Showing 252001 words to 255000 words out of 403653 words

Chapter 85 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

24

kunamar, amma ya sha kuka kam, dik abin da suke yi a kan idanun Mahreen suke yinsa, a ranta take cewa. "Wannan Yah Omar ɗin dai an yi rago, kannen nasa ma sun fishi jarumta, sai ka zauna kana kukan ciwo dan wauta?".

Daga gefe can kuma uncle Jahiz ne ya je neman Zee a part ɗin mama bayan ya baro bedroom na Akka, dan ba zai iya barci ba sai ya sanyata a idanunsa, ya kamu da zazzafar soyayyarta ne da alama. Da ya je bai ganta ba sai ya tambayi Khadijah ina take?! Nan take faɗa mashi ai bata nan. Bai kawo a ransa matsala suka samu da Aneesa ba, yasa hannu ya ɗauki babyn Khadija ya nufi waje da shi, Allah ya gani yana kaunar yaron nan over, kamar shi ya haifesa haka yake jinsa.

Bayansa Khadijah ta bi da kallo, take fuskarta ta bayyana alamar damuwa da rashin jin daɗi, gabanta faɗuwa yake yi a dik time da ta kalli uncle Jahiz. Kai tsaye part na momma ya nufa dan duba Zee a wajen. While shi ma Dr Raj yana can bedroom ɗinsa yana fama da juyi da tinaninta. Ita kuwa ta haye bed ɗin mama Haulat ta yi kwanciyarta, har da shigewa cikin bargo. My people's anya gaba ƙwaƙwalwarku zata iya ɗaukar cakwakiyar kingdom of power?......🤔

To kun ji abubuwan da suka faru bayan barin smart kingdom ɗin, dan haka mu koma Paris ɗinmu.
Auta ta buɗi baki zata wa Hoorain magana sai jin voice ɗin mace ta yi daga bayanta tana faɗin. "Wacece ke kuma?". A miliyan Auta ta juya dan ganin wacece? Ita dai tasan babu wata mace a gidan nan tun da suke zuwa, a nan suke sauƙa idan suka zo, Smart baya kaisu gidansu wajen mom ɗinsa, a nan suke zama, to bata taɓa ganin mace ko ta ji muryar mace ba, kuma wannan ba muryar Pretty bane gaskiya. To ko muryar waye?.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








Wata kyakkyawar baturiya ce tsaye a kan kafafunta, tana nan dai cikin irin wannan shiga tasu ta turawa, ta zubo gashinta ta zaman shoulder ɗinta ta gaba, ga wani shegen high heel a kafafunta mai tsinin gaske. From up to down Auta ta bita da kallo kafin ta ce. "Ke yakamata in yi wa wannan tambayar".

Tana kai karshen maganar ta cigaba da yin wayar da take yi. Cike da takun ƙasaita ta tako izuwa gaban Auta, hannu tasa ta kwace wayar dake hannunta, cikin zafa Auta tasa hannu zata kwaci wayar. Hatana ta yi tare da binta da wani kallan ƙasƙanci kafin ta ce. "Kin dai ɗan yi kama da baby, dik yadda aka yi kina da wata alaƙa da shi, amma hakan na shi ne zai sa na ɗaga maki kafa ba, ke har kin isa ina magana zaki cigaba da yin waya?".

Auta zata yi magana suka ji alamar an buɗe kofar parlour, to jinin sarauta dai ba karya ba, cike da izza ta ce. "Bani da lokacin shashasshu irinku, bani wayata". Kallna banza ta bita da shi, zata yi magana kenan suka ji muryan Smart yana kwala kiran sunan Auta, harara ta dallawa yarinyar kafin tasa kai ta wuce ciki.

A parlour ta iskosa yana zaune saman sofa, kusa da shi ta je ta zauna tana faɗin. "Yah Omerish gani nan". Kamar zata tambayesa wacece a gidan nan kuma dama akwai mace a gidan ne, sai kuma ta yi shiru, ranta a ɓace wancan mata katse mata waya da jaruminta. Hannunta ya riko cikin nasa, a natse ya ce. "Menene yake damunki?".

