Showing 183001 words to 186000 words out of 403653 words

Chapter 62 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

124

karanta Alqur'ani mai girma zai kuma yi haddarta.

Ganin ya yi shiru yasa ta ce. "Baka gamsu bane in kawo maka wasu hujojin masu karfin da dole ka gamsu Ronnie?".

Da sauri ya girgiza mata mai alamar a'a ya gamsu, sannan ya ce. "Dan Allah ki bani tarihin Imam Mahadi ko kaɗan ne yau kam, kullum sai na tambayeki amma baki faɗa mun".

Jinjina kanta ta yi, sannan ta fara magana kamar haka.
"Zan baka tarihin Imam Mahadi ko dan saboda yadda jama'a suka ɗaukesa, wasu sun karyata bayyanarsa, wasu kuma sun faɗi yadda zai bayyana ba'a dai'dai ba, sun ruɗar da mutane game da bayyanarsa".

Shiru ya nitsu yana jinta, cigaba ta yi da cewa.

"Imam Mahdi Allah ya yarda da shi, shi ne ɗaya daga cikin manyan alamomin tashin alkiyama. Addinin Musulunci ya yi bayani a kan zuwansa, kuma ya na da mahimmanci a fahimtar al’amuran da za su wakana kafin ranar alkiyama. Menene Ma'anar Mahdi ma farko tukun nan?".

Shiru ta ɗan yi tana kallansa, ganin bai motsa lips ɗinsa da nufin yin magana bane yasa ta ɗaura da cewa.
"Sunan Mahdi yana nufin wanda Allah ya shiryar zuwa gaskiya. Shi mutum ne da Allah zai zaɓa domin ya jagoranci al’umma zuwa ga adalci da gaskiya a lokacin da duniya ta cika da zalunci da barna. Asalinsa daga zuriyar Annabi Muhammad (SAW) yake. Yana daga cikin zuriyar Nana Fatima, ƴar Annabi (SAW) Sunansa da sunan Annabi iri ɗaya ne sak. Sunansa Muhammad shi ma, kuma sunan mahaifinsa Abdullah, kamar dai Annabi Muhammad (SAW). Zai cika duniya da adalci. Zai bayyana ne a lokacin da duniya ta cika da zalunci da fasadi, sannan zai dawo da adalci da gaskiya. Annabi Muhammad (SAW) ya ce Al-Mahdi yana daga cikin zuriyata, daga cikin ƴaƴan Fatima ka duba Sunan Abu Dawud, Hadisi mai lamba 4286 a nan manzan Allah ya yi wannan magana".

"Manzon Allah ya sake cewa za a cika duniya da zalunci da danniya, sannan Allah zai kawo wani daga cikin iyalina wanda zai cika ta da adalci da gaskiya kamar yadda aka cika ta da zalunci da danniya ka duba cikin sunan Abu Dawud, Hadisi mai lamba 4285, Annabi ya ce Imam Madih zai bayyana ne a Makka kusa da Ka’aba, inda mutane za su rantsar da shi a matsayin jagoransu. Aikin da zai yi a zamansa a duniya sun haɗa da.Yaki da zalunci. Zai jagoranci yaƙi da azzalumai da masu rushe gaskiya. Zama jagoran musulmi. Zai haɗa al’ummar musulmi karkashin jagoranci guda. Zai taimaki Annabi Isa (AS) A lokacin zuwansa, Annabi Isa (AS) zai sauka daga sama, sannan su yi aiki tare wajen tabbatar da gaskiya. Ahlus-Sunnah wal-Jama’ah. Sun gaskata da zuwan Imam Mahdi kamar yadda hadisan Annabi suka tabbatar. Suma ƴan Shi'a sun yi imani da Imam Mahdi, suna cewa shi ne Imam na goma sha biyu daga Imaman su, wanda yanzu yana boye kuma zai bayyana a nan gaba a cewarsu. Wannan shi ne takaitaccen tarihin bayyanar Imam Madih".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Wani lokaci Imam Madih zai bayyana?. Shin bayan zuwan su dijjal ne zai bayyana ko dai sai ya zo kafin su dijjal?".

Kai Ronnie yana da san yawan tambaya, dama kuma dik mai ilimi kuma mai san kara faɗaɗa iliminsa dole ne ya rinƙa tambaye tambaye. Allah sarki ita kuwa tun da tana san ya shiryu, bata gajiya da tambayoyinsa. Gyara zama da kyau ta yi, a nitse ta fara bashi amsarsa kamar haka.

"Bayyanar Imam Mahdi, Dajjal, da sauran manyan alamomin tashin alkiyama suna da tsari da Allah ya tsara, kuma akwai bayani a hadisan Annabi (SAW) game da wannan. A mahangar addinin Musulunci, Imam Mahdi zai bayyana ne kafin bayyanar Dajjal, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar musulmi a lokacin wannan fitina mai girma wato fitinat dijjal. Zuwansa ba a lokacin da aka sani ba ne. Annabi Muhammad (SAW) ya ce, lokacin bayyanar Imam Mahdi ba wani abu ne da mutane za su iya hasashe da cikakken tabbaci ba. Amma zai bayyana ne lokacin da musulmi suke cikin matsananciyar bukatar jagora, sun jigata suna cikin kunci da wahala game da azabar azzaluman shugabanni, a lