Showing 174001 words to 177000 words out of 403653 words

Chapter 59 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

105

hour bari ya zo. Jinjina mashi kai kawai Jaish ya yi ba tare da ya yi magana ba, hayewa bed ɗinsa ya yi ya kwanta da nufin ya yi barci ko da na 30 mins.

Sai dai kuma yana kwanciya tinane tinane suka cika mashi barin har da tinanin yarinyar da ta kawo mashi abinci a yanzu, haka kawai ya tsinci kansa da tinanin face ɗinta yadda ta tsare shi da idanu tamkar ta san shi, da tinanin yadda ta sha kwalliya har lallen hannunta yake fisgarsa gareta.

Siririn tsaki ya ja tare da ƙoƙarin kawar da banzan tinanin a cewarsa, sai dai kuma tinanin taki tafiya, saboda idan baku manta ba dama ya ce kamar da akwai wani gurbi da yake ji a cikin zuciyarsa ya rasata, to zuciya kuma yau taga burbin da ta rasa ba dole ta takura mashi ba, ai ya yi ya yi ya dai'na tinanin yarinyar nan sai ya ƙasa.

Daga karshe wayarsa ya ɗauko tare da miƙewa zaune a zuwan ya fasa yin barcin tin da wani banzan tinani ya sako shi a gaba. Balcony ya koma ya zauna ya shiga latsa wayar tasa bayan ya kunna data.

Sai dai fa ko da ya koma balcony ɗin tinaninta yaki sakesa, dik abin da yake yi face ɗinta ƙwaƙwalwarsa take kwaso mashi, abin har ya fara ɓata mashi rai.

A ɓangaren momma kuwa, magana ta sirri suka yi da Jawad har karfe 4 daidai ta cika, sannan suka rufe maganar tasu kowanne ya miƙe dan ya yi sallah, momma na miƙewa ta ce mashi kada ya manta ya turo mata Jannat ɗin fa.

Da okey ya amsa mata tare da fita ya nufi wajen Jaish dan su tafi masallaci a tare.

After some hours. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i. Momma da Chuchu ne zaune a saman bed ɗin Momma suna jiran mama Haulat ta kawo masu Mahnoor, sai hira suke yi irin ta uwa da ƴa cike da so da kauna.

Sallamar mama Haulat ta dakatar da su a in da suka mayar da kallansu a kanta, tana rike da hannun Mahnoor dake sanye da kyakkyawan abaya mai shegen tsada launin army green.
Ɗan zaro idanu Chuchu ta yi tana kallan Mahnoor, da yake shekarunsu kusan ɗaya sai girmansu ma yazamana ɗaya.

Ƙasa shanye mamakinta Chuchu ta yi har sai da ta ce. "Momma wacece wannan?"....

Da hannu momma ta nunawa Mahnoor gefenta da ta zauna, sannan ta buƙaci da mama Haulat ta basu waje kuma nan da 30 mins ta kawo mata alkyabbar Mahnoor zata kaita wajen King. Cikin girmamawa mama Haulat ta amsa sannan tasa kai ta fita.

Haɗe Mahnoor da Chuchu momma ta yi a in da ta yi masu nasiha mai ratsa jiki da kyau, sannan ta tambayesu da ya ake yin wankan haila da na janaba?. Ita Mahnoor ta karanta wannan, amma kunya ya hanata faɗa, ita kuma Chuchu iliminta bai kai nan ba, so bata karanta ba, dikkansu biyu babu wadda ta fara period a cikinsu, shiyasa ma Chuchu bata nemi yadda ake yi ba.

Ganin sun yi mata shiru ne yasa ta fahimci basu sani ba ne, dan haka sai ta ɗan yi gyaran murya kaɗan kafin ta fara magana kamar haka.
"Wannan tambayace da yakamata ace kowacce mace tasan amsarsa, nasan yanzu mata dayawa basu san yadda ake yi ba, amma bari in yi maku bayani dan dayawan mata su karu".

