Showing 336001 words to 339000 words out of 403653 words
wasa yake yi ɗin nan ba.
Sai dai tana ɗago kanta suka kalli juna ido cikin ido sai ya nemi dik wani zafin da ya ɗauka ya rasa, kwayar idanunta sun sanyaya mashi rai lokaci guda. "Tashi muje to". Shi ne kawai abin da ya iya faɗa mata. Ba musu ta miƙe daga jikinsa........... "Zash muje yawo". Ya faɗa yana kallonsu. Miƙewa Bobo ya yi ya kwanta yana faɗin sai sun dawo shi babu in da zai je. Shi kuwa Zash ya miƙe tsaye yana faɗin su je zai samesu a can bari ya je gidansu Bobo ya ɗauki Pinkish and beauty sai su je a tare daga nan sai su wuni a nan a tare. Sosai Bobo ya ji daɗin wannan al'amari, saboda ko ba komai yau zasu huta da masifar mom ɗinsu. Haka kuwa aka yi.
Smart dan dolensa ya ɗaukesu suka fita, in ba haka ba Pretty ba zata barshi ya zauna lafiya ba, sai dai kuma ko da suka fita ɗin ma bai tsira ba, dan tana manne da shi, dik in da zai shiga taki rabuwa da shi saboda shegen tsoro. Sai ma da suka shiga katafaren wajen shaƙatawa dake ƙarƙashin teku, wajen ne na glass da kana ciki kana iya kallan yadda manya da ƙananan kifaye da sauran halittun ruwa suke shawagi. Ita dai Auta ta saki jiki sai kallo take yi tana ɗaukar hotuna kala kala, kai tsaye tana turawa Hoorain ɗinta. Ita kuwa sarkin tsoro ta ƙanƙame shi dan dole ya rungumeta suka rinƙa yawo a ciki. Da suka je restaurant na cikin wajen, dik san abinci irin nata a wannan rana dai ta ce ba zata ci wannan abincinba, ba yadda Smart bai yi ba taki, har ce mata ya yi zai bata a baki, amma taki yarda, ba komai yasa taki ci ba face abincin ruwa ne, a wajen basa sayar da komai sai namomin cikin ruwa, gani ta yi sun bata kyama sosai wasu halittun, sai daga baya Smart ya fahimci tana da kyankyani ne, dan haka sai ya ce a kawo mata kifi wanda aka cire kayarsa tsab, dan yasan halinta, ba iya gyarawa zata yi ba, ta ci kaya ta barshi da wahala.
Da aka kawo mata ta ji daɗi sosai ta kuma ci, dan shi wannan ta saba ci a wajen Kamran!. In short yau dai sun sha yawo sosai yadda yakamata, a taƙaice dai kafin su koma kingdom of power sun yi sabo sosai da sosai, sai dai dik zaman da suke yi su uku a cikin gidan da iya Smart kawai Pretty take magana, bata taɓa cewa su Bobo ko sannu ba, har ranar da zasu tafi kingdom of power sannu bai haɗata da su Bobo ba, kuma a tare suke zaune, nan suke kwana, amma yarinyar nan tamkar bata san da su a gidan ba....... Dole in ɗan taƙaita wasu gurare domin manyan gurare da suka fi mahimmanci suna gaba, so dan haka mu je zuwa!!. Mu je ga kingdom of power.
Su uku suka shirya tafiya kingdom of power, suka bar su Bobo su kaɗai a gida cike da kewarsu, Auta baki har kunne zata je ta ga Hoorain, ita dai Pretty koma ina zasu je bata da matsala, bama ta san ina suka nufa ba, kawai tana rike da hannun Auta har Bobo and Zash suka kaisu airport, har suka shiga cikin jirgi suna manne da juna!!.
