Showing 180001 words to 183000 words out of 403653 words
kallanki, na san zaki dawo ai rigimamma kawai". Ya kai karshen maganar yana janyota ta faɗa saman kirjinsa.
"To yanzu na bada hakuri kuma na yi rarrashi, baby ya bada hakuri ko?". Ya sake faɗa ƙasa ƙasa yana kallan face ɗinta. "Ni wannan hakurin ya mun kaɗan, sam ban yarda ba, sosai zaka rarrasheni". A shagwaɓe ta yi maganar.
Kamar mai raɗa ya ce. "To na yarda rarrashin ya yi kaɗan, kuma zan yi mai yawa, amma sai kin dawo daga school, anjuma da daddare zanzo sai na yi rarrashi mai yawa kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana ɗan shafa bayanta. Ɗago kanta daga saman kirjin nasa ta yi. "Promise me first!". Ta yi maganar tana miƙo mashi tafin hannunta.
Ɗaura nasa tafin hannun a saman tata ya yi, sannan ya ce. "I promised you that zan zo da daddare in yi rarrashi mai kyau".
Siririn murmushi ta saki tare da matsawa kusa da shi ta manna mashi sumbata a lallausan kumatunsa, ƙasa ƙasa ta ce mashi take care, sannan ta yunkura zata fice daga cikin motar. Rikota ya yi jikinsa dik a mace, a hankali ya ɗan matseta a jikinsa kafin ya matsar da face ɗinsa dab da ita. Sumbata ya bata a kumatu shi ma yana mai faɗa mata ta kula da kanta sosai. Daga haka ya ɗauki ledar chocolate ɗinta na ɗazun da taƙi karɓa ya miƙa mata yana kallanta.
Karɓa ta yi da sauri ta fito daga cikin motar, da kallo ya bita tana tafiya har sai da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke ajiyar zuciya tare da dawo da kallonsa ga makunnin motar. Da kyar ya iya tasarta ya nufi gida wajen Ammo da shopping ɗin da ya yi.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
Gabaɗaya hall ɗin tsit suka nitsu saboda tsoron bomb ɗin, gabaɗaya yawan jami'an dake wajen sun tsaya cak, kowannensu idanunsa a kan Ramish dake kasa ya kasa ɗago kansa, saboda wani irin ɗaci da ransa ya yi mashi.
Bilal yana tsaye a kusa da Abbie, saboda ya razana shi ma ya miƙe tsaye kafin mutanen can su yi barazana da bomb ɗin.
Wani irin tsawa mutanen suka daka a kan wai Ramish ya miƙe tsaye, har da cewa shi kaɗai suke da buƙata a taron nan, su basu zo nan da nufin su cutar da kowa ba, shi suke san ɗauka, in yana san cetan ran jama'arsa to dole ya tashi ya bisu. Ajiyar zuciya Ramish ya sauke kafin ya yunkura ya miƙe tsaye.
Yana miƙewa suka sake daka mashi tsawa a kan ya sauko kasan stage ɗin ya ƙariso gabansu ya zube gwiwowinsa a ƙasa..... Babban magana!!.
Ko kaɗan bai damu da abin da suke faɗe ba, hankalinsa bai tashi ba. Slowly ya kai kallansa a kan Leesharh dake kwance jininta na zuba tamkar an buɗe hanyar ruwa. Ta wutsiyar idanunsa ya kai kallansa a kan Bilal wanda shi ma shi yake kallo.
Blinking eyes ɗinsa Ramish ya yi sau biyu, da alama magana ce tasu ta jami'ai, dan kunsan suna karɓar irin wannan horo ta magana da gaɓɓan jikinsu saboda shiga matsala irin wannan sai su yi magana ba tare da sanin kowa ba su fahimci junansu.
Jinjina kansa Bilal ya yi tare da dunkule hannunsa sai ya sake warewa. Yana warewa Ramish yasa hannu cikin zafa a aljihun Suit ɗin jikinsa kafin kowa ya ankara ya zaro pistol gun, a tare suka zaro shi da Bilal.