Shiru dai suka yi babu wadda ta yi magana, Mahnoor dai ta lura su fa ƴan gidan nan basa jin kunya kwata kwata, mijinta Jaish da guyson ne kawai masu kunya, su biyun nan ne masu kunya a ganinta.............. Lallai Mahnoor baki da kunya in ji ni princess Teema, wai har da uwar mijin nata ma bata da kunya kenan? Amma kuma fa gaskiya ta faɗa, ko shi Jaish daga ina ya samo nasa kunyar? Dan dai momma kam bata da shi, kada ku ce na ce na ce ɗin...........🥱

"Wanka a Musulunci yana da matakai daban daban bisa ga dalilin yin sa. Wankan Haila wanka ne da mace take yi bayan gama al'ada domin komawa cikin tsarki. Ga yadda zaku yi shi. Abu na farko niyya, a zuciya ki yi niyyar wanke jikinki daga haila zuwa tsarkin. Sannan sai bisimillah. Ki ambaci sunan Allah Idan ba a cikin banɗaki kike ba, dan ba'a ambatar sunan Allah a waje mai najasa, so in dai a ɓanɗaki ne no need for bismillah. Abu na uku wanke hannaye, ku wanke hannayenku sau uku. Abu na huɗu alwala. Ku yi alwala kamar yadda ake yi don sallah. Na biyar wanke kai. Ku jika gashin kai da ruwa sosai har ya gama jika. Abu na shidda shi ne wanke jiki gabaɗaya. Ki fara daga gefen dama, sannan ki wanke gefen hagu. Bayan kin kammala wankar zaki iya shafa sabulu mai kamshi ko turare a gefe gefen gabanki don kawar da warin haila. Ku lura da kyau wajen wanke gashin nan, Idan mace tana da gashin da ke tattare, ma'ana ta tsefe kai, to dole ta tabbatar da ruwa ya isa har fatar kanta, kunga kuwa sai ta jiƙa gashin sosai, a wannan gaɓar ana samun matsalar fahimta, wasu suna cewa sai mace ta tsefe kai zata yi wankar haila, to ingantaccen magana ba gashin kanta ake san ruwan ya taɓa ba, fatar kanta ake san ruwan ya jiƙa wanda idan bata tsefe kai bama tabbas sai ruwa ya fi shiga fatarta, dan haka ku lura da wannan".

Tin da momma ta fara magana dik suka wani yi ƙasa da kai suna sauraronta da kyau, sai satar kallan Mahnoor Chuchu take yi, taga kyakkyawa ƴar gayu kamar ita.

Cigaba momma ta yi da cewa. "Wannan shi ne wankar haila cikakke, shi kuma wankan janaba ana yin sa ne bayan saduwa ko mafarki (nocturnal emission.) Yana daidai da wankan haila, sai dai ba dole ba ne mace ta yi amfani da turare bayan sa. Shima matakan yinsa gasu nan kamar haka. Niyya, bisimillah, wanke hannaye sau uku, wanke al'aura, yin alwala, jika gashin kai da ruwa, wanke jiki gabaɗaya, wannan shi ne wankar janaba".

Shiru suka yi, gara mah Mahnoor ta daure ta ce da momma sun gode. Ina fatan ba iya su Mahnoor bane kawai suka ilmantu da ilimin alkalamina? Allah ka kara mana ilimi mai albarka mai amfani ka sakawa iyayenmu da suka tsaya mana wajen ganin mun samu ilimi ingantacce wanda har jama'a suna ilmantuwa daga garemu, a koda yaushe ba zan gaji da cewa ku mun addu'a kowace iriya ce in dai na alkhairi ce a gareni ina kauna kuma zan ji daɗi sannan ina godiya Allah ya bar kauna, ni ko baki kaunata ma ki daure ki mun addu'ar alkhairi please.

Chuchu ce ta tambayi momma wacece Mahnoor?. Cikin nitsuwa momma ta fayyace mata ita tsab, sannan ta ɗaura da cewa tana fatan zasu haɗa kai tamkar yadda Jawad da Jaish suke tamkar twins.

Riko hannun Mahnoor Chuchu ta yi, fuska ɗauke da fara'a ta ce. "In Sha Allah momma muma zamu kasance tamkar twins kamar dai su Yah Jawad.

