Showing 300001 words to 303000 words out of 403653 words

Chapter 101 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

132

royal palace ɗina, na mayar da matansa kuyanguna, na mayar da ƴaƴansa masu yi mun hidima, mazan kuma masu ɗeben kewa, na sa ya ɗanɗani ɗacin da ya ɗanɗana mana na kashe mun mahaifi da ya yi ya kuma ruguje Thomas family!!".

"Wannan kuduri naki ba zai taɓa kasancewa ba, na sha faɗa maki ki hakura kawai". Wata murya ce ta furta hakan a yayin da take ketowa izuwa cikin parlourn. Kyakkyawar matashiyar yarinya ce da bazata wuce 23 years ba duniya, fara ce tas kamar madara, kyakkyawar gaske ajin farko, tana shirye cikin alkyabbarta na sarauta na alfarma wanda ya sha kwalliya da duwatsun lu'ulu'u, da ganinta kasan jinin sarauta ce. Kwayar kyawawan idanunta sun kasance hazel eyes ne mai ɗan duhu, hakan yasa ya yi kama da green eyes sosai. Idanun nata basu da girma sosai, amma suna da kyau matuƙa.

Queen Zarina zata yi magana Ude ya rigata da cewa. "Ke Rishma kina da hankali kuwa? Ita kike faɗawa magana gatsau haka?". Da wani irin kallo ta bisu, da kaga wannan kallan kasan na takaici ne, sannan ta ce. "Ude idan baka tuba ba, babu shakka zaka mutum a kaskance, zaka mutu mutuwa mafi munin da ko kare sai ya fika daraja a wajen mutuwa........."

Dan dole ta haɗiye sauran maganar nata saboda wani irin uban tsawan da ya daka mata, ba shiri ta yi tsit tana jin kirjinta na bugawa da karfi karfi.
"Keeeeee Rishma, ki iya harshenki ko kuwa na datse maki shi a yanzun nan!!!!". Shi ne abin da Ude ya faɗa...... "Ude ba zan iya harshe na ba, ka rigada ka ketare iyakarka, na dai'na jin tsoron dik wanda baya tsoron Allah, tin kan lokaci ya kure maka Ude ka tuba...... ". A miliyan ta haɗiye maganar nata sakamakon nufarta da ya yi gadan gadan tare da cire hannu zai ɗauke mata fuska da mari. Sai dai kuma bai kai ga sauke mata marin ba aka rike hannunsa cak ta baya. Cikin wani irin fusata ya yi zafan juyowa dan yaga wani mai karan kwana ne ya rikesa. Sai wani irin huci mai zafi yake fitarwa, ran maza ya ɓaci. Ita dai Queen tana tsaye tana binsu da kallo.

"Kada ka sake ka ɗaura hannunka a jikinta Ude, idan kuma ka yi gangancin yin hakan tabbas hannunka ba zai sake kasancewa naka ba, dan sai na datse maka shi!!". Shi ne abin da wanda ya rike hannun nasa ya faɗa. Wani kyakkyawa mutum ne wanda da ka gansa kasan ɗan uwan princess Rishma ne, dan suna kama sosai, yana tsaye tsayuwar jarumta, cikakken namijin gaske ne, fari tas da shi, yana sanye da wani irin kaya mai kama da na warriors, sai dai ba su bane, wannan kayan jarumai ne.

Mamaki tamkar Ude zai sume a wajen ne ya bayyana a saman face ɗinsa, da kyar ya iya cewa. "Rishan ni yau kake kira da Ude?"....... Wani irin kallan kuna ya bisa da shi kafin ya yi wurgi da hannunsa da ya rike, sannan a gadarance ya ce. "Da kana da wani suna ne bayan Ude?". Babbar magana!.

