Showing 207001 words to 210000 words out of 403653 words

Chapter 70 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

89

ba, daga karshe ma da aka ce mashi Auta taki cin abinci zata iya cutuwa.

Murje idanunsa ya yi ya ce ta mutu idan taga dama, amma babu ita babu auren mayaki, da ya bata shi gara ta mutu ɗin. Tashi sense, jin wannan furuci na King yasa suka fahimci ba fa zai saussatawa Hoorain ba tun da dik yadda yake san Auta ya ce ta mutu ai shikenan kuma sai dai a bishi da ido. Daga haka suka sallama babu Auta babu Hoorain.

Dik wannan bidiri da ake yi wlh Jaish yana jinsu bai saka baki ba, dan bai ga abin faɗe ba. Dik duniya an rasa mai shawo kan King a wannan gaɓa, yaki bawa momma damar ta zauna da shi ma, dan yasan zata iya kuresa, da ta zo ɗakinsa zai fice izuwa part na Akka, saboda baya san sassautawa kowa a kan wannan al'amari.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

AUTA😥🔥

Kwance take a saman bed ɗin momma, yanzu King ya saka mata tsaro da idanu sosai wai dik dan kada ta je wajen Hoorain, bata fita ko nan da can, tana cikin ɗaki, ita ma ba dan bata da lafiya ba King ya yi niyar hukuntata saboda kawai dan ta so Hoorain ta yi laifi, rashin lafiyarta ya ja ya kyaleta.

Guyson yana zaune kusa da ita yana cigaba da dannar zuciyarta yana bata hakuri, su Mahnoor suna tare da momma a parlour suna hira, momma dai tana ganin musifa kala kala a cikin gidan nan, sai dai ta dogara ga Allah shiyasa har yanzu bata faɗi ƙasa ba.

Wayar momma dake kusa da ita ne ya fara kara alamar shigowar kira. Ɗauko wayar ta yi, lokaci guda ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, a fili ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil, sannan ta yi picking call ɗin.

Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Hello momma". Gabanta ne ya sake bada dum dum, da kyar ta iya amsawa. Kai tsaye ta cikin wayar aka ce mata. "Ina Zunaira?". Mai maganar kamar muryar Abu Abdussalam haka.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Zunaira tana barci......." Bata gama faɗar hakan na diff aka katse kiran. Miƙewa tsaye ta yi, cikin hanzari ta nufi part ɗin King tana faɗawasu Mahnoor kowacce ta wuce ɗakin mijinta dare ya yi.

Miƙewa suka yi gabaɗayansu, Mahnoor ta wuce part ɗin Jaish, a sati ɗaya da Mahnoor ta yi da Chuchu har ta koyi wasu abubuwa, Chuchu tana koya mata kula da miji, Mahreen ma sai kara wayewa take yi a wajen mama Haulat, Pretty tana tare da Mahreen a wajen mama Haulat, yanzu hankalin kowa a tarshe yake a kingdom of power.

Mahnoor ta nufi part ɗin Jaish, Mahreen and Pretty suka nufi wajen mama Haulat, dama ita Chuchu tana kirjin Yah Jawad a yanzu, Zee ma miƙewa ta yi ta koma bedroom na Aneesa, yau Khadijah ta dawo cikin family part, an sallamota daga asibiti, shi kuma mai napep ɗinsu da yake ya samu karaya har yanzu bai samu sauki ba.

Sai kuka Auta take yi guyson yana ta rarrashinta, shi ma dai ba wani ƙoshin lafiya sosai ke garesa ba, amma ya daure yana ta lallaɓata.

Zuciyarta kamar zai fashe ta ɗago kanta, fuskar da ya yi jaga jaga da hawaye, muryarta a dashe ta ce. "Yah Omar ka faɗa mun me Hoorain ya yi da ya cancanci wannan hukunci daga wajen daddy? Bafa shi ya ce yana sona ba, ni na fara cewa ina sonsa, kenan laifine in so wanda zuciyata take so?". Ta kai karshen maganar tana mai da kanta ta kifa a saman pillow.