Sosai momma ta ji daɗin furucin Chuchu, miƙewa ta yi ta nufi toilet tana faɗin bari ta yi wanka tana zuwa. Tana shiga toilet Chuchu ta dawo da kallanta a kan Mahnoor.

"Ina fatan zaki ɗaukeni kamar twins sis ɗinki?". Ta tambaya tana kallanta. Jinjina mata kai Mahnoor ta yi tare da cewa In Sha Allah sun zama ƴan uwa. Ɗan rungumeta Chuchu ta yi tana faɗin. "Gaskiya kina da kyau sosai".

Ɗan siririn murmushi Mahnoor ta saki kafin ta amsa mata da. "Kema kyakkyawa ce sosai ai".

Sallamar Jawad ya katse masu hirar tasu. Da sauri Chuchu ta dawo da kallonta a kansa. Ganin shi ne yasa ta yi saurin sakin Mahnoor ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana murmushi. Rungumeta ya yi yana faɗin. "Shi ne aka barni aka zo wajen momma ko?".

"Kai Yah Jawad, yanzu fa nazo kuma momma ɗin ce ta kirani". Jinjina kai ya yi kafin ya ce. "Nima momma ɗin ce ta tura mun text a kan inzo, ina take?". "Ta shiga wanka, Yah Jawad ga matar Yah Jaish fa". Ta yi maganar tana ɗan raba jikinta da nasa.

Kai kallansa a kan Mahnoor ya yi, maganganun sirrin da suka yi da momma ɗazun ne kawai ya faɗo mashi a ransa, ƙaƙalo siririn murmushi ya yi ya sakar mata kafin ya ce. "Sannunki".

Kasa ta yi da kai tana ɗaga mashi gaisuwa cikin girmamawa. Chuchu sarkin iya soyayya sai ta ce. "Mahnoor kin ji momma ta ce mu zama kamar twin irin Yah Jawad da Yah Jaish ko?". Gyaɗa mata kai Mahnoor ta yi alamar e ba tare da ta yi magana ba.

"To wannan shi ne Yah Jawad ɗin da ake magana a kansa, shi ne twins ɗin mijinki, kuma shi ne mijina ni". ....... Dogon hancinta Jawad ya ja, kasa kaɗan ya yi da murya kafin ya ce. "Da gaske ni mijinki ne my Jannawad?". Ya yi maganar yana ɗaga mata gera guda.
Dukan wasa ta kai mashi a kirji tana faɗin. "A'a ba kai bane". Hannun nata ya riko. "Sarkin rigima, zo mu je ki bani abinci yunwa nike ji".

"Ka manta momma ta ce ka zo ne?". Ɗan jinjina kai ya yi. "Yeah na manta ne, to bari in jirata". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta suka koma saman sofa suka zauna. Shigewa jikinsa ta yi ta hau bawa flowers ɗinta ruwa. Sai datar kallansu Mahnoor take yi tana ayyana irin haka zasu yi da Jaish ɗinta idan ya fara sonta. Lokaci guda ta tina lokacin da suke Jimeta suke soyayya a gonar bappa, gabanta ne y faɗi dik sai ta ji babu daɗi.

Jawad da Chuchu basu ji kunyarta ba suka cigaba da zuba soyayyarsu har momma ta fito daga wanka. Umarni ta ti wa Jawad a kan shi da Jaish su sameta a part na King nan da 20 mins. To okey ya amsa mata sannan ya miƙe ya fita.

Dawo da kallanta a kan su Chuchu ta yi, ku shirya mu je wajen daddynku ko?. Ta yi maganar tare da wucewa dressing room ɗinta. Tana shiga mama Haulat ta shigo ya kawowa Mahnoor alkyabbarta, ita kuma Chuchu ta miƙe ta nufi bedroom ɗinsu dan ta shirya da wuri.

After some minutes, gabaɗaya sun hallara a gaban King, wato da Chuchu, Jawad, Jaish and Mahnoor. A nan ne momma ta sanar da Jaish wacece Mahnoor, ta kuma ce mashi ta bashi ita amana, ya sani marainiyace, kada ya yi abu domin ita mommar, dik abin da zai yi ya yi domin Allah y kuma duba maraicin yarinyar nan.