(STOP MY PEOPLE'S!! 🖐️ Na ce stop!!.🖐️ Yaseen irin ƙwaƙwalwar mutane ne da ni! Wlh irin ƙwaƙwalwarku nike da shi!! Ta ya za'ayi ku rinƙa ce mun kamar ba ƙwaƙwalwar mutane irin naku nike da shi ba wai?! To irin naku ce da ni, kawai dai abin da na sani shi ne kowa da irin girman ƙwaƙwalwarsa, kun gane ai?. Masu mamakin yadda na haɗe masarautu biyar dikka nike story a kansu, kuma kowanne da cakwakiyar, dik yawan mutanen ciki bana mance ko mutum ɗaya ko na ɗauki sunan wanna na bama wannan kuma stop na ce🖐️ yauwa kuna ganewa ko? Tabbas ku zaku ga akwai wahala, amma ni a wajena Allah ba wani abin bane, dik suna a cikin kwakwalwata ne shiyasa bana mantawa, kuma batu na gaskiya ni ina rubutu da zuciya da ƙwaƙwalwata ne shiyasa, idan na sanyawa zuciyata zan yi abu to is very very hardly na kasa yi! To paka paka kwakwalwarmu iri ɗaya ne kun ji? And amsar last tambaya shi ne e ni ina karanta Bibles sosai gaskiya, tin ina primary school na fara karatunsa, a hannun wata friend ɗina mai suna Rejoice James na fara karɓa na fara karantawa, kuma har yau idan na yi ra'ayi ina karantawa, so karatun Bible ba haramun bane ba!. Daga ƙarshe kuma ita rubutu baiwace sosai wlh da Allah yake bawa bayinsa, ina kuma miƙa ɗinbin godiyata a garesa da ni'imar da ya yi mun, ina alfahari da ilimin addinin dana zamani ya bani, ka zalika ina farinciki da ni'imar rubuce rubuce da ya yi mun, bugu da kari ina godiya da basira game da falalar ƙwaƙwalwa mai girma da ya bani, alhamdulillah, babu abin da zan iya biyan Allah da shi face godiya game da bauta bisa ƙaida, wlh ina matuƙar alfahari da farincikin da dik wani littafin da na rubuta da kuma wanda zan rubuta a gaba, dan dik littafan da na rubuta alhamdulillah na samu abin da nikeso. Dan wlh dikkansu sun faɗakar, sun wa'azantar kai babu ma kamar wannan RAWANIN ZALINCI, littafin nan ya fita daban sosai, tin ban kammala shi ba na samu sakonni da dama a kan yadda mutane suka karu da shi matuƙa, gaskiya I really appreciate that!! And really like you guy's. Much love...💘
🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥
Tin kafin jirginsu ya yi landing airport ta cika da shirga shirgan sabbin motocin da King ya sayo dan wannan biki. Jaish ne ya jagoranta tawagar zuwa ɗaukarsu, Jawad and uncle Jahiz dik suna tare, guyson ma ya je, amma su Omaid sun ki zuwa.
Jirginsu na sauka ba tare da ɓata lokaci ba suka fito, Auta na rike da hannun Pretty, while shi kuma yana bayansu. Jaish da Jawad ne suka fara nufarsu, fuskar Smart tamkar wanda aka aikowa da saƙon cewa wutar jahannama zai shiga, shi kansa Jaish sai da ya ji gabansa ya faɗi ganin face ɗin yayan nasa. Sannu da zuwa suka haɗe baki wajen yi mashi shi da Jawad, sai dai bai amsa ba, ko kallon in da suke bai yi ba, burinsa kawai ya isa gida su yi ido biyu da King, yau sai ya sanar da shi dalilinsa na hana Auta wanda take so, ya sanar da shi dalilinsa da yasa yake san lalatawa yarinya rayuwarta....... KAI YA AKA YI SMART DA AKA ƁOYEWA BATUN AUREN YA SAN DA ZA'AYI BIKIN? WA KUKE TUNANIN YA FAƊA MASHI?.
Kai tsaye mota ya nufa, da sauri suka rufa mashi baya, bai ce da su ko uppan ba ya shiga mota, sai huci yake yi, ita kuma Auta da bata san me yake faruwa ba, sai murna take yau zata sanya Hoorain a idanunta, bata sanar da shi zata dawo ba, wai surprise take san yi mashi. Dik ta ƙosa su isa gida, ga shi dare ne, daɗin satar hanya ta je wajensa kenan.
