Showing 396001 words to 399000 words out of 403653 words
ta shigo room na Auta, irin dogayen rigunar shan iskan nan ne a jikin Auta ɗin, rigar tana da ɗan siririn hannu, while a dai'dai gwiwarta ta tsaya mata, tana gajin dattijuwar ta yi gaggawar saukowa ƙasa daga saman bed ɗinta ta nufeta da sauri, kwandon mai shake da kayan fruits dake hannunta Autar ta karɓa tana faɗin. "Mama ai da baki wahalar da kanki ba, sai in zo in ɗauka da kai'na". Ta yi maganar tana kallon kayan fruits ɗin kafin ta ɗago da kallanta a kan tsohuwar, yau shi ne kallonta na farko da fuskar dattijuwar.
Wani irin faɗuwar gaba ta ji dan taga wannan kamar ba tsohuwar gaske bace, kada ku manta yaran Momma they're gifted!. Amma sai ta kawar da tinanin nata tare da juyawa ta koma wajen bed ɗinta, a saman bedside drawer ta ɗaura kwandon tana cigaba da kallon dattijuwa ta kasan ido, juyawa ta yi tana tafiya har da ɗan ɗingisawa irin na tsoffi............... Yanzu Fisabilillah my people's ku faɗa mun mutum mai irin zuciyar Auta meyasa zaka so kasheta? Yarinyar da babu ruwanta, bata da girman kai, ga girmama manya, bata duba da talaucinsu ko aiki a karkashinsu da suke yi, da zarar mutum ya girmeta zata bashi girma koma wanene!.
Komawa saman bed ɗinta ta yi ta zauna tare da ɗauko wayarta tana duba sakon mutuminta, dan koba komai a yanzu kalamansa suka sanyata farinciki, tana samun annashuwa. ..............Wai ina mijinta Abdussalam ne? Allah sarki ya dawo Dubai, dan a tinaninsa ta mutu, har ya cire rai da ita, sai dai kuma har yau har gobe sonta yana a cikin zuciyarsa, kullum sai ya yi mata addu'ar samun rahama, ita kuwa tana nan ta mance da wani Abdussalam, dan Smart ya ce mata kada ta damu Abdussalam ya saketa, yanzu ita ba matar kowa bace, so dan haka ta mance da wani Abdussalam ta fara sabuwar rayuwa!. Amma fa dan ta yi farinciki Smart ya faɗa mata haka, ba wai dan Abdussalam ɗin ya saketa ba!!!.
Ɗan siririn murmushin da tsawon watanni bai samu gurbi a face ɗinta bane ya bayyana a fuskarta a lokacin da take karanta saƙon guy ɗin can, hannu ta miƙa ta ɗauki apple a cikin kwadon fruits da dattijuwa ta kawo mata, wato tana shan fruits tana karanta saƙonsa abin zai fi sugar. Bakinta kai tsaye ta kai apple ɗin zata gatsa kenan unexpected taga harbi da kifiya an harbi apple ɗin hannun nata ya faɗi ƙasa tare da kifiyar. Zabura ta yi ta miƙe tsaye tare da gefar da wayar hannunta dan ta tsorata sosai.
Cikin natsuwa ya tako izuwa cikin ɗakin, sanye yake da security uniform, wlh kayan sun yi bala'in yi mashi kyau matuƙa, tamkar dam shi aka yi, uniform ɗin su Smart ne, ƙasa ya yi da kansa cikin girmamawa ya ce. "Kiyi hakuri ranki ya daɗe, ban yarda da inganci apple ɗin bane shiyasa na dakatar dake daga sha, sannan a doka sai na bincike abinci kafin ki ci, ban bincike bane shiyasa na hanaki ci!". Da kyar ya iya kai karshen maganar saboda yadda words ɗinsa suke sarkewa, da alama hakan yana da nasaba da yanayin shigarta, ɗaya ne daga cikin jami'an dake kula da lafiyarta, mai kawo masu abinci ne!. Ya kai karshen maganar tare da mayar da kwari da bakarsa ya maƙala a bayansa kamar wani warriors!.
