Showing 129001 words to 132000 words out of 403653 words
kira, hakan yasa Sharifat ta dawo da kallanta a kan Leesharh, cikin sauri kamar maras gaskiya ta kawar da kallanta tana ɗan kame kame.
"Leesharh wayarki na kara kuma private number ne". Cewar Sharifat.
Wani irin dum dum Leesharh ta ji kirjinta ya buga, domin kuwa ko bata ɗaga ba tasan masu nikaf ne. Jiki ba kwari ta juyo ga Sharifat. Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta nufo Sharifat. Wayar Sharifat ta ɗauko ta miƙa mata.
Tana karɓa wayar ya katse. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har sai da Sharifat ta ɗan yi mamaki. Kunna data Leesharh ta yi haɗe da shiga cikin Whatsapp ɗinta.
Sakon Yah Bilal kawai ta gani a ciki har wajen massages guda biyar. Sake satar kallan Sharifat ta yi, sai taga baiwar Allah ta mayar da hankalinta a kan hiran da suke yi da guyson.
Buɗe sakon ta yi cikin sauri kamar wadda take kan gangara.
"Leesharh zaki bimu ne?". Sharifat ta katseta da jefa mata wannan tambaya. A hanzarce ta fita daga kan mgs ɗin Bilal ta kashe wutar screen ɗin wayar, sannan ta jingina bayanta da jinin stool.
"Ba lallai ba, amma Sharifat in tamnayeki dan Allah". Cewar Leesharh ɗin. Da kallo ɗaya zaka yi wa idanunta kaga tsantsar rashin gaskiya da razana a cikinsu.
Dakatar da abin da take yi Sharifat ta yi, sannan ta bata hankalinta dikka.
"Sharifat dan Allah karin haske da karin ilimi zaki yi mun kin ji". Cikin raunin murya ta yi maganar.
"Okey ba damuwa ina jinki". Ta yi maganar tare da ɗaura wayarta a saman pillow dake kusa da ita.
"Labari zan baki sai ki yanke mun hukunci bisa ilimin addini kin ji?".......... Jinjina kai Sharifat ta yi haɗe da cewa. "To ina sauraronki.
"Misali yanzu Shafiat wasu mata da miji masu halin kirki da dattaku ne suka tsinci wata yarinya, tun tana jaririya cikin tsummarta suka tsinceta, suna riketa tamkar ƴar cikinsu na tsawon shekaru biyar, matar nan ta yi mata komai na rayuwa, haka shi ma mijin matar, ya ɗauketa tamkar ƴar cikinsa, ya nuna mata kauna fiye da tinaninki, duniya dik ta ɗaukar ƴarsu ce, harta danginsu suna ganin matsayin yarsu, Allah bai taɓa basu haihuwa na shiyasa suka cewa kowa ƴarsu, kuma basa kusa da danginsu suna wata ƙasa ne, hakan yasa kowa ya yarda da ita ƴarsu ce".
Kara nitsuwa Sharifat ta yi dan jin wannan labari, kun san ta da san karance karancen labarai.
"Lokacin da yarinyar ta kai shekaru biyar a duniya sai Allah ya karɓi ran wannan mata tasa, hakan yasa ƴan uwansu suka ki tausayin wannan yarinya a in da suka ce to ya auri kanwar wannan mata dan ya cigaba da rike ƴar ƴaruwanta kenan, haka kuwa aka yi, wannan tsintacciyar yarinyar ta sake samu uwa a karo na biyu, to wannan uwar ce ta riketa har yarinyar ta kai shekaru goma sha huɗu".
Sai jinjina kai Sharifat take yi labari ya fara sugar, har da cewa Leesharh ta rinƙa rinƙa yin labarin da wuri please, dan so take ta ji komai da wuri.