Jaish yana san tambayar yayan nasa me yake faruwa, amma yana fargabar amsar da zai iya bashi, dan haka sai ya danne har suka isa gida. Motocinsu na dakatawa ya juyo da nufin ya tambayesa, sai dai ina, kafin ya yunkura tuni Smart ya yi waje, kafin ya fito ya bi bayansa ma har ya shiga elvator ya yi sama abinsa. A gaggauce Jaish ya bi bayansa dan jin meyakefaruwa. Ita kuma Auta ita da Pretty suka biyo Yah Jawad zuwa cikin gida, Auta ta yi mamakin ganin cikar jama'a a gidan nasu, amma bata kawo cewa batun aurenta ake yi ba, hankalinta ma baya a kansu, burinta kawai ta je ta yi wanka ta isa ga abin kaunarta su ga juna, ta yi kewarsa sosai.
Kai tsaye part na King Smart ya nufa, sallamar ma a cikin zuciyarsa ya yi, ya kuwa yi sa'ar samun momma a ciki, yana shiga ya tsaya a bakin door tare da harɗe hannayensa a saman kirjinsa yana bin King da momma da kallo, suna zaune saman bed, suna duba jadawalin yadda taron zai kasance, da kuma ɗinbin dukiyar da suka ware dan yi kyaututtuka. Jin motsin shigowa yasa suka yi gaggawar kai kallansu kan door. Wlh dikkansu sai da gabansu ya faɗi time da suka ɗaura idanunsu a kansa. Muryar momma har rawa yake yi wajen cewa. "Omerish har kun iso ne?"
Idanunsa a kan King ya yi shiru bai amsa mata ba, aka ce ɗan na gada ya fi ɗan na koya, dik jaruntakar King sai da ya ji ya sha jinin jikinsa, saboda wani irin kallon da Smart yake binsa da shi, kuma kun san idan mutum bai yi adalci ba to fa shi kaɗai ya rinƙa tsarguwa kenan yana jin kamar ba daɗi.
"Omerish lafiya kuwa?". Momma ta faɗa a dame, ta yi maganar tare da saukowa kasan bed ɗin da nufin ta nufesa. Sai dai bata kai ga nufarsa ɗin ba ya ɗaga mata hannu kallansa a kan King. With harsh voice ya ce. "Why? Metayi maka da ka rantse dole sai ka kuntatawa rayuwarta? Shin kai akwai wanda ya yi maka irin hakan ne?!". Ya maganar ko kaɗan bai kyafta idanunsa daga kallon da yake yi wa King ba.
Momma zata yi magana ya yi saurin cewa. "Momma please let me ask him first, ya faɗa mun dalilinsa na san sanyamu cikin bakinciki".
Cikin natsuwa King ya ajiye file na hannunsa a saman bedside drawer, sannan ya sauko ƙasa, idanunsa a kan ɗan nasa ya amsa da. "Saboda na hanata auren mutumin da da shi da gawa dik ɗaya ne shi ne kake ganin na kuntatawa rayuwarta?".
Kai tsaye Smart ya amsa da. "Ba wai gani nike ka kuntatawa rayuwarta ba, kai tsaye na tabbatar da ka kuntatawa rayuwarta!". Babbar magana!!.
"Zunaira ba zata auri mayakin can ba, saboda da shi da gawa dik ɗaya ne, daga yanzu zuwa kowani lokaci a kan hanyar mutu yake, kobama haka ba, Zunaira jinin sarauta zata aura kamar ita, wannan shi ne gata a gare ta!....." "Gata!". Smart ya maimaita kalmar kafin ya ce. "Dad kowa ma a kan hanyar mutuwarsa yake, ba abin mamaki bane a wajen Allah ka mutu ka bar mayakin da kake ikirarin shi gawa ne, and koma menene shi waye ya mayar da shi hakan? Ba kai bane? Ai bai cancanci haka daga gareku ba, kada ka manta rayuwarsa ya saka dan cetar taku da kula da dukiyarku, me aibunsa? Shin ba irinsu nema yakamata ku sakawa da kyakkyawar alkhairi ba?!". Cikin harsh voice ya yi maganar, dan ya fahimci sankai ne kawai yake ɗawainiya da daddyn nasu.