Wai a ina Smart ya baro mana gawar Pretty ne? Wato ko a jikinsa tun da ba Auta bace ta mutu ko?.

Da farko kamar Auta zata ɓoye mashi abin da yake faruwa, amma da taga bata da wani sauran hanya sai ta sanar da shi game da soyayyarta da Hoorain, da ɓatar da ta yi zuwa forest da taimaka mata da Pretty ta yi da komai dai dik ta sanar da shi, ta kai karshen maganar tana kuka dan ta tina irin soyayyar dake tsakaninsu.

Shiru Smart ya yi ba tare da wani yanayi ya bayyana a tattare da shi ba, kamar dai bai damu ba. Miƙewa ya yi tare da riko hannunta suka haura sama, sai sharar kwallah take yi, dama ga bakincikin an kwace waya an hanata yin magana da shi. Da alama Smart da King halayyarsu iri guda babu banbanci, amma my people's me kuke tunani ne, wai shin ya Smart ya yi da Pretty ne? To mu je dai zuwa, koma dai menene lokaci zai yi mana alkalanci.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Ummie and friend ɗinta hajiya two seater ne zaune a saman sofas a parlourn Ummie, yanzu hajiyar ta zo, daga gani kasan akwai abin da suke shiryawa, sai kuskuskus ƙasa ƙasa suke yi, hajiya two seater dai kusan kullun tana cikin nikaf matar nan, sai idan ta zo keta tsaron gidan Abbie ne securitys suke ce mata sai ta cire nikaf kafin ta wuce, dan su ga wacece, ko da kuwa Ummie ta yi masu waya ta sanar da su bakuwarta na zuwa, to basa barin ta wuce sai sun ga face ɗinta. Nikaf or face mask baya keta gate na farko na gidan Abbie, dole ka ciresa kafin ka wuce.

••••••••••••••••••••🔥

Jakarta ta buɗe ta ciro kwalin STENDRA guda ɗaya ta miƙawa Ummie tare da miƙewa tsaye, ƙasa ƙasa ta ce. "To ni zan wuce dare ya yi, yanzu ma ba dan saboda ke ba ba zan fito ba, ga sakonki nan, kada ki wuce saka mashi guda ɗaya idan ya yi yawa ne biyu dan gudun matsala a iya ganoki, dan yana da karfi fiye da tinaninki". Yadda take maganar tsab zaka fahimci wannan ta yi degree a iya munafurci da makirci.

Jinjina kai Ummie ta yi tare da miƙewa tsaye tana zuba mata godiya, sai uban murmushi take yi burinta zai cika. Gaba hajiya two seater ta yi tana kara jaddada mata kada ta wuce sanyawa Ramish wannan kwaya guda ɗaya kacal, dan yana da karfi sosai, daga karshe ta rufe mata da cewa idan ya sha da minti 15 zata fara yi mashi aiki, dan haka sai ta shirya. Ummie baki har kunne ta amsa da to. Har Hajiya zata fita parlourn Ummie ta yi saurin cewa.
"To ya batun Leesharh fa? Yakamata mu yi gaggawar kawar da yarinyar nan tin kan lokaci ya kure mana, kina ji dai ya faɗa maki Abbie yana tarayya da yarinyar nan a ɓoye, kuma ni ba zan iya jurar hakan ba". Ranta a ɓace ta kai karshen maganar.

Ajiyar zuciya hajiya two seater ta sauke kafin ta ce. "Kada ki damu, ai yanzu yazama wajibi mu ɓatar da Leesharh, idan ba haka ba zata zame mana babban barazana, amma kada ki damu zan dawo gobe dan jin result na maganin nan, a nan zamu tattauna maganar tata in faɗa maki hukuncin da muka yanke, amma kafin nan ki shiryawa Leesharh fita barin cikin gidan nan, kin dai san ba ta yadda za'ayi mu iya ɗaukarta a cikin gidan nan saboda mahaukatan tsawon nan naku masu sanya hantar cikin mutum ta kaɗa da kuke da shi, amma ki nemo wani aika ko wani dalilin da zai sa ta fita daga ita sai driver kawai".
Jinjina kai Ummie ta yi, har zuciyarta ya ayyana mata yadda zata aika Leesharh shopping ita da driver kawai ba tare da Sharifat ko bodyguards ba, tasan ta yadda zata ɓullowa komai.

