannan abin, ka ɓuya nakasa ganinka..........." Bata kai karshen maganar ba Ronnie ya tureta da karfi ta tafi sai saman lion chest na Black Tiger.

Murmushi ya saki kafin ya ce. "Dama a manne da juna na sameku, ni na rabaku, yanzu kuma da zan tafi shi ne na mayar daku yadda na ganku". Yana kai karshen maganar ya yi zafan fita daga cikin ruwan wai dan ma kada Black Tiger ya kama shi, abin gwanin ban dariya kuma gwanin birgewa. Yana fita bai dakata ba ya yi gaggawar barin wajen ya koma cikin bedroom ɗin Black Tiger. Ita kuwa Sweetie ƙoƙari kwace abin dake idanunta ta yi dan ta samu gani, sai dai ta ƙasa, saboda yadda kuka san padlock aka sanya aka datse hanki ɗin, yaki kwancuwa ko kaɗan.

(Anya ba Black Tiger ya rike shi ya hana shi kuncuwa ba kuwa? Ɗan duniya ba! Ka gansa kaman wani salihi, ɗan rainin wayo.😅🥱)

"Big bro please remove this thing for me". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar. Kamar babu Black Tiger a wajen, ya yi banza da ita idanunsa a kan face ɗinta, kaman mai nazarin wani abin. Laluɓe ta fara yi tana ɗan tattaɓa jikinsa dan ta tabbatar da yana wajen ne ko dai baya nan, ta yi magana without reply, shi ne take zaton ko dai baya wajen ne.

Lokaci guda ya yi wani danko hannunta ɗaya cikin zafa, ba komai yasa hakan ba kuma face a garin laluɓenta take ƙoƙarin sake capke mashi hero kamar dai ta ranar..... Ajiyar zuciya ta sauke jin ya damki hannunta, hakan yasa ta fahimci yana wajen kenan. Can ƙasa ta tsinkayo lion voice ɗinsa yana faɗin. "Na yarjewa yarjejeniyarki, amma kada ki wuce gona da iri".

Yarjejeniyar me kuke tinanin ta ce su yi? Sweetie akwai wayo sosai wlh, da alam tarko ta ɗana mashi. "To shikenan na yarda, amma yanzu dai kwance mun wannan abin". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

"Hakan baya cikin yarjejeniyarmu, and ai bani na ɗaura maki ba". Ya faɗa a sanyayye sosai................ Ɗan rainin wayo, so yake ya yi ta kalle mata fuska kada ta san ya kalla, shiyasa ya ce ba zai kwance mata ba, saboda ba kara mun kyau ta yi ba a yadda ruwa ya jiƙata, gashin kanta ya kwanto har face ɗinta, lip's ɗinta sun kara kyau matuƙa saboda ruwa da ya taɓasu, gashin gaban goshinta sun kara kwanciya luff, ko makiyinta ya ganta yasan ta yi kyau over, kuma sai ya shagala da kallonta bare kuma shi Black Tiger da ba kiyayya suke yi ba, bashi da wata matsala da ita, hasalima yanzu yana san ta kasance da su dan ya lura kaso 60 cikin ɗari na farincikin Ronnie yana tattare da ita, so bashi da wata matsala da ita yanzu...... Ni kuwa nace ba dole ta zama farincikin Ronnie ba tun da ta bashi kalmar shahada, ta janyo shi cikin haske, dole ya yi farinciki idan yana tare da ita.

"Please mana our big bro, nasan baya cikin yarjejeniyarmu, amma kuma ai akwai batun kada ka bari wani abin cutarwa ya zo kusa da mu ko?". Ta faɗa tana ƙoƙarin kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata. "Wannan ai ba abin cutarwa bane, da na cutarwa ne Ronnie ba zai ɗaura maki ba". Ya yi maganar tare da sakinta. Yana saketa tamkar wadda aka turo haka ta tafi ta faɗa saman lion chest ɗinsa again...... "Allah abin cutarwa ne shi ma". Cikin muryar kuka ta yi maganar.

Banza da ita ya yi, bai da niyar kwance mata, ɗan rainin wayo dan bai gaji da kallan madarar kyan da Allah ya yi mata ba, sai ya fake da cewa ai ba shi ya ɗaura mata ba, dan haka ta nemo Ronnie ya kwance mata, har da dagewarsa irin da gaske yake yi shi fa. Kamar zata yi kuka ta bar jikinsa ta fara laluɓar hanyar fita. Allah ya bata nasara ta samu ta fito, idanunsa a kanta bai hanata ba, haka ta fara laluɓe har ta isa wajen stair case, ga ruwan dake zuba a jikinta, bata san ta isa wajen ba, tana ɗaga kafa ta sauke sai ta tafi gabaɗaya ta yi ƙasa, tin daga kan step na farko ta yo kasa har karshe, dik kuma yana ganinta bai taimaka mata ba, bai kuma yi amfani da magic wajen tsayar da ita ba, ya barta ta isa ƙasa dik ta bubbuge jikinta, har ta dan ji ciwo a hannu. Azaban da ta ji ne yasa ta saki ihu mai sautin da ya ja hankalin Ronnie dake zaune saman sofa yana shan tea mai zafi sosai.