Mutanen suna ganin haka sai suka yi ƙoƙarin danna bomb ɗin su kunna, sai dai kafin su yi motsi Bilal da Ramish suka harbesu a tare lokaci guda, Ramish ya harbi ɗaya Bilal ma ya harbi ɗaya a goshinsu. Tare suka zube ƙasa, ashe kallan da Ramish ya yi wa Bilal maganar da suka yi kenan, abin da yasa suka yi haka kuma shi ne idan Ramish shi kaɗai ya ce zai harbesu kafin ya harbi ɗaya ya sake harbin ɗayan to ɗayan zai kunna bomb ɗin, dole a tare za'a harbesu idan ana san kowa ya tsira.
Suna harbinsu gabaɗaya jami'an dake wajen suka yi kansu da gudu dan su duba bomb ɗin a kunne yake ko a kashe yake. Mayar da gun ɗinsa cikin aljihunsa Ramish ya yi, juyawa ya yi ya da nufin ya isa ga Leesharh kamar walkiya haka Bilal ya rigasa isa gareta. Bata numfashi kamar rai ya yi halinsa ne.
Cak Bilal ya ɗauketa jami'ai uku suka rufa mashi baya izuwa wajen motocinsu, shi kuma Ramish ya haɗa kan family sannan ya bawa jami'an su umarni da su wuce mashi da waɗan nan mutane h-q zai bi ta kansu amma ba yanzu ba, bari ya gama da case dake gabansa na Leesharh tukun nan, zuwa anjuma idan ya tabbatar da Leesharh bata mutu ta dalilinsa ba zai zo ya binciki mutanen.
Hankalinsa ya tashi sosai, ya kuma yi mamakin yadda aka yi Leesharh tasan za'a harbesa har ta sadaukar da nata ran a kansa! Dik yadda aka yi tasan wani abin, dan haka in dai bata mutu ba zai tsaya ta samu lafiya ko dan ya samu wasu amsoshi daga bakinta.
Kunsan dik taurin zuciyar mutum in dai aka yi mashi irin sadaukarwar da Leesharh ta yi mashi wlh dole zuciyarsa ta raunata ta kuma sassauta, to shi ma hakan ne, sai da ya ji wani iri a ransa, tambaya ɗaya yake yi wa kansa shi ne meyasa Leesharh ta bada ranta ta ceci shi?. Wannan ne babban damuwarsa.
Haɗa kan family ya yi suka nufi gida. Da gudun gaske motocinsu suka danna cikin gida, sai kuka Sharifat take yi kamar ranta zai fita, ta shiga damuwa da tashin hankali sosai. Ummie kuwa addu'a kawai take yi Allah yasa Leesharh ta mutu.
Suna shiga gida tun motocin basu gama yin parking ba Bilal ya fito da gudu ya buɗe gidan baya ya ɗauko Leesharh a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa Ramish da Dr Raj suka rufa mashi baya, dan su dubata. Da sauri shima Abbie and Sharifat suka fito suka rufa masu baya.
Kai tsaye a&e ɗinsu suka nufa da Leesharh. Hankalin Bilal idan ua kai miliyan a tashe yake a zahiri, amma bamu san me yake a cikin ransa ba, shin tashin hankalin me ma yake yi, yana damuwa Leesharh ta mutu ne ko kuma yana damuwar ta bada ranta ta ceci Ramish? To wannan dai dik bamu sani ba.
A tare Dr Raj da Ramish suka shigo cikin room ɗin. Bilal yana ƙoƙarin sanya karfi ya yage rigar jikin Leesharh Ramish ya dakatar da shi. Da mamaki suka dawo da kallonsu a kan Ramish ɗin. Dr Raj ya yi mamakin ganin yadda Bilal ya tashi hankalinsa sosai har ya rasa control saboda Leesharh, sai kace wata tasa ta jini ko da akwai wata alaƙa a tsakaninsu! Abin da mamaki, tabbas yasan Bilal mutum ne mai tausayi, amma ya nuna san Leesharh sosai wanda sun san ba halinsu bane.