Cigaba ta yi da cewa. "To dama wannan uwa ta biyu da yarinyar ta samu macece mai masifar san kuɗi, dan haka bata zama, tana zuwa gidan larabawa ta yi masu aikatau, suna bayanta kuɗi sosai, shi kuma wannan mijin yana sana'ar gasa nama ne a ƙasar da suka je in da nace maki dama sun yi nisa da danginsu ɗin. Ana nan watarana wannan mata ya ce zata fara tafiya da yarinyar nan gidan aikinta dan ta rinƙa tayata aiki, mijin yaki yarda ya ce yarsa karatu take yi, matar ta tsayar da bala'i a kan lallai dole wannan yarinya ta bat karatu ta rinƙa binta wajen aiki, dan yanzu kuɗi shi ne mutum, babu abin da karatu yake tsinanawa mutum, in short wannan mata ta fi karfin mijin ta yadda tasa dole ya yarda yar nan karatunta ya salwanta ta fara bin mamanta neman kuɗi aikatau gidan larabawa".
"Rayuwarsu ya cigaba da tafiya a haka, suna shan wahala a gidan larabawa, amma haka suke daurewa, sai watarana tsautsayi yasa mahaifiyar yarinyar nan ta zubawa wata yar larabawa ruwan zafi a jiki by mistake, nan take uwar yarinyar ta fara dukan mahaifiyar yarinyar, kuma a gaban yarinyar, sai hakuri yarinyar take bata amma taki yarda, dukanta take yi da dik abin da ta samu, kuma wlh yarinyar ba wani konewa sosai ta yi ba, amma haka ta rinƙa dukan uwar yarinyar, a garin ɗaukar abin duka har ta ɗauki wuƙa ta cakawa mamar yarinyar a ciki".
Dai'dai lokacin da ta zo wannan point ɗin sai da idanunta suka ciko da kwallah, ita kuma Sharifat wani irin zabura ta yi tare da zaro idanu, wannan wace iriyar labarice.
Leesharh bata bata damar yin wani magana ba ta ɗaura da cewa. "Sosai wannan balarabiya ta razana ganin ta cakawa matar wuƙa ta kuma faɗi ƙasa, hankalinta ya tashi, ta rikice ta rasa ya zata yi, yarinyar matar kuma da ta ga komai yadda ya faru, ita ma tashiga tashin hankali, hakan yasa ta juya zata gudu ta bar gidan ta je ta kira mutane, haka babu tausayi babu imani wannan balarabiya ta kamata, ta damka mata wukar da ta yi kisan a hannunta, sannan ta danneta ta saka mata wuta a baki ta yadda yarinyar ba zata iya sake yin magana ba bare har ta faɗi ga abin da ya faru, in takaice maki labari dai laifin kisa ya koma kan wannan yarinya a matsayin ita ya kashe mahaifiyarta".
Idanun Sharifat ne suka ciko da kwallah, saboda labarin ya taɓa mata zuciya. Ita kanta mai bada labarin hawaye take yi.
"A takaice haka aka kai wannan yarinya prison, an yanke mata hukuncin kisa amma sai ta yi zaman prison ta jira lokacin da zata cika shekaru 18 kafin a kasheta. Ana haka sai wasu mutane suka zo suka fitar da ita daga wanna gida na prison da sunan zata yi masu wani aiki, yarinyar taki karɓar aikin saboda tana tsoron me zai je ya dawo, sai suka ce mata ai taimako zata yi, wani za'a kashe zata taimaka mashi, hakan yasa wannan yarinya ta yarda, ta karɓi sannan aiki".
Ƙara matsowa bakin bed Sharifat ta yi tana sharar kwallah, dik da bata san labarin na gaske ne ko kirkirowa Leesharh ta yi ba abin ya yi mugun bata tausayi.
"In takaice maki labari dai sai wannan yarinya ta zo ta fara wannan aiki, kwatsam sai ta fahimci amfani da ita ake yi a cutar da mutane bayin Allah, shi ne sai ta yi ƙoƙarin bijirewa waɗan da suka sakata a aiki, ba zato ba tsammani suka yi mata barazana da sun kama babanta da yake sana'ar gasa namarsa a bakin kasuwa, suka ce dole ta yi wannan aiki idan bata yi ba kuma zasu kashe babanta, ni yanzu abin da nike so ki faɗa mun a nan shi ne meyakamata wannan yarinya ta yi? Kada ki manta babanta da ya yi mata komai a rayuwa, ya inganta rayuwarta ya zama gatanta shi ne za'a kashe idan bata yi wannan aiki ba, sannan kuma aikin da zata yi cutar da mutane zata yi, kai in taƙaice maki kashe mutum ma za'ayi amfani da ita ayi, me kike tinanin yakamata ta yi?". Ta kai karshen maganar wani irin kuka mai tsuma zuciya yana ƙoƙarin kubce mata.