Kunsan mutumin da kunya, dik abin da momma take faɗa yana jinta amma ya sunkuyar da kansa kasa kamar babu shi a cikin ɗakin. Haɗesu ta yi ta yi masu nasiha mai ratsa zuciya, ta tunatar dasu girman Allah, ta kuma tunatar da su cewa aure sunana ne na manzan Allah wanda ya fi kowani sunna girma da kima, ta kara jaddawa Jaish da ya kula da Mahnoor tsakaninsa da Allah, daga karshe ta rufe da cewa su wuce bedroom ɗinsu da matansu.

Sai da ta gama maganarta tsab sannan King ya ɗaura nasa shi ma, cikin nitsuwa ya yi masu nasiha shi ma haɗe da karfafa masu gwiwa ya kuma ja kunnen Chuchu da Mahnoor a kan su yi wa mazansu biyayya, daga karshe shi ma ya rufe da su tashi su wuce bedroom ɗinsu.

Miƙewa Jawad da Jaish suka yi a tare, suka wuce gaba Chuchu da Mahnoor suka rufa masu baya. Suna tafiya King ya dubi momma dake zaune a bakin bed ɗinsa. "Na bawa matar Jaish kwautan kujerun makka guda biyar, idan kin je Jimeta ki sanar da iyayenta da wanda ta zaɓa su shirya bana su je Makkah, sannan ina da special kyauta a gareta a matsayina na mahaifi a gareta, akwai kyautar gaisheni da ta zo ta yi zan bata sai kun dawo daga Jimeta".

Matsawa momma ta yi jikinsa, ta kwantosa tana zuba mashi godiya, kamar jira dama yake yi haba ai sai ya fara al'amura.

🔥🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥🔥

Cike da tashin hankali Abbie ya bi bayan Ummie dan ya dakatar da ita daga aikata kudurinta. Sai dai ina kafin ya fito parlourn har ta fice. Cikin zafa ya taka da sauri sauri ya bi bayanta. Tana cab zata shiga part ɗin su Ramish ya kwala kiran sunanta. Tana jin ya kirata ta yi saurin rugawa ta afaka cikin part ɗin su Ramish. Allah sarki dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, sai ya ji kamar in da yake tsaye ta yi wani irin juyawa da karfi, nan take ya ji kamar zai faɗi.

Dafe bango ya yi ya fara bin jikinta ya juya izuwa part ɗinsa. Ita kuwa Ummie, sai da ta shiga cikin part ɗinsu sai ta rasa me zata ce masu ne ma, ta ce su zo suga ta kama Abbie da wata mace nan kuma Ramish ya dallah mata mari kafin ya yi yunƙurin zuwa, dan tasan halinsu sarai, to ya zata yi ta ja su izuwa part ɗin Abbie su ganewa kansu? Ta jefawa kanta tambayar.

Tana tsaye a tsakiyar parlourn tana tunane tunane sai ga Ramish and Bilal sun fito a lokaci guda, suna shirye cikin arabs jallabiya zasu tafi musque. Sun ɗan yi mamakin ganinta a part ɗinsu da asuba haka, Ramish dai ya yi kamar bai ganta ba ya zo zai wuceta, Bilal ne ya tsaya tambayarta me take yi a nan?.

Dai'dai lokacin su Dr Raj ma suka fito da sauri, suma tsayuwa suka yi dan ganinta a nan. Tashin hankali ne ya bayyana a tattare da ita, kame kame ta fara yi masu, can kuma wani idea ya faɗo mata, da sauri ta ce masu su je part ɗin Abbi yana nemansu abu ne na gaggawa.

Basu tsaya tambayarta me yake faruwa ba, dan tun dq suka ganta a nan da wannan lokaci sun san ba lafiya ba, dan haka suka yi zafin namar nufar part ɗin Abbie. Already dama shi Ramish da bai tsaya kulata ba can ya nufa, saboda ya saba zuwa wajen Abbie da asuba su tafi masallaci a tare, so sai ya nufi can.