Cikin nitsuwa Ramish ya tako ya kariso bakin bed ɗin da Bilal ya kwantar da ita, in a cool voice ya ce. "Rai'na ta ceta ta shiga haɗari, dan haka da kai'na nima zan cetota daga haɗari". Yana kai karshen maganar ya buɗe drawer dake kusa da bed ɗin, cikin zafa ya kwaso kayan aikin cire bullet irin su. Irrigation Syringe, Retractors, Suction, Machine Forceps, Scalpel, Local Anesthesia, X-ray Machine, Sutures, Sterile Gauze Pads, Antiseptic Solution.
A gaban bed ɗin ya zo ya zubesu saman wata tables dake ta gefe dai'dai in da kanta yake.
Su Abbie da suka shigo yanzu ne suka tsaya cirko cirko suna kallansa yana aiki cikin zafa da kulawa.
Almakashi ya fara ɗaukowa, rigar jikinta ya yanke tin daga farko har karshe, ya tsaga rigar biyu kenan, wani farar vest wadda ta ji jaga jaga da jini ne ta bayyana a ciki. Saman breast ɗinta kaɗan bullet ɗin ya sameta, hakan yasa ya yanke iya hannun vest ɗin kawai. A saman table ɗin ya mayar da almakashin ya ajiye.
X-ray Machine ya ɗauko, komai da zafa yake yi duba da halin da take ciki na zuban jini sosai, wannan machine yasa ya fara bincikar dik wasu jijiyoyi da gaɓaɓɓan dake kusa da in da aka harbeta ɗin, dan ya tabbatar da in da bullet ɗin yake ya kuma tabbatar da cewa bai taɓa wata jijiya ko wani joint or kashin jikinta ba.
Da sauri Dr Raj ya nufosa domin ya taimaka mashi, hannu ya ɗagawa Dr Raj alamar baya buƙata, shi ma zai rama cetan ransa da ta yi ne da kansa, zai yi iyaka ƙoƙarinsa dan yaga ya ceceta. Sharifat sai shessheƙar kuka take yi tana rungume da Abbie, Ummie dai taki biyosu nan, ta wuce part ɗinta. Abu Abdussalam yana cikin tashin hankali, da kaga face ɗinsa zaka san yana cikin tashin hankali bawan Allah.
A hankali Ramish ya sauke ajiyar zuciya lokacin da ya kalli tabbas bullet ɗin bai taɓa koɗaya daga cikin abin da yake gudun ya taɓa ba, bullet ɗin yana tsakiyar namar kirjinta, sai dai saura kaɗan ya huda ƙashinta.
Cikin zafa ya ajiye X-ray machine ɗin. Sannan ya ɗauko Antiseptic Solution, a hanzarce ya fara tsabtace wajen da bullet ɗin ya fasa namar ya shiga ciki. Yadda kuka san computer haka yake yin aiki.
Tsab ya tsabtace wajen, sannan ya ɗauko Local Anesthesia don rage mata zafi.
Dik da idanunta a datse sai da ta ɗan ciza laɓɓanta a lokacin da yake gudanar da aikinsa, alamar tana jin azaba, the way take jin azaba the way take kara datse idanu.
Lokacin guda tausayin Leesharh ya ratsa zuciyarsa, dan yasan azabar bullet, su da suke matsayin jami'ai, zaratan jaruman maza ma bata sauki suke iya jure azabar bullet ba bare ita da take mace kuma yarinya, ai dole dik wani mai zuciya a kirjinsa ya tausaya mata.
Scalpel ya ɗauko. Shi kansa sai da ya ɗan datse idanunsa a lokacin da yake buɗa namar kirjin leesharh da wannan Scalpel ɗin dan ya samu damar iya zare bullet ɗin. Yana aiki cikin zafa, amma kuma dik wata karfe da zai ɗaura a jikin Leesharh a hankali yake yi mata cikin tausayawa.
Yana buɗe namar wajen jini ne ya kara bulbula da karfi tamkar ruwa ya fasowa kansa hanya.
Da sauri ya ɗauko Irrigation Syringe da ɗayan hannunsa ya fara tsabtace jinin yana sharesa. Sannan ya ɗauko Suction Machine ya yi amfani da shi wajen toshe jinin dan ya samu saukin yin aikinsa. Abin ku da jami'i, ya kware a wannan fanni na cire bullet.
