Showing 324001 words to 327000 words out of 403653 words
komai ba, sai dai zuciyarsa ta gagara hakura har sai da ya nemi Mahreen ya kalleta ba tare da saninta ba, kaunar Mahreen a jininsa take wlh, dan ita ta fara kula da shi a kauye, kowa ya gujesa ban da ita, shiyasa take ta daban a ransa!.
Ganin ta gagara motsawa a wajen ne yasa guyson ya riko hannunta tare da cewa. "Let me escort you ki je ki wanke face ɗin naki a part naku sai mama Haulat tai maki wani make up ɗin mai kyau". Sam bata yi musu ba ta bisa, dan dama so take yi ta bar wajen. Kunyar momma yasa ta gagara motsawa. Ta kasan ido Jaish ya bisu da kallo har suka fita, sannan ya miƙe tsaye. "Momma ina zuwa". Tsabar farincikin da Momma ta shiga na tina Mahnoor a rayuwarsa da ya yi yasa ta gagara yin magana, sai sakin cool murmushi kawai take yi, shi ma ya lura da yadda ta shiga farinciki, ya ji daɗin abin matuƙa.
Bayan su Mahnoor ya bi, dama ba wani fita da zai yi, kawai ya biyota ne ya ga yadda zata kare da ƴan gida, wato a fakaice dai ya rama abin da ta yi mashi, ta sanya shi jin kunyar bappa matuƙa, tamkar ya natse cikin ƙarƙashin ƙasa a wancan ranar, to shi ma yau ya rama kunya tamkar ta natse cikin ƙasa.
Lokacin da ya shiga bedroom ɗin har guyson ya wanke mata fuskar yana tayata goge shi da towel, ya ce ta zauna a saman mirror chair bari ya yi mata wani kwalliyar mai kyau, dan shi ma ya iya make up sosai zamansa da Sharifat a Dubai, so ta zauna zai yi mata wani kwalliyar mai kyau.
"Waye ya ce ka wanke mata fuska Omar?". Daga bakin kofa suka jiyo voice ɗinsa, a tare dik suka kai kallansu a kansa, yana tsaye ya ɗaure fuska tamau,wai irin sai ya ja mata rai sosai kafin ya fahimtar da ita yasan wacece ita a garesa, yanzu ba zai faɗa mata ya tina komai ba.
"Yah Jaish baka ga kwalliyar bashi da kyau bane? Shiyasa fa na wanke mata zan yi mata wani". A ɗan shagwaɓe ya yi maganar!...... "A haka nike san ta rinƙa kwalliya kullum, kada ka sake wanke mata, kuma a haka zata fita, in bata san a ganta sai dai kada ta fita daga nan ta zauna, amma ni irin kwalliyar nike so". Ya kai karshen maganar tare da shigowa ciki, bilhakki da gaskiyarsa fa ya zage yake maganar, wai irin kada ma su zaci wasa yake yi. Kallan juna suka yi ita da guyson, take idanunta suka cika da kwallah, kenan sai dai ta yi ta zama a cikin ɗaki ba zata fita wajensu Chuchu ba?. Ga shi ya ce irin kwalliyar kawai yake so, wannan ai ba kwalliya bace, hauka ce. Shi ma guyson sam bai ji daɗin batun ba, amma da yake yayansa ne ya zartar da hukunci, sai kawai ya yi na'am da hukuncin, ya kuma yi dabara ya zame jikinsa ya gudu abinsa, ba ruwansa da shiga tsakanin ma'aurata.
Yana fita suka ci karo da Mahreen zata shigo part ɗin, dan tin jiya bata haɗu da Mahnoor ɗin ba. Sai da gabansa ya faɗi, take wani irin fargaba ya lulluɓesa. Sai dai kuma sai satar kallonta ta katsan ido yake yi, Chuchu ƴar wanka ta tsantsara mata kwalliya mai shegen kyau, ta wani kele cikin riga da wando arabiyans dress, ta yi rolling na veil a kanta, gata fara launin kayan dark ash, sai kyanta ya kara bayyana, ɗan bakin nan nata ya sha lips balm kamar zai ɗiga, sai wani turo shi take yi, kamar ma bata san rufe shi sosai, sai wai yauki take yi bata san taka kasa.
