Showing 213001 words to 216000 words out of 403653 words
MieMie ce ta capki zancen da cewa. "Daddy ni kaina baka taɓa sanya hannu ka dakeni ba, ba ni ba, na tabbatar gabaɗaya tun daga kai'na har kan Obaid baka taɓa ɗaura hannunka a jikinmu da sunan duka ba, kuma dik mun san cewa kafi san Auta fiye da kowa, dan Allah daddy ka dubi irin san da kake yi mata, ka yi mata afuwa ka dubi irin san da take yi wa Hoorain..........".
Kasa ƙarisa maganar Aunty MieMie ta yi sakamakon wani irin kallo da King ya wurgo mata, cikin kakkausar murya ya ce. "Wlh na yi rantsuwa da girman Allah, ba zan taɓa bawa Hoorain Zunaira ba, idan zata mutu ta mutu, ba zan yi kaffara ba, wlh billahi na yi mata iyaka da shi, babu ita babu shi, idan taki kuma to tabbas zan sa a kashesa".
Ai Auta tana jin karshen maganar King bata san lokacin da ta zabura ta miƙe tsaye ba, kisa kuma? Ta maimaita a ranta, ba komai ya ɗaga mata hankali ba face tasan mahaifinta baya magana biyu, tsab zai aikata abin da ya yi niyya, tabbas zai iya sawa a kashe Hoorain.
Cigaba da magana cikin bada umarni King ya yi yana mai kara kausasa murya. "Daga rana irinta yau ko parlourn nan na haramtawa Zunaira fita, zata kasance ne a cikin ɗakin mahaifiyarta, dakin takalma ban yafe ta yi domin fitowa waje ba, sannan na taraku a nan ne dan ku shaida na bawa Abdussalam aurenta, (Abdussalam ɗin Abu Abdussalam kenan) ko taki ko ta so shi ne mijinta, kuma ba zan jira wai sai ta girma ba, dan girma ya kare tin da har tasan ta je wajen Hoorain, har tasan tana san Hoorain, cikin ƙanƙanin lokaci za'ayi auren ya wuce da ita Dubai!!!!".
Da alama ran King ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, dik cikin parlourn babu wanda bai tausayawa Auta ba, har momma ta ji tamkar tasa kuka, amma ta daure tana jin zafin hukuncin King a ranta, amma fa Mammie ta ji daɗin hakan, dan ita burinta ta gansu cikin kunci a kullum.
Ƙasa ɗaukarta kafafunta suka yi, durkushewa ƙasa ta yi a saman gwiwowinta a gaban King, tana kuka tamkar ranta zai fita, ta kasa yin magana sai kerma da jikinta yake yi, lokaci guda jikin nata ya ɗauki zafi raw kamar wuta, alamar zazzaɓi, kanta na sara mata da karfi karfi, tana san rokon King da ya yi hakuri ya yi mata afuwa amma ta kasa iya buɗan baki ta yi magana.
Lokacin guda wani irin lallausan kamshi ya daki hancin kowa dake cikin parlourn, gabaɗayansu sai da suka shaki wannan kamshi suka lumashe idanu. A miliyan Auta ta kai kallanta a kan kofar shigowa cikin parlourn.
Da karfi ta furta. "Yah Omerish". Ta yi maganar ne ba tare da taga kowa a wajen ba, da alama kamshin perfume ɗinsa da ta ji ne ta furta sunansa. Lokaci guda gabaɗaya parlourn suka kai kallansu a kan kofar shigowa ganin taga wajen ta kuma furta sunan da basu taɓa jinsa ba.
A miliyan Sarina ta miƙe tsaye tana cigaba da kallan kofar shigowa tana shaƙar wannan daddaɗar kamshi da yake buga mata hanci.
Ruɗewa Auta ta yi ta fara ƙoƙarin nufar kofar fita. Tsawan da King ya daka mata ne yasa ta dakata cak kallanta a kan kofar shigowa.
