Showing 15001 words to 18000 words out of 403653 words

Chapter 6 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

22

na ɗaure da wata dankareriyar Rolex-pnd wanda a kalla kuɗinsa ya kai 18 million dollars. Sai tashin kamshin perfume ɗin Mf yake yi, wanda kuɗin wanna perfume ɗin ya wuci tunaninku.

Wayarsa ya ɗauka ya nufi waje a gaggauce, ko kallan abin da Heleena ta kawo bai yi ba, ya fice.

Kamar dai yadda dad ya saba saka mashi takunkumi na idan zai fita sai da tsaro gaba tsaro baya, hakance ta kasance, da ya ce wa dad shi fa yanzu ba yaro bane dan Allah su kyalesa ya shakata, shi jarumi ne ba rago ba.

Da sauri mom ta karɓi zancen da cewa shi yaro ne kuma dole ta saka idanu a kansa.

Ni dai nace mom bata san dik saka idanunta a kansa na banza bane, domin kuwa shi da dad dai sun mata wayo, sun gwada mata kwarewa suna can bayan fage suna sharholiyarsu da rocket.

Kamar zai yi masu gardama, amma farincikinsu shi ne nasa, dan haka ya raba masu sumbatar kauna a kumatu tare da wucewa ya nufi jerin gwanon motocin da aka jera domin shi.

Sai dai kamar kullum gidansa ya je ya baro securitys ɗin ya ɗauki tsadaddiyar motarsa ya wuce World ɗinsa, wato duniyarsa, dan yana bala'in kaunar wannan rocket factoryn nan nasa fiye da komai, nan ne duniyarsa, yana alfahari da baiwa da ilimin da god ya bashi.

Yau ta kama saturday ne, garin ya yi shiru sosai, kowa yana makale a gida, ga wani uban sanyi dake zuba kamar ana watso dissa, a haka kuma bai sanya jacket a gida ba sai da ya je gidansa ya ɗauki wani katan puffer jacket ya sanya.

Weekend ba aiki ba zuwa office, kowa yana cikin gida, su kuma a yau ne suke gwada lunching manya manyan makamansu da suka ɗauki tsawon watanni suna haɗasu, sun yi aiki tukuru domin tabbatar da ingancin dik abin da zasu haɗa, sun sadaukar da lokutansu ba dare ba rana suna aiki, fatan komai ya dai'daita yadda suka tsara kawai suke yi.

A lokacin da ya isa world ɗin nasa har an gama shirya komai na tashin makamin, shi kaɗai ake jira da ya zo ya saita in da zata nufa ya saketa, shararren makami ne wanda ya ɗara bmt-59 a girma, a kullum burin Smart ya kirkiran wasu makaman da babu masu kwatankwacin haɗarinsu a duniya, ya zamana su ne na farko da zasu mallakesa, to yanzu ya yi nasarar kirkiran kala ɗaya wanda ya sha wahala wajen kirkirota, ya kuma ɗauki tsawon watanni, yana fatan yanzu idan ya gwadata ta tafi yadda yake so.

Babban yaronsa a wajen mai suna Robbert ne ya fara isowa garesa ya tarbesa domin sanyaya mashi ransa. A tare suka ranƙaya izuwa room na GUIDANCE SYSTEMS COMPUTER'S.

Wato ɗaki ne mai cike da na'urorin controlling na nuclears ɗin da suke kyarawa, wasu irin mahaukatan systems ne masu ban mamaki, masu aiki babu kama hannun yaro, babu batun sanyin battery ko tsufa, dik bayan kwana uku ake zubo sabbi saboda tsaro, dan kuskure kaɗan idanun suka yi an shiga ɗari ba uku ba, so suna da karfin aiki fiye da tunaninku, dan ba kamar sauran systems da kuka sani bane.

Gaban wani dankararen guidance system computer ya tsaya.

"Everything is ready sir". Cewar Robbert dake tsaye kyam kamar mutum mutumi ta gefensa.

Jinjina kai kawai ya yi tare da sanya hannunsa a saman glass na na'urar, touch screen computer ce.