Wani irin daɗi ta ji ganin sun nufi part ɗin Abbie, har da tsalle ta daka tana murmushi, sai kuma lokaci guda ta nitsu tare da wucewa da sauri ta rufa masu baya tana ayyana yadda zakunan samarin Abbie zasu yi kaca kaca da Leesharh, dan in dai suka sameta a haka kasancewarsu musulmai ne kawai zai hana ba zasu cinye namarta ɗanya ba.

Suna shigowa suka tsaya cirko cirko kamar waɗan da aka dasa, kallan Abbie suka tsaya yi, Ramish yana rike da hannunsa yana tambayar meyasame shi jikinsa dik jini haka?. Abbie zai yi magana ganinsu Bilal da Ummie sun shigo yasa ya yi shiru, Ramish ya lura da Abbie baya san yin magana a gabansu dan haka sai ya ce masu su je masallaci zasu biyosu daga baya.

Ummie kuwa hankalinta a tashe t fara bin gadan Abbie da kallo tana zaro idanu, babu Leesharh babu alamarta a saman bed ɗin, abin ya bata mamaki. Abin da bata sani ba shi kansa Abbie mamaki yake yi haɗe da tambayar kansa ina Leesharh ta shiga, domin kuwa lokacin da ya bi bayan Ummie domin ya bata hakuri kada ta kira su Ramish, kafin ya dawo ne Leesharh ta bar bedroom ɗinsa, da y dawo ɗakin bai sameta ba.

Tambaya ɗaya yake yi shi ne ina take ya aka yi kuma ta bar bedroom ɗinsa? Yana shigowa da bai sameta a saman bed ba ya fara nemanta har cikin toilet, sai dai da gaske babu ita babu labarinta a cikin ɗakin, hankalinsa ne ya yi mummunar tashi, dan yana ganin kamar waɗan da suka yi ƙoƙarin cutar da ita a farko ne suka zo suka ɗauketa, abin da zai sanar da Ramish kenan, zai sanar mashi da ya biyan Leesharh bedroom ɗinta ya duba mashi menene ya sameta, bai kai ga yin hakan ba su Ummie suka shigo, shiyasa ya yi shiru?.

To ina Leesharh? Waye ya ɗauketa?.

"Babu wata matsala?". Cewar Bilal. "Yeah babu zaku iy tafiya zamu biyoku daga baya". Ramish ya faɗa idanunsa a kan Abbie yana kallan tashin hankali a cikinsu.

Dr Raj ne ya ce. "Yah Ramish jini ne fa a jikin Abbie kuma ka ce mu tafi?". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba. Juyawa suka yi suka nufi hanyar fita, ɗakin ya rage daga Ummie da ta yi mutuwar tsaye, sai Abbie and Ramish.

Da wutsiyar ido ya wurgawa Ummie kallo, nan take ta sha jinin jikinta, tin bai yi magana ba ta yi saurin wucewa ta fita waje tana mamakin da al'ajabin ɓacewar Leesharh a ɗakin haɗe da bakincikin burinta bai cika ba, ta so su Bilal su yi kaca kaca da ita, amma Allah ya tsallakar da ita, ciza laɓɓanta ta yi tare da furta akwai gaba ai, wato bata janye kudurinta ba kenan.

Me Abbie zai sanar da Ramish? Me zai faru? Ina Leesharh? Waye ya ɗauketa? Dik a gaba zaku ji.

Magana suka yi na tsawon 30 mins, sannan Ramish ya fita daga bedroom na Abbie ya nufi bedroom ɗin Leesharh. Da shigarsa bai fi 10 mins ba ya fito ya koma part na Abbie. Jim kaɗan suka fito a tare da Abbie suka nufi masallaci.

Yau saɓanin kowacce rana da suke dawowa da wuri, yau sai karfe 9 na safe Abbie da Ramish suka dawo cikin gidan, koda suka dawo kuma part na Abbie suka wuce, nan suka zauna suka cigaba da tattaunawa, da alama wani bincike suke yi a sirrance, ko Ummie basu bari ta sani ba.

After some hours. Da misalin karfe 4 na yamma, katafaren hall ɗin da zasu yi taro ya cika makil da jama'a, taro ake gudanarwa bisa ƙaida, doka da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login