Kamar wani maras gaskiya ya ce mata. "Sannunki". Yana magana cike da ƴan kame kame, kamar fa tsoronta yake ji, shi kaɗai ya bi ya dibirbirce. Harara ta dallah mashi wadda ta sanya shi haɗiyar yawu da kyar, cike da gadara ta ce. "Kada ka sake yi mun magana, kai ɗan iska ne ni kuma mai mutumci"..... Kai innalilahi, wai kunji ita mai mutumci, to ai mutum baya cewa ga abin da yake da shi, dik wanda yake da abu ba sai ya faɗa ba, mutane da kansu zasu faɗa mashi yana da kaza, dik mai cewa yana da shi to bashi da shi ne, in yana da ba zai faɗa ba, yanzu fisabilillah kunga Mahreen ta yi kalar mutumci? Innalilahi wannan yarinya zata kashe mutum da dariya, ko da yake dama ance yabon kai jahilci ne, kuma hakan ce, jahilci na ɗawainiya da ita shiyasa take yawan yaba mashi kanta, ban da jahilci ba zata yi ba ai, zata bari ne a yabeta!.
"Ki yi hakuri". Shi ne abin da ya faɗa mata, kai ta sa zata wuce tana wani dallar mashi harara da waɗan nan shegun idanun nata masu saka shi ya shiga shakku da zargin kansa ko ya yi mata laifi ne. Har ta ɗan yi nisa da shi sai ya juyo da kallonsa a kanta. "Ki yi hakuri Mahreen, ba zan iya dai'na yi maki magana ba, dan kina daga cikin mutanen dake burgeni nake kuma kauna". Ya faɗa idanunsa a kanta. Cak ta dakata da tafiyar da take yi, wai irin ita ma zata yi na ƴan gayun nan, cike da yanga ta juyo, from head to toe ta bisa da kallo kafin ta ce. "Ni kuma bana sanka, bana mu'amala da ƴan iska, bana san ragwayen mutane, kuma daga yau ba sunana Mahreen ba, Aunty Chuchu ta ce sunana big girl, dan haka sunan da zaka rinƙa kirana da shi kenan, big girl". Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta cigaba da tafiyanta. Binta da kallo ya yi yana mamakin yadda take da shegen tsiwar tsiya, wai big girl, siririn murmushi ya saki, lallai Chuchu ma bata san zaman lafiya da take koyawa Mahreen rashin mutunci kala kala, yo in banda abin Chuchu ma Mahreen har za'a kara koya mata wani abin bayan sanka sankan rashin mutuncin da ta iya? Tab gaba akwai show kenan, lallai kuwa. A wani ɓangare na zuciyarsa kuma tinani ya fara yi a kan me zai yi ya birge wannan haɗaɗɗiyar babyn mai tafiya da hankalin mai lafiya, shi dai har yau kome ta yi birgesa take yi!.
Ya jima tsaye a wajen yana tinanin abin da zai yi ya birgeta har ta fara respecting ɗinsa, daga karshe ya wuce zuwa in da zai je.
Shi kuwa Jaish guyson yana fita ya wuce saman bed ɗinsa ya kwanta yana satar kallanta ta witsiyar ido, sai da ya kwanta sannan ya ce ta mayar da kwalliyar dake kan face ɗinta tamkar yadda ta tashi ta gani, haka yake san ganinta. Yana gama faɗar hakan ya mai da idanunsa ya lumshesu. Shiru ta zauna tana jin tamkar ta fasa ihu, a cikin zuciyarta ta ce bata san sai yaushe zata ji daɗin rayuwarta ba, kullun tana cikin ƙunci ita. Cike da damuwa ta fara yin abin da ya umarceta.
Allah ya shirya mana Jaish, ku ce Amin! Wai ya tina wacece ita ɗin ma ba zai barta ta samu farinciki da natsuwa ba, sai ya wahalar da ita kafin ya faɗa mata yana santa? Wannan ai iskanci ne, raina ya fara ɓaci fa........🥱
To bari mu leƙa wani wajen mu dawo.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
BAYAN WASU ƳAN KWANAKI.
