Showing 42001 words to 45000 words out of 403653 words
shi kansa bai san takamaiman in da kofar take ba, amma zai bincika masu, to shi ne ita uwar ƴan rashin tsoro ta je dan ta fara bincikawa da kanta, bayan kuma Ronnie ya gaya mata ta yi taka tsantsan kada ta sake shiga gonar yayansa, in ba haka ba zata rasa ranta ne a banza, amma kunga yarinyar nan bata ɗauki zancensa a bakin komai ba, ta yi fatali da komai ta yi biris.
Babban parlournsa ta shiga, babu komai sai daddaɗar kamshi dake tashi, ko'ina very very clean, kamar sabbin kaya aka zuba.
Wucewa ta yi ta nufi ɗaya daga cikin bedroom dake cikin parlourn, ba ainahin bedroom ɗinsa ba.
Babu wani ɗar ta gwada sanya password irin na ɗakin Ronnie, ga mamakinta sai gani ta yi kofar ya buɗe, wato ba ina ga daga kan Sweetie karfin hali ya kare yarinyar nan. Kila ma ba dai'dai tasaka password ɗin ba kawai an buɗe mata kofar ne dan a shirya mata tarko, amma sam bata gane ba!.
Har da wani ɗan siririn munafikin sallama ta yi yadda kukasan ɗakin Pretty zata shiga.
Tashin sense, ai tana shiga cikin ɗakin sai ganinta ta yi a wani irin kungurmin forest, wata duniya daban, wanda ganinsa kawai zai iya sa mai karamar zuciya zuciyar tasa ta buga ya mutu.
Ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba na ganin wanna kungurmin forest bakin kirin mai cike da abin tsoro, gabaɗaya bishiyoyin cikin forest ɗin suma jikinsu ya yi bakin kirin, ga wasu irin kawunan mutane, ga kasusuwan kwarangwal, abin dai sai wanda ya gani, ga wasu irin inuwa dake gilmawa ta gaban idanunta tamkar na wasu gungun aljanu, a gabaɗaya dajin nan babu wani abu mai ɗan dama dama da zaka iya gani, sai zallar madarar abin tsoro mai firgita kwakwalwa.
Dik tsananin karfin hali irin nata sai da ta yi balai'n rasaza, ta kasa iya furta ko uppan, jikinta har kerma ya fara yi, sai ta fara danasanin meya kawota.
A hankali wani irin inuwar wani dogon halitta mai tsayin gaske ya fara nufo in da take tsaye, sam bata iya ganin wanna halitta, inuwarsa ne kawai zaka gani.
Da kyar ta iya ɗaga kafarta da ya yi mata bala'in nauyi, a hankali ta fara ja da baya, inuwar yana kara tinkarota, jininta sai rawa yake yi, ta kasa iya furta sunan Allah da ya kawo mata ɗauki.
Ganin da gaske wannan halitta ita yake nufowa yasa ta zage da iya karfinta na karshe ta tattare karfinta dikka ta juya da karfin gaske dan ta gudu ta fita waje, sai dai kash tana juyowa kofar ɗakin ya rufe kansa da wasu irin mahaukatan locks masu ban mamaki wanda bata san da su a jikin kofar ba sai a yanzu.
Nan take gabaɗaya empire ɗin Black Tiger ya ɓacewa ganinta, ya zamana iya dajin ne kawai a wajen, kasar dajin in da take takawa kenan bakin kirin yake kamar gawayi.
Tashin sense, wani irin dukan tara tara kirjinta ya yi, da karfi ta wage baki ta kurma ihu, sai dai sam voice ɗinta baya fita, kamar ma bata yi ihun ba.
Cike da fargabar abin da zata gani a hankali ta juyo kirjinta na dikan uku uku jikinta na kara tsananta kerma.
Wani irin mahaukacin ihu ta saki lokacin da ta gama juyowa ga wannan halitta dake nufota. Tin daga wanna ihu kuma bata sake iya ji ko ganin wani abin ba, ido da ido da ta yi da halittar yasa idanunta suka makance ta dai'na ganin komai, kunnuwanta suka kuramce ta dai'na jiyo sautin komai.