Sallama suka yi ta raka hajiya zuwa wajen elvator, sannan suka yi bye bye hajiya tana yi mata addu'ar samun nasara a kan dikkanin burikanta.

Ciki Ummie ta koma, dama ita take haɗa mashi abinci dayawa lokuta, Sharifat mai kaiwa ce kawai. Da sauri ta nufi dry kitchen dan shirya mashi cappuccino, dan tasan zai buƙata. Sai dai fa, bata kai ga fara haɗawa bama sai ga Sharifat ta shigo cikin kitchen ɗin tana faɗin. "Ummie na je bedroom ɗinki bakya ciki, Yah Ramish yana san cappuccino"............ Wani irin faɗuwar gaba Ummie ta ji ya dira mata, sai ta ji shakkar saka wannan magani, amma da yake shaiɗan la'ananne ne sai ya fara kara mata confidence a kan ta jajirce zata yi nasara, har da raya mata ya yi cikar buri da biyan buƙata ya fi kwana masallaci, take ta ji kwarin gwiwa, cikin dabara ta ce.

"Okey zan haɗa mashi, amma jeki ɗaki ki jirani ina zuwa". Ta faɗa tana satar kallan cameras dake cikin kitchen ɗin. Da okey Sharifat ta amsa mata tare da juyawa ta komai ciki, tana sanye da jelly dressing. Kamar yadda ta saba haɗa mashi cappuccino haka ta haɗa yau ma, bata zuba maganin a cikin kitchen ɗin ba, saboda Cameras dake ɗaukarta, sai ta ɗauki cup ɗin ta fito waje. Kai tsaye bedroom ɗinta ta nufa, sai dai bata kai ga shiga ciki ba ta tsaya a wani ɗan corridor dake tsakanin parlour da bedroom ɗin, a wajen babu Camera kuma akwai ɗan duhu, a nan ta tsaya ta fito da maganin, a maimakon ta saka mashi guda ɗaya ko biyu kamar yadda aka yi mata kashedi, sai ta ɓallo guda huɗu ta banka mashi a ciki. Tsayawa ta yi har sai da maganin ya narke a ciki, sannan tasa spoon ta gauraya shi sosai, sai ta bar spoon ɗin a cikin cup ɗin.

Kana ganinta kaga maras gaskiya, amma da yake Sharifat yarinya ce sai bata iya fahimtar halin da Ummie take ciki ba, fargaba kamar zai kashe matar nan, amma saboda karfin hali sai dannewa take yi. Ta zo ta miƙawa Sharifat plate and cup ɗin, sannan ta wuce cikin toilet ɗinta tana jin kirjinta tamkar zai fashe saboda fargaba da tsinkewar zuciya. Ita kuwa Sharifat, karɓa kawai ta yi ta wuce abinta, zuciyarta na ta tuna mata Leesharh.

•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Zaune yake a cikin bedroom ɗinsa yana tinanin yadda aikinsa yake gudana, ga mama ta sako shi a gaba tana saka mashi pressure sosai a kan bayyanar Smart, ta matsa mashi wai sai ya yi mata bincike dan ita bata yarda Smart ɗan King bane, wai sai dai momma saboda kwaɗayin mulki ta hayo Smart a matsayin ɗa.