Wasu bakon lambobi ya shigar kafin nan ainahin cikin na'urar ta buɗe, go come ya shigarwa ƙwaƙwalwar rocket da zasu harba ɗin, sanna ya yi setting ɗin iya gudunta da suke buƙata, ya kuma yi setting na iya tafiyar da zata yi da nisan da zata yi ta juyo.

Sannan ya duba payload ɗinta da kyau. Already nuclear ɗin tana a saman launch pad ɗinta, su Robbert sun shiryata da kyau, amma dik da haka sai da Smart ya kara duba launch pad ɗin da kyau, ba wai dan bai yarda da ingancin kwarewar su Robbert ba ne, tsaro ce kawai, dan yasan ita samun kuskure a kanta dai'dai yake da ɗaukar rayukan mutane da dabbobi bila adadi.

Hege Smart ya san nuclear in and out, tun basu tasheta ba ya haɗa mata heat shields, saboda kara nuna kwarewa a kan aikinsa, kun san na gaya maku nuclear bata haduwa da waje mai zafi, so dole sai an haɗata da heat shields mai karfi wato garguwar zafi wanda suke bata iska mai sanyin gaske, mai kareta daga zafi.

Hankalinsa ya mayar kan fetur ɗinta, nasan zaku yi mamakin jin cewa tana da fetur, to ba fetur kai tsaye kamar wanda ake amfani da shi a motocin yau da kullum ba ne. Ana amfani da wasu nau'ikan man gas propellants masu ƙarfi waɗanda suka bambanta da mai na yau da kullum.
Ana saka mata Liquid Propellants, Liquid Oxygen (LOX) da Liquid Hydrogen LH2 da dai sauransu.

Karfin fetur na yau da kullum ba shi da isasshen ƙarfin samar da kuzari don ɗaga nuclear izuwa sararin samaniya, shiyasa ba'a amfani da shi. Ana buƙatar mai da ke samar da hayaƙi mara yawa don kada ya shafi tsarin nuclear da yanayi. Yanayin Zafi nuclears suna buƙatar mai da zai iya jurewa matsanancin sanyi ko zafi, wanda fetur na yau da kullum ba zai iya yi ba. Fatan waɗan da basu da ilimi a kan nuclear sun samu karin haske?.

Bayan ya duba waɗan nan abubuwa dik sun shiryu yadda ya da ce, sai ya dawo da eagle eyes ɗinsa a kan engines ɗinta dan tabbatar da lafiyarsu, dik sai anbi waɗan nan matakan domin gwada nuclear, aiki ne tukuru sosai.

Dogon nazari ya ɗan shiga a kan dukkan matsalolin fasaha da na tsaro da za a iya fuskanta wajen tashin nuclear.

Sannan ya shiga tsara yadda nuclear za ta tashi, wace hanya za ta bi, da kuma inda za ta sauka, tsarin tashi, da tsarin dawo.

Ana bibiyar nuclear yayin da take hawa sararin samaniya don tabbatar da ta bi hanyar da aka tsara mata. Dayawa nasan zasu tambayi ta ya ake yi nuclear ta dawo bayan tashinta, to idan Smart ya harbata in zata dawo zaku gani, kuna tare da Smart zaku samu ilimi kan nuclear matuƙa dan yana da ilimin kimiya fiye da tunaninku, kuna tare da alkamin princess Teema taku ta amana zaku samu ilimi sosai ta bangare dikka biyu, wato boko da Arabic kai harma da kimiya mai tafiya da zamani In Sha Allah.

Sai da ya tabbatar komai yana intact, sannan ya danna tashinta.


Gabaɗaya jami'an dake kusa da launch pad ɗin sai da suka sanya hannayensu a kunnuwansu suka toshe da karfi, sannan suka sunkuya kasa. Wani irin mahaukacin fita nuclear tayi wanda hakan ya haifar da karamar girgizar kasa a wajen, kun san tana da balai'n karfi, dik in ta fita sai ta girgiza ƙasa.

