Showing 150001 words to 153000 words out of 403653 words

Chapter 51 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

42

balai'n san karatu, tana zuwa govment school dake kusa da unguwarsu, dik da makarantar a lalace sai a hankali, hakan bai hanata zagewa ta mayar da hankali a kan abin da ake koyar da ita ba, tana da hazaƙa sosai, suna cikin ƙuncin rayuwa matuƙa, amma dik da haka basu kuskura sun yi wani abin da zai kaucewa faɗin Allah ba, sun kula da kansu da dokikin Allah, sun cigaba da jure wahala.

Wani lokaci idan yunwa ta yi yunwa har bara suke fita su yi, in kuma suka je yin bara duniya ta lalace sai lalatattun cikin mutane su nemi lallata mata jika, hakan yasa ta datse batun neman taimako wajen kowa, suka dukufa suka mai da lamuransu ga Allah dan ya taimaka masu ba sai an ci zarafinsu ba.

Wataranar Friday wannan matashiyar budurwa zata je karɓan hutun kammala primary school bayan rubuta common entrance, sun shirya ɗan ƙaramin party na dai'dai ƴaƴan talakawa, dik da bata kai ko biyar nata wajen haɗa kayan wannan party ba, amma ta shiryar dan ta je ko gani da ido ne taga masu yi.

A hanyarta na zuwa school mota ya bugeta, bata ji ciwo sosai ba, saboda mai motan ba gudu yake yi ba, da yake bawan Allah ne mai sanin yakamata ga ilimin addini sai ya tsaya ya ɗauketa ya kaita asibiti.

A nan aka ɗan dudduba dik in da ta ɗan kukkuje aka yi mata dressing ɗinsa tsaɓ tare da bata magunguna. Ya biya kuɗin sannan ya ɗaukota a mota tana yi mashi kwatance har ya maido da ita gida. Bayan ya sauketa a kofar gida tana rike da ledar magungunanta a hannu, har zai juya kan motarsa kuma sai ya fasa ya dakata.

Dama aikinsa kenan yin aikin alkhairi, yana da tausayi da jin kan talaka, hakan yasa ya kashe motar ya fito, a lokacin yarinyar ta shige cikin gida. A kofar gida ya tsaya ya daka sallama cikin nitsuwa. Daga waje yana iya hango cikin gidan saboda rurrujewat ginin, yanayin ginin ma ya ja hankalinsa ya ji yana san bin bayan yarinyar.

A maimakon ya ga yarinyar ta fito sai yaga wata dattijuwa ta fito, cikin girmamawa ya yi mata sannu tare da neman izinin yana san yin magana da mai gidan, a tinaninsa mahaifin yarinyar kenan.

Babu wani ɓoye ɓoye ta sanar da shi babu wani mai gida a nan sai ita da jikarta, kuma ba gidansu bane na hayane. Sosai ya ji tausayinsu ya kama shi, da Allah yasa abincinsu na hannunsa sai yazamana sanadiyyar canzawar rayuwarsu, shi ya sai masu wannan Daula da suke ciki a yanzu, ya canzawa yarinyar school izuwa makaranta mai bala'in tsada na manyan kai, ya sanya masu tsaronsu da kyau, a yanzu haka wajen motoci biyar ne suke jerin gwano idan zasu kaita school, rayuwarta gabaɗaya ya canza tamkar ba su taɓa yin rayuwar ƙaskanci da wahala ba a baya. Shiyasa idan ka yi hakuri ka miƙa lamuranka ga Allah sai ka huta wlh, dan Allah idan ya tashi taimakonka ta in da baka yi zato ba zaka ga canjin da babu wanda ya isa ya baka a duniya.

Wannan shi ne kaɗan daga cikin tarihin waɗan nan bayin Allah. Time to time wannan bawan Allah yana zuwa duba lafiyarsu, ba komai yasa hakan ba kuma face wannan dattijuwa ta sanar da shi iyayen wannan matashiya sun rasu, marainiya ce, shi kuma yana bala'in san ganin ya taimakawa marayu, yana jin ƙan marayu sosai, dik wani abin da suke so ya sayi waya ya basu dan su rinƙa kiransa su sanar da shi, ba kuma su kaɗai ya taɓa yi wa haka ba, shi ɗabiarsa ce taimakon mutane.

Yana da tarin makudan dukiya sosai, bashi da aiki sai duba marasa karfi yana tallafa masu sosai, kullum kuma arzikinsa ƙara haɓaka yake ta ƙara yi. Yarinya ta goge ta zama yar gayu, ga kyau ga ilimi, ga shagwaɓa da kyan diri, kamar ka taɓata jini ya zuba.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Kwance take a saman wani bed round da shi haka, kamar pool haka bed ɗin yake, irin rest bed ɗin nan ne wanda mattress ɗinsa yake can kasa haka. Ta tada kai da cinyar dattijuwa, sanye take da ƙananun kaya na shan iska, rigar mai siririyar hannu ce izuwa gwiwarta, sai dogon wando mai laushi, dattijuwa ta ɗaure mata gashin kanta kashi biyu, bakinta sanye yake da wani irin lips balm mai shegen kyau da sheki. Sai tashin daddaɗar kamshi take yi.

Fuskar nan tata tamkar zata saka kuka, ta shagwaɓesa sosai, tana turo baki ta ce. "Ammo baby ya jima yanzu bai zo gidan nan ba, ya ɗauki lokaci sosai wannan karan, ina kewarsa sosai wlh, ni kamar in je nemansa".

Tana da sanyayyar murya mai daɗin sauraro, akwai nitsuwa sosai a cikin kalamanta, sai dai akwai shegen shagwaɓa kuma. Baby shi ne sunan da take kiran wannan bawan Allah da ya taimaka masu, tun tana karama yake ce mata baby ita ma tana ce mashi, so hakan tasa sunan ya zauna, a da idan tana kuka ne yake amfani da wannan suna yana rarrashinta, har dai sunan ta zauna.

Shafa kanta Ammo dattijuwar kirki ta yi, cikin nuna tsantsar kulawa ta ce. "Ni kai'na ina kewarsa, ban san me ya hana shi kawo mana ziyara ba, an ɗauki lokaci gaskiya". Cike da tausayawa babyn ta yi magana, dan kuwa tasan yadda suka shaku sosai, tin yarinyar tana karama bata da wajen wasa ko zama sai jikinsa, yana da bala'in san yara kuma yana san ganin yana wasa da su.

"Ammo dan Allah mu kirasa a waya mana yau kam". Ta yi maganar tana miƙewa zaune. "Jeki ɗakina sai ki ɗauko wayar ki kawo mu kirasa". Cewar dattijuwa.

Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyarta, har sai da ta saki ɗan siririn murmushi wanda ya ƙara fito da kyanta. Da sauri ta fito daga cikin wajen, ta nufi ɗakin kakar tata tana sakin murmushi. Da kallo Ammo ta bita tana tausaya mata.

Har zata shiga cikin ɗakin sai kuma ta tsaya cak, a hanzarce ta juyo da kallonta baya, shiru ta ɗan tsaya kaman mai nazarin wani abin, kamar mai raɗa ta ce. "Baby come out, I heard your breath, my heart beats with your name". Ta faɗa tana ɗan tura baki.

Shiru bata ji alamar komai ba, ɗan motsawa ta yi kamar zata dawo baya, sai kuma ta cigaba da tafiya tana faɗin. "Tsabar kewarka da nike yi ne ya ja nike jin zuciyata tana bugawa da sunanka a kurkusa, ashe ba haka bane".

Tana ƙoƙarin tura kofar ɗakin kakar tata sai ta juyo da sauri. Tana juyowa suka yi 4 eyes da kyakkyawan face ɗinsa tana ɗan sakar mata siririn murmushi.