"Omerish yana da kyau ka san cewa ni fa daddynku ne, ba zan taɓa yin abin da zai cutar da ku ba, kuma yakamata ka koyi magana da ni cikin girmamawa, saboda gidan sarauta kake, baya ga ni mahaifinka ne ni sarki ne mai jagorantar al'umma guda!!".
"Dad a haka na iya magana, da kowa a haka nike yi!!".
Ran King ne ya kara ɓaci sosai, dama tin ɗazun danne ɓacin ran nasa yake yi saboda baya san su samu saɓani da ɗan nasa.
"Okey, to Hoorain bawane, kare ne mai tsaronmu, dan haka a kan wannan hanya zai mutu, Zunaira ba zata taɓa zama mallakinsa ba, Omerish ka fita mun daga ɗaki!!". Cikin tsananin ɓacin rai King ya yi maganar!. Smart ya ɓata mashi rai sosai, bai so ace Smart yana magana no respect haka a garesa ba, abin ya koma mashi rai matuƙa. "Dad Zunaira ba zata auri zaɓinka ba, zaɓinta zata aura, kuma Hoorain shi ne zaɓinta, shin akwai wanda ya taɓa tauye maka hakkinka ne dad da zaka nemi ka tauyewa rayinya nata?!". Shi ma Smart cikin fushi ya yi maganar.
Abin da momma take gudu shi ne ya faru, tin ɗazun sai ƙoƙarin dakatar da su take yi, amma abin ya ci tura, ga shi har sun jawo ɓacin rai ya shigo cikin al'amari, shaiɗan yana neman yin galaba a tsakaninsu...... "Zamu gani idan kai ka haifa mun Zunaira ɗin sai kasa ta auri wanda ba zaɓina ba!!". King ya faɗa da kausasshiyar murya. "Zaka gani dad, tin wuri kafin ka ji kunya ka canza wannan abin, idan ba haka ba kana ji kana gani zan hana wannan aure".
Tin da ya shigo ɗakin yana tsaye yadda yake bai motsa ba, sai iya magana cike da iko da isa!.
Cikin zafa gadan gadan King ya nufesa yana faɗin. "Ni kake faɗawa zan gani kuma zan ji kunya?. To idan har ka haifu kasa in ji kunyar!!". Ko kaɗan bai ji tsoron daddyn nasa ba dik da yana nufosa ya amsa mashi da. "Zakuwa ka gani, in dai baka canza ka bawa Zunaira zaɓinta ba to tabbas zaka sha kunya, kuma Allah ma ba zai kyaleka ba, zalincin ya yi yawa...".
Kara hasala zuciyar King ya yi, da zafa ya ƙarisa wajen da nufi ya ɗauke Smart da zazzafar mari, sai dai kuma Momma ta yi gudun shiga tsakaninsu, yau taga tashin hankalin da bata taɓa zata ba, hankalinta a tsananin tashe ta rike hannun King da yake ƙoƙarin kaiwa Smart mari, jikinta har kerma yake yi ta fara bawa King hakuri. Shi kuwa Smart ko jezau bai yi ba, kamar ba shi aka nufa da mari ba.
"Rahilarh ki matsa mun daga gabana, dik abin da ya faru ba ke kika ja mun ba? Dik cikin ƴaƴana akwai wanda ya isa ina faɗa yana faɗa ne? Dik suna da tarbiya kuma suna respecting ɗina, kin cutar da ni Rahilarh, kin zalunci zuciyata, kinsa yau ɗan cikina, ɗan da na fi kauna sama da kai'na ne ya tsaya a gabana ina faɗa yana faɗa har yake ce mun zan yi danasani a rayuwata saboda rashin tarbiya!"....... Nisawa Smart ya yi, ya ji King yana ƙoƙarin zagan mashi daddynsa na France, wato shi ne bai bashi tarbiya ba, maganar ta kora ransa sosai, cike da takaici ya ce. "Suma ƴaƴan dake da tarbiyar nan gaba kaɗan zasu dai'na yi maka biyayya idan har zaka cigaba da tauye masu hakkokinsu kana zaluntarsu dan wani san zuciya taka, suma zasu dai'na bin umarninka a lokacin da zasu fahimci suna da ƴancin kansu". Cikin kunar rai ya kai karshen maganar.
