Showing 369001 words to 372000 words out of 403653 words
irin ta kara nuna bata da lafiyar nan.
"Aesh ko dai mu wuce hospital ɗin nan ne?". A ɗan rikice ya yi maganar. "A'a mu je airport ɗin dai mu dawo". Ta faɗa tana sake yunkurwa zata bar jikin nasa. Sake riƙota ya yi, take suka zubawa juna idanu a kurkusa, wani irin kallo mai cike da sirrika suke aikawa junansu.
"Idan kika tashi jiri ba zai sake ɗibarki ba? Ko in kaiki mota da kai'na?". Ya faɗa idanunsa sosai a cikin nata. Ƙasa iya basa amsa ta ta yi, abin da yake cikin zuciyarta yana neman fin karfinta.
"Aesh" ya faɗa yana mai da kallansa kan soft lips ɗinta da suke ɗan kerma kamar mai jin sanyi. Bata iya amsawa ba. Zai sake yin magana wayarsa ta fara ringing. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Let's go, kinga kin sa har jirginsu ya sauka ban isa airport ba, dan ma babu nisa nan da 5 mins zamu isa". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa da ita a jikinsa. A haka suka nufi waje. Ajiyar zuciya ta sauke, hankalinta ya kwnata, burinta na ɓata mashi lokaci ta hana shi shan wani cappuccino ko cin wani abin ya cika.
Sai dai daga shi har ita basu lura da cappuccinon da ya zube a kasa ba, ya canza kala daga brown zuwa dark green sosai, kamar ba cappuccino ba, suna fita wannan tsohuwa ta yi gaggawar zuwa domin tattare komai, a gaggauce ta goge cappuccinon da ya zube, tasan basu sha komai ba, dan dik abin da suke faɗa kada ku manta tana jinsu, ranta bai so hakan ba sam, ranta ya sosu, haka ta kwashe kayan abincin ta fita da shi tana tinanin irin hukuncin da zata yi wa Leesharh, ba zata kyaleta ba sai ta hukuntata! Dan tana ganin kamar ita take sanya Ramish yana tsallake tarkonsu, kuma hakan ce, sau da dama Leesharh tana shiga tsakaninsu ba tare da ta san ta shiga ba, kamar dai yadda ta ɓarar da abincin ɗazun da suka yi karo, kun ga bata san akwai wani abin a cikin abincin ba ta ɓarar, to haka dayawan lokuta sai sun yi shiri a kansa sai ta shiga tsakani ta watsa komai.
Daren jiya Ramish zai fita ta hana shi ta hanyar ce mashi tana tsoro kuma ita ba zata iya fita waje a daren nan ba bare ta bisa, haka ya fasa fita, kuma sun shirya mashi mugun abu a fitar da zai yi, kunga Leesharh ba tare da saninta ba a nan ma ta shiga tsakaninsa da su!!.
---------------------------------------🔥🔥
Bai direta a ko'ina ba sai a cikin mota, da gudun gaske ya shiga ya figi motar suka bar gidan. Saboda gudun da yake yi yasa suka yi saurin isa airport, a dai'dai lokacin su Smart suka fito daga cikin jirgin yana rungume da gawar Auta. Ai Ramish yana ganinsu haka bai san lokacin da ya ɓalle kofar motar ya fito waje ba, take ya ji zuciyarsa ta amsa, hankali nan da nan ya tashi, a ruɗe ya ce. "Yah Omerish meyake faruwa? Meyasameta?".
Dai'dai lokacin Bilal ya yi parking motarsa shi ma ya fito. Smart bai yi magana ba ya buɗe gidan baya na motar Ramish ya kwantar da Auta a ciki, sannan ya yi juyo ga su Jaish. "Ku bi Bilal izuwa gidan uncle, bari in je ni da Zunaira, ka kula da Omar". Fitowa ita ma Leesharh ta yi daga cikin motar tana kallan Smart, sai da gabanta ya faɗi yadda ta ga face ɗinsa.