Tun da ta tashi da safe yau bata ji motsinsa ba, kuma bata nemesa ba, sai dai a karkashin zuciyarta ta damu matuƙa da san jin ina yake yau bai leƙota ba? In dai yana nan baya taɓa ɗaukar 2 hours ba tare da ta sanya shi a idanunta ba, to ina ya je yau?. Zuciyarta ta jefa mata tambayar da bata da amsarsa. Shiru ta luluƙa duniyar tinanin dik abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninsu, take irin salon da ya rinƙa nuna mata a fitansu da suka yi ya fara dawo mata a cikin kwakwalwarta.
Lokacin guda ta saki murmushinta mai kayatarwa wanda ya kan jima bai samu gurbi a face ɗinta ba, sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta lumshe idanunta, cikin ƙankanin lokaci ta tsinci kanta cikin wani irin farinciki na musamman, har da wani nisawa kamar.......... 🤫
Can kuma da tinanin Sharifat ya ratso cikin brain ɗinta, cikin gaggawa face ɗinta ya yi saurin canzawa, siririn tsaki ta ja tare da haɗe rai. A hankali ta miƙe ta sauko kasan bed ɗin, waje ta nufo domin tasamawa kanta abin da zata sanya a bakin salati, dan yunwa ya fara addabawa cikinta. Kitchen ta nufa, gidan babu kowa sai daddaɗar kamshi dake tashi. Dattijuwar dake kula da ita ta yi barci a nata bedroom ɗin dake kusa da na Leesharh ɗin.
Hot tea ta haɗawa kanta mai daɗi, sannan ta ɗauko small chop a plate ta nufo waje, da alama yau bai yi breakfast a gida ba, dan kuwa alama ta nuna ba'a shiga kitchen ɗin nan ba yau. Bedroom ɗinta ta koma, bata jin daɗi dai, amma haka ta tuttura abin da zata iya ci, sai da ta ji cikinta ya ɗan cika, sannan ta miƙe ta fito da kayan waje, komawa ta yi ta hau gado, ta cigaba da tunane tunanenta wanda babu jimawa barci ya yi awon gaba da ita again.
Wunin ranar dai gabaɗaya a ɗaki ta wuni, sai zuba barci take yi tana kara tashi. Wasa wasa sai har karfe 10 na dare bata ji motsinsa ba, abin ya gefata a cikin damuwa matuƙa, har ji ta yi kanta na yi mata ciwo, tinani ya fi ɗari a cikin ranta, wani ɓangare na zuciyarta ya ce mata baya nan, wani kuma ya ce mata yana nan yana cikin bedroom ɗinsa kila wani abin ne yasame shi yasa ya kasa iya fita, dan haka ta je ta duba shi. Tinani dai kala kala, daga karshe sai ta miƙe ta nufi toilet, a gurguje ta yi wanka haɗe da ɗauro alwalar barci, fitowa ta yi ta shirya cikin ɗaya daga cikin sleeping dress ɗinta dake gidan, ta shafa mayukan da ya saya mata, ta yi shirinta tsab, ta kuma yi kyau sosai abinta, ta hau gado ta kwanta a zuwan zata share tinaninsa a ranta, amma sai kuma ta kasa, domin kuwa tana kwanciya tinanin ya dawo mata sabo pil.
Dogon tsaki ta ja tare da miƙewa zaune, hararar ɗakin ta fara yi sai ka ce shi ya yi mata laifi, siririn tsaki ta sake ja kafin ta zuro kafafunta kasan bed ɗin ta miƙe tsaye, kai tsaye ta nufi waje, tana tafiya tana harare harare. Har ta kai bakin door sai kuma ta dawo ta ɗauki hijabi ta ɗaura a saman sleeping dress ɗin nata, ta wuce tana kumbura kumatu. Kai tsaye ta nufi master room ɗinsa, ko tsoron nufar ɗakin bata yi ba, amma ta ji tsoron abin da zata tarar dangane da shi, fargabarta ɗaya ace bashi da lafiya ne ya kasa fitowa waje.