A hankali aka turo kofar parlourn, Jaish ne ya sanyo kai kafin Smart namu na kasar France ya rufa mashi baya. Ihun sunansa da karfi Auta ta yi Yah Omerish sannan ta tafi da gudun gaske ta faɗa jikinsa tana sakin kuka mai sauti.
Gabaɗaya parlourn zaro idanu suka yi suna kallonsa. A miliyan momma ta miƙe tsaye tana dafe saitin zuciyarta dake mata barazanar tarwatsewa........... King kuwa, ya zaro idanu ya kalli Auta ya sake kallan Smart, saboda kaman dake a tsakaninsu, shi dai Auta kawai ya sani, to wanenne wannan mai kama da ita ɗin? Ya jefawa kansa tambayar cike da mamaki game da ƙaguwa da san jin wanene?.
Cikin wani irin murya a mai kama da marairacen murya momma ta furta. "Omerish meya kawoka nan? Meyasa ka zo? Meyasa baka sanar da ni zaka zo ba?".
A miliyan King ya dawo da kallonsa a kan Momma, ita ma Akka ta dawo da kallanta a kan momma, nan ta dikka family suka dawo da kallonsu a kan momma.
"Dama ni nasan tabbas a shekarun baya karya Rahilarh ta yi mana, a lokacin da wancan matsala ta faru tabbas nasan Rahilarh munafurtarmu ta yi". Cewar Mammie da ta gaza iya haɗiye abin da yake ranta.
Sarina kuwa, miƙewa tsaye ta yi kallanta a kan Smart da ya rungume Auta yana cigaba da goge mata hawaye yana kallan momma, shi bai bi ta kan King bama, dan bai ma san wanene King ba, iya momma da yaranta kawai ya sani, bayansu shi bai san kowa a cikin kingdom of power ba.
My people's me kuke tinanin ya kawo Smart kingdom of power? Me alaƙarsa da momma? Ya aka yi yasan su Jaish bai san su Ramish ba? Me ya faru a shekarun baya da suke ikirarin momma ta munafurcesu?. To dama na faɗa maku a week ɗin nan zaku sha surprises, taku dai har kullum Princess Teema queen of surprise!!.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
34
"Omerish". King ya maimaita sunan kallansa a kan momma da ta miƙe tsaye tana zaro idanu. Lokacin guda ta fara kame kame alamar rashin gaskiya.
"Wani isasshe ya sanya Zunaira kuka a cikin gidan nan? Dama abin da kike ɓoye mun kenan momma? Yau tsawon 2 month kenan tin kafin na yi tafiya (duniyar wata) har na yi na dawo kullum idan na kiraki na ce ina Zunaira sai ki yi ta kauce mun, ashe zalintarta ake yi kika ɓoye mun? Shiyasa hankalina ya gasa kwanciya mana! Me ta yi maku kuma waye ya mareta a face ɗinta?!!" Cewar Smart, ya kai karshen maganar cikin kakkausar murya.
Gabaɗaya parlourn tsit suka yi an rasa mai bashi amsa, dan dik sai da suka sha jinin jikinsu ganin kwarjin dake face ɗinsa, an rasa mai tanka mashi, shi kansa Jaish shakkarsa yake yi dik da sun yi sabo matuƙa, amma yana shakkar wani ɗan abin da ya saɓa ya haɗasu.
Akwai wanda ya taɓa tina lokacin da Jaish yake yi wa su Omaid nasiha time da zasu koma school? Kun tina a cikin nasihar da yake yi masu ya ce in basu natsu sun mai da hankali a kan karatu ba zai mayar da su ƙasar Faransa! Kun tina wannan lokaci? To wajen Smart yake nufi kenan, baku ji su Omaid ɗin sun ce ya yi hakuri gara masu Yah Ramish a kan Faransa ba? Basa san zuwa wajen Smart dan ubansu zasu ci, sau biyu suka taɓa kai mashi ziraya kafin su dawo sai da suka haddace rabin Alqur'ani mai girma, suka natsu kaman wasu malaman da'awa, da suka koma Dubai sai suka watse...........😅
King dai kusan suman tsaye ya yi, saboda ganin abin yake yi tamkar a mafarki, ya aka yi Smart yake kama da Zunaira over haka?.