Da gudu ya ajiye cup ɗin a saman table dake gabansa ya nufota yana tambayarta lafiya kuwa. Kuka ta saka mashi kawai ba tare da ta yi magana ba, duƙawa ya yi ya ɗauketa cak ya yi waje da ita, har ya canza kayansa izuwa na sport, sarkin san wasanni ba. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma da ita, a nan ya kwance hanki ɗin ya yi ta rarrashinta har ta yi shiru, sannan ya ce ta je ta yi wanka ta canza kaya, ba musu ta bi umarninsa. Yau da ta yi wanka irin shigar mutanen birnin ta yi, wato umbrella gown mai maɗauri a tsakiya, ta yi kyau sosai, gashin kanta saboda samun kwanciyar hankali ya kara tsawo sosai, har ya kusa zarce mazaunanta, ya kuma kara tura kala sosai. Kwace saman bed ta iskosa yana kallan chandelier ɗin ɗakin nasa, a gefensa ta zauna, cike da nuna kauna ta ce. "Lovely bro ina san zuwa church ɗinku".

Zaro idanu ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. "Mezaki je ki yi?". Ya yi maganar tare da miƙewa zaune suna fuskantar juna. "Babu kawai ina san zuwa ne in gani". Shiru ya ɗanyi kafin ya ce. "To gobe idan kika dawo daga school zamu je a tare by 4:00 ko 4:30 haka". Sosai ta ji daɗin amincewarsa, cike da murna ta matsa ta sumbacesa a kumatunsa, siririn murmushi ya saki kafin ya ce. "Kin san wani abu sister?". Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata sani ba. Tana ta sakin ƙayataccen murmushi.
Kashe murya sosai ya yi kafin ya ce. "Ina san ganinki a tare da big bro, kuna kyau sosai, dan Allah ki rinƙa kasancewa a tare da shi, kinga yanzu kin fara canza mana shi ko?". Shiru ta ɗan yi alamar kamar bata ji daɗin maganar ba, sai kuma ta saki siririn murmushi kafin ta bashi amsa da. "Ina fatan ya sauya, ya canza ya zama musulmi, ina yi mashi kwaɗayin rahamar Allah sosai". Ɗan zaro idanu Ronnie ya yi. "Kina nufin ba kya san yayana? Dik abin da kike yi mashi kawai kina yi ne dan ya musulunta?". Jinjina mashi kai ta yi alamar ba shakka haka ne, sannan ta ɗaura da cewa. "Ko kaɗan babu soyayyarsa a rai'na, soyayar Kamran ce kawai a raina, and na fi jin sonka a rai'na ma sama da yayanka, ina jin yayanka tamkar ɗan uwana ne na jini wanda ina ga hakan ce tasa bana jin sonsa na soyayya a rai'na, kasan wani abu?".

Kasa bata amsa ya yi ko ya motsa daga in da yake, ya kafeta da ido mamaki kamar ta kashe shi, shi dik tinaninsa tana san yayansa shiyasa yake tayata yakin neman soyayyarsa, bai san ita wanda take so ma daban ba ne...............Dik da bai amsa mata ba hakan bai hanata cigaba da yin maganar da take da niyya ba. "Yayanka ya haɗa dik abin da kowacce mace zata so a duniya, nasan kasan da cewa komai isar mace idan ta gansa sai ta faɗa mashi, amma ni kaunarsa nike a matsayin ɗan uwa na jini haka, soyayyar Kamran ne kawai a rai'na".

Shiru ya yi na almost 3 mins kafin ya nisa, sannan ya saki ƙayatattcen murmushi. "Sister a labarin da kika bani kin ce mun Kamran ma ba musulmi bane ko?"............. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. "To meyasa baki taɓa tsayawa ki jajirce a kansa lallai sai ya musulunta ba? Ko shi baki yi mashi kwaɗayin rahamar Allah ne?"....... Shiru ta yi kamar mai tinanin abin faɗe, da alama ya ɗaureta da magana.

"Baki da amsa ko? Dama ai ba zaki iya bani amsa ba, amma ni zan baki amsa, dalilin da yasa kika tsayawa big bro kika zage kina san ganinsa a cikin ni'ima ta Ubangiji ba komai bane face so, shi ne wanda kike yi wa so na gaskiya, dik wanda zaki so to a bayansa ne........." A gaggauce ta tari numfashinsa da cewa. "No Ronnie, ko ɗaya ban taɓa san yayanka ba, in dai kaunarsa". Jinjina kai ya ɗan yi. "Kin san soyayya ne ma da zaki iya banbanta wanda kike kauna da wanda kike so?". Ya tambaya kamar shi ma ya san me so ɗin, da dalilin ɓacewar Floris daga garesa ne fa ya fara fahimtar me soyayya, amma har ya fara zaƙewa zai nuna shi ya sani.

Da sauri ta jinjina kai kafin ta amsa da. "Niko na san soyayya, soyayya ai ayoyi gareta a cikin Alqur'ani mai girma, idan ka ɗauki suratul Ali Imran sura ta uku aya ya 31 da ɗaya, wanna aya tana magana ne a kan ainahin soyayya ma, wato soyayyar Allah ga bayinsa, sai kuma cikin suratul Ar rum, sura ta 30 aya ta 21, wannan tana magana ne a kan soyayyar ma'aurata wato mace da namiji, kazalika cikin suratul ma'ida, sura ta biyar aya ta 42, nan ma magana ce kan kauna, cikin suratul Maryam, sura ta 19 aya ta 96, Allah yana magana a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login