A wani irin slow ta ɗago idanunta ta sauke a kansu. Murya tamkar a mafarki ta ce. "Ina ainahin mai kawo mana abinci?". Nisawa ya yi, har yanzu kaifin ƙwaƙwalwarta yana nan bai ragu ba, dik da ciwon da ta sha, tsawon wata uku tana jinya, amma babu abin da ya sauya!.
Ta yi mashi tambayar ne dan tana son ya sake yin magana ta tabbatar da abin da take zargi!. "Baya nan, an canzasa da ni ne, daga yau nine zan rinƙa kawo maku abinci". Cikin wannan sanyin murya tasa dai ya yi maganar!. Kurawa fuskarsa idanu sosai ta yi, yana sanye da mask a face ɗinsa, iya idanu kawai zaka gani a waje. Ya ɗauki tsawon wata ukun nan a tare da su, amma yana tare ne da securitys da suke bakin gate, baya daga ta ciki, shiyasa bata san shi ba, yau ne ganinta na farko da shi da Smart ya canza shi ya ce ya dawo ciki ya zama mai kula da ita sosai!.
"Ban taɓa tinanin zaka yi mun wasa da hankali ka yi tinanin ba zan iya ganeka ba! Dik duniya My hero ne kawai zai iya irin wannan harbin da ka yi, saboda shi ɗin bahago ne, da hagu yake harbi, da hagu yake faɗa, da hagu yake komai, kuma nasan da cewa tabbas kai ne shi, dan kana shigowa nan zuciyata ta amsa, ta bada bugun da tsawon wata uku bata buga haka ba, a kansa kawai zuciyata take yin irin wannan bugu". Ta kai karshen maganar idanunta sun cicciko da kwallah sosai.
"Ranki ya daɗe ban gane a kan me kike magana ba!". Ya faɗa can ƙasa, cikin wannan sanyin murya tasa dai. Zafafan hawaye ne suka fara bin kuncinta, rasa me zata ce mashi ta yi yasa ta durkushe gwiwowinta a saman mattress ɗin tare da rushewa da wani irin kuka mai tsananin taɓa zuciya, kukan da ta ɗauki sama da wata uku yana cinta a zuciya ta kasa samun damar yin sa sai yau.
Har cikin ransa ya ji tsananin zafin kukan nata, amma sai dai Smart bai bashi damar ya kusanceta ba, bashi da ikon rarrashinta a yanzu, dole ya daure ya juya zai fita cikin zafa sabo kukan nata yana taɓa shi, idanunsa a kanta sosai.
HOORAIN!! Ba shakka shi ne, Auta bata yi karya ba, kuma zuciyarta bai buga a karya ba, soyayyarta a garesa gaskiyace, dole idan ya kusantota ta ji hakan a ranta. QUEEN OF SURPRISE na ce ku karɓi wannan yau kuma!!.
Tabbas Hoorain yana a tare da ita a cikin wannan gida, kuma Smart ya ɗaukesa daga kingdom of power tun lokacin da Dr ya ce zuciyarsa ta dai'na harbawa, ya umarci su Ansar da su yi shiru kada su faɗawa kowa. To bama shi ne surprise ɗin da QUEEN OF SURPRISE na zo baku ba, babban surprise ɗin shi ne kun san da cewa Zunaira matar Hoorain ce? A rana ɗaya aka ɗaura auren Smart and Pretty, Zunaira and Hoorain, da sa bakin Abbonsa kuma, shi ya yi mashi waliyi, kamar yadda uncle Muhammad ya zama waliyin Auta. Idan baku manta ba Smart ya ce mata ya yi mata alkawarin zata mallaki Hoorain, a lokacin da King ya ce mashi ya kawo mashi Zunaira, suka ɓoye batun aurar da ita zasu yi, basu san dik abin da suke yi a gidan Smart yana sane ba, tuni yasan aurenta za'ayi, wannan dalilin yasa ya ɗaura mata aure da Hoorain tin kafin su dawo kingdom of power, ita kanta bata san da wannan aure ba, shi kansa Hoorain ɗin bai sani ba, iya Abbonsa ne kawai ya sani.