Babbar magana, dik wanda ya fahimci wannan labari da Leesharh ta bayar a kan take magana ya sarawa yarinyar nan, lallai ba shakka an cuci Leesharh sosai, ta sha wahalar rayuwa, ashe ba da hakkinta aka kaita gidan AAJ ba ma, innalilahi wa inna ilahir rajiun, kenan ba iyayenta na gaskiya bane ma take san taimakawa, to wacece ita kenan? Ina iyayenta na gaskiya kuma suke? Meyasa aka jefar da ita har waɗan nan suka tsinceta? Wani irin shawara kuke tinani Sharifat zata bata? Wani irin makoma kuke yi mata tinani? Shin zata cigaba da yi wa masu nikaf aiki ko akasin hakan? Tayaya zata kuɓuta daga sharrinsu? Kenan iyayenta cirani suka jo yi a Dubai wannan iftilai ya afka mata? Lallai yakamata mu san labarin Leesharh dallah dallah da kuma in da aka tsinceta! Akwai cakwakiya babba kuwa. Amma ba shakka anyi wasa da rayuwar baiwar Allahn nan.
Haka kawai Sharifat ta tsinci kanta da jin cewa wannan labari da Leesharh ta bayar gaske ne kuma kamar dai labarin yana da alaƙa da ita Leesharh ɗin duba da yadda take kuka kamar ranta zai fita..... Ba dole ta yi kuka ba, an kashe mahaifiyarta a gabanta, sannan an ɗaura mata laifi, bugu da kari ana sanya mata wuta a baki ta yadda ba zata iya magana ba, lallai akwai zalinci matuƙa a wannan lamari, ancutar da ita kwarai. Wai ya aka yi masu nikaf ma suka santa? Shi ma wannan babbar abin tambaya ne. To koma dai me lokaci zai yi mana alkalanci.
Princess Teema taku ta amana bani da lafiya, da kyar na iya yi maku wannan update ɗin dan kada na barku a cikin kewa, ku mun addu'a, idan kun samu typing errors ma amin afuwa, zazzaɓi da ciwon kai ya sa na kasa iya ƙarisa editing ɗin.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
20
Ganin Sharifat tana hawaye kuma tana kallanta yasa ta ɗan yi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta dakatar da kukan nan da take yi, cikin raunin murya da kyar ta iya cewa. "Labarin ya taɓa mun zuciya sosai Sharifat".
Sharifat zargi zuciyarta ya fara yi, dik san da take yi wa Leesharh hakan bai hana ta fara ƙoƙarin gane gaskiya ba. Leesharh tana da kwakwalwa sosai, so ta fahimci kamar kallan zargi Sharifat take yi mata, gudun kada asirinta ya tunu sai ta yi saurin shanyewa, sannan ta kwarara zuciyarta.
"A school fa wata class mate ɗita ta bani wannan labarin, ta ce in taimaka mata da shawara, hakan yasa kema na baki dan ki kawo naki shawarar".
Ajiyar zuciya Sharifat ta sauke, dan kuwa hankalinta ya ɗan kwanta jin abin da Leesharh ta ce, da a tinaninta a kanta abin yake faruwa, amma tin da ta ce labari aka bata sai ita ma ta ɗauko handkichief dan goge hawayenta.
"Yanzu wani shawara zaki bada ke ma?". Leesharh ta sake jefa mata tambayar cike da matsuwa na san jin amsar da zata bata, a ƙagare take.
Goge hawayenta tas Sharifat ta yi, sannan ta gyara zama, cikin sanyin murya ta ce. "Kuskure ne dan wasu sun cutar da kai kai ma ka ce zaka cutar da wasu!".
