Showing 84001 words to 87000 words out of 403653 words
shi ma, saboda bai taɓa ganin Daula haka ba.
Mahreen ta ƙanƙame Mahnoor sai kuka take yi, momma ta yi ta yi tayi shiru amma taki, ita dai a mayar da ita wajen bappanta kada a kasheta, so su da yake basa jin fillanci sai basu san me take faɗe ba, guyson dai ya wuce part ɗin mummyn Chuchu abinsa, ya ce sai su Mahreen sun yi wanka zai dawo wajen mommarsa, sai ɓata rai yake yi momma ta kawo masu ƴan datti, bai ma san cewa Mahnoor matar Jaish bace.
Suna sako kafarsu a parlourn momma Jaish dake zaune saman sofa shi da Jawad da aka sallamesu daga asibiti ɗasun ya miƙe tsaye da nufin zai bar part ɗin, dama tun ɗazun suke zaman jiran momma a wajen, so yaga kamar ba zata iso da wuri bane yasa ya miƙe da nufin ya je part ɗinsa ya kwanta.
Ai Mahreen tana ganinsa ta dagata da yin haukar da take yi masu, tuni ta manta da in da take, ai a miliyan ta watsa a guje ta je ta faɗa a jikinsa.
Mahnoor ma wani irin ajiyar zuciya mai karfi ta sauke, ta kasa kawar da idanunta daga kansa, ya canza sosai cikin kwanaki bakwai, ya koma sak yadda yake da, hasken fatarsa ta dawo yadda take, ga gashin kansa da ya tara a kauye yanzu ta sha gyara, ba ƙaramin kyau ya kara ba, yana sanye da sleeping dress launin up white, shi ma Jawad kayan barci launin up white ce a jikinsa, dama su fa kayansu iri ɗaya suke sakawa, komai nasu kusan ɗaya kamar tagwaye.
Cikin zafa Jaish ya finciketa daga jikinsa, da karfi ya wurgata gefe guda, ransa ta yi mummunar ɓaci, kallan ƙazamiya ƙasƙantacciya ya yi mata, bai santa ba ta zo ta wani rungumesa.
Ƙoƙarin dalla mata mari ma ya yi cikin fushi, da sauri Jawad ya riƙesa yana faɗin......... "Haba mutumin meyayi zafi haka?".
Momma dai turus ta tsaya tana kallonsu, sam bata yi mamakin hakan ba, dan tasan dikka ƴaƴanta sam basa san datti, basa san kazanta, dole Jaish ya gansu a matsayin datti, saboda kayan jikinsu dik a koɗe sosai suke, gara ma ita Mahnoor doguwar rigar bikinta ta saka, shi yana da ɗan kyan gani.
Da gudu Mahnoor ta kwace hannunta daga rikon da momma ta yi mata, ta kariso cikin parlourn ta rungumi Mahreen dake ihu ta ji azabar wurgar da ita da Jaish ya yi, ta bugu sosai.
Kwace rikon da Jawad ya yi mashi ya yi, da sauri ya nufi hanyar fita waje dan ya je ya cire kayan jikinsa dan ta taɓa, in baku manta ba mugun kyama Jaish yake da shi, kun tuna farkon zuwansa garinsu yadda ya rinƙa kwarara amai saboda bappa ya taɓa shi? To yanzu ma hakance.
Akwai tashin hankali, my people's kuna tinanin Jaish zai yarda da Mahnoor a matsayin mata kuwa? Akwai fa matsala. Amma my people's nace ba, who noticed that Jaish and Jawad shekarunsu ɗaya kuma shekarun mstansu ma ɗaya?........ 🤔 A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA.............. MUJE ZUWA AKWAI ABUBUWA A GABA MASU BAN MAMAKI, KUN SAN INA SAN IN YI TA SURPRISING ƊINKU AI.