"Aesh shiga gidan baya ku zauna da Zunaira". Cewar Ramish kenan. Da sauri ta shiga tana kallan Smart, ta ɗaga kan Auta ta ɗaura a saman cinyarta, sai a lokacin ta lura da guyson, Allah sarki ta jima rabonta da shi, tin da ya koma kingdom of power bai sake zuwa Dubai ba, ta yi kawarsa sosai mutumin kirki. Gidan gaba na motar Ramish Smart ya shiga ba tare da ya yi masu magana ba, yau first time na haɗuwar Smart and Ramish face to face kenan, Ramish ya ci burin ya haɗu da yayan nasa mai tayasa aiki mai taimaka mashi, sai dai sun haɗu a wani irin yanayin da word can't explain how they're feeling, sai ma lokacin da su Ramish zasu fahimci Zunaira bata raye, uhm!!.
Bilal na kallon Ramish har cikin ido, ba dan Smart dake wajen ba da babu abin da zai hana bai ci kwalar rigar Ramish ya faɗa mashi dalilinsa na gudunsa ba, ya kirasa a waya baya ɗauka, ya nemesa kamar hauka bai gansa ba, wlh har kuka sai da ya yi da hawayensa, ashe dama Ramish yana cikin Dubai, to me ya yi mashi da zafi har haka da zai yi mashi irin wannan hukunci? Tare suka taso, tare suke komai, rana tsaka Ramish ya gujesa dole abin ya gigita shi, har rama sosai ya yi wlh, albarkacin Smart yasa bai yi magana ba, yasan koma menene yanzu tin da yayan nasu yana nan zai warware masu komai, zai aje ye su ya ji menene ya haɗasu faɗa.
Shi ma Ramish kallon Bilal ɗin ya yi ido cikin ido, lokaci guda ya ji zuciyarsa ta damu, wlh yana bala'in son ɗan uwan nasa fiye da kansa, dik sai ya ji bai kyauta ba, ko da Bilal yana da sa hannu a cutar da shi bai kamata ya juya mashi baya ta irin wannan sigar ba, kuma yasan Bilal ɗin ba zai iya jurewa ba, amma haka ya sharesa, gaskiya bai kyauta ba, take ransa ta ɗacaca, haka ya shiga mota ya tayar suka bar airport ɗin zuciyarsa cike da tinani kala kala. Bilal ma zuciyarsa tana zogi ya tada motar suka wuce gidan Abbie.
Suna fitowa airport Ramish ya ce. "Yah Omerish ina zamu je?". Kai tsaye Smart ya ce. "Gidanka, and kada ka bari kowa ya san muna nan, kada momma ta sani shiyasa ban wuce family house ba".
Shin kun san dalilin zuwan Smart Dubai kuwa? Zai fara ne daga kan King Badeen kakansu kenan, wato Akka bata isheshi gani ba, bari ya fara da mai bawa Akkan da kanta umarni kafin ya koma kansu, yanzu zuwan na King Badeen ne, sai sun faɗa mashi a wace aya ce Allah ya banbanta mutane, ya ce kuma a yi banbaci kamar yadda suke yi, tun daga nasi har bakara sai sun nuna mashi a in da ya ce mai arziki mai daraja ne mara arziki kuma mara daraja ne, uhm abin babba ne. My people's ni fa bana san kanku ya ɗauki zafi sosai shiyasa nike sake maku cakwakiyar nan a hankali hankali, kun gane ai?. Ina tausaya maku ne.......🥱
"In Sha Allah babu wanda zai san kuna nan, amma Yah Omerish please tell me meya samu Zunaira". Cikin raunin murya ya yi maganar. "Mutuwa ta yi". Smart ya faɗa can ƙasa ƙasa. Ai wani irin mahaukacin birki da Ramish ya taka sai da Smart ya buga kansa da jikin glass na door, tashin hankali, ita kanta Leesharh bata san time da ta zabura ba!!.