Tsabar karfinta sai da ƙasan wajen da ta tashi ya rufta ya yi wawakeken rami, a miliyan ɗari ta fita.

Ajiyar zuciya Smart ya sauke ganin aikinsa ta yi kyau, makamin da ya shafe watanni yana haɗata yau komai ya tafi dai'dai har sun lunchata, abin ya yi mashi daɗi matuƙa.

Rest room ɗinsa ya nufa dan ya ɗan kwanta ya huta. Da sauri Robbert ya bi bayansa ko zai buƙaci wani abin ya biya mashi buƙatarsa.

Suna shiga cikin room ɗin ya nufi wajen drawers ɗinsa. A hankali ya buɗe drawer, kamar wanda baya son taɓa komai.

DIAZEPAM INJECTION ya ɗauko haɗe da sirinji.

Wani irin zaro idanu Robbert ya yi na ganin wanna allura ta DIAZEPAM da ya ɗauko, allurar barci ce, wato shi fa Smart baya tsoron a mutu, fisabilillahi ka tashi nuclear ta yi sama sannan tsabar iskanci ka ɗauko alluran barci zaka yi wa kanka? Idan nuclear ta tashi dawowa waye zai tareta?.........🤔

Ko in aka samu wata matsala ba fata muke yi ba waye zai kula da wanna ɓangaren?.

Robbert ya tsorata amma kuma bashi da bakin iya yin magana, yana ji yana gani Smart ya dannawa kansa DIAZEPAM ɗin nan a jinin jikinsa.

Saman bed ya haye ya kwanta tare da barin kayan alluran a saman drawer Robbert ya zo ya tattare kenan.

Nan take idanunsa suka fara dishi dishi yana kallon ɗakin bibbiyu. Robbert yana tsaye a bakin door room yana ta al'ajabin Smart, da yake shi sabon jami'i ne, bai saba da halin Smart namu uban jan aji da jiji da kai ba.

Wayar Smart ce ta fara ringing, yana gani dishi dishi ya lalubo wayar daga aljihunsa. Idanunsa bibbiyu take ganin mashi wayar. Sunan mom ce ya bayyana a saman screen ɗin, amma ya gaza iya gane abin da yake rubuce, sai yake ganin kamar Heleena aka saka............😅

Ganin hakan yasa ya ja godon tsaki tare da ya wurgar da wayar a gefensa, kafin wani ɗan lokaci barci ta yi awon gaba da shi. Bashi da number Heleena fa, kawai sharrin alluran barci ne yasa ya ga kamar numberta ne.

To Smart team ina fatan kun shirya tarar wanna bujumin nuclear idan ta juyo.🤔

A gaskiya Smart ɗan ikkan zamani ne, wasa yake da nuclear kamar wanda ya samu ƴar tsana, to thank god dai idan ta juyo ta kansu zata dawo ba kanmu ba, ga shi ka yi barci ba mai kashe engines ɗinta ya rage mata gudu a yayin dawowa, sai ta afko maku a miliyan ta yi sama da ku tun da kai iskancinka ya wuce misali, ni dai na yi nan. Smart team sai a shirya zaman makoki dan da alama za'ayi rashi!.🥱



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

==========🔥🔥🔥===========




ALKALAMIN

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






======JIMETA🔥YOLA========

A tare da Mahreen bappa suka dawo cikin gidan, a lokacin su Jaish sun ɗan jima da tafiya, iyaka rashin jin daɗi bappa ya ji, har kansa ya ji tana yi mashi ciwo, gabaɗaya sai ya ji duniyar ta yi mashi wani irin, dan Allah ya gani yana kaunar Jaish, ya ma mance da auren da ya haɗa a tsakaninsa da Mahnoor, shi yanzu bakincin ɗaukar mashi yaron da suka yi ne a ransa.

Shiru ya zauna a cikin ɗakinsa yana tunanin mafita, while ita kuma Mahreen tana ta aikin matsa mashi. Sai faɗi take.

"Bappa dan Allah ka tashi ka je ka karɓo mana hammanmu, su dawo mana da shi".