•••••••••••••••••FOREST••••••••••••••••🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
•••••••••••••••••FOREST••••••••••••••••🔥
••••••••••••••••AFTER SOME TIMES🔥
Zaune Pretty take a kasan wani bishiyar zaitin mai bala'in tsayin gaske. Tana zaune suna fuskantar juna ita da Zunaira, ta yi shiru tamkar mai tinanin wani abin, ga dikkan alamu akwai damuwa a tattare da Zunaira sosai, sai dai ita Pretty a yau babu alamar damuwa a tattare da ita.
Meya haɗa Zunaira da ta mutu kuma da Pretty? Muje zuwa. Kada ku manta alkalamina ɗan alkawari ne, dan haka ya yi maku alkawarin samun surprise dayawa a cikin labarin nan, so yanzu haka mun fara buɗe babin surprise ne, Princess Teema taku ta amana Queen of surprises. Muje zuwa dan jin me ya haɗa Auta da Pretty kuma? Ina Team Zunaira? Princess Teema tana tayaku murna Zunaira is alive.
Auta tana sanye da kayan Pretty a jikinta, ta yi rama sosai, ta sha jinya ta sha bakar wahala baiwar Allah, har ta fita a hanyacinta, idan kuka ganta yanzu ba zaku taɓa yin zatan ita bace, saboda wahala da ta sha, har duhu sai da hasken fatarta ya yi, idanun nan nata sun kara girma saboda rama.
Fuskarta ya ƙanƙance, ita ma yanzu ta zama irin Pretty babu ɗaura ɗan'kwali sai dai su saki gashi har baya, coz ita Zunaira gashin nata ma in ka gani sai ka san ta ci uwar wahala, dik ya cukurkuɗe kamar ba ita ba.
Wasu irin fresh fruits ne a gabansu cikin kwanto irin wanda Mammar kamran take amfani da su, wato kwanton da ake zuba timatir. Ba cin fruits ɗin suke yi ba, Auta tana tinanin gida da su Chuchu yanzu tsawon lokaci bata a tare da su, ita kuma Pretty Allah ne kaɗai yasan me a cikin zuciyarta, dan bata bada daman ya fito fili a san halin da take ciki ba.
Har yanzu akwai ɗan sauran magani manne a cikin Zunaira in da Hoorain ya caka mata wuƙa, wajen ya warke alhamdulillah, dan har tana iya tafiya da kafafunta.
"Alhamdulillah my Queen ta samu lafiya".......... Daga bayansu suka ji wannan murya wanda ko basu juyo ba sun san shi ne, dan shi kaɗai ne garesu a cikin wannan forest ɗin.
Auta ce ta juyo haɗe da kai kallonta a kansa, ita kam Pretty bata juya ba, kamar fushi take yi da shi........... Kamar dai kullum yana nan cikin wannan shiga tasa, ga dikkan alamu su Pretty har yau basu san ya kamannin face ɗinsa take ba.
Ɗan yake Auta ta yi mashi, baiwar Allah ko tana cikin damuwa murmushi baya ɓata daga kan face ɗinta, murmushi sadakace in ji Manzon Allah (S.A.W)
"Na ji sauki Alhdulillah".......... Ta bashi amsa tana ƙoƙarin faɗaɗa murmushinta da dole.
Tsareta da idanu ya yi tamkar zai cinyeta, bai sake yin magana ba, ita ma bata sake yin magana ba, ta dai kawar da kallonta daga kansa, tsoronsa take ji sosai, saboda yanayinsa, amma hakan baya hana ta yi mashi murmushi ta kuma yi mashi magana idan ya zo, saboda shi da Pretty su suka ceci rayuwarta, da yanzu babu ita a doran duniya.
Ba komai yasa take tsoronsa ba kuma face zubin halittarsa, cikakken sadaukin warrior ne sosai da sosai, and wani lokaci yanayi mata yanayi da Hoorain da ba zata taɓa iya mantawa da shi a rayuwarta ba, ta in da kuma yake yi mata yanayi da Hoorain shi ne rashin yarda ya buɗe fuskarsa a garesu, tin da ta fara samu sauki ta fara magana in ya zo tana rokansa da ya buɗe fuska su ga juna, sai ya ce mata sai wani lokaci, yana yawan zama a tare da ita lokacin da take jinya, suna hira dik da ba sosai ba, amma baya yarda idan ta kawo zancen buɗe fuska, wannan dalili ya ɗarsa mata tsoronsa a ranta, tana tsoron waɗan da basa buɗe fuska a yanzu.
Batu na gaskiya wannan ba Hoorain bane, basu ma da haɗi, Hoorain yana Daular Queen Zarina, sai dai shi ma wannan yana da nashi dalilin da yasa baya san buɗe fuakarsa a garesu ne kamar yadda shi ma Hoorain yake da nashi dalilin, amma ba mutum ɗaya bane sam, ita dai Auta tana tsorace da masu rufe face ɗinsu ne kawai wanda dani da ku kuma dik mun san dalilin tsoronta a kansu.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
"Omnish yau ba zaki yi mun magana bane?". ........... Ya yi maganar yana zagowa ta gabansu.
Turɓune fuska ta yi, tana turo baki ta ce. "Yau ba zan yi magana da kai ba". ........ "But why?"....... Ya yi maganar dai'dai lokacin da yake tsugunnawa a gabansu. Hannu ya kai ya ɗauki lemu mai ɓawo guda ɗaya daga cikin kwandon gabansu. Cikin nitsuwa ya fara ɓare lemun yana satar kallon Auta ta wutsiyar ido.
"Ba kai ne kace ba zaka sake wuce kwana ɗaya baka zo garemu ba, amma yau ka kai kwana biyar baka zo ba". Cewar Pretty sarkin mita da raki. Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar. Tana kai karshen kuma ta miƙe da sauri ita a dole ta yi fushi zata tafi ta basu waje. Sak dai yadda take yi wa Kamran idan ya ɓata mata rai ta yi fushi.
Cikin zafa ya yi saurin riko hannunta, Pretty tana bashi ciwon kai da shegen shagwaɓa da saurin kukan nan nata, ga shi bata jin lallashi da wuri............. "Haba my baby, to ki yi hakuri ba zan sake ba, kuma nima ai ba dan san raina nike rabuwa da ku ba, idan da dan san raina ne ba zan rabu da ku ba ai, ina san kasancewa daku sosai, amma bani da damar yin hakan, kiyi hakuri kinji rigimammiya kawai"................. Dik maganganun da yake yi idanunsa a kan Auta da take ta binsu da kallo, ita dai Pretty ta shiga ranta sosai, tana burgeta bare ma idan tana yi wa wannan sadauki shagwaɓa, sosai take jin daɗin kallonsu a tare.
Kuka Pretty ta saka mashi wai dan ya ce mata rigimammiya a karshen maganarsa, shikenan ya sake jijjigo wata rigimar............ Dan dolensa ya gyara zama a kasan wannan bishiya, ya ɗaura Pretty a saman laps ɗinsa ya hau rarrashi.
A saman kirjinsa ta kwantar da kanta tana turo baki ita a dole ranta ya ɓaci........ Cigaba da ɓare lemun hannunsa ya yi yana satar kallon Auta, da yake face ɗinsa a rufe sai iya idanunsa ne kawai a buɗe, idan ka gansa zaka yi zaton lemun yake gani, amma Zunaira yake gani, ita kuma tana ta kallon Pretty da ta gama tafiya da imaninta.
Shiru wajen ya ɗan yi na ƴan sakanni da ya kammala ɓare lamun, sai ya rabata kashi huɗu, Pretty dake zaune saman laps ɗinsa ya ɗauki ɗaya ya sanya mata a baki yana dawo da ainahin kallonsa a kan face ɗinta.
Buɗe bakinma Pretty sai ta ja mashi aji sai kuma ta yi shagwaɓa, amma haka ya jirata ta gama shan kamshinta kafin ta ɗan buɗe mashi bakin nata, shi ma kaɗan ta ɗan buɗe.