Ƙasa iya yin magana Ramish ya yi, tamkar wanda aka datsewa baki, da bai taka burki bama ai da mutuwa zasu yi, dan babu abin da zai hana bai saki kan motar nan ba, irin wannan tashin hankali. A miliyan ya juyo da kallansa a kan Smart da yake kallon hanya, da hannu ya yi mashi alamar da ya kunna motar su je. Kasa yin magana Ramish ya yi, sai yake jin kamar kunnuwarsa basu ji mashi abin da yayan nasa ya faɗa daidai ba, yana san sake tambayarsa tongue ɗinsa ta yi mashi wani irin balai'n nauyi. Sake nuna mashi hanya Smart ya yi a kan su tafi, dan dole ya tashi motar yana ta faman sauke ajiyar zuciya yana addu'ar Allah yasa ba dai'dai kunnuwarsa suka ji mashi ba.
Sai ƙoƙari haɗa kalmomu dake kama da mutuwa a cikin zuciyarsa yake yi dan ya fitar da kalmar da Smart ya faɗa ba mutuwa ba, wai irin zai ce wata kalma mai kama da mutu kenan sai ya ce haka Smart yake son cewa ya manta ya ce mutuwa. Da haka suka isa gida, tin bai gana kashe motar ba Smart ya fito ya buɗe gidan baya, ko kaɗan bai bi ta kan Leesharh ba ya ɗauki Auta ya nufi cikin gida kamar gidansa.
A gaggauce Ramish ya kashe motar ya bi bayansa, ita ma Leesharh da gudu ta rufa masu baya. A parlour saman kujera ya shinfiɗe Auta, sannan ya ciro wayarsa ya dannawa number Zash kira, yana ɗagawa ya ce mashi. "Mun iso everything is ready". Yana kai karshen maganar ya katse kiran. Dai'dai lokacin Ramish ya shigo ciki, har tsoron sake tambayar yayan nasa yake yi, dan zuciyarsa ba zata iya ɗaukar jaddada mashi mutuwar Auta ba, a bakin kofa ya tsaya ya ƙasa ƙarisowa ciki.
Binsa da kallo mai ɗauke da fassara kala kala Smart ya yi kafin ya ce. "Zoka zauna mu yi magana akwai in da nike san zuwa". Kai ya ɗan girgiza yana kallon gawar Auta ya sake kallan Smart, alamar ba zai iya ƙarisowa ciki ba. Nisawa Smart ya ɗan yi kafin ya ce. "Zunaira bata mutu ba, shikenan zo ka zauna".
Wani irin dogon numfashi da Ramish ya ja tare da dafe saitin zuciyarsa shi zai tabbatar maka da suna bala'in kaunar Auta fiye da kawunansu, sonta a cikin jinin jikinsu yake!!. A hankali ya karisa ya zauna kusa da ita, dai'dai lokacin ita ma Leesharh ta shigo.
"Zunaira bata mutu ba, ta shiga doguwar suma ne, Zash zai kawo likitocin da zasu lura da ita, zan barta a nan a hannunka, ka bata kulawa sosai wanda nasan ba sai na faɗa maka ba zaka yi hakan, kada ka bari kowa yasan tana raye, ina san dad ya ɗanɗani azabar da ta ji a zuciyarta lokacin da ya yi mata sanadiyar mutuwar wanda take so, ko mijin nata kada ka bari yasan tana raye, zamu bari a matsayin ta mutu, sai ta samu lafiya sosai, idan tana san zama da Abdussalam ɗin sai a barsu, idan kuma bata so sai a raba auren". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kanta. Yau tin da ya ɗaura idanunsa a kan Ramish yake yi mashi wani irin kammani kamar Hoorain haka! Shi da yake yasan kamannin Hoorain tin yana Paris, akwai hotunansa ma dayawa a wayarsa wanda shi Hoorain ɗin yake turawa Auta a lokacin da suke soyayya!.