"Okey ba zaku iya faɗa mun wanda ya mari Zunaira ba sai ran kowa ya ɓaci ne?". Smart ya yi maganar cikin kakkausar murya again.
Tsit suka yi har lokacin an rasa mai iya tanka mashi, Sarina tini ta sha jinin jikinta, a tinaninta yadda Smart yake a hotonsa da ta sato daga ɗakin momma haka yake a zahiri, sai taga ina, wannan da zafi sosai yake.
•••••••••••••••••••🔥
Uncle Abbas ne ya yi ta mazan miƙewa tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Mahaifinta ya hukuntata". Wani irin kallo ya jefi uncle Abbas da shi wanda yasa su Dr Raj zaro idanu waje, dan kallo ne mai kama da mugun kallo.
"Saboda shi mahaifinta ne sai aka ce ya zalinceta? Meta yi mashi? Shi yaga face ɗin Zunaira ya yi kalar wanda za'a ɗaura hannu da sunan duka a kai ne?". Yana magana yana bin uncle Abbas da mugun kallo.
Tashin hankali, zaro idanu gabaɗaya parlourn suka yi, barema ita momma da ta fi kowa shiga damuwa, dan kana ganinta zaka san tana cikin tashin hankali.
A karo na biyu uncle Abbas ya sake yin karfin halin cewa. "Mahaifinta fa nace maka ba wani ba, and wanenen ma kai da ka shigo mana cikin family without our permission?".
Shiru Smart ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Then so what idan mahaifinta ne shi? Akwai in da aka bashi damar ya zalinceta ne?". Shiru gabaɗaya parlourn suka yi suna kallansa da mamaki, hankalin kowa a tashs, wai King yau ake cewa meyasa zai hukunta Zunaira? Tashin hankali lallai Smart ya zo da sabon alamari.
Uncle Abbas ne ya sake yunkurawa zai yi magana Smart ya ɗaga mashi hannu cikin zafa alamar ya ja bakinsa ya yi mashi shiru a wajen. Cike da isa ya ce. "Bana san na sake jin ka bani amsa, babu wasu mutane a cikin parlourn ne sai kai?". Ya yi maganar yana mai da kallansa a kan King da ya rasa bakin magana kawai yana kallan momma.
Jaish ne ya ce. "Yah Omerish uncle Abbas ne fa, he's our second dad, why kake yi mashi magana haka?". .............. "So what idan kanin dad ne? Da shi na yi magana ne da zai rinƙa amsa mun?".
Zaro idanu Akka ta yi tana kallan Smart. (Akka taga wanda ya fita iya hau😅)
Shiru Jaish ya yi bai sake yin magana ba, dan shi yasan waye Smart. Akka ce ta katsesu da cewa. "Wanenen kai wai da ka shigo cikin family na kake neman tayar mana da hankali ka canza mana alkibla?". Ta faɗa tana ɗaure fuska sosai. Dan ita ma Akka ta sha jinin jikinta ne yadda taga yake mugun kama da Auta, sai ta sha jinin jikinta.
Wani irin kallo ya bi Akka ɗin da shi, shiru bai amsa mata ba, bashi ma da niyar amsa mata.
Mummyn Chuchu ce ta miƙe tsaye, cikin sanyin murya da magana cike da dattaku da sanyin word irin na uwa ta ce. "Ai kamannin dake face ɗinsa kawai ya isa ya baku amsar wanenen shi ba sai kun nemi ji daga bakinsa ba, babban yayanku ne mana, ku baku ga kamanninsa da Zunaira ba ne? Baku ga kamanin Rahilarh a face ɗinsu bane?".