Shiyasa kuka ga da ana ta batun bikinta da Abdussalam ya yi banza da su , dan yasan me ya aikata, ya so sanar da su cewa Auta matar aure ce a ranar da za'a ɗaura aure, amma lura da ya yi da irin tsanar da King ya gwadawa haɗin Auta da Hoorain yasa ya dakata da sanar da su ya shiga wani bincike, dan haka a kan auren Hoorain aka ɗaura na Abdussalam, yanzu Hoorain ne mai mata ba Abdussalam ba, abubuwa sun yi wa Smart yawa sosai ne a lokacin da Hoorain ya mutu a idon duniya shiyasa ya ja gefe yana kallonsu yana wani aikin na daban, a nan ne ya fara binciko tarihin maman Hoorain da King, wannan dalilin yasa ya dakata da barin Hoorain da Auta su yi zaman aure, sai ya bar Hoorain a Paris ya bar Auta a kingdom of power.
Time da ta ji labarin Hoorain ya mutu ta suma ya dawo da ita Dubai, da ya sanar da Hoorain hankalinsa ya tashi sosai, har kuka ya yi mashi a kan ya barshi ya zo ya ganta, wannan dalilin yasa ya sanya shi ya yi shiga irin na jami'ansu dan ya biyosu su zo wajenta ya ganta, da ya zo kuma ya rinƙa haɗa Smart da Allah a kan ya barshi ya kasance a gidan, ya yi mashi alkawarin ba zai taɓa bari ta ganesa ba, sanin irin karfin son da yake yi mashi yasa Smart ya ce Hoorain ya kasance da securitys dake bakin gate kada ya zo ciki, dan kada a samu matsala, a hana Hoorain yana samun damar ganinta daga nesa, sau da dama tana tsayawa a jikin window tana kallan harabar gidan, ta nan yake ganinta.
Yau kawai da safe Smart ya ce Hoorain ya koma mai kula da ita a cikin gida, wancan jam'i dake kula da ita kuma y koma bakin gate, har yanzu da nike yi maku magana Hoorain bai san Auta matarsa bace, kamar yadda ita ma bata san shi ne ainahin mijinta ba, sannan bayan Smart, commander, uncle Muhammad babu wanda ya san da wannan magana.
Abin da Smart yake gudu shi yake son faruwa ga shi da kallo guda Auta ta gane heronta, wai a hakan ma ya ja mashi kunne a kan kada ya yi wani motsin da zai sa ta gane shi, kada kuma ya yi mata magana, sannan idan ta kama dole ya yi magana to ya canza murya yadda ba zata gane ba....... Smart yana so ne ya gama bincike, ya tabbatar da Hoorain ɗan waye ne a tsakanin King and commander kafin ya basu damar sanin sun mallaki juna, shiyasa yake yi masu iyaka a yanzu. KAI JAMA'A KU TAFAWA SMART, YA CIKAWA AUTA ALKAWARINTA YA TSAYA MASU SUN MALLAKI JUNA, SAI DAI KWAI CAKWAKIYA MAI GIRMA A GABA, YANZU HOORAIN DAN WAYE NE? SHI NE BABBAN TASHIN HANKALIN, KADA AZO YAZAMANA YAYANTA! DOLE SMART YA NESANTASU DA SANIN CEWA MA'AURATA NE SU, SANNAN KUMA YA SU KING ZASU JI, BA SHAKKA SMART YA CIKA ƊAN HALAK.
(Wai an ce maku a banza na bar Hoorain ya shanyewa Auta baki ne?🥱 To matarsa ce halacɗinsa, a book ɗina ai ba'a taɓara kun gane ai? Sai idan akasi aka samu misali kamar Leesharh da Ramish wanda su kunga kaddara ce ta afka masu, amma haka kawai a book ɗina ba'a lalata gaskiya, ina ƙoƙarin tsayawa tsayin daka wajen ganin na tsabtace rubutuna, yauwa idan da aurene a sha shagali!.)