Me kuke tinanin ta gani ya makantar da ita? Me kuke tinanin zai faru da ta kurmance?
Yanzu wasansu zai fara, shin kuna tunanin dama zasu zubawa Sweetie ido ta musuluntar da su Ronnie ne? Su da jininsu na tsanar musulinci ce? Akwai matsala fa! Sweetie ta taro yakin da a yanzu dai ba iya shi zata yi ba! Saboda a yanzu ita kanta bata san wacece ita ba, bata san baiwar dake gareta ba bare ta yi amfani da shi wajen yakarsu ita ma dan ta taimakawa kanta da mutanen da zasu yarda da ita! Bata san ina ta dosa ba a halin yanzu, fatana dai Allah yasa kada su wujijjiga mana rayuwarta ko ma su shafe babinta a doran duniya!!.
===========================💘
DUBAI.🔥
Al'umma dai sun ki nutsuwa su kwantar da hankalinsu, saboda suna ganin mutuwa zasu yi, jami'an nan sun yi iya ka bakin ƙoƙarinsu kowa ya nutsu dan ma su iya gane kila makiyan suna a tare da su, amma ina kowa neman hanyar fita yake yi, dik da an rufe gates ɗin amma sun ki tsayuwa waje guda.
Gungun jami'ai ne suka yi wa ahalin Abu Abdussalam zobe domin su tabbatar da sun fitar da su lafiya lou.
Sai dai fa Ramish da aka hara yaki motsawa daga in da yake bare har ya bi ayarin Abu Abdussalam su koma gida.
Ya dai ce Bilal ya kasance a tare da Abbie ɗin nasu, shi yana nan bari ya tabbatar da dik wanda ya zo nan dominsu ya koma gida lafiya ba tare da kwarzani ba, ba yadda Abu Abdussalam bai yi da shi a kan yazo su tafi ba amma yaki yarda.
Hankalin Abu Abdussalam a tsananin tashe, saboda yasan Ramish ɗin aka hara kunga bai kamata ya tsaya a wajen ba, amma yaki tafiya, burinsa ya kama wanda ya yi wannan harbin.
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Kaiwa suke suna sake komawa, suna safa da marwa a tsakiyar katafaren parlournsu, gabaɗaya zufa ce take ta keto masu, ta wanke fuskokinsu tamkar waɗan da aka watsawa ruwa, gabaɗaya parlourn da suke ɗin A.c ne a kewaye ta ko'ina, amma a haka suke haɗa wannan zuba saboda bala'in zilmi da fargaba da suke ciki, fatansu ɗaya shi ne Leesharh ta ɗauki wanna call ɗin, saboda wannan shi ne kawai damar da suke da shi, in har wanna dama ya kubce masu to abubuwa biyu dole su faru, na farko dole za'a kara tsananta tsaro a gidan Abu Abdussalam wanda ba zasu sake samun irin makamancin wanan dama ba, sannan dole su Ramish zasu shiga binciken wanenen yake yi masu wannan aiki?.
Sun san wanene Ramish tsab zai iya kamasu, dan kwararrene a aikinsa, dole su shiga tsananin tashin hankali.
Sai kiran wayar hannun Leesharh suke yi babu kakkautawa.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
Call ɗin farkon ne ya katse na biyu ya sake shiga, Sharifat tana rike da hannunta ɗaya, call ɗin yana gab da katsewa ta sanya babban yatsarta zata ɗauka.
Kamar daga sama aka bugeta ɗaya daga cikin jami'an da suka yi masu zobe, jama'a ne suka ture shi by mistake ya yi baya baya, to da yake ita da Sharifat ce a kusa da shi sai ya bugeta, ta ɗan yi baya ta bugi Sharifat wayar hannun nata ya faɗi ƙasa.
Ina cikin cunkosan jama'ar nan ba ta yadda za'ayi ta tsugunna dan ta ɗauki wayar, tashin hankali iya tashin hankali ta shiga, ta rasa ya zatayi, ga shi wannan ɗauka call ɗin da zata yi shi ne aiki na karshe da zata yi wa masu nikaf a shirmenta wai sai su bata babanta.