Kum san menene yake tsakanin Ude da Rishma and Rishan? To Ude babban yayansu ne, ya juya masu baya saboda Queen Zarina, ba zaku taɓa fahimtar wani kulli bane a wannan masarauta sai nan gaba kaɗan, ta ya aka yi su Rishan suke matsayin musulmai shi kuma Ude dake matsayin babban yayansu yake katon krista? Ya aka yi Ude dake matsayin mijin Queen bai zauna a kujerar mulki ba sai ita? Meyasa yake biye mata kaman ita take da shi? Meyasa ya juyawa ƴan uwansa dikka baya ya bi addinin matarsa ya kuma damka mata ragamar garin a hannunta tana yin yadda ta so? Ina dattijo mahaifinsu Rishan yake? Menene dikka wannan rikicin. Gaba kaɗan zaku sha mamaki a kan wannan masarauta da kullin dake cikinta, akwai gagarumin case.

Sumar tsaye Ude ya yi, ya ƙasa yin wani ƙataɓus, bai taɓa zatan kannensa zasu juya mashi baya ba, su kuwa sun gaji da yi mashi nasiha ne, sun gaji da biye mashi suna sa ran zai juyo ya musulunta su koma yadda suke a da can baya, ya karɓi karagar mulkinsa ya cigaba da gudanarwa bisa adalci kamar a baya, sun gaji da dik abin da yake yi, yanzu babu wani sauran ɗaga kafa, dole su yi fito na fito da shi dan su samu salamar ciwon dake cikin zuciyarsu.

Wucewa Rishan ya yi ya riko hannun Rishma tare da janta suka fice daga cikin parlourn. Ko sau ɗaya Queen Zarina bata yarda ta ɗaura idanunta a kan Rishan ba, alamar akwai wata a ƙasa kenan, ta dai bisa da kallo da ya juya yana tafiya tana mamakin rikiɗewarsa..... A gabaɗaya kingdom of Justice ɗin nan, babu cikakken jarumi na cikin gida biyun Rishan, shiyasa suke shakkarsa, zance na gaskiya har Ude shakkarsa yake yi, idan yana magana a waje ba'a tankawa, namijin gaske ne. Har suka kurewa ganinsu Ude bai iya furta word ba, ya shiga ruɗani. Tsafin Zarina ya kasa yin aiki a kan mutane biyun nan, wato da Rishan da Rishma, kullum suna tare da Dattijo Muzaffar shi yake taimaka masu da shawari a kan dik abin da ya taso masu, su biyu suke rayuwarsu bayan juya masu baya da yayan nasu ya yi!.

Sai dai suka fice daga parlourn ne ya dawo da kallonsa a kan Zarina dake tsaye kamar bata a wajen, a hankali ya buɗi baki zai yi mata magana kenan ta yi saurin ɗaga mashi hannu. "Har yanzu yara ne, ka yi masu uzuri". Ta kai karshen maganar tare da wucewa fuuuuuu kaya na jan ƙasa, kamar wata kunfa ta wuce sama, tana wani taku mai kama da magic walk, sannan fuskarta ya nuna tabbas akwai wani abin, sai dai ita baka taɓa iya karantar ina ta dosa, baka sanin me zata aikata sai lokacin yin abu kawai kaga aiki da cikawa, ba shakka akwai abin da take da niyar yi a kan Rishan da Rishma, saboda yadda ta kallesu da suna barin parlon ba kallan lafiya ba. Matsawa kusa da stair case ɗin Ude ya yi yana cigaba da kallonta har ta kurewa ganinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya koma fada.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Zaune suke cikin wani haɗaɗɗen park mai matikar ɗaukar hankali, ya kaita yawace yawace sosai daga karshe ya biyo da ita a nan dan su ɗan huta. Sai dai fa dik wannan yawon da suka yi taki sakan jiki da shi. Dik in da suka je tana takure waje guda, bata ma san motsawa, dan dai yana matsa mata ne yasa take yarda tana binsa.

Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park ɗin ta gefe tana kallan yadda big girls suke nishaɗi suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta ɗaukarwa kanta alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waɗan nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar gidan Abbie, ba zata zauna ba.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








50



Zaune take saman wani tsadadden kujera dake cikin park ɗin ta gefe, tana kallan yadda big girls suke nishaɗi suna kaiwa da komowa, ta yi nisa cikin tinanin mafita a gareta, so take yi dik ta yadda za'ayi ta guje mashi, dan ta ɗaukarwa kanta alkawarin ko zata ci amanar kowa ban da Sharifat da Jasra na gidan AAJ, dan waɗan nan mutane biyun sune duniyarta, dan haka a kan ta auri Ramish gwara ta gudu ta bar gidan Abbie, ba zata zauna ba.

Tana can tana tinani shi kuma ya yi masu oder kayan sha mai tsabta, tsada da haɗuwa, bata san time da ya yi ba sai gani ta yi an ajeye mata abu a gabanta. A hankali ta ɗago da kanta ta ɗan saci kallansa ta ƙasan ido, while shi ma ita yake kallo, ya ga ta saci kallonsa, amma sai ya basar kamar bai gani ba ya ce mata bismilla ta sha mana. Kai ta ɗan girgiza mashi kafin ta amsa mashi da a'a ba zata sha ba ta ƙoshi.

Ƙasa sosai ya yi da murya, tamkar mai raɗa ya ce. "Please Aesh, ko kaɗan ne? Ba dan ni ba, dan Allah"...... Yunƙurawa ta yi zata yi mashi magana ya yi gaggawar sake cewa. "No Aesh, don't say anything please, kawai ki sha". Haɗiyi abin da ta yi niyar faɗa ta yi, sannan ta kai hannu ta rike stro dake ciki haɗaɗɗen cup ɗin, ɗan jujjuyasa ta yi kaɗan kafin ta ɗan duka ta sanya bakinta. A hankali ta ɗan zuƙa. Slowly ya ɗan lumshe idanunsa, dan har cikin ransa ya ji wannan zuƙa da ta yi, nisawa ya yi kafin ya ɗan kawar da kallonsa daga kanta yana mayarwa kan wayarsa dake vibrate. Call ɗin Bilal ne ya shigo, kamar zai yi picking sai kuma ya fasa tare da kashe wayar ma mai gabaɗaya, ya tura cikin aljihunsa sannan ya harɗe hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa, gabaɗaya ya zuba mata waɗan nan dara daran idanun nasa yana kare mata kallo.

A hankali take cigaba da shan abin tana ɗan tsuke fuska alamar ya yi mata sanyi sosai. Kamar ance ta ɗago ido tana ɗagowa suka yi four eyes, ɗan zaro idanu ta yi like wow and like kallan me kake mun?! Shi kuwa gera guda ya ɗan ɗaga mata kafin ya sauke ajiyar zuciya, abin gwanin birgewa sosai....... Wani irin kallo ta wurga mashi mai kama da harara, shi kuwa ya yi mata nuni da idanunsa izuwa kan cup ɗin alamar ta cigaba da shan abin da take sha bai san iskanci.
Make kafaɗa ta yi tare da girgiza kai, sannan ta ɗan ture cup ɗin gaba alamar ba zata cigaba da sha ba kenan. Ɗan jinjina kansa ya yi like irin yarinya baki sanni ba ne. A fili kuma sake nuna mata cup ɗin da ido ya yi alamar ta cigaba da sha...... Wannan kallo dai mai kama da harara shi ta sake binsa da shi kafin ta nuna mashi cikinta da hannu alamar ta ƙoshi ba tare da ta yi magana ba, alamar dai yau ƴar kurma kurma suke jin yi. Ɗan kawar da kallonsa daga kanta ya yi kafin ya ɗan yi gyaran murya kaɗan, sannan ya ce. "Aesh you're giving me to much of headache".