Siririn sallama ta yi a bakin kofar shiga bedroom ɗin. Shiru babu alamar motsin mai rai da ta jiyo, jim ta ɗan yi kirjinta na bugawa da ɗan karfi karfi, tana fargabar tura kofar ta ga menene a ciki. Almost 3 mins tana tsaye a wajen, tsananin fargaba yasa ta ji tamkar ta juya ta hakura da zuwa ta duba shi, amma zuciyarta ta kasa amsar hakan, ba zata iya barci ba ko ta koma, ba zata samu sukuninta da natsuwarta ba idan har bata tabbatar da yana lafiya ba.
Tamkar mai rawar sanyi tasa hannu ta tura kofar bedroom ɗin nasa, kirjinta na tsananta bugawa, da kyar ta sake yin wani sallamar kafin ta kutsa kai ciki. Lokaci guda ta saki nauyayyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a ciki, sai sanyi da kamshin mai ratsa zuciya dake ta shi, tin da babu kowa a ciki hakan yasa ta fahimci lallai lafiyarsa lou tin da har ya fita baya nan. Ta ji sanyi a ranta, dan haka ta ɗan tsaya tana bin bedroom ɗin da kallo na ƴan mitocin da basu gaza 3 ba, tana yawan jinjinawa tsabta da shegen san kamshinsa, baya shiri da datti ko kaɗan.
Haka ta gama kalle kallenta ta juya da nufin ta bar ɗakin. Step biyu ta taka sai kuma ta tsaya cak kallanta a ƙasa, kamar wadda aka dakatar. Can kasan maƙoshinta kamar mai raɗa ta ce. "Ka yi hakuri ba da gangan na shigo maka ɗakin ba, akwai dalili". Ta kai karshen maganar tare da ɗago da kallanta a kansa.
Yana tsaye a bakin door na shigowa, ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa, sanye yake da sleeping dress, da alama bai jima da dawowa ba, hannunsa rike da cup, kamar dai daga kitchen ya fito, da alama tin safe bai ci komai ba, ga alamar wahala a tattare da shi, yunwa da gajiya ya tattara a saman face ɗinsa, idanunsa sun yi jajir sun ɗan kumbura, kamar wanda barci ke binsa bashi, face ɗinsa ta ɗan yi fayau haka, kamar wanda ya taso daga zazzaɓi, sai dai ya yi kyau sosai, lips ɗinsa sun kara tura red sosai alamar ya ɗan rasa natsuwarsa na ɗan lokaci.
Wani irin faɗuwar gaba ta ji ganin irin dressing dake jikinsa, ga rigar ma gabaɗaya gabanta a buɗe, wide chest ɗinsa a waje. Ɗauke kallanta daga kansa ta yi tana jin kirjinta na bugawa da karfi karfi. Ya tsareta da ido babu ko kyauftawa, tabbas ta yi kyau cikin wannan hijabi, sai dai shi, dressing dake ƙarƙashin hijabin yake san kallah, ta rufe ta kuntata shi, gabaɗaya kallansa a kan surar jikinta, idanunsa kamar wani ɗan maye yau!.
"Am...... In..... To..... Ummm zan iya wucewa in tafi bedroom ɗina?". Ta yi maganar voice ɗinta na sarkewa, kamar wata maras gaskiya. Ɗan ɗage shoulders ɗinsa ya yi tare da sake saukesu alamar whyn't, zata iya wucewa kenan. Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, kanta a ƙasa taki sake ɗagowa su haɗa ido, dressing ɗinsa yana haukatar da tinaninta sosai, dan haka bata san cigaba da kallonsa yana canza zuciyarta, zai sanyata ta ci amana a banza, ita kuma ba zata ci amanar Sharifat ba!!!....... LEESHARH tamu ta amana mai amana, wai ba zata ci amana ba, ta dage fa a kan lamarinta, ta riki gaskiya da amana, mazamaza ku yi koyi da ita!!......😅
A hankali ta tako tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta matsa kusa da door ɗin, a tinaninta idan ta matsa zai bata hanya, sai ta ga akasin haka, yana tsaye yana binta da mayen kallo kamar a buge yake. A ɗan gefensa kaɗan ta dakata, kamar zata ɗago ta kallesa sai kuma ta fasa, cikin natsuwa ta furta. "To ai babu hanyar wucewa sai ka matsa"........ Bai san lokacin da ya ɗaga gera guda ba, irin haka ne? Sai kuma ya ɗan matsa mata hanya kaɗan wanda shi kansa yasan ba zai ishata wucewa ba, wato dai barin bakin kofar ne ba zai yi ba saboda iskancin nasa yau kuma ta motsa.