Kasancewar hankalinsa baya'a jikinsa sai ya zamana sam baya jin diran kamalan Mahreen a kunnuwansa.

Kamar daga sama ya ji tana faɗin. "Bappa Adda Mahnoor fa tana can tana ta kuka, dan Allah ka je ka ɗauko mana shi".

Jin batun Mahnoor yasa ya tuna da ita, a hanzarce ya miƙe ya fito. Da gudu Mahreen ta biyo bayansa, dan a tunaninta bayan Jaish zai bi.

Ɗakinsu ya nufa domin ya duba ƴar marainiyarsa. Ita kuma Nenne tuni ta ruga gidan Arɗo dan ta gayawa gwaggonta ai an ɗauki Jaish, yau farinciki a wajenta ba'a misiltawa.

Sai wani daɗi take ji tamkar wani abin kirki ne ya faru.

Tun daga bakin kofa bappa ya fara tsinkayo shesshekar kukanta, hakan ya bashi damar kara ɗaga kafa domin ya isa gareta. Tana a kwance saman mattress ɗinsu, ta haɗa kai da jikin pillow sai kuka take yi kamar ance mata Jaish ɗin mutuwa ya yi ko kuma ba zai dawo ba har abada, ko da yake hakance fa tun da su Ramish sun tafi da shi Abuja, ya bar Adamawa kenan.

Sam bata ji shigowar bappa ba, sai dai ta ji an zauna kusa da ita, kamar mai raɗa ya ambaci sunanta, daga jin muryarsa cike yake da karaya haɗe da sagewar dik wani kwarin gwiwa da yake da shi, ba komai yasa ya ji wannan rashin kwari da cire tsammani ba face yadda suka ɗauki Jaish ba tare da sun buƙaci ganinsa ba.

Bugu da ƙari Mahreen ta gaya mashi basu yi wa kowa magana ba, sannan shi ma Jaish bai buƙaci da su nemi kowa ba, tun daga nan bappa ya yanke tsammanin Jaish zai waiwayesu, kuma hakance, dan dakamar wuya, su Ramish basu kyauta ba da basu nemi bappa da ya riƙe masu ɗan uwa tsawon watanni kusan shekara ba, hakan ya nuna sun nuna basu son wata alaƙar dake tsakani and basu da buƙatar sake waiwayar garin, gaskiya basu yi halarci ba sam.

Amma da yake su maza ne basu ji komai game da hakan ba, da mata ne suka zo ɗaukarsa kun san dai dole zasu nemi wanda ya riƙesa, dayawan lokuta a irin wannan part ɗin maza basu san me ya dace su yi ba, kullum suna tunani ne irin na maza basa waiwayawa su duba raunin tunani, idan kuma ya haɗe masu babu mace a gefensu sai taɓarar tasu ta kara yawa, su kasa yin abin da ya dace, da akwai mata a gefensu cikin wannan tafiya wlh ba zasu bar kauyen nan ba sai sun nemi bappa sun yi mashi godiya har ma su yi mashi kyauta!!.

Ta ji voice ɗin bappanta, amma kuma bata iya amsa mashi ba, saboda kukan da ya fi karfinta, da sauri Mahreen ta ƙariso wajen, saman mattress ɗin ta haye tana amabatar Mahnoor, Mahnoor.

Bappa ya rasa me zai ce mata, ya rasa da wasu kalamai zai yi amfani wajen shawo kanta, ya rasa me zai yi, ya zauna shiru ba zai iya jure kukanta ba, ya yi rarrashi kuma bashi da kalaman faɗe.

Sallamar da suka ji a tsakar gidan ne ya ja suka kai kallonsa bakin kofa shi da Mahreen.

"Kawu Ibrahim ka shi go mana". Cewar Mahreen.

Allah sarki, shi bappa da farko ma bai ɗago muryan mai sallamar ba, tsabar yana cikin damuwa, sai da ya ji Mahreen ta ce kawu Ibrahim ne ya gane.

Hannun Mahnoor ya riƙo tare da ce mata. "Zo muje".