Tsayayyan cikakken namiji ne mai cikar surar mazanta, yana sanye da three-piece suit launin ash colar, kyakkyawa ne sosai fari tas da shi, murmushinsa tana da laushi mai kwantar da hankali haɗe da ƙayatarwa, idan ya yi maka shi sai ka ji hankalinka ya kwanta.

"Baby waye ya ce ki juyo ne?". Ya faɗa murya a sanyayye ga zaƙi da daɗin sauraro.

Idanunsa a kanta, kirjinsa sai da ya buga ganin irin shigar dake jikinta, gata budurwa, komai a cike fam.

Turo baki ta yi, tamkar zata fashe da kuka ta ce. "Baby ina kaje kwana dayawa baka zo ba?".

Nisawa ya yi, ɗan lumshe idanunsa ya yi. "Baby bana ce ki rinƙa sanya hijabi ba?". Shiru ta yi tana kallansa. Gera ya ɗan ɗaga mata, hakan yasa ta yi saurin cewa. "To ai a cikin gida nike yasa ban saka hijabin ba, amma yanzu zan je in saka".

Jinjina kai ya yi. "To jeki ki saka sai ki zo parlon in faɗa maki dalilina na rashin zuwa kwana biyu". Da okey ta amsa mashi tare da shigewa ciki da sauri. Bayanta ya bi da kallo yana ganin yadda take tafiya mazaunanta suna yi mashi kwalele ta baya. Sai da ta shige cikin ɗakin shi kuma ya juya ya koma wajen Ammo yana sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Bawan Allah yanzu ma daga gidan gajiyayyu marasa karfi ya fito, kayan tallafi ya je ya kai masu. Yana da farar zuciya sosai fiye da tinaninku.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






Saman sofa ya zauna yana fuskantar Ammo dake zaune saman nata sofan ita ma, ganinsa ya zo gidan yasa ta dawo saman sofa ta zauna.

Cikin girmamawa ta ce mashi. "Ka ganta kuwa?".
Kai ya ɗan jinjina mata yana faɗin. "Ai da ban sanyata a idanu na ba ba zan iya fitowa in dawo nan ba".

Murmushi Ammo ta saki tana mamakin irin shakuwar dake tsakaninsu, tana ganin shakuwar ta yi yawa sosai, a ganinta basu kai ya yi masu irin wannan ba, sai ga shi kuma ya shaku da su sosai haka.

Sallamarta ya katse su. Tin da ta shigo kallonsa a kanta, a saman sofar da yake zaune ta zo ta zauna, cike da zumuɗi ta fara jero mashi tambayoyin meyasa ya kwana biyu bai zo ba?.

"Sorry baby, aiki ne ya mun yawa, yau ɗin ma da kyar na samu lokaci na leƙo, kuma yanzu ma ba jimawa zan yi ba, dan yanzu haka jirana ake yi, amma dai ki sani koma menene kina rai'na a koma ina nike". Ya kai karshen maganar idanunsa a kanta........

Zata yi mashi magana suka haɗa idanu da Ammo, girgiza mata kai Ammo ta yi dan tasan abin da zata faɗa, gardama zata yi mashi a kan kada ya tafi, kuma Ammo ta hanata yi mashi haka, ta hanata yin gardama da shi.

Shiru ta sunkuyar da kanta tana san yin magana amma ba dama. Ganin kamar taso yin magana sai kuma ta yi shiru ne yasa ya saci kallan Ammo ta wutsiyar ido, dan yana zargin ita ta hanata magana. Dai'dai lokacin Ammo ta miƙe haɗe da cewa bari ta zo. Dabara ta yi zata basu waje, dan ta lura idan tana wajen bai cika yawan magana ba, kamar tana takura masu. Wani lokaci idan baby tana faɗa mata irin hiran da suka yi sai ta yi ta mamaki, a gabanta shiru shiru yake, ba dan tasan halin jikar tata baya karya ba da sai ta karyatata. So a gaban Ammo baya magana sai ta basu baya ne yake zuba hira da baby kamar ba gobe.