Tura mata lemun ya yi yana dawo da kallonsa a kan Auta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, wasu zafafan hawaye suka fara bin ƙuncinta, ba komai ya ja hakan ba face abin da yake yi wa Pretty ya tuna mata da ita da guyson, ta yi kewan ƴan uwanta sosai, ba dan sadauki yana kula da ita yana rarrashinta haɗe da kawar mata da damuwar da take ciki ba wlh da bata san ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi ba, bata taɓa rabuwa da ƴan uwanta ko nan da can ba sai a dalilin Hoorain, wannan abin ba zai taɓa gogewa a ranta ba har abada.
Kanta a ƙasa, bai san hawaye take yi ba, sai ya ɗauki lemu guda ɗaya cikin wanda ya raba, bata yi zato ba sai ganin hannunsa ta yi yana ƙoƙarin cusa mata lemun a bakinta. Da sauri ta ɗago kanta, karap suka haɗa ido, ya ɗan yi mamakin ganinta tana kuka, ita kanta Pretty ta yi mamakin hakan.
Tashi ta yi daga saman laps ɗinta ta koma kusa da Auta, ɗan rungumota ta yi tana faɗin............ "Allah sarki meyasa kike kuka kuma ƴar uwa?".
Shiru bata amsa masu ba, ita kaɗai tasan me take tinani, ita kaɗai tasan raɗaɗin da yake cikin ranta.
"Omnish jeki ki kawo mun maganinta kin ji?"............ A faɗa a sanyaye. Ɗan zaro idanu Pretty ta yi, a ɗan tsorace ta ce. "Ciwonta ne yake yi mata zafi?".
Kai ya gyaɗa mata a alamar e, hawayenta Pretty ta fara share mata, cike da tausayawa ta ce. "Ki yi shiru ki dai'na kuka, In Sha Allah ciwonki zai yi sauki, yanzu zan kawo maki maganinki, amma ki dai'na kuka, bana san ganin kina kuka"......... Oh Pretty sarkin iya tsara zance idan ta yi ra'ayi, in bata yi ba kuma sai ka yi zatan wawuya ce ko kurma.
Jinjina mata kai kawai Auta ta yi ba tare da ta yi magana ba, goge mata hawayen da ƴan hannayenta Pretty ta yi kafin ta miƙe da sauri ta nufi makwancinsu dan ta ɗauko maganin.
Tana tafiya ya matsa kusa da Auta sosai, dama wayo ya yi wa Pretty ta tafi shiyasa ya ce ta je ta ɗauko mashi magani, idan ya matso ya ce zai ɗaura Zunaira a kan cinyarsa ko wani abin makamancin haka kuka Pretty take yi ta ce ai kafarsa nata ne ita kaɗai shiyasa ya yi mata wayau ta tafi.
Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta, shi kansa sai da ya ji wani irin abu ya tsaya mashi a makoshinsa mai wuyar haɗiyewa. Kallanta ya yi ido cikin ido, gabansa ne ya ji ya fada dum dum haka. Ɗayan hannunsa yasa ya fara goge mata sauran guntun hawayen dake face ɗinta, cikin sanyin murya can ƙasa ƙasa ya ce.
"Kin manta cewa kin mun alkawarin ba zaki sake zub da hawayenki a banza ba ne?".
Shiru bata iya amsa mashi ba, sai ma ji da ta yi kamar ta tashi ta gudu a wajen, dan dai yana da girma da kima a idanunta wanda ba zata iya yi mashi abin da zai ɓata mashi rai ba ne yasa ta danne, ba za kuma ta taɓa manta halaccinsa a gareta ba. Ƴar Halak kenan.
Ganin bata yi magana bane yasa ya sake matsawa kusa da ita sosai, a hankali ya ɗan rungumota da nufin ya yi mata rarrashi irin wanda yake yi wa Pretty. Dik da yake sadauki sai da ya ji wani irin shock a jikinsa, kamar wanda aka jonawa lantarki, har sai da ya ɗan saketa jin abin da bai taɓa ji ba. Amma kuma yana san ta yi shiru kuma ta yi mashi magana, dan haka sai ya daure ya sake rungumota a jikinsa, yana jin wani irin bakon yanayi haka ya daure ya fara rarrashinta tare da tuna mata da alkawarin da ta yi mashi a kan ba zata sake yin kuka ba.