Sarai ta fahimci magana yake nema da ita, dan haka sai ta yi kamar bata gane ba, ta matsa tare da ɗan kame jikinta, ta raɓa shi zata wuce. Yana binta da kallo sai da ta isa dab da saitin kirjinsa yasa ɗayan hannunsa ya janyota jikinsa, take ya sauke wani sanyayyar ajiyar zuciya, ita kanta ajiyar zuciyar ta sauke, har da wani ɗan kwantawa a jikin nasa, irin ita ma tana ra'ayi kenan. Can kuma sai ta tuna da ƴar uwarta Sharifat, da sauri ta yunkura zata bar jikinsa tana wani ƴan kame kame. Hannunsa ya ɗaura a saman bayanta kafin ya furta. "Menene kuma?"....... Tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Ramish Sharifat fa? Kasan dai kai take jira ko?.........". Wani irin kallo mai kama da harara da ya wurga mata ne yasa ta yi saurin haɗiye maganar nata.
Gently ya ce. "Daga yau kada ki sake mun maganarsu a nan, na tsanesu dikkansu, kuma su nike zargi a kan abin da ya faru a tsakanina dake, zan kuma tabbatar da hakan soon". Zaro idanu ta yi jin cewa Sharifat tana daga cikin waɗan da yake zargi, ita dai zata iya rantsuwa da Allah Sharifat ba zata aikata wannan ɗanyan aiki ba, ɗan gara ma Ummie zata iya cewa zata iya aikatawa, amma Sharifat da take baiwar Allah, yarinya mai hankali da natsuwa, kai gaskiya da kamar wuya wlh.
"Amma Yah Ramish Sharifat fa.........". Yatsarsa ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗinta alamar ta yi mashi shiru, wani irin shock ya ji lokacin da ya ji soft lips ɗin nata, sai da tsikar jikinsa suka mimmiƙe, da sauri ya ɗauke hannunsa tare da cewa. "Me kika zo yi a ɗakina ma tukun nan?"....... Shiru ta ɗan yi, dan bata san me zata ce ya kawota ba, bata son yasan ta damu da shi har ya yi zatan ta fara son shi ne, dan ita babu gudu babu ja da baya a maganarta. Jinin Hausa Fulani, magana ɗaya take yi babu sauyi....... My people's mu gaya mata gaskiya ko mu barta duniya ta gaya mata?. Yen yen yen, wai magana ɗaya take yi ƴar ƙaniya, na make bakinta ne maras kunyar karya. Ki zauna nan ga su Sahibatu can suna rububin Ramish kamar su mutu, sai sun kwace shi zaki ga riƙon amana a idonki ƴar ƙaniya.
"Babu amsa ne?. Ko dai kin zo duba ni ne? Kin yi kewata ne?". Cikin ɗan zoyala ya yi maganar. Lallausan kallo ta bishi da shi mai narka zuciya kafin ta ce. "Ko ɗaya, meyasa zan zo dubaka? Meyasa zan damu da kai? Meyasa zan yi kewarka bayan bani da wata haɗi da kai?"........... "Da gaske baki da haɗi da ni?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e bata da haɗi da shi.
Rage buɗuwar idanunsa ya yi, ya zamana tamkar mai jin barci, sannan ya juyar da ita ta zamana bayanta ne ke manne da kirjinsa, hannunsa dake saman bayanta ya dawo da shi saman shafaffiyar cikinta,