Aikuwa tana tafiya ya juyo suna fuskantar juna da ita, a nitse ya ce. "Faɗa mun abin da kike san faɗa mun Ammo ta hanaki". Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Ammo zata yi mun faɗa idan na faɗa maka".

Hannayenta ya riko cikin nasa da nufin ya yi mata dabara ta faɗa mashi, sai dai kuma wani irin shock da ya ji har tsakiyar kansa ne yasa ya yi saurin sakin hannun nata yana ɗan jan numfashi a hankali, yarasa me ya shiga tsakaninsa da ita, wata ɗaya ne kawai bai kawo masu ziyara ba, amma kuma a wannan wata ɗayan kullun yana cikin tunaninta, ga shi ya zo kuma ya kasa iya rike koda hannunta saɓanin da da kullum suna manne da juna idan ya zo.

"Ba zan faɗawa Ammon kin faɗa mun ba ai, ni kaɗai zan ji, kin ga bata nan ai ko?".

Kai ta gyaɗa mashi alamar e ...... "Good my baby, to faɗa mun menene?". Tsabar shirinta sai da ta fara jujjuyawa wai dan taga da gaske Ammo bata yi masu laɓe ba, kada ta jiyosu, sai kace akwai masu shigowa parlourn dama, ta wani tsaya tana waige wiage. Binta da kallo kawai yake yi, idan tana wannan shirirtar tata ba ƙaramin tafiya da tinaninsa take yi ba, yana jin daɗin ganin tana ire iren wannan abin.

Sai da tabbatar babu kowa, sannan ta yi ƙasa sosai da murya, kamar mai raɗa ta ce. "Dama cema maka zan yi kada ka tafi, ni ban gaji da kallanka ba, kuma na yi kewarka sosai"..................... Ajiyar zuciya ya sauke. "Ammo ta hanaki ce mun kada in tafi ne idan na zo?". Ya jefa mata tambayar kallansa a kan yatsun hannunta da suke dogaye kyawawa.

Kai ta gyaɗa mashi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa. "Ta ce in dai'na takura maka ina maka kuka zaka dai'na sona, wai idan ina yi maka haka zaka dai'na zuwa ma, zaka ce ina damunka". Ta kai karshen maganar idanunta suna cikowa da kwallah.

"Da gaske zaka dai'na zuwa idan ina cewa kada ka koma?"....... Girgiza mata kai ya yi, a karo na biyu ya sake riƙe hannayenta, Allah sarki ya saba ne, wani irin shock ya sake ji, hakan yasa ya yi saurin sakinta. Jingina kansa da jikin sofar ya yi, ya fara mamakin wannan abin gaskiya.

"Kenan da gaske Ammo take yi zaka dai'na zuwa kuma zaka dai'na sona?". Muryarta ta daki dodan kunnnesa, hakan yasa ya yi saurin dawo da kallansa a kanta. "Ko kusa ko alama, hasalima daɗi nike ji idan kina ce mun kada in tafi".
Wani irin daɗi ta ji, har ta saki murmushi, zata sake yin magana Ammo ta shigo hannunta rike da waya hakan yasa ta haɗiye maganar tare da dawo da kallanta a kan Ammo ɗin.

"To tashi ki je uncle ɗin islamiya ya zo". Cewar Ammo kenan. Turo baki ta yi, sam bata san rabuwa da shi, amma ba yadda ta iya, miƙewa ta yi yana turɓune fuska ta ce. "Baby na tafi islamiyya". Kai kawai ya jinjina yana kallanta ba tare da ta yi magana ba. Shigewa cikin ɗakin ta yi.

Waje Ammo ta samu saman sofa ta zauna idanunta a kansa, sai kallan baby yake yi har ta shige ciki, sannan ya sauke ajiyar zuciya. Yana ƙoƙarin lumshe idanunsa muryar Ammo ta katse shi da cewa. "Har yaushe zaka cigaba da ɓoye mata waye kai?".