Ba musu ta tashi ta bisa. Waje suka fito, Ibrahim kanin mamanta yana tsaye rike da wata sanda a hannunsa, ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Idanunsa jajir kamar wuta.

"Jaɓɓama lale Ibrahim". Cewar bappa.

Da yauwa ya amsa idanunsa na a kan Mahnoor da dik fuskarta ya yi jajir kamar jan kosai saboda kuka, kun san farar fata idan tana kuka, har wani ja na musamman face ɗin yake yi, bare ma wajen dogon hancin nan nata ya yi jajir sosai.

Matsowa ya yi ya karɓeta daga hannun bappa yana faɗin ta yi hakuri. Ɗan kwanciya ta yi a jikinsa tana ɓoye fuska, soyayyar Jaish ya ja ta manta da batun kunya har ta bari kukanta na rashinsa ya fito fili kowa ya gani, sai a yanzu dik ta ji kunya ya mamayeta. Sai ta wani ɓoye fuska a jikin kawu Ibrahim.

"Ibrahima lafiya kuwa?". Cewar bappa, ya yi tambayar ne bisa ganin kamar ran Ibrahim ɗin a bace, ga idanunsa sun yi jajir sosai.

"Babu komai babbo, dama na zo kara tabbatar da abin da na ji kuma nasan dama zai iya faruwa ne, amma kukan Mahnoor ya riga da ya bani amsa".

Shiru bappa ya ɗan yi dan bashi da abin sake cewa, Jaish ya jefa shi cikin matsala, ga yanayin al'adarsu yanzu zasu ɗauki laifin dik su ɗaura a kansa, bare dama ya hana Faisal ita, ai shikenan kuma ya kara shiga uku da dangi, sai kuma abin da Allah ya yi.

"Bobbo zan tafi da Mahnoor zuwa gida". Ya yi maganar ne rai a dakile, dan idan ransa ya kai miliyan wlh a yau ya ɓaci sosai, tin ainahi yana balain tausayawa Mahnoor baiwar Allah.

Bappa bai iya ce mashi ko uppan ba, dan bai san me zai ce mashi ba, kuma at this point bai isa ya ce zai hana shi tafiya da ita ba, shi kansa zai so a tafi da ita, su je Inna ta rarrasheta ko za'a samu ta yi shiru.

Ibrahim ya lura da cewa ɓacin ran da yake ciki sam ko rabin na bappa bai kai ba, dan ya lura bacin rai ya hana bappan yin magana. Dan haka sai ya ɗan sassauta ya danne nasa ɓacin ran ya ce. "Bobbo bari muje ko?".

Kai kawai bappa ya iya gyaɗa mashi ba tare da yin wani yunkuri ba. Jiki ba kwari Ibrahim ya ja hannunta suka nufi waje, sai binsu da kallo bappa yake yi. Da sauri Mahreen ta bi bayansu, dan kun san tana kaunar ƴar uwarta.

Suna tafiya bappa ya shige cikin ɗakinsa, saman ƴar gadonsa ya hau ya kwanta, ya yi iya yinsa ya rufe idanunsa ko zai ji saukin abin da yake ji har barci ta yi awon gaba da shi, amma ina ya kasa, idanun ma sun ki rufuwa.

Kamar a mafarki ya hango suit ɗin Jaish da suka tsinto shi da shi makalle a jikin kusa ta bayan kofar shigowa, tun ranar da bappa ya cire mashi suit ɗin ya makala a wajen babu wanda ya taɓa taɓa shi.

A hanzarce ya miƙe zaune a saman gadon, tunani ya fara yi a kan watakila zai iya samun wani abin mai muhimmanci a cikin aljihun kayan, hakan yasa ya yi saurin miƙewa tsaye, da sauri ya diro kasa.

Kai tsaye kayan ya je ya ciro, a bakin gadon ya koma ya zauna, dik jikinsa a mace bawan Allah. Aljun kayan ya fara laluɓewa. Cikin sa'a ya fito da wallet a aljihun wandon.

Ɗan kurawa wallet ɗin ido ya yi kafin ya ajiye a gefe ya sake mayar da kallonsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login