Ai a miliyan su Dr Raj suka zaro idanu, a zabure mama ta miƙe tsaye, hankalinta a tashe sosai ta ce. "No........ Impossible!!, ta ya aka yi ya zama yayansu? Kin dai san bayan Ramish babu wani babba a gidan nan ai!".
Uncle Jahiz ne ya miƙe tsaye shi ma, a kan momma ya tsayar da kallonsa, a nitse ya ce. "Momma ki warware mana wanene shi, dan nasan ke kaɗai zaki bada wannan amsa mu fita cikin duhun ruɗani".
Yana rufe maki Smart ya dubi King ido cikin ido, talk without respect ya ce. "Me Zunaira ta yi maka ka daketa?".............. Subhanallah, idanun da jama'ar cikin parlourn nan suka zaro sai ya bawa mutum tsoro, hankalinsu ne ya kara tashi, ba'a taɓa yi wa King magana yadda Smart ya yi a yanzu ba, King fa, tab lallai akwai matsala.
Momma ne ta katse shi cikin ɗan ɗaga murya.
"Omerish daddynku ne fa! Meyasa zaka yi magana haka without respect?"........ Ɗan waro idanunsa a kan King ya yi kafin ya ce. "Ko baki faɗa mun ba i already knew that she's my dad, bcoz of his face, yana kama da su Ramish, so ai already knew that, kawai ya faɗa mun dalilin da yasa ya daki Zunaira?".
Tashin hankali, King kuma daddyn Smart? To fa!! Ya aka yi hakan ta kasance? Daddynsa na Paris fa? Waye shi da har suke kama sosai?...... Tsit suka yi, gabaɗaya Mammie ta ji cikinta sai murɗawa yake yi, mama hankalinta ya kara tashi sosai, a tinaninta Ramish shi ne magajin mahaifinsa, tana jin daɗi itace mai power, har tana hasashen gaba kaɗan ita ce zata zama mai murza kambun power crown da ya fi kowani crown karfin iko, ta yi mulki san ranta, ta gama tsara plan ɗinta rana tsaka kawai a wargaza mata komai a wani ce Smart ɗan King ne? Tab aikuwa ba zai yiwu ba.
Auta dai ta kwanta shiru a jikinsa tana shessheƙar kuka, Omaid and Obaid da yake sun san ko waye Smart sai suka kara natsuwa suna kallan wannan tashin hankali da aka shiga. Ita kuwa Mammie burinta kawai a warware masu wannan cakwakiya dan tasan wani mataki yakamata ta ɗauka.
"Tambayarki fa nike yi Rahilarh, wanenen wannan?". Cewar King, dan hakurinsa ta fara kurewa, saboda ya zo har wuya yanzu, abin ku da jinin sarauta, basa ɗaukar raini, maganar da Smart ya yi mashi without respect shi ne ya bakanta ransa yake san hukunta Smart, amma sai yasan wanene shi tukun nan, dan tin da ya ɗaura idanunsa a kan Smart ɗin ya ji wani irin kaunarsa ya ratsa mashi zuciya........ Babbar magana!!.
"Ɗan kane". Tashin hankali, momma ta bawa King amsa tana kallan cikin idanunsa. Zaro idanu King ya yi tare da sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, ɗana kuma?. Ya maimaita kalmar a cikin ransa. Lokacin guda ya ji wani irin sanyi ta ratsa zuciyarsa, dik da bai san ta ya aka yi Smart ya zama ɗansa ba, ba shakka ya ji sanyi a ransa, sai dai kuma ta wani ɓangare ya ji ransa ya sosu matuƙa, dan dik cikin ƴaƴansa babu wanda ya taɓa yin gigin yi mashi magana yadda Smart ya yi mashi, kowa respecting ɗinsa yake yi sosai.
Uncle Jahiz da ya ji zancen kamar a mafarki ne ya yi saurin cewa. "Momma how comes hakan zai kasance bamu sani na?". A ruɗe ya yi maganar.
Wani irin tsawa mama ta daka wajen cewa. "Ina hakan ba zai yiwu ba! Ta ya akayi ya zama ɗansa? Hauka ne abin?!!".