Retractors ya ɗauko, cike da kwarewa ya fara amfani da shi wajen rage tsokar dake ta cikin fatar in da bullet ɗin yake. Bayan ya rage sai ya ɗauko, Chlorhexidine, ya yi mata amfani da shi dan ya kara tsabtace wajen harbi saboda da ya yanke namar wajen an samu zubar jini.
Ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa komai ya daidaitan mashi yadda yakamata. Forceps. Wannan kayan aiki ne mai kama da almakashi, ana amfani da shi don kama bullet ɗin cikin sauƙi, cikin nutsuwa da tausayawa ya sanya forceps ɗin, a hankali ta kama bullet ɗin. A hankali hankali ya fara jan bullet ɗin yana zaro shi waje.
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya ciro bullet ɗin, cikin wani kwano mai ɗauke da ruwa mai sanyi da Dr Raj ya kawo mashi ya jefa bullet ɗin, sannan ya yi hanzarin ɗauko sutures ya fara ƙoƙarin haɗe wajen ya ɗinke mata.
Dik cikin ɗakin sai da suka tausayawa Leesharh, harbi a kirji namiji ma yaya aka cika bare kuma a kirjin mace, ai abin da ciwo matuƙa wlh.
Ramish bai fita daga ɗakin na sai da ya tabbatar da ya kammala komai, sannan ya nufi waje da sauri. Cikin zafa Bilal ya rufa mashi baya, kai tsaye h-q suka nufa a tare. Shi kuma Dr Raj ya matsa kusa da Leesharh dan ya ƙara dubata, lallai ba shakka shi ma ya ji yana kaunarta yadda ta bada ranta ta cetan mashi ɗan uwansa, a yadda Ramish yasa harbi ba sau ɗaya ba sau biyu ba da ace wannan harbin ta samu zuciyarsa ai shikenan sun rasa shi, amma ta tare mashi, a gaskiya yazama nauyi a wuyansu da su tsaya tsayin daka wajen ganin sun ceci rayuwarta ita ma.
Matsawa kusa da bed ɗin Abbie da Sharifat suka yi domin su dubata, baiwar Allah ta ji wahala har face ɗinta ta kumbura sosai lokaci guda, ta zama kamar ba ita ba. Shi dai Yah Rizwan baya nan, ya ɗan yi tafiya zuwa ƙasar China dan bunƙasa kamfanoninsa.
To Leesharh sai dai mu ce Allah ya tashi kafaɗunki kawai, Allah yasa kina da rabon shan ruwa a gaba, Ramish kai kuma Allah yasa ka kama masu nikaf mu ji dalilinsu na bibiyar rayuwarka da suke yi mu kuma ji maciya amanar da suke cin amanarka.
🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥
Sweetie ta samu lafiya cikin yardan Allah, sai kuma sabon walaƙanci da ta karo yarinyar nan, sam bata da tsoro, ya battaba dai jikin sarauta ne da gaske yake gudu a jikinta, akwai ta da karfin hali da jajircewa.
Zaune suke a saman bed ɗin Black Tiger a bedroom ɗinsa ita da Ronnie tana yi mashi bayanin kan yadda ake gudanar da sallah dallah dallah, Black Tiger ya tafi fada, kun san dama sun ce idan za su yi karatun addini a part ɗinsa zasu rinƙa yi dan a nan ne ba zai iya ganin abin da suke aikatawa ba ko?
To hakan kuwa aka yi, tana ta yi wa Ronnie bayani yadda zai yi sallah, tana sanye da doguwar riga irin shigar mutanen birnin Black world, ta yi balai'n kyau, ta saki wannan kyakkyawan golden white hair nata sai sheki yake yi, ya sha gyara, Ronnie ya ce kayan basu taɓa yi wa wata mace kyau irin yadda suka yi mata ba, ta ji daɗin yaba kyanta da yake yawan yi, ranta na sanyaya sosai.
Dik abin da take koya mashi yana rikewa sosai a cikin kwakwalwarsa, saboda akwai brain shi ma, ga shegen san karatu kamar me.
Suna zaune suna fuskantar juna, kamar wasu yaya da kanwa, gwanin birgewa, yana sanye da hoodies milk color a jikinsa. Sai wani binta da Koreans eyes ɗinsa yake yi.