A gaggauce ya fice daga ɗakin. Tana ɗago kai taga baya nan ta yi saurin dirowa kasan bed ɗin, a lokacin har anfara kiraye kirayen sallar isha'i, waje ta nufo da gudu dan ta bi bayansa, saboda wlh tasan shi ne, heronta ne. Shi kuwa yasan zata biyosu dama, sai ya ɓuya mata a in da ba zata gansa ba, dan kada ta ganesa ya karya alkawarin da ya ɗaukawa Smart yaja Smart ɗin ya mayar da shi Paris ya sake nesantasu, gara mashi a nan koba komai yana samun damar ganinta bawan Allah, shi ma fa ya sha jinya, almost 1 month yana fama, sai dai Smart ya ce mashi ya yi hakuri Zunaira bata yi aure ba, an warware auren, dan haka ya kwantar da hankalinsa, sai a sannan ne ya samu natsuwa!!. QUEEN OF SURPRISE ina miƙo gaisuwar gareku my people's.....….. 🙌💘🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
63
Waje ta nufa da gudu domin ta duba shi, tamkar wadda bata a cikin hayyacinta, dik ta firgice tana wani irin kuka mai tsuma rai, dama a kusa zuciyar take, kiris take nema!.
Daga in da yake laɓe ya ji ba zai iya barinta ta fita waje da irin wannan shiga dake jikinta ta nufi securitys ɗin nan ba, kun san shi da shegen kishi, ina ai ba zai iya daurewa ba. Kasa cigaba da ɓuya ya yi, tana dab da buɗe kofar parlour ta fita ya yi gaggawar nufarta. Ta baya ya sanya hannu ya toshe mata baki game da rufe mata idanun da ɗayan hannun nasa. Baya ya yi da ita kai tsaye sai bedroom ɗinta. Ciki ya mayar da ita, bai saketa ba har suka kai wajen bed, yana zuwa ya zaunar da ita tare da zame hannunsa, sannan cikin sanyin muryan nan yasa dai ya ce. "Kada ki sake fita ko parlour ne!". Ya kai karshen maganar tare da juyawa zai fita.
Cikin zafa ta miƙe tsaye, hawaye tamkar an buɗe tap an kure mashi gudu, da kyar voice ɗinta yake fita ta ce. "In dai baka son in fita waje to ka bayyana mun kanka matsayinka na herona, in kuma ba haka ba ka cigaba da ɓuya to tabbas ba iya waje ba, gidan dikka zan bari koma duniyar bakiɗaya, dan ban ga amfani zamana a raye bama, ace kana numfashi kuma muna waje ɗaya sannan kana guduna! For what reason?" Ta jefa mashi tambayar a yayin da zuciyarta tamkar zai yi bindiga saboda tsananin tashin hankali da damuwar abin.
Dik abin da suke yi Smart yana kallansu, dan idan baku manta ba ya zuba secret cameras sosai a gidan ta in da babu wanda zai san da su, so dik abin da yake faruwa yana gani. A lokacin ya kammala zubawa Pretty iskancinsa son ransa, ya kwanta yana jinta tana kuka ƙasa ƙasa, ya ce idan ya ji bakinta tana kuka sai ya sanya wuta ya konasa, shi ne yasa take kuka ƙasa ƙasa dan kada ya ji!.
Banza da ita Hoorain ya yi ya cigaba da tafiyarsa, zuciyarsa tamkar zata yi bindiga shi ma.
"My Hero". Ta ambata cikin wani irin murya mai matuƙar raunin da komai taurin zuciyarka sai ka ji ta ratsaka, shi kansa Smart wani irin tausayinta ne ya kama shi sosai, hakan yasa ya fita daga side na camerar tasu ya shiga massage na wayarsa, dama da phone ɗinsa ya yi connected na cameras ɗin.