Kowa ya ji maganganun mama yasan meyasa take faɗin hakan. Ita dai mummyn Chuchu shiru abinta, amma dai ita ma ta ji babu daɗi a ranta dik da tasan cewa dama ba ita bace da mulki tin da Ramish ya girmewa Bilal, amma dai ranta ya ɗan sosu kaɗan bayyanar Smart.
Mammie kuwa mutuwar tsaye ta yi, tabbas tasan momma ta ɓoye Smart a rikicin da aka yi a baya, amma bata taɓa zatan irin wannan bayyana Smart zai yi ba, yaro ya fi ubansa zafa, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, ya dame King a zafin zuciya da jiji da kai, ga shi da magana kai tsaye babu wata ɗar ɗar, kuma magana a kaifafe, ga uban kwargini. Sosai hankalin Mammie ya kara yashi over, tinaninta ɗaya ya za'ayi su ga bayan King ga wani zakin ɗan nasa ya kara bayyana, idan ma ta ce zata auri King ɗin wlh waɗan nan zakunan ƴaƴan nasa zasu iya cinyeta da ranta, kai ta ko'ina abin babu sauki a gareta.
"Ki yi mana bayani ta ya aka yi wannan ya zama ɗana?". Cewar King kenan. Jinjina kai momma ta yi kafin ta ce. "Kowa ya samu waje ya zauna".
Babu musu suka koma saman sofas da suka tattashi suka zauna suna jiran momma ta kora masu bayani.
"Omerish ka samu waje ka zauna bari mu yi magana ko?". Cewar Momma. Bai musa ba ya wuce saman sofa mai zaman mutun uku ya zauna tare da zaunar da Auta a saman laps ɗinsa, sannan ya ce Guyson ya taso ya zo ya zauna a kusa da shi.
Da sauri guyson ya taso, dama tin ɗazun yake san yin magana amma ya kasa, dan shi ya fi kowa sabo da Smart, dik in aka yi karamar hutu a school sai ya je France, Auta kuma sai ta je Dubai Smart yake tura jirgi ya ɗaukota karkashin kulawar Jaish ba tare da sanin kowa ba, wani lokaci kuma Jaish ɗin ne yake ɗaukarta daga kingdom of power ya ce sun tafi yawo sai su wuce wajen yayan nasu a Faransa ɗin, in short dai guyson ya fisu sabo da shi sosai.
Shi kuma Smart ya fi shakuwa da Auta, dan kamar yadda take kama da shi a fuska haka jininsu ya yi matuƙar haɗuwa, tamkar ransa yake santa, yanzu haka dalilinta ya zo kingdom of power, dan tin kafin ya tafi duniyar wata yake san momma ta haɗa shi da ita, amma momma tana yi mashi kona kona, ba komai yasa ba kuma face Auta ɗin ta ɓata a lokacin, momma tana gudun faɗa mashi ta ɓata dan kada ya ce zai zo ko ya ɗauki wani mummunar mataki, shiyasa taki faɗa mashi, idan ya kira guyson ma ya haɗa shi da Auta shi ma ya yi ta yi mashi kwana kwana dan momma ta hanasa faɗa, haka Jaish ma, daga karshe da ya gaji ne yana dirowa daga tafiyar da ya yi ya ɗaga jirgi sai kingdom of power, kun ji dalilin zuwansa.
Gabaɗaya parlourn tsit suka yi bisa umarnin King, sun zuba idanu suna jiran su ji me momma zata ce, kowa idanunsa a kanta. Akka ta lura Smart ya fita zafa sai ta natsu, dan ta lura shi ya gado ainahin zuciyar king Abdul Malik, su King Zuhair dik basu gada yadda yakamata ba, ga wanda ya fisu zafa, tsit kuke jinta a parlour kamar babu ita!!.
Gyara murya momma ta yi kafin ta fara jawabi dallah dallah kamar haka.
"Kamar yadda na faɗa Omerish ɗanka