Tamkar bata ji sa ba ta cigaba da binsa da wani irin kallo, har cikin zuciyarta take rasa natsuwarta a dik lokacin da take kallonsa, sai dai kuma bata wani ɗaukar hakan a matsayin wani abin azo a gani, ta fi ɗaukar abin ma a matsayin tsoronsa saboda abin da ya shiga tsakaninsu.

Suna a haka masu kawo oder suka sake sauƙe masu tsadaddun plate masu shake da kayan fruits kala kala very fresh a ciki. A gabanta yanzu ma suka sauke, kallansa ta yi cike da mamaki kafin ta ce. "Wannan fa?".... "Is yours". Ya bata amsa yana kallan yadda kankanar ta yi balai'n kyau, sun yankata shape of heart kanana da manya, gata jajir zata yi zaƙi.

"Ni gaskiya na ƙoshi mu tafi gida". Ta faɗa kallanta a kansa..... "Babu in da zamu je matsawar baki sha fruits ɗin nan ba". With full confidence ya bada amsar, irin da gaske yake yi ɗin nan. Bata da zaɓin da ya wuce dole dole ta sha, tamkar zata saka mashi kuka ta kai hannu saman plate ɗin, sai kuma ta ƙasa ɗaukar komai, saboda yadda aka yayyanka fruits ɗin shape of heart ya yi matuƙar birgeta, tamkar ance masu masoya ne suka yi oder, basu san waɗan nan abokan faɗa bane.

Ta shagala da kallan fruits ɗin tana tinanin wanda yakamata ta fara ɗauka unexpected ta ga hannunsa a cikin plate ɗin, a hanzarce ta saci kallansa, sai dai kash, tana ɗagowa suka haɗa ido, da sauri ta kawar da kallonta a ranta tana faɗin shegun idanunsa a wajen kamar ball, sai ya yi ta kallan mutum, kuma ga idanun nasa da shegen saka mutum cikin shakku da tsoro, sai yasa ka ji baka yarda da kanka ba, shi tsabar kwarewarsa a aiki ma kana haɗa ido da shi zaka ji baka da gaskiya koda kana da shi, yasa ka ka ɗaurawa kanka laifin da baka aikata ba dan bala'i irin nasa.... Kai Leesharh da Ramish duniya ne, wai yasa ka kaɗaurawa kanka laifin da baka aikata ba, wlh Leesharh akwai ƴar air nike faɗa maku, ta za'ayi baka aikata laifi ba ka ce ka yi? Ko da yake sai dai idan baka tsargu ba, tsab zaka ce ka yi bayan baka yi ba.

Shikuwa bawan Allah, kankana ya ɗauka tare da sanya mata a hannunta. "Idan na tsaya jiranki ki zaɓa za mu kwana a nan, oya take this one". Ya kai karshen maganar yana sanya mata shi a cikin hannunta, sannan ya janye hannunsa baya. Ɗan ɗaure fuska ta yi tare da wurga mashi hararar kasar ido, a cikin zuciyarta ta ce mugu kawai, ba zan yafe maka ba koma me zaka yi mun. A fili kuma ta kai kankantar saitin bakinta ta ɗan gatsa. Wani irin sanyin daɗi ta ji kankanar ta yi mata, ga zaƙi ga shi daga freezer aka cirosa, ai bata san time da ta sauke ajiyar zuciya ba, babu wanda ya ce Leesharh kara ta sake mayar da ragowar bakinta a gaggauce zata sake gatsa, sai dai kuma bata kai ga gatsan ba ya kai hannu ya kwace kankanar, dama ta gatsi rabin heart a gatsan farko, dan haka sai ya kwace rabin ya kai ɗan bakinsa.

Ai a miliyan ta ɗago da kallanta a kansa, kawar da kansa ya yi tamkar bai aikata komai ba, harara ta dallah mashi kafin ta sake daukar wani kankanan. Sarai ya kalleta, amma ya yi kamar bai ganta ba, shi dai burinsa ya ga ta dawo da walwalarta tamkar da, ya ga ta koma fara'a tana murmushi ta saki jiki, shiyasa yake tsokanarta dan ta saki jiki da shi. Amma ita kuma sai wani dojewa take yi tana nuna halin bosawa, irin ita fa ba zata sauko ɗin nan ba.

