Showing 402001 words to 403653 words out of 403653 words
na yarda daga yau zan ajiye addinin musulunci na bi kristanci!!". Babbar magana, tashin hankali kenan!!! Zaro idanu Ronnie ya yi yana kallanta, dama a ransa yasan dik jan kunnen da ya yi mata a kan kada ta yi magana in suka zo dik na banza ne, saboda ya san ba'a ɓarna a gabanta ta yi shiru, sai dai bai taɓa zatan ta haka zata yi fito na fito da su a bainar nasi ba, tana neman jefasu cikin cakwakiya tasa shi ma a gano ya musulunta, shi wai ya zai yi da Sweetie ta ɗan rage zafa a kan addini ne? Ya jefawa kansa tambaya. A hankali ya ɗago ido dan ya saci kallonta.
Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Dik matsoraci baya da'awa, ni bana tsoron dik wani hukuncinsu, abin da na sani shi ne dole ko a bakin zaki nike zan faɗa cewa Allah shi ne Allah shi kaɗai, ba zan taɓa yarda da akasin hakan ba, koda ina tsakanin mutuwa da rayuwa!! Ka dai'na tsoron bayin Allah, ka ji tsoron mahaliccin bayin ne kawai!!".
Da farko ya yi niyar dallah mata harara, zafafan kalamanta yasa ya fasa, saboda ta fishi gaskiya.
Kallan tsab pastor ya yi mata kafin ya tambayi who's she?. Ronnie yana ƙoƙarin basa amsa ta rigasa da cewa. "Mai gaskiya wadda bata goyan bayan karya kuma bata shakkar faɗar gaskiya a koma ina!! Sannan kuma wadda take rike da fitillah mai haske ta zo haskaku a cikin duhun da kuke, ta fitar da ku daga cikin duhun kai zuwa hasken musulunci".
Tin da ta fara magana Black Tiger yake kallanta yake mamakin karfin hali irin na yarinyar nan, kai ka ji wai mai gaskiya, Sweetie akwai abin dariya wani lokaci, bilhakki da gaskiyarta ta zage zata yi masu wa'azi, ta ɗaure fuska tamau wai irin su san ba wasa take yi ba.
Fitarsu ke da wuya Black Tiger ya farfaɗo daga sumar da ya yi, shi ne ya zauna yana kallansu.
"A cikin injila ta yahaya chapter 1 verses 1 a nan ne Yesu ya ce shi ne Allah!". Cewar pastor kenan. Da gadara da full confidence ɗinsa ya faɗa, shi nan irin shegen nan, wai ya kawo hujja...... A karo na biyu Ronnie ya yi mamakin biyewa Sweetie da pastor ya yi, bai yi tinanin zai biye mata ba, abin da bai sani ba shi ne, shi maras gaskiya a dik in da yake in dai ka yi magana sai ya biye maka, saboda yana san wanke kansa ya nuna shi mai gaskiya ne, mai gaskiya na ainahi baya damuwa da sai jama'a sun yarda da shi, burinsa kawai Allah ya yarda da shi, idan Allah ya yarda da shi to da izininsa zai sanya jama'a su yarda da shi!!.
Wani irin sanyi Sweetie ta ji ya ratsa zuciyarta, abin nema ya samu, dama so take pastor ya biye mata ta kaisa ƙasa, har ita zai kawowa wani hujja, muje zuwa. Gyaran murya ta yi kafin ta fara da cewa.
"A'a, cikin Bible gabaɗaya babu in da aka ce Annabi Isa (A.S) shi ne Allah!!. Akwai wurare da ake nuni da cewa shi yana da matsayi na musamman, amma a cikin littafin Injil (Bible) dayawa daga cikin maganganun Annabi Isa (A.S) suna nuna cewa shi bawan Allah ne kuma manzon Allah. Dik kuma zan kawo maka hujjoji masu karfin da zaka gamsu idan ka buƙata".
Binta da kallo gabaɗaya jama'ar cikin church ɗin suka yi, shi kansa pastor kaman ya ɗan tsorata ne ko yaya ne, sai ya ce. Ta fitan mashi a church yanzun nan. Gyarawa ta yi ta zauna kafin ta amsa da babu in da zata je har sai ta gama amayar da abin da ya kawota, babbar magana kenan. Rai a matuƙar ɓace pastor ya bada umarni ga securitys su zo su fitar da ita. Kan kace me wasu shirga shirgan securitys sun shigo cikin zafa da nufin sun zo su ɗauketa su yi waje da ita.
Aikuwa suna zuwa Ronnie ya miƙe tsaye, da wani irin mugun kallo ya bisu wanda yasa suka ci wata uwar birki ba tare da sun shirya ba, kun san gabaɗaya birnin tsoron Ronnie suke ji, shi ne zakarar da ya buge kowa, dan haka suka kasa motsawa daga in da suke tsaye, saboda tsoronsa. Hararar ya bisu da shi kafin ya nuna masu hanyar fita da hannunsa ɗaya, ba tare da ya yi magana ba, ai a miliyan suka juya suka fita. Ta witsiyar ido ya bi pastor da kallo kafin ya tsayar da kallansa a kan Sweetie, cikin natsuwa ya ce. "Kina da hujoji a kan maganarki ne?". Ya yi mata wannan tambaya ne ba dan bai san tana da hujjijo ba, sai dai ya kare kansa, irin ya nuna shi bai san komai ɗin nan ba, kuma yana yiwa su pastor kwaɗayin Rahmar Allah, so zai so ta cetosu daga duhun kai izuwa haske.
Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas tana da hujjijo kafin ta ce. "Ina da hujjijo kwarara sosai Ronnie". "To kawo mana su". Ya faɗi hakan tare da komawa ya zauna. Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke, hankali ya kwanta, buƙatarta ta biya, rai ya yi sanyi, abin nema ya samu, dan haka cikin natsuwa ta cigaba da cewa.
"A cikin Injila ta yahaya chapter 17 verses 3 yana rubuce cewa. Kuma wannan ita ce rai madawwami (Allah kenan), su san kai Allah wanda kai kaɗai ne na gaskiya, da kuma wanda ka aiko Yesu Almasihu wato Annabi Isa kenan"
"Wannan yana nuna cewa Allah shi ne kaɗai na gaskiya, kuma Yesu (Annabi Isa) manzonsa ne. In bai yarda ba ya duba cikin Bible ɗin yanzu zai ga hakan, dan haka Annabi Isa dai bai ce ayi bautarsa ba, kuma dik mai kaunarsa na gaskiya ma ba zai bauta mashi ba!!".
"Kazalika cikin injila ta Matiyu chapter 26 verses 39 tana nan a rubuce lokacin da Annabi Isa (A.S) ke addu'a yana cewa. Ya UBANGIJINA ka ɗauke mun wannan kofin, amma kada nufina ta cika, sai da sanka".
"Wannan yana nuni da cewa Annabi Isa yana da UBANGIJI da yake roƙonsa dik abin da yake da buƙata, ba shi ba ne ALLAH. Sannan a cikin injila ta Markus chapter 12 verses 29 Annabi Isa (A.S) ya ce. Ku Isra'ilawa ku ji UBANGIJI ALLAHNMU UBANGIJI ɗaya ne tak da bashi da abokin tarayya. Wannan ya bayyana cewa ALLAH ɗaya ne, ba Annabi Isa ba, dan da bakinsa ya ce ALLAH ɗaya ne kuma ba shi bane!!".
"To amma me yasa wasu Kiristoci ke cewa Annabi Isa ALLAH ne?". Ta jefawa kanta tambayar da tasan babu mai bata amsa, dan haka sai ta bawa kanta amsa da cewa. "Akwai wasu wurare da aka fassara su da cewa Annabi Isa yana da wata alaƙa ta musamman da ALLAH, kamar Yahaya chapter 1 verses 1 da ka ambata a baya". Ta yi maganar idanunta a kan pastor, dan shi ya ambaci cewa a shafin farko na Injila ta yahaya Annabi Isa ya ce shi ne ALLAH, dan haka sai ta ce. "A farkon shafin layin farko tana nan a rubuce cewa. Abu kalma ce, kuma Kalmar tana tare da ALLAH, Kalmar ita ce ALLAH...........Waɗanda suke da ra'ayin Trinity, wato masu ra'ayin cewa UBANGIJI uku ne, Uba, ɗa, da ruhu mai tsarki, to su sukan yi amfani da irin waɗannan ayoyi su kafa hujja kan cewa annabi Isa ne ALLAH. Amma a cikin Bible gabaɗaya, babu inda Annabi Isa ya ce shi ne ALLAH, ko ya umarci mutane su bauta masa, sannan kai kanka ka sani har yanzu akwai saɓani tsakanin masu tafsirin Bible kan wannan batu, kuma da yawa daga cikin Kiristoci da kansu sun yarda cewa an canza Bible tun asali, kawai san zuciyarsu suke bi kamar dai kai ma, ina da tabbacin kasan an canza Bible. Wannan yasa musulmai suke da aqidar cewa Annabi Isa (A.S) bawan ALLAH ne kuma manzonsa, ba ALLAH ba, saboda ku kuna da Bible sun fi kala goma, mu kuma Alqur'ani guda ɗaya ce, tin ranar da aka saukar da ita har yau babu ko wasali ɗaya da aka canza, bama wanda ya isa ya canzata!! Saboda kalamul lah ce ita!!". Ta kai karshen maganar tare da dakatawa tana mayar da numfashi.
Ronnie ya ji daɗin wannan batu, abin ya yi mashi sugar sosai, ya sanyaya ransa, har wani ajiyar zuciya ya sauke, ya ji kwarin gwiwar zai tsayawa Sweetie tin da ta faro wannan batu ta dire aya, ta yi mashi kaca kaca da pastor yau.
Sai dai basu ankara ba sai gani suka yi pastor ya harbo bell dake gabansa sai kan gaban goshin Sweetie ya sauƙa, take ya fasa mata goshi sai jini, cikin tsawa da kakkausar murya ya ce. "Yarinyar banza, ni zaki zo kina kalubalanta? Yaushe aka haifeki da har zaki ƙaryata littafanmu? Wacece ke a duniya? Littafan da suke tun tsawon shekaru aru-aru? Ke har kin isa in duba Bibles saboda ke? Ku mutane kun ji fa! Wannan ƴar wannan aba ce take ja in ja da ni!". Ya yi maganar yana ɗaga hannu yana kallan mutanen dake a cikin church ɗin. Kun san aka ce idan kare bashi da gaskiya sai ya fara daka haushi dan ya tsira daga harin mutane, to shi ne shi ma Father church yake yi kenan, dik ya bi ya firgice yana wasu muzurai, shi nan bilhakki a kan gaskiyarsa yake!
My people's me kuke tinanin zai faru a cikin wannan Church ɗin? Uhm akwai kallo fa. Musulmi ku ce Allahu Akbar!
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