"Yah Omerish amma me yake faruwa ne? Dama bata san Abdussalam ɗin ne aka yi auren?". Ramish ya tambaya!. Jinjina mashi kai Smart ya yi kafin ya faɗa mashi dik abubuwan da suka faru na yadda King ya hanata Hoorain har hakan ya yi sanadiyar mutuwar Hoorain ɗin, da ta ji Hoorain ɗin ya mutu shi ne ta shiga doguwar sumar nan! Sosai Ramish ya ji ɗacin abin da dad ɗin nasu ya yi, tsabar ɓacin rai bai san lokacin da ya ce. "To shi dad ɗin akwai wanda ya taɓa hanashi san ransa ne? Amma me Hoorain ya yi mashi bayan soyayya da Zunaira? Hukuncin ya yi tsauri".
Kai tsaye Smart ya ce. "I think Hoorain ɗansa ne ko kuma suna da wani kwakkwarar alaƙa a tsakaninsu"............ Wata uwar zabura Ramish ya yi, with harsh voice ya ce. "Ɗansa kuma? How comes?".......... Dan furzar da iska mai tsananin zafi daga bakinsa Smart ya yi kafin ya ce. "Dik ajiye waɗan nan batutuwa, yanzu dai zan turo jami'ai guda goma su yi tsaron gidan nan, zan turo wasu biyu daban kuma su yi tsaron Zunaira sosai, ban yarda a bata komai daga wani waje ba ba tare da sanin jami'an dana wakilta ba, ban yarda ta ci wani abinci ba face wanda waɗan nan jami'ai zasu girka mata, sannan su zasu rinƙa yi mata komai, kai dai ka saka idanu a kansu, kuma zata so ganinka a kusa da ita. Idan na gama bincike a kan koma menene you will get the result, maybe zan dawo gareku cikin satin nan, maybe kuma zan iya fin hakan".
Tashin sense, shiru Ramish ya yi yana mamakin abubuwan da suka faru, wannan wace iriyar musifa ce? Ya jefawa kansa tambayar. Zuba mashi idanu Smart ya yi yana kallan face ɗinsa, dik yadda aka yi Smart yana hasashen Ramish ɗan waye, tausayinsa ne sosai ya kama shi, ya zai ji idan aka toni asalinsa? Gaskiya King bai yi mashi adalci ba sam sam.
"Don't trust anybody my brother, idan da dama kanka ma kada ka yarda da shi gabaɗaya, ka kula sosai". Cewar Ramish.............Jin jina kai Ramish ya yi kafin ya ce. "Yah Omerish ina jin kamar Raj ba kanina bane, saboda abubuwan da suka faru".
Tausayinsa ne ya sake kama Smart, kamar kuwa yasan gaskiya. "Kaninka ne, ka dai'na barin shaiɗan yana sanya maka banzan tinani a ranka, keep praying, everything will came and end"........ Shiru ya ɗan yi, shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa. Smart zai sake yin magana idanunsa suka sauka a kan Leesharh dake manne da jikin bango tana binsu da kallo. Ɗan zaro idanu Smart ya yi, saboda tsantsar kamanninta da Zash da ya gani, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa.
Dai'dai lokacin Zash ɗin ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama, ga wasu shahararrun Drs guda uku biye da shi a baya. Miƙewa tsaye Ramish ya yi yana faɗin. "Zash wanene ya faɗa maka ina nan?". Harara ya wurga mashi kafin ya ce. "Awww our bro ka ɗauka sai ka faɗa mun in da kake ko?". Ɗan ɗaure fuska ya yi tare da cewa. "Stop please, wai ya aka yi kasan gidana?"....... "Kana mamaki ne?". Smart ya katsesu. Da sauri Ramish ya juyo da kallonsa a kan Smart ɗin. "E Yah Omerish, friend ɗina ne fa, kuma ni ban taɓa zuwa da shi nan ba, ban san ya aka yi yasan nan ba".
Miƙewa tsaye Smart ya yi. "Ni na turo shi wajenka domin in san dikkan ƴan uwana, ba jami'i kasa da kai bane kamar yadda kake tunani, shi bama SWAT bane, ya shiga jikinka ne kawai bisa umarnina, assistant ɗina ne a wajen aiki, jajirtaccen jami'i fiye da tinaninka, yanzu kuma ni na ce ya zo nan da Drs dan su duba Zunaira".