"Ba laifi bane, amm kuma ki sani abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hangosa ba, tabbas daddy ya ɗan kauce a wani gaɓar, amma ki sani saboda sanki yasa ya yi hakan dikka". Cewar guyson.

"No Yah Omar, ba so bane, idan so ne ku so abin da nike so, zuciyata zafi take mun Yah Omar, ni kam ina ganin mutuwa kawai zan yi".

Da sauri ya katseta da cewa. "Kada ki sake cewa ba sanki muke yi ba, kin san yadda kike a zuciyar kowa dake gidan nan kuwa?". Miƙewa zaune ta yi tana goge kwallah. "Yah Omar idan har kana sona kuma kana supporting ɗina to ka tabbatarmun da hakan yanzu ta hanyar kaini wajen Hoorain!".

Tashin hankali, zado idanu guyson har kamar idanunsa zasu faɗi ƙasa. "Kin san me kike faɗe kuwa?".
Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas tasan abin da take faɗe....... "No Zunaira, no, i can't do that, kin san hukuncin da zamu fuskanta a kan hakan kuwa? Kin san daddy zai iya tsaremu a prison ko baki sani ba? Kin manta cewa dik wanda ya taka dokar daddy hukunci na hawa kansa ko da ɗansa ne ko?". Ya jefa mata tambayar cikin ruɗu da tashin hankali.

A hankali ta koma ya kwanta, wani irin kuka ne ya ci karfinta, tana wani irin shessheka ta fara magana ƙasa ƙasa. "Ni dama nasan kai ma kana cewa kana supporting ɗina ne kawai dan ka kwantar mun da hankali amma ba wai dan kana san zaɓina ba". Tana kuka tana faɗa.

Allah sarki guyson, idanunsa sun ciko da kwallah sosai, kamar zasu zubo, murya ya karaye ya ce. "Zunaira ki dai'na faɗin hakan, wlh da gaske ina san zaɓinki, ina sansa sosai, dik abin da kike so ina sonsa, amma ki fahimceni, babu ta yadda za'ayi na kaiki wajen Hoorain, idan daddy ya sani kinsan ransa zai yi mummunar ɓaci, kuma zai hukunta mu".

Miƙewa zaune ta yi, so take yi ta yi mashi wayo ya kaita taga jaruminta, kasan bed ɗin ta sauko a in da ta nufi jikin bangon kusa da toilet, binta da kallo ya yi yana mamkin in zata je. Kafin ya farga sai yaga ta fara buga kanta da jikin bango tana sambatu a kan kowa baya san zaɓinta gara kawai ta kashe kanta kowa ya huta. Dim fa salan yaudarar guyson take san yi, tasan halinsa da raunin zuciya, zai iya aikata komai idan yaga zata cutu, shiyasa ta yi mashi dabara haka.

Da gudu ya diro kasan bed ɗin, kai tsaye ya nufeta, cikin zafa ya damko hannunta ya janyota ta faɗa jikinsa, hat gaban goshinta ya fashe ya fara jini, hawaye guyson ya fara yi, cikin kuka ya ce mata. "Ba zaki kashe kanki ba, tabbas zan kaiki ɗakin duhu wajensa koda daddy zai hukuntani, ɗauko alkyabbarki ki zo mu tafi". Ya faɗa tare da saketa yana kai hannu ya fara goge hawayensa.

Bata bi ta kan kukan da yake yi ba, da sauri ta ce. "Yah Omar ba sai na saka alkyabba ba, kawai mu tafi". Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "No ki sitirta jikinki, kinga dai kayan barci ne a jikinki, maza ɗauko alkyabbarki bari in duba akwai mutane a parlour ne". Ya kai karshen maganar tare da nufar parlourn yana cigaba da goge hawayensa.

Dressing room na momma ta nufa da gudun gaske. Alkyabba ta ɗauko ta fito, tana fitowa shi ma yana shigowa cikin room ɗin, ya duba parlour babu kowa. Murya ƙasa ƙasa ya ce. "Zo mu tafi babu kowa a parlour".