Ɗan zaro mata idanu Leesharh ta yi. Ganin hakan yasa ta ce.
"Bari na baki missali yadda zaki fi fahimta, waɗan da suka rike mata baba ta sani in suka cutar da shi to tabbas Allah ne zai yi mashi sakayya tin da babu abin da ya yi masu, haka zalika ita ma idan ta ce hujjanta shi ne babanta ta cutar da waɗan da basu ji ba basu gani ba to fa ta sani suma Allah zai yi masu sakayya, bata da ƴancin cutar wani idan ba shi ya cutar da ita ba, in dai shi ya cutar da ita wannan tana iya rama dai'dai da abin da ya yi mata".
"Misalin cikin suratun Nahl, aya ta 126 Allah ya ce
وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُمْ بِهِۦ ۖ وَلَئِن صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِّلصَّٰبِرِينَ
"Allah ya ce Idan an cutar da ku, yazamana kuna san ramawa, to ku yi ramako daidai da abin da aka azabta ku da shi. Amma idan kun yi hakuri, to haƙiƙa hakuri shi ne mafi alheri ga masu yin ta".
"Wannan aya na nuni da cewa idan wani ya zalunci mutum, yana da damar ramawa daidai da abin da aka yi masa, dai'dai fa kada ya ƙara ko ɗiko, amma idan ya yi hakuri ya bar wa Allah, to Allah zai yi mashi sakayya da abin da bai taɓa zata ba".
"Haka ma a cikin suratul shura, aya ta 40 Allah ya ce
وَجَزَٰٓؤُا۟ سَيِّئَةٍۢ سَيِّئَةٌۭ مِّثْلُهَا فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّٰلِمِينَ"
"Sakamakon mugunta ita ce mugunta irin ta, amma wanda ya yi afuwa kuma ya daidaita komai cikin ruwan sanyi da yafiya, to ladansa yana wajen Allah, lallai Allah ba ya son azzalumai da zalinci"
"Dan haka a shawarata ni dai shi ne ta barsu da Allah, kada ta damu idan sun cutar da babanta, ta sani wanda ya halicci baban nata ya fita sonsa, kuma yana ganin komai, sannan ki sani Allah bai yi alkawarin agazawa azzalumai ba, dik abin da suka yi wa babanta Allah zai yi mashi sakamakon. Cikin suratul Hajj, aya ta 10 inda Allah (SWT) yake cewa
ذَٰلِكَ بِمَا قَدَّمَتْ يَدَاكَ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَيْسَ بِظَلَّٰمٍ لِّلْعَبِيدِ
"Wannan azaba sakamakon abin da hannayenka suka aikata ne, dan Allah ba mai zaluntar bayinsa ba ne, dik wani hukunci da kuka ga ya hau kanku to ku sani tabbas kun aikata ba dai'dai bane aka hukuntaku. Wannan aya na nuni da cewa dik wanda ya aikata zalunci ko wani nau’in cin zarafin mutane, zai fuskanci sakamakon abin da ya aikata, Allah ba mai zalunci ba ne, kuma kowane mutum zai ga sakamakon ayyukansa, ko na alheri ko na sharri".
"Haka zalika a cikin Suratul zumar, aya ta 24 Allah ya ce.
أَفَمَن يَتَّقِى بِوَجْهِهِۦ سُوٓءَ ٱلْعَذَابِ يَوْمَ ٱلْقِيَٰمَةِۚ وَقِيلَ لِلظَّٰلِمِينَ ذُوقُوا۟ مَا كُنتُمْ تَكْسِبُونَ
Dik wanda ya kare kansa daga mummunar azaba, wato ya guji aikata ba dai'dai ba, to a ranar ƙiyama zai zama wanda ya tsira! Su kuma azzalumai za'a ce masu za ku ɗanɗana abin da kuka kasance kuna aikatawa. Wannan aya ta kara jaddada cewa azzalumai ba za su tsira ba, kuma Allah zai saka wa kowa daidai da abin da ya aikata".