Ran King idan ya kai miliyan to fa a wannan gaɓar ta ɓaci, zuciyarsa a tafashe ya kwace rikon da momma ta yi mashi, yana huci kamar wani zaki ya damki wuyar rigar Smart. Momma bata ɓata lokaci ba wajen sake shiga tsakaninsu, cike da tashin hankali ta fara faɗin King ya yi hakuri ya sake shi a bi komai a hankali, tasan koma me ya faru ita ce sila, kowa laifinta zai gani, kuma hakan take laifinta ne, ita ta kai Smart in da tarbiyarsu ya saɓa da na gidan sarauta, krista ce fa ta tarbiyartar da shi, kunga kuwa dik abin da suka gani sai dai su ja baki su yi shiru kawai.
"Momma ki kyalesa ya yi dik abin da yake ganin zai iya yi, amma dai Zunaira ba zata taɓa auren zaɓinsa ba!". Smart ya faɗa ko a jikinsa, dan shi zafin da King ya ɗauka ma ko ɗaya bata dame shi ba, saboda yasan ba komai bane idan aka danganta da zafinsa idan ya ɗauka. Rai a matuƙar ɓace Momma ta ce. "Omerish idan ka sake saka baki kan batun auren Zunaira ban yafe maka ba, haba mana, kasheni kake san yi ne? Meyasa baka tinanin kuncin da zaka sakani a ciki? Meyasa ka canza kake san ɓacin raina abin da a baya shi kafi tsana fiye da komai? Meyasa menayi maka da zafi haka?". Ranta ya kai kololuwar ɓaci ne, tana san sasanta abu shi kuma Smart yana neman kara lalata komai, shiyasa ta yi wannan furucin!.
Jin saukar kalamanta ya yi tamkar saukar aradu, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, a fusace ya sa hannu ɗaya ya ɓanɓare hannun King daga wuyarsa, cikin zafa ya juya ya bar ɗakin yana wani huci kamar mayinwacin zaki. Yana fita King ya dubi momma, a dakile ya ce. "Kin gani ba? Kinga irin abin da kika ja mun ba? To daga yau na haramtawa Omerish komawa kasar France, ya dawo kenan, ba zai sake komawa ba, dole ya zauna da mu a nan ya koyi tarbiya da girmamawa na gidan sarauta, ki kira iyayensa na can ki sanar masu na ɗauki ɗana kenan!!".
Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya koma cikin ɗakin, ransa sai tafarfasa take yi. Shiru momma ta tsaya, ta rasa waye zata bi, ga Smart ya ɗauki zafi ya fita, ga kuma King shi ma ya ɗauki zafi, to waye zata bi dan ta rarrashesa kenan? Ta jefawa kanta tambayar, yau fa ake yinta.
A gefe guda kuwa. Auta ta tsala wankarta tsab, sai murna take yi zata ga jaruminta, dan kada a gano akwai wanda zata je gani yasa bata saka wani kayan azo a gani ba, sai ta sanya sleeping dress masu mutunci, riga mai dogon hannu da wando shi ma dogo. Ta sanya headband a kanta, ta ɗauki wayarta ta nufo waje, wai dan ma idan ta haɗu da wasu kada su zargi wani wajen zata je. Har ta kai bakin kofa ta juyo ta ce. "Pretty ina zuwa, dik wanda ya zo nemana ki ce ina wajen Yah Omerish kin ji?". Pretty dake kwance saman gado bata amsa mata ba, yau miskilancin ta motsa kenan. Sanin cewa ta jita yasa Autar bata damu da sai