Ai tin kan ya faɗi haka ta yi saurin wucewa. Hannunta ya riko suka fito, ina wannan hanyar sirrin nasu da Hoorain ya taɓa kawota wajen a lokacin da mayakan Queen Zarina suka kawowa kingdom ɗin hari? Kun tuna lokacin da ya ɗaukota daga gonar King ya kawota wajen su momma a wajen?.

To ta wannan hanya suka bi, underground kenan, ko da suka shiga wajen sun rufo kofar kamar ba'a taɓa buɗewa ba, da sauri ya kunna hasken wutar wayarsa, saboda babu haske a wajen. Hannunta ya ja da sauri suka bi ta wajen, sai shera hawaye take yi, shi kuma sai rarrashinta yake ta kara yi. Sun yi tafiya mai nisa kafin su tsaya a wani waje mai ɗan faɗi idan da hanyar suka rabu kashi uku, tsayawa ya yi yana tinanin wani hanya ce wadda zata sada shi da prison na kingdom ɗin nan? Dan a cikin prison ɗin ɗakin duhu yake.

Ya ɗauki a kallah 5 mins yana tinani kafin ya jata suka sake miƙewa kai tsaye suka nufi wajen. Kunsan masarauta idan ta kai masarauta akwai ire iren waɗan nan hanyoyi na sirri ta ƙarƙashin ƙasa waɗan da zasu sadaka da kowani ɓangare na cikin Kingdom ɗin ya kasa, dik salan dabarun yaki ne.

Guyson kamar bai san komai ba, amma sai ga shi yasan hanyar sirri, kai tsaye ya kaita har in da ɗakin yake, sannan ya tsaya da kyau wajen tinanin a dai'dai ina kofar take? Amfani ya yi da ƙwaƙwalwarsa da Allah ya bashi wajen gano kofar,. Duƙawa ƙasa ya yi Auta ta haye saman shoulder ɗinsa, karfinsa yasa wajen miƙewa da ita tsaye, dan shi tsawonsa ba zai kai ya iya buɗe kofar ba, sai ya ɗagata dan ta buɗe.

Hannunta tasa wajen tura kofar, ba koface kamar kowacce kofa ba, tiles ce ta yadda ba za'a taɓa gane akwai kofa a wajen ba sai wanda yasan da wajen, so dikka kofofin hanyar underground ɗin nan tiles ne ta ciki.

Tura tikes ɗin ta yi ta buɗe ta ciki kenan, tiles ɗin ya buɗe ta in da Hoorain yake kenan.

Ganin ya buɗe yasa guyson ya ce. "Ki haura ki je ki gansa, kada ki wuce 5 mins dan kada a nememu, sannan ki kula akwai masu gadinsa daga ta waje, kada ki bari su ganki".

Okey kawai ta amsa da shi kafin ta yi gaggawar haurawa ta fito ta cikin ɗakin, Allah sarki guyson, saboda yana san farincikinta saman shoulders ɗinsa ta taka da kafafunta ta haura sama, amma ko kaɗan bai damu ba, shi dai taga Hoorain ta yi farinciki ya wadatar.

Tana hayewa ta ce ya mashi. "Yah Omar ɗakin akwai duhu sosai, ka miƙo mun wayarka zan haska in gansa".

Kai ya girgiza mata kafin ya ce. "A'a ki je haka kawai, idan kika saka haske a ɗakin masu gadinsa dake waje zasu san an shigo ciki, da waje haka ki laluɓi in da yake kawai a cikin duhun".
Juyawa ta yi ta kalli cikin ɗakin, wani irin bakin duhu ta gani mai razanarwa, a hankali ta sake jiyowa ta kalli guyson dake kallanta.

"Ki je babu abin da zai faru In Sha Allah, ki kula sosai". Shiru ta tsaya tana jin tsoron shiga cikin ɗakin, saboda duhun. Kara mata kwarin gwiwa sosai guyson ya yi har sai da ta yarda ta miƙe tsaye, a hanzarce ta mayar da tiles ɗin ya rufe, ta fara laluɓen Hoorain a cikin duhu tana ambatar sunansa ƙasa ƙasa.