Sosai ta shiga tashin hankalin da har bata san lokacin da hawaye suka fara wanke mata fuska ba.
A tunanin Sharifat saboda tashin hankalin da suka shiga a yanzu ne yasa take kuka, dan haka sai ta shiga bata hakuri tana gaya mata babu abin da zai samesu lafiya lou zasu koma gida.
Ina ai ita tasan me take tunawa, cigaba da kukanta kawai ta rinƙa yi tana jin zuciyarta tana yi mata zafi.
A haka aka fita dasu ta baya, babban tashin hankalinta na biyu bata taho da wayar ba, a tunaninta ta ina zata yi magana da masu nikaf ta ji ta gama aikin ne ko da saura?.
Tun da suka dawo gida take kuka ta ki ta yi shiru, Sharifat ta yi lallashi har ta gaji amma ina taki ta yi shiru.
Dan dole Sharifat ta rabu da ita ta je ta yi wanka tare da zuwa ta shirya cikin female arabs jallabiya, ta yi kyau sosai.
Wayarta ta zo ta ɗauka domin ta kira number yayanta, dan hankalinta yaki kwanciya ganin ba'a tare da shi suka dawo ba, ta shiga damuwa sosai, dan dai kawai ba yadda zata yi ne.
Numbersa ta shigar ta fara kira. Wayar ta yi ringing har ta katse ba'a ɗauka ba, Leesharh na kwance saman gado har lokacin tana murzan kukanta.
5 miss calls Sharifat ta yi wa Ramish amma bai ɗaga ba, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, dik sai ta ji kanta yana jujjuya mata, addu'a ta fara yi Allah Ubangiji yasa yana lafiya.
Miƙewa ta yi ta shiga toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shinfiɗa dadduma, sallar mangariba ta gabatar tare da nafilfili ta shiga yi mashi domin Allah ya kare mata shi, wlh Sharrifat tana kaunar Ramish sosai.
Addu'oi sosai ta rinƙa yi mashi a cikin sujjada. Ta ɗauki almost 4 hours a saman dadduma tana karatu da addu'oi bayan idar da sallah isha'i da ta yi, har kwallah sai da ta yi mashi!.
Abin ya yi matuƙar ɗaga mata hankali.
Daga karshe bayan ta kammala ne ta miƙe ta dawo wajen gadon, a lokacin Leesharh ta dai'na kuka sai ajiyar zuciya take saukewa.
Wayarta Sharifat ta ɗauka, number Abbie ta kira. Bugu ɗaya ya ɗauka. Kamar zata yi kuka ta ce.
"Abbie kana gida ne?".
Abu Abdussalam dake kishingiɗe a saman wani shinfiɗa tasa ta alfarma mai kama da shinfiɗar sarakuna a cikin rest part ɗinsa ne ya amsa mata da yana gida kuma yana wajen hutawarsa.
"To Abbie gani nan zuwa".
Da okey ya amsa mata. Katse kiran ta yi tare da fara matsawa Leesharh a kan ta tashi zu je wajen Abbie.
Har da ce mata. "Tin da ni kin ki ki ji rarrashina zaki ji na Abbie ai, sarkin tsoro kawai, ke daga jin anyi harbi da bullet zaki wani fara kuka! A haka kuma zaki auri Yah Bilal kenan?".
Allah sarki Sharifat har ta bani tausayi, bata san cewa ba wannan ne a gaban Leesharh ba, hmmm wanna shi ne Sharifat tana goya yar kunama.
"Ni Sharifat ki tafi kawai babu in da zan je". Da kyar voice ɗinta yake fita saboda kuka.
"Allah babu in da zan je ba tare da ke ba, kawai ki tashi mu tafi".
Make kafaɗa ta yi haɗe da tirjewa ita lallai ba zata je ba. Matsa mata Sharrifat ta cigaba da yi dan ba zata iya ganinta a cikin damuwa ta kyaleta ba.
Hannu ta kai ta riƙo hannunta tana ƙoƙarin janta ta mikar da ita tsaye dan dole.