Mamaki ne ya kama Ramish, dama ya yi mamaki a lokacin da Zash ya shiga hukumar SWAT, dan da kallo ɗaya ya yi mashi yasan wannan kwararren jami'i ne sosai, amma sai ya bar abin a ransa, suka cigaba da kasancewa a tare, ashe kuwa hakan ce, jami'i ne. Yana can yana mamaki har su Drs sun dukufa a kan Auta dan jadada aikinsu. Smart bai jira ba ya wuce haɗe da yi masu sallama, haka ya zo ya wuce Leesharh ba tare da ya sake ɗaga idanu ya kalleta ba. Mayar da hankalinsu su Ramish suka yi kan samawa Auta lafiya, babu wanda ya damu ko ya mayar da hankali kan kamannin Leesharh da Zash bare har su yi bincike!!.
A can kingdom of power kuwa, lokacin da King ya tabbatar da Zunaira fa mutuwa ta yi ta bakin Jaish, wlh yanke jiki ya yi ya faɗi, sai dai suka kwashesa zuwa hospital, doguwar suma ya yi, sai da ya shafe kwana biyu a sume likitoci suna ta kokarin a kansa, daga bisani aka dawo jinyarsa a gida bayan ya farfaɗo, sai da ya ɗauki good 3 weeks yana jinya, baya furta komai sai dai ya yi ta binsu da kallo, kuma dik da haka bai yi danasanin hana aurenta da Hoorain da ya yi ba, ya dai yi fatan da wani take so ba Hoorain ba ba shakka da zai bata shi ko da ba jinin sarauta bane, Hoorain ne dai baya kaunar haɗa jini da shi.
Momma bata san Auta ta rasu ba, sun ɓoye mata, ko da ta dawo daga Dubai sai ce mata suka yi tana wajen uncle Muhammad na France, wato daddyn Smart kenan, hakan yasa bata wani damu ba. King dai ya sha jinya, dan wlh har Auta ta farfaɗo ta fara samun lafiya sosai shi bai koma dai'dai ba, kuma kusan kamar commander ya zama, dan wani lokaci sai ya rinƙa magana kamar Auta tana kusa da shi, kamar yana tare da ita suna hira. Abin ya tada hankula matuƙa, yanzu uncle Abbas shi ne yake kula da mulkin kingdom of power, King yana jinya.
Gudun kada guyson ya samu taɓin hankali yasa Smart ya sanar da shi Auta bata mutu ba tana raye, ya kuma sanya Ramish ya haɗasu suka ga juna, ranan sun sha kuka sosai, tin da Auta ta farfaɗo bata yi magana ba sai ranar da guyson ya zo wajenta, a nan ne ta yi magana, ta yi kuka, ta kuma yi wa Hoorain addu'a, daga nan Ramish ya ce tun da ana hutun school a bar guyson ya kasance a tare da ita, dan a dalilin zuwansa wajenta sauki ya kara samuwa har tana magana, Smart ya yi na'am da hakan, shi kuma yana kingdom of power, rashin lafiyar da King yake ciki yasa bai tada balli a kan amsoshin da yake so ba, ya ɗaga kafa zuwa dad ɗin nasa ya samu lafiya.
RAMADAN KAREEM!!.
Ana gobe za'a ɗauki azumi, sai shirye shirye ake ta yi na tarar wata mai falala mai albarka, unexpected Smart ya ga diran mom ɗinsa a kingdom of power, ta ce ba zata iya zama ba tare da shi bane, tin da yaki dawowa shi ne ta biyo bayansa, ya ji matuƙar daɗin ganinta, ya kuma jin babu daɗi yadda ya bari ta yi kewarsa, matar da tin da ya taso fara'a kawai yake gani a face ɗinta, ta so shi fiye da yadda take san kanta, macen kirki adala, ya yi mata addu'ar samun haihuwa sau ba iyaka, ya ji dama ace yana da damar sama mata aihuwa da sai ta gaji da ƴaƴa.
Sosai su momma suka karɓeta hannu bibbiyu, momma ma ai sai zama yar kallo ta yi a tsakanin Smart da mom ɗinsa, dan kuwa ya tare a