Ɗakin tsit baka jin motsin kowa, tamkar babu halitta mai rai dake a ciki. Sai yawo take yi a cikin duhu amma sam bata ga alamar zata ga halitta a ciki ba, har ta fara karaya ta fara jin kamar zata hakura. Can wani tinani ya zo mata a kan ta yi shiru tsit in dai yana cikin ɗakin tabbas zata ji sautin numfashinsa ko kuma bugawar zuciyarsa. Haka kuwa aka yi, ta tsaya shiru tare da kasa kunnuwanta dan saurara.

A hankali sautin numfashinsa haɗe da bugawar zuciyarsa dake fita da karfi karfi ya fara ratsa dodan kunnenta. Natsuwa ta kara yi domin sauraron ta ina sautin yake fitowa. Fahimtar daga ina ya fitowa yasa ta fara takawa ta nufi wajen a hankali hankali tana sanɗa.

Unexpectly ta ji ta daka tuntuɓe a in da ta buga kanta da kirjinsa, ko bata ga face ɗinsa ba tasan kirjinsa ne daka, da sauri tasa hannunta ta fara laluɓar jikinsa dan ta ji a wani hali yake ciki. Allah sarki, ɗaure yake cikin sarkoki masu girma da kauri, a tsaye yake a kan kafafunsa, a horon dama babu kwanciya, idan wata guda aka yankewa mutum haka zai kasance a tsaye tsawon wannan wata gidan, abinci ma masu gadi zasu bashi a baki, bashi ba motsawa, shiyasa dik wanda ya shiga ɗakin dubu dik ranar da aka fitar da shi kafafunsa basa iya takawa. Dan ko dare ne a tsaye zaka yi barci, kafafu da hannaye dik a ɗaure suke da sarƙa, kuma an ware maka su ba ta yadda zaka yi ka zauna, abin dai gwanin ban tausayi.

Sosai hankalin Zunaira ya tashi, bugawar da kirjinta yake yi ne ya kara tsananta, kuka ta fashe da shi tare da fara jijjiga Lion chest ɗinsa tana ambatar sunansa a hankali.

Shiru bai amsa mata ba, babu alamar zai amsa mata ba, kuma yana numfashi bare ace ya suma, yana jiyota, magana ne ya ƙasa yi mata tamkar an ɗaure tongue ɗinsa, Allah sarki azaba ce ta yi mashi yawa, a yadda yake ɗauren nan jini ne yake zuba daga damatsan hannunsa da ya sha horo wajen warriors da King ya wakilta dan hora shi, sun dakesa da bulalar kaca mai kifiyoyi a jiki, sannan suka zanya mashi gishiri a dik in da fatarsa ta fashe dan tsananta mashi horo, ya kara jin azaba kenan.

Da yake a cikin duhu ne ɗin Zunaira bata ga wannan ba, ita dai kuma kawai take yi tana jijjiga ɓulɓul ɗin breast ɗinsa. Ganin ba zai amsa mata ba yasa ta laluɓi saman face ɗinsa ta ɗaura hannunta a kumatunsa, a hankali ta ɗaga kafafunta ta kara tsawo, a saman kirjinsa ta kwantar da kanta tare da laluɓar ɗan bakinsa da hannunta dan ta yi shin an rufe mashi baki ne.

Yatsanta ta tura cikin bakinsa tana cigaba da ambatar sunansa, gabaɗaya kayan jikinta sun ɓaci da jininsa ba tare da ta sani ba.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, can ƙasan maƙoshinsa, da kyar ya iya furta. "My Hoonaira".

Jin alamar kamar ya yi magana yasa ta yi saurin ɗago kanta daga kirjinsa tare da kara ɗaga kafafunta ta haɗe fuskokinsu, hankalinta a tsananin tashe ta ce. "My Hero ka yi magana ne? Ka yi mun magana ne? Please kana jina? Meyasa ka yi mun shiru?". Out of control take zuba surutan nata.