Jama'a kun ji mun wata lukutar bala'i a wajen mama, fisabilillahi momma ta yi kala da masu yunwar mulki? Kada ku manta fa ita momma ƴar King Badeen ce! Sannan kanwa ga su Abu Abdussalam ƙososhin gwamnati, ga daddyn Smart wato babban yayanta president ne, su uncle Rahab dik jiga jigan ƴan siyasa ne, bayan haka shi kansa Smart ya isheta har ta gama rayuwarta bazata nemi komai ta rasa ba, kuna dai gani Auta Gimbiya Zunaira yar karamar kanwarsa ma ya mallaka mata tampatsetsan gida har haka bare mommarsa? Jama'a ku tayani gani, Jaish kawai yana da dukiyar da zai iya rike gabaɗaya ahalin King har da su mama ɗin har karshen rayuwarsu ba zasu nemi komai su rasa ba, kai in short auta kawai ta mallaki dukiyar da ya take na uncle Abbas a yawa daga hannun brothers and uncles ɗinta, ji da ita suke yi, amma wai irin wannan mata mama take cewa ta hayo yaro dan yunwar mulki? Hankali zai ɗauki wannan batu kuwa?.

Shiyasa Ramish bai wani bi ta kan batun ba, saboda shi yasan wacece momma da ahalinta, kada ku manta a hannun Abu Abdussalam ya girma, Abu Abdussalam kuma ai kunga yayan momma ne dik da cewa yayan daddynsu ne ma, dan haka shi yasan momma ba zata yi hakan ba, shi zai fi kowa bada labari a kan kirki da adalcin familyn momma.

Akwai lokacin da ya so barin gidan Abu Abdussalam ya koma gidansa da ya mallaka da ɗinbin dukiyarsa, amma Abbie ya ce babu in da zai je su kasance a tare, so shi yasan halin gabaɗaya ƴaƴan King Badeen.

Shiru ya yi yana tinanin yadda zai kama masu nikaf, shi yanzu wannan ne a gabansa ba bala'in mama ba. Sallamar Sharifat ya dawo da shi daga duniyar tinanin da ya afka. Kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa. Ita kuwa kallonsa ta shiga yi babu kakkautawa, yana sanye da pj's a jikinsa launin light milk.

Hannunta ɗauke da cup na cappuccinon da ya buƙata ta kawo mashi, gabansa ta kariso ta ɗaura cappuccinon a saman table tare da komawa gefe guda ta tsaya tana jiran ko zai buƙaci wani abin. Yunwa yake ji, tin safe rabonsa da abinci, abubuwa sun sha kansa, dan haka sai bai ɓata lokaci wajen ɗaukar cup ɗin ba.
Cikin natsuwa yake sipping na cappuccinon ba tare da ya kawo a ransa akwai wani abin a ciki ba, saboda kullum ita ta saba kawo mashi abincin, kunga ba zai taɓa yin zaton ansa wani abin ba. Sai dai fa ya ji ɗanɗanon cappuccino ya ɗan canza, kamar ya yi zaƙi dayawa fiye da kullum, amma sai ya yi tinanin sugar ce ta kubce, yana jin yunwa dan haka ba zai tsaya ƙaƙalen nan nasa da ya saba ba.

"Yah Ramish in tafi?". Ta faɗa tana kallan face ɗinsa. Kai ya gyaɗa mata alamar e ta tafi. Juyawa ta yi tana tafiya tana waigosa, while ita kuma Ummie tana can tana murnar burinta ya cika, so take kawai Sharifat ta dawo ta tambayeta ya sha ko bai sha ba.

Sharifat na fita ya miƙe tsaye yana cigaba da shan cappuccinon, da yake yana jin yunwa har ya kusa shanyewa ma saura kaɗan. Parlournsu ya fito, babu kowa, da alama Bilal ya yi barci, dama shi Rizwan baya nan. Kai tsaye ya nufi ɗakin da Leesharh take kwance rike da cup ɗin. Ƙasa ƙasa ya yi sallama, tun daren jiya da ya fita ɗakin bai sake dawowa ba, dan baya san sake haɗa idanu da ita, ta caza mashi kai jiya.