"Sweetie ina san ki faɗa mun a in da zan samu ainahin Ingila in karanta, dan ina san sanin ainahin saƙon da yesu ya zo da shi". Cewar Ronnie kenan, yana magana yana ɗan murza mata ƴan yatsun hannunta dake rike cikin nasa. Sun bajewa Black Tiger a saman bed ɗinsa kamar nasu ne. Floris dai tana can wajen Angela, yanzu Floris ta fara yarda da zugin da master Devil yake yi mata, shiyasa ta ja baya da su sosai, amfani yake san yi da yarintarta ya kama Ronnie, ce mata ya yi idan ta taimaka mashi zata mallaki Ronnie, ita kuma sai ta yarda.
Ɗago kai ta yi suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce. "No need ka karanta ingil a yanzu Ronnie".......... "But why?". Ya jefa mata tambayar da alamar damuwa a face ɗinsa, da alama da gaske yake yi yana san sanin ainahin abin da annabi Isa ya zo da shi.
"Saboda ingila ba zata dawo duniya ba, Annabi Isa zai dawo duniya, sai dai idan ya dawo shi ma ba zai yi amfani da ingila ba, zai dawone yana mai bin bayan Annabi Muhammad (S.A.W) so dik hukuncin da zai yanke a yayin dawowarsa zai yanke ne bisa amfani da kalamul lah, wato Alqur'ani mai girma".
Ɗan zaro idanunsa ya yi, cike da mamaki ya ce. "Kenan dama yesu zai dawo duniya?".......... Jinjina mashi kai ta yi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa.
"Tabbas zai dawo duniya, wannan magana tana da asali daga hadisan Annabi Muhammad (SAW), wanda ya tabbatar da dawowar Annabi Isa (AS) a ƙarshen zamani. Daga cikin hadisan da suka zo kan hakan akwai. Hadisin Abu Huraira (RA) ya ruwaito Annabi (SAW) ya ce. Ina rantsuwa da wanda raina ke hannunsa, haƙiƙa zai sauko maku da ɗan Maryam a cikinku a matsayin mai hukunci na adalci, zai kashe batun cin alade, zai hana haraji, kuma kuɗi za su yawaita har ba wanda zai karɓa, hadisin yana nan a cikin Sahih al-Bukhari hadisi mai lamba 2222, sai Sahih Muslim hadisi mai lamba 155".
"Sannan Abu Huraira (RA) ya sake ruwaitowa. Annabi (SAW) ya ce. Ba wani annabi da zai kasance a tsakanina da Isa, wato bayan manzan Allah babu wani annabi da za'a sake yi sai Annabi Isa da zai dawo. Lallai Isa zai sauko duniya, kuma zai yi hukunci da shari'ar Musulunci. A cikin Sahih Muslim hadisi mai lamba 2365. Ma'anar Wadannan Hadisan shi ne, Annabi Isa (AS) zai dawo a ƙarshen zamani, amma ba a matsayin sabon annabi ba, sai dai a matsayin mai bi ga shari'ar Annabi Muhammad (SAW) Zai yi hukunci da shari'ar Alqur'ani da Musulunci, ba da Injila ba. Zai tabbatar da adalci, ya kawar da shirka, ya karya gicciye, ya hana cin naman alade, kuma ya hukunta duniya bisa dokokin Musulunci. Wadannan dalilai sun nuna cewa Annabi Isa (AS) ba zai zo da sabuwar shari'a ba, ko ya yi amfani da littafin da ya zo da ita a baya wato ingil, sai dai zai zama mai bin shari'ar Annabi Muhammad (SAW). Wannan yana daga cikin alamomin ƙarshen duniya da kuma tabbacin cewa Musulunci shi ne cikakken addini har zuwa ƙarshen zamani, dan haka ba sai ka wahala wajen neman karanta Ingila ba, ka karanta Alqur'ani mai girma dan ma ka kara sanin girman Allah ka ji ko?".
Shiru ya yi yana tinanin lallai ba shakka Annbi Muhammad fiyayyen halitta ɗin ne da gaske kamar yadda Sweetie ta faɗa mashi, lallai zai yi biyayya ga Annabi Muhammad iyaka iyawarsa, tabbas zai