Silent talk ya yi wajen cewa. "


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️







Silent talk ya yi wajen cewa. "My Hoonaira dama zaki sake yin tinanina har kizo in da nike?".
Kuka mai narka zuƙatan masoya ta saka mashi, a hankali take ɗan bubbuga hannunsa a saman lion chest ɗinsa, da kyar muryarta ya samu damar fita ta fara faɗin.

"Kamanta dama na faɗa maka ko zan mutu babu gudu ba ja da baya ne? Ba zan taɓa iya rabuwa da kai ba, kai ɗin jinin jikina ne, please my Hero kada wani wuya yasa ka juya mun baya, In Sha Allah zamu yi nasara, nasan daddy yana kan fushi ne, idan ya sauko zai saurareni, please ka t............".

Wani irin tari ne ya kubce mata wanda ya sanyata dan dole ta haɗiye sauran maganganunta, hannunta tasa da sauri ta toshe bakinta gudun kada tarinta ya fita ya sanya masu gadin su fahimci akwai mutum a ciki.
Su fa Modarawa haka suke da zuciyar bala'i, kada ku ga laifin King, zuciya a jininsu take, basu isa su cirewa kansu ba, shiyasa kuka ga King a haka, wai baku ga dikka jikokin Akka idan sun fusata haka suke rikiɗewa su zama basa ji kuma basa gani bane? To gado ne shi ma wannan tin zamanin jahiliyyah.

Allah sarki yana san rungumarta ya rarrasheta amma babu dama, saboda dikka hannayensa a ɗaure suke. Yana jin raɗaɗin kukan da take yi har cikin ransa tana ratsa shi, amma babu halin taɓuka komai, muryarsa bata fita sosai yake ta faman ce mata ta yi shiru ta daure, sam bata jin me yake faɗe, sai da ta yi kuka sosai har tasa zuciyarsa ta fara yi mashi ciwo, sannan ne ta komar da kanta saman kirjinsa ta kwantar tana shessheka mai taɓa zuciya.

A hankali ta zame hnnunta daga ɗan bakinsa, sannan ta ɗago kafafunta tare da sanya hannayenta ta saƙalo wuyarsa da shi, ta haɗe fuskokinsu waje guda, murya a sarkafe ta ce. "My Hero, promise that ko wani hali zamu shiga tabbas zaka tsaya a kan soyayyarmu babu gudu ba ja da baya".

A yadda take maganar lausasan lips ɗinta suna taɓa nashi yasa gabaɗaya ya jisa a wani sabon babin na yanayi, gabaɗaya sai ya kara jin kasala sosai, dama ba wani kwari ne da jikin nasa ba. Da kyar ya iya cewa. "Ba zan taɓa juya maki baya ba my princess, dik wahalar da za'a bani matsawar ina numfashi to tabbas zuciyata zata yi kowacce bugawarta ne da sunanki, ba zan janye ba sai dai a kasheni ko kuma ke ki juya mun baya!!".

Kai ta fara girgizawa kafin ta ce. "Ba zan taɓa juya maka baya ba ka ji?". Kai kawai ya jinjina mata yana cigaba da sauke numfashi mai ban tausayi.

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Khadijah and Zee ne zaune a saman sofa a part ɗin mama bedroom na Aneesa. Su biyu ne kawai a cikin ɗakin, sai hira suke yi Zee tana jin daɗi Khadijah ta samu lafiya.

Khadijah dai ciwo bai rage mata komai ba, sai kiba ma da ta kara, kumatunta ɓulɓul gwanin sha'awa, momma ta ce ta fara bawa babynta nono tin da ta samu lafiya, dan nonon uwa ba ƙaramin abu bane, idan yaro ya rasa shi ma sai kuga ya girma ga shi ga shi nan ne kawai.

So tana rike da babyn a hannunta, dikkansu kayan Aneesa suka sanya, sun yi kyau matiƙa, sai dai dik in ka kalli

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login