Cikin ɗaga murya Leesharh da ranta ya gama ɓaci ta ce.
"Ki sakeni babu in da zanje nace maki! Wai ana dole ne?!"
Sam Leesharh bata san ta daka mata tsawa haka ba, ranta ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.
Zaro idanu Sharifat ta yi ba tare da ta saketa ɗin ba, nan take kuma sai ta ji zuciyarta ya tsorata da Leesharh, a take ta fara tunanin anya kukan tsoro Leesharh take yi kuwa? Anya babu wani abin a kasa kuwa? Kukan ne ya wuci na hankali yanzu kam.
Ganin Sharifat ta zaro idanu ne yasa ta fahimci abin da ta aikata, dan haka sai ta yi kasa da kantah haɗe da riƙo hannayen sharifat cikin nata.
"Ki yi hakuri sister, ban san na yi hakan ba".
Kamar wadda aka sanyawa battery Sharifat ta ce. "Leesharh kukan me kike yi?".............. Ta yi maganar idanunta a kan Leesharh babu ko kyaftawa!.
Nan fa Leesharh ta fara zazzare ido tana ƴan kame kame, ta rasa me zata ce, ita da kanta tana neman tonawa kanta asiri.
"Am....... Ba........... Ba........ Babu komai". Ta faɗa murya a sarke.
"Tun da ni ba zaki faɗa mun ba tashi mu je wajen Abbie sai ki faɗa mashi". Cewar Sharifat.
Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "Okey bari in yi wanka sai mu je".
Kamar zata ce mata su je kawai, sai kuma ta ce bari ta kyaleta ta yi wankan zai fi.
Toilet ta miƙe ta shiga dan ta yi wanka. Sharifat ta zauna a bakin bed tana jiran fitowarta.
A bakin wash hand base ta tsaya tana kallon kanta a cikin mirror, Allah sarki har idanunta sun kumbura saboda kuka, haƙiƙa Leesharh tana cikin tsaka mai wuya baiwar Allah, daga gidan yari ta wuce wannan ukubar kuma, Allah dai ya bata ikon cin jarabawarta.
Ta jima sosai tsaye tana kallon kanta kafin daga bisani ta wuce wajen haɗa ruwan wanka, dik jikinta a mace kamar anzare mata laƙa.
Sharifat na zaune tana ta istigifari tana rokan Allah da yasa Ramish ɗinta yana nan lafiya, har Leesharh ta fito ɗaure da towel ta sameta.
"Kisaka irin jallabiyata mu yi iri ɗaya Abbie zai ji daɗin hakan". Cewar Sharifat, ta yi maganar dai'dai lokacin da Leesharh zata shiga dressing room ɗinsu dan shiryawa.
Jinjina kai ta yi haɗe da amsawa da okey sannan ta sa kai ta wuce.
In short a shirye Leesharh ta fito cikin kaya irin na Sharifat, tin bata karisa in da Sharifat take ba ta miƙe ta nufeta.
Hannunta ta rike suka nufi waje. Kai tsaye wajen Abu Abdussalam suka nufa.
Yana kishingiɗe saman shinfiɗar ga kayan marmari a gabansa, yana sanye da white arabs jallabiya, dattijon arziki kenan.
Yana ganinsu ya miƙe zaune, a saman shinfiɗar suka zauna, Leesharh ta gefen damarsa Sharifat ta gefen hagunsa.
Sharifat tana rike da wayarta irin na Leesharh a hannunta.
"Barka da dare Abbie". Sharifat ta faɗa.
Bai kai ga amsawa ba Leesharh ma ta faɗi hakan. Cikin muryar dattaku ya ce.
"Yauwa ƴaƴana.............. Leesharh menene ya sami idanunki?"
Kasa ta yi da kai tana ƙoƙarin fara ƴan kame kame.
"Abbie tin daga wajen taron nan da taga anyi harbi ta fara kuka, nayi ta rarrashinta ina faɗa mata babu abin da zai sameta amma taki yin shiru har sai da muka dawo gida".
Tin da Sharifat ta fara magana kallonsa yake a kanta har ta dire, sannan ya dawo da kallonsa a kan Leesharh.
Yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi maganar Ramish ya shigo wajen bakinsa a ɗauke da sallama.
A miliyan Sharifat ta kai kallonta a kansa, shi kuwa hankalinsa sam baya a kansu, yana sanye da sleeping dress riga da wando milk color masu bala'in kyau, ya yi kyau sosai, dik da bashi da fara'a kullum fuska a ɗaure, amma da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci yana cikin damuwa, ya ƙara tsuke fuskarsa sosai, ya haɗe gerar kasa da ta sama.
Saman sofas dake wajen ya zauna, sai wani kara tsare gida yake yi yana cin magani.
Wani irin mummunar razanannen faɗuwar gaba Leesharh ta ji a lokacin da ta ɗaura idanunta a kan wayar dake hannunsa, tabbas wayarta ce da masu nikaf suka bata, to ya aka yi wayar ta zo hannunsa?. Ta jefawa kanta tambayar.
Dakatawa da yiwa Leesharh magana Abu Abdussalam ya yi tare da mayar da kallonsa a kan Ramish.
"My son ka dawo?".
Cike da ƙaguwa da san jin amsar da Ramish zai bashi ya yi tambayar, cike kuma da tsananin fargabar abin da zai ji.
Jinjina kai Ramish ya yi ba tare da ya yi magana ba.
"To meyafaru and kiran me suka yi maka?". Cewar Abu Abdussalam.
Ya jefa mashi tambaya cike da damuwa, dama tun ɗazun Ramish ya dawo daga wajen taron suna tattaunawa da Abbie ɗin nasu, yanzu ba jimawa jami'ansa suka kirasa a waya shi ne ya tashi ya tafi, ya ce da Abbie yana zuwa yanzun nan, dawowarsa kenan.
Wayar Leesharh dake a hannunsa ya miƙewa Abu Abdussalam.
Karɓa Abbie ya yi yana jiran a kora mashi bayani, shiru Ramish bai yi magana ba, kamar wanda baya san motsa lips ɗinsa, ya yi kasa da kai kamar mai tinanin wani abin.
Gajiya da ƙaguwa da Abbie ya yi da san jin bayani ne yasa ya ce. "My son meyake faruwa ne?".
Shiru Ramish ya kara yi har na tsawon good 2 mins.
Sai kallansa Leesharh take sata kirjinta na dukan uku uku, ji take yi tamkar zata mutu, gabanta sai mummunar faɗuwa yake yi, alamar rashin gaskiya ne karara ya bayyana a saman face ɗinta, har wani zufa take ji yana keto mata.
Ita ma Sharifat sai satar kallonsa take amma ita kallon soyayya take yi mashi ba ta wata manufa ba, dan ma dai tasan baya san yawan kallo ne yasa take kallonsa a sace, da a sarari zata gansa.
Sarai Abbie ya gane cewa ƴarsa ta kamu da san Ramish da jimawa, amma ya zuba masu idanu yana ganin gudun ruwansu, baya san kuma ya faɗawa Ramish Sharifat tana sansa, ya fi san Ramish da kansa ta gane hakan ya kuma faɗa santa da kansa ba tare da an haɗa su ba.
Sai dai Abbie abin ya fara damunsa yanda har yanzu babu wani canji a tattare da Ramish, ko kallo baya ɗaga idanun ya yi wa Sharifat, abin ya tsayawa Abbie a wuya, ba shi kuma da burin da ya wuce ya ga wannan haɗin ta yiwu, yana ji da ƴar nan tasa matuƙa.
Sai da Ramish ya gama hatsewa da jan ajinsa, sannan ya ɗan gyara zamansa, ba tare da ya ɗago ya kalli ko mutum ɗaya daga cikinsu ba ya fara yin magana kamar haka, cikin sanyi murya haɗe da nutsuwa ya ce.
"Wannan waya da na baka makunnine na tashi nakiya".
Ɗan zaro ido Abbie ya yi, matsalarsa da Ramish kiwiya wajen yin magana, sam baya san buɗe baki ya yi magana yadda ya dace,