"Dan haka dik wanda aka zalunta ya barwa Allah, kada ta yarda ta bari Allah ya kamata tana zaluntar waɗan da basu ji ba basu gani ba, ta koma ga Allah ta kai kukanta a kan babanta, ba wai dan Allah bai san halin da take ciki ba, yana sane da komai, amma ta koma garesa ta kai karansu a kan abin da suka yi wa babanta, kada ta yarda ta cuci kowa".
Tin da Sharifat ta fara magana ta ƙasa kunne take sauraranta cikin nitsuwa, kuma tabbas ta gamsu da kalaman Sharifat, tabbas Allah da ya halicci babanta ya fita kaunarsa, dan haka ta bar masu nikaf da Allahn baban nata kawai, shi zai yi mata maganinsu.
Tana tsaka da wannan tinanin ne wani sako ya kara shigowa wayarta. Sai da ta ɗan saci kallan Sharifat ta wutsiyar idanu kafin ta buɗe saƙon. Taga Sharrifat hankalinta ya koma kan wayarta da guyson yake kiranta, ya tura mata saƙo a what'sapp ya jita shiru bata amsa ba, shi ne ya kira ya ji lafiya tana online bata bashi amsa ba.
"Sharifat ina zuwa, zan je gidan wata class mate ɗina". Cewar Leesharh kenan. Dan yanzu saukin da ta samu har ta koma school.
Cikin halin ko in kula ta amsa da. "In zo in rakaki ne?". Da sauri ta girgiza kai tare da cewa. "A'a ba sai na wahalar dake ba, yanzu zan je in dawo, wasu handouts zan karɓa".
Jinjina kai Sharifat ta yi, sannan ta sake cewa. "Waye zai kai ki to?". Kai tsaye ta amsa da. "Yah Bilal ne zai kai yi, dama tin da safe mun yi magana da shi".
Cike da murna Sharifat ta ɗago da kallanta daga kan wayarta izuwa kan Leesharh ɗin, fuska ɗauke da murmushi kamar ba yanzu ta gama sharar kwallah ba, har farinciki ya baibaye zuciyarta baiwar Allah. "Allah yasa idan kun je kafin ku dawo a hanya ku ƙullah soyayya da Yah Bilal, ai bama zan biku ba dan kada na shiga hakkin masoya, Allah ya mallaka maki zuciyar Yah Bilal sai a haɗa aurenmu".
Sharifat da karfin hali take, ita da bata samu nata soyayyar ba take faman nemawa wata, har da wani za'a haɗa aurensu, ko yaushe ta mallaki zuciyar Ramish har zasu yi aute?.
Girgiza kai kawai Leesharh ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, dan ita tasan abu ne wanda ba zai taɓa yiwuwa ba ta samu soyayyar ɗaya daga cikin King Badeen or King Zuhair familys, bata kai ba, amma Sharifat sai wani hakikancewa take yi tana haɗata aure da Bilal karfi da ya ji, ita a suwa wai?.
Mayafin kayan jikinta ta ɗauka tare da matsawa ta mannawa Sharifat sumbata haɗe da yi mata sallama, sosai Sharifat ta zage tana addu'ar Allah yasa kafin su dawo soyayya ta kullu, banda girgiza kai babu abin da Leesharh take yi. Haka ta wuce ta fita abinta.
Ita kuma Sharifat ta cigaba da hira da guyson ba tare da ta kawo wani mummunar tinani a ranta ba.
After some times.
•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
Tuki yake yi a hankali cikin nitsuwa, dare ta yi, a kallah lokacin karfe 10 zata yi, zaune take a kujerar gaban motar hannunta rike da bakar laida mai ɗan girma.
Dik da tana sanye da nikaf hakan ba zai hana mu iya gane cewa Leesharh bace, saboda idanunta da yanayin jikinta, kai komai sak Leesharh ce.
Yana tuki yana waigowa dik bayan second ya kalleta, har sai da ta gaji ta ce. "Yah Bilal kada fa mu je mu samu accident".
Maganar da ta yi ne ma ya kara tabbatar mun da Leesharh ce, dan babu banbanci a voice ɗinsu.
"Ai ke ɗin ce, ba zan iya kawar da kallona daga kanki ba, dole ina juyowa in ganki in ba haka ba sai a