Dan dole ta haɗiyi kukan nata, saboda ya iya rarrashi sosai, ko da yake dik wanda zai rarrashi Pretty ta yi shiru lallai ba shakka ya iya rarrashi, dan Pretty sai Allah.
Murya can ƙasa ƙasa haɗe da kuka ta ce.
"Ka yi hakuri ba zan sake ba". Da yake tana kuka sai voice ɗin nata ya yi tamkar a shagwaɓe ta yi maganar, ba ƙaramin ɗarsa wani abin a ransa wannan magana tata ya yi ba.
Ƙasa sake yin magana ya yi, wannan sadauki ya shiga yanayi, abin ku da ba'a saba ba, an saba da datse kan mutane da takoba, ba'a saba shukan fure ba, sai ya zamana kaman wani ɗan fari a gabanta, ya hau aikin binta da ido kawai, daga ta yi mashi shagwaɓa sau ɗaya shikenan ya birkice.
(Anya ba zamu kai sadauki wajen Yah Jawad ya koya mashi karatun shuka flowers ba kuwa my people's?🤔😅🌝)
Jin ya yi shiru bai amsa taba yasa ta yi tinanin ko dai ransa ne ya ɓaci yaki sake kulata, dan haka sai ta kara marairace murya, a wannan karon cikin shagwaɓar gaske ta ce......... "Na yi alkawarin ba zan sake ba, dan Allah kayi hakuri, kaga ma na goge hawayena". Ta kai karshen maganar tana kai hannunta saman fuskarta.
Haba tuni sadaukinmu ya kara shiga yanayi, kamar ba shi ba, sai ya ji kamar an canza shi ne lokaci guda, ya kasa iya yin magana.
Allah sarki ta zaci fushi yake yi, sai ta kai hannunta ta riko nasa hannun, kamar zata saka kuka ta shiga bashi hakuri. Dik sai kara rikita shi take yi, da kyar ya iya samu ya juya hannunta ya koma cikin nasa, a hankali ya furta ta yi shiru dan Allah ta dai'na magana, dan tana kure tinaninsa.
A dai'dai lokacin Pretty ta dawo hannunta ɗauke da sak irin kwaryar da aka basu magani a lokacin da suke jarirai, ganinta yasa ya yi saurin sake Zunaira ya ɗan ja baya kaɗan.
Karɓar maganin ya yi Pretty ta zauna kusa da shi, a gefensu ya ajiye ba tare da ya bawa Auta ba, Pretty bata nemi jin meyasa bai bawa Autan ba, sai ta kwanto jikinsa ta fara aikin zuba mashi shagwaɓa da ta saba.
Haka suka kasance cikin farinciki suna hira yana satar kallon Auta na tsawon lokaci, har sun shagala sun mance da zai tafi sannan ya kawo masu batun lokacin tafiyarsa ya yi. Kuka suka saka mashi su biyun dikka, Allah sarki wlh basa san zama su biyu a cikin wannan kungurmin dajin, amma to ya zasu yi? Dole su hakura dan sadauki dai bai san ƙasarsu Gimbiya Zunaira ba, ita ma bata san ta ina take bama bare tasan in da garinsu yake, ba hanyar komawa.
Hakuri ya rinƙa basu yana rarrashinsu har sai da ya samu suka ɗan nitsu, sannan ya rakasu har sabon bakwancin da ya yi masu ya kuma ƙawata masu shi, bai mayar da Pretty ainahi in da suka taso a tare da mom ɗinsu ba, ya canza mata waje, har yau har gobe kuma yana wahalar neman Sweetie, ba dare ba rana, dayawan lokuta idan ya shigo forest ɗin kafin ya je in da su ke