Wannan kalma tasa ya fasa lumshe idanun nasa a in da ya sauke kallansa a kanta. Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya amsa da. "Bansan har izuwa yaushe ba, abin da kawai na sani shi ne ba yanzu zata san wanene ni ba, ni yanzu zan tafi saboda ana jirana, kila in dawo da daddare, kila kuma sai gobe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye.

Da kallo Ammo ta bishi tana mamakinsa, ta ƙasa amsa sallamar da yake yi mata, har sai da ya fice sannan Ammo ta farga da ya tafi. TO FA WANENEN SHI KUMA?.

Yana fita ta fito sanye da hijabinta har ƙasa, hannunta rike da kyakkyawan jaka mai ɗauke da litattafan addini da Alqur'ani mai girma. Sallama ta yi wa Ammo tare da nufar waje.

Da kallo mai kama da kallan tausayi Ammo ta bita har ta fice. A tinaninta babyn nata ya tafi, sai kumbura kumatu take yi tana ɓata rai ya isa wajen kyakkyawan rumfar da suke karatu, already malam ya zo yana jiranta. A saman table dake wajen ta ɗaura jakarta, saman chair ta zauna tana turo baki. Tin da ta shigo wajen malam yake kallanta, yaga alamar kamar ranta a ɓace, bai iya hakura ba har sai da ya ce baby yau lafiya kuwa?.

Babu komai ta amsa mashi da shi tare da janyo jakarta ta fito da Alqur'ani ta fara buɗe in da zata bada hadda.

Shi kuwa yana zaune a cikin motarsa, tin da ta fito daga cikin gida ya kafeta da idanu har ta isa wajen karatun nasu, ya kasa tada motar ya tafi, da alama maganar da Ammo ta yi mashi ya taɓa zuciyarsa, kamar ya tado mashi da wani abin. Dik abin da take yi yana kallanta, bai ta fi ba har sai da ta gama bayar da haddanta cikin Suratul tauba, malam ya yi bismillah ya fara ƙara mata, dan ta kawo si dai'dai babu tangarɗa.

Ya jima dai yana ganinsu kafin ya tashi motarsa da kyar ya tafi. Da yake baby bata san da wace mota ya zo ba, hakan yasa bata fahimci hana nan ko ya tafi ba, saboda dik motocin da suke parking space ɗin gidan nasa ne. Sai da ta ji tashin mota a yanzu ne ta fahimci ashe yanzu zai tafi. Ta so ta sake ganinsa, amma ba dama, tana ganin motarsa ya danna waje, shi ma ta cikin mirror yake ganinta har ya fita. Yana fita ya kara gudun motar, a miliyan ya keta kan titi ya tafi.

Ita kuma ta cigaba da karatunta rai babu daɗi. Dik abin da yake faruwa Ammo tana tsaye a gaban windown parlour dake fuskantar harabar gidan tana kallansu.


🔥🔥🔥🔥FOREST🔥🔥🔥🔥

Sun ci karfin dafiyar da suke yi, abu kaɗan ya yi masu saura su fita daga cikin wannan dajin, sai dai yamma ta yi masu sosai, Hoorain ya fahimci dole sake kwana a forest ɗin nan ya kamasu, dan haka tin kafin rana ya faɗi dare ya yi masu sai ya yi saurin samun waje mai tsaro, mai ƙawa da ɗaukar hankali ya tsaya. Daga in da ya dakata zuwa in da mammar Kamran take basu da nisa, kun tuna wajen zaman su Sweetie na farko kafin Sadauki ya canza masu? To a arear wajen ya dakata ya fara ƙoƙarin haɗa masu wajen da zasu kwana gobe da asuba su cigaba da tafiya.

Suna dakatawa Auta ta hau takura mashi da shagwaɓar yunwa take ji, hakuri ya bata har sai da ya gyara masu in da zasu kwanta ba tare da wata matsala ba, saboda kada duhu ya riskesa bai kammala ba. Waje mai kyau da haɗuwa ya gyara mata ita

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login