Zaune take a bakin bed ɗinta, ta fito daga wanka kenan ba jimawa, yanzu tana iya yin wanka saboda ciwon ya warke, sai dai har yanzu tana karkashin dokar kada ta bar ruwa ya taɓa wajen, so cikin dabara take wankar. Yau tana sanye da riga mai siririn hannu zuwa gwiwowinta, sai doguwar wando daga ƙasa, Dr ya ce ta rinƙa barin wajen ciwon nata yana shan iska, shiyasa yanzu riguna masu siraran hannu kamar vest kawai Sharifat take kawo mata, anma kusa sallamarta, dan sauki ya samu.

Jin motsin mutum yasa ta ɗago idanunta, dama tana rike da wayarta tana latsawa ne. Tana ɗagowa ya yi saurin cire idanunsa a kanta, dama kallan tsab ya tsaya yake yi mata kamar an ce mashi tana kama da wata ko ance mashi idan ya zo ya kare mata kallo za'ayi mashi tambaya a kanta a ɗakin jarabawa. Kuma abin da zai baku dariya surar jikinta yake kallah ba ita ba, bare ma shape ɗinta, in baku manta ba na faɗa maku Leesharh tana da shape sosai, tana da diri.

Ji ya yi kamar an sungulesa da ya tsaya kare mata kallo. "Barka da dare Yah Ramish". Ta faɗa tana mayar da kallanta ƙasa. Shiru ya yi bai amsa ba. Almost 3 mins yana tsaye, sai can kuma cikin natsuwa ya ce. "Zaki iya zuwa ɗakin binciken mu? Dan ina buƙatar hakan, akwai wasu tambayoyi da nike san amsoshinsu daga gareki". Ya kai karshen maganar tare da ɗan gyara tsayuwarsa da kyau.

Kanta a ƙasa ta ce. "A shirye nike dan amsa dikkanin tambayoyinka". Jinjina mata kai ya yi, ya kuma ji daɗin amsarta da har yasa ya sauke ajiyar zuciya. "Zamu iya tafiya yanzu". Ya faɗa tare da juyawa ya yi gaba. A hankali ta miƙe tsaye, vail dake ɗaure a kanta ta ware ta yafa a kan nata dan ya ɗan rufe mata shoulder ɗinta, bata jin daɗin ganin jikinta a buɗe ko da kaɗan ne, kun dai san mu Nigerians wlh mun fita daban, mun fi kowa kunya fa nike faɗa maku, kunya kuma shi ne cikon addini, idan babu kunya ba za'a samu tausayi ba, idan babu tausayi ba za'a samu imani ba, idan kuma babu imani ku faɗa mun me amfanin mutum?.......🤔

Bayansa ta bi yana tafiya kamar wanda bashi da lafiya saboda kasala. Ta yi mamakin ganin ta hanyar da suka bi, ta kai shekara a gidan amma bata taɓa sanin wannan waje ba, kuma a part ɗinsu ne, bata taɓa zatan akwai wani hawa a sama bama, saboda a tinaninta su ne a hawa na karshe, ashe akwai wani hawa, ta sha madarar mamaki lokacin da ta kalli wani siririn stair case mai amfani da remote a cikin part ɗin nasu. Har tsoron haurawa sama ta ji, dan taga stair case ɗin kamar zai nitse da ita ne, yana nan a kanannane kamar indomie, fargabarta na biyu ma kada su hau ya karye da su dan ya yi sirantaka.

Sai da ta ga ya hau babu abin da ya faru sannan ita ma tasa kafarta kamar ba zata taka ba ta hau. Ai a miliyan ta sauko jin stair ɗin yana yin kamar akwai spring a jikinsa, irin idan ka taka sai ya yi ƙasa, in ka cire kafa sai ya yi sama, dik confidence ɗinta ta ji ba zata iya hawa wannan waje ba. A jikinsa ya ji kamar ta kasa haurawa, dan dama already yasan wannan stair case ɗin matsoraci ko mai hawan jini ba zai iya hawa ba, sai su jaruman maza.
Sai da ya haura sama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login