Haka ya cigaba da tsokanarta har ta sha fruits ɗin mai ɗan yawa, sannan ta ɗauki tissue dake wajen ta goge bakinta. Tana cire tissuen daga bakin nata ya miƙo mata hannu alamar ta bashi, ba musu ta miƙa mashi, a tinaninta zai jefar ne, sai kuma taga akasin haka, domin kuwa bakinsa ya goge shi ma kafin ya jefar. Mamakinsa ne sosai yakamata, bata yi zatan hakan ba, shi kuwa ido ya bita da shi yana karewa jikinta kallo, lokaci guda tinanin abin da ya faru a tsakaninsu ya dawo mashi cikin kwakwalwarsa, a wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ya tsinci kansa, ya kasa iya zare idanunsa daga kanta.

"Yah Ramish please ka mayar da ni gida ka ji? Kaga fa har karfe 9 na dare ya yi, a waje fa muka yi sallar azahar ga shi har dare bamu koma ba, Allah barci nike ji". Ta kai karshen maganar tana ɗan ɗaure fuska, wai irin yasan ba da wasa take yin nan ba......... A cikin zuciyarsa ya furta. "Why Aesh take mun kama da royal family? Meyasa ko magana take yi sai in rinƙa ganin kamar Zash ne yake magana?". A fili kuma sai ya ce. "Kina san mu koma?"............. Kai ta gyaɗa da sauri alamar e. Jinjina kai ya yi kafin ya ce to ta tashi su tafi. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana ta faman buga hamma, miƙewa ta yi cikin natsuwa, sai dai tana ɗaga kafa da nufin su tafi kafa ya ce baki isa ba.

Wani irin murɗa mata da cikinta ya yi ne yasa dan dole kafarta ta dakata, abin kamar wasa, da farko dai sai ta daure, a karo na biyu tana sake yunkurwa zata ɗaga kafa cikin ya sake murɗa mata da karfi, ƴar kara ta saki wadda bata ma san ta saki ba, a gaggauce ta sanya hannu ta dafe cikin nata, wasa wasa ta sake sakin ihu mai ɗan sauti wanda dik bata san ta yi ba. Da farko shi ma ya zaci wasa take yi, sai da ta yi kara na biyu ne ya fahimci da gaske take yi, cikin natsuwa ya miƙe ya iso in da take, hannunsa yasa ya tallabota yana faɗin. "Aesh are you okey?".

Kai ta shiga girgiza mashi cikin azaba tana datse idanunta gam da karfi, ganin da gaske take yi kuma hankalin jama'a ya fara dawowa kansu yasa bai tsaya ɓata lokaci ba ya yi gaggawar ɗaukarta cak suka nufi cikin motarsu. Ta ƙanƙame shi sosai tana datse lips ɗinta alamar azaba take sha. Gidan gaba ya sanyata tare da zagowa ta ɗayan side ɗin ya shiga. Kifa kanta da gwiwonta ta yi tana cigaba da datse lips ɗinta tana ɗan murkusoso tamkar wadda take shirin yin ɓarin ƙaramin ciki. Hannunsa yasa ya janyota jikinsa, cike da tashin hankali yake tambayarta menene yake damunta? Bai taɓa sanin zai damu da ita dan ta shiga damuwa ba sai yau, ya shiga tashin hankalin da bai san ya shiga ba.

Ƙasa iya amsa mashi ta yi, tana cigaba da murkusosonta tana nishi sama sama. Gabaɗaya sai ya rikice ya rasa meyakamata ya yi mata, sai kawai ya rungumeta a jikinsa yana mai ce mata sorry kawai...... Ta ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka kafin cikin ya fara lafa mata, a hankali

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login