Cak ya dakata da tafiyar da yake yi jin sunansa da ta kira. Saukowa kasan bed ɗin ta yi, ta tsaya a wajen, cikin rawar murya ta ce. "Dama akwai ranar da zata zo kana raye ina kuka ka nuna baka san ina yi ba? Dama dik alkawarin da ka mun ba gaske bane? Dama wasa kawai kake yi mun? In kuwa haka ne meyasa ka bari na kamu da sanka har haka? Meyasa ka cutar da zuciyar da bata san komai ba face kaunarka? Meyasa a dik duniya ni kaɗai ka zaɓi ka cutar? Menayi maka my Hero? Wannan shi ne sakamakon son da na nuna maka kenan? Abin da zaka saka mun da shi..............". Kasa ƙarisa maganar ta yi saboda wani irin kululun bakinciki da ya toshe maƙoshinta, cikin wani irin tari mai sauti ta fara ƙoƙarin cigaba da maganarta, sai dai ina, ta gagara yin hakan, sam sam voice ɗinta yaki fita, hannu tasa ta dafe saitin wuyarta tana cigaba da tari mai sauti wanda sai da ta sanya shi juyowa babu shiri.
A dai'dai wannan lokacin wayarsa ta yi kasa alamar shigowar sako. Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro wayar, ganin message na Smart da ya yi saving numbersa da babban yaya ne yasa ya yi gaggawar buɗe sakon.
"Ka rarrasheta kawai tin da ta rigada ta ganeka, but kada ka yi crossing line dana ja maka!". Smart ba zai iya jure ganin ta a irin wannan hali ba, shiyasa ya ce ya rarrasheta kawai!.
Shi ne abin da saƙon ya ƙuntsa, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, dama ko Smart bai yi mashi massage ba, ba zai taɓa tafiya ya kyaleta a wannan hali da take a ciki ba, dama dole zai tsaya ya rarrasheta, dan zuciyarsa ba zata iya jura ba, yanzu ma da kyar ya danne. Tin da yake a rayuwarsa bai taɓa danne wani abu mai tsananin azaba ba irin wannan tashin hankali da ta shiga! Idanunsa sun kaɗa sun yi jajir kamar wuta!.
Cikin natsuwa ya taka ya nufi in da take, mayar da wayarsa a cikin aljihunsa ya yi, a gabanta ya tsaya tare da yin ƙasa da kai, cikin natsuwa ya ce. "Am so so sorry Hoonaira, ba zan sake kwantanta makamancin hakan a gareki ba, dan Allah stop all this, please kin ji?". Ya kai karshen maganar tare da sanya hannunsa ya riko nata dake wuyarta tana tari. Kara jaddada mata da tuba yake yi ya yi. Ina ai babu bakin magana, ta rigada ta kure maganarta, yanzu idan ta buɗe baki zata iya haɗiyar zuciya!.
Ganin hakan yasa ya saki hannun nata tare da nufer dispenser ya ɗebo mata ruwa mai sanyi sosai a cikin cup, sannan ya dawo in da take a tsaye. Miƙe mata ruwan ya yi a kan ta sha, sam baya son taɓa jikinta saboda yasan ba matarsa bace, shiyasa yake yin ɗan nesa nesa da ita. Karɓar ruwan ta kawo hannunta zata yi, sai dai ina, kakkarwa sosai hannunta yake yi wanda yasan ba zata iya rike cup ɗin ba, hakan yasa ya matsa dap da ita tare da sanya mata cup ɗin a baki a kan ta sha!.
A hankali ta fara karɓar ruwan tana sauke wani irin ajiyar zuciya mai ɗauke da sirrika dayawan da take buƙatar lokacinsa domin buɗe mashi waɗan nan sirrika. Lokacin guda Smart ya ji soyayyarsu ya yi matuƙar birgesa, take ya ji gabaɗaya jikinsa ta motsa, har ɗan lumshe idanunsa ya yi irin abin ta shigesa yadda yakamata ɗin nan.
Tana gama shan ruwan ta faɗo saman massive chest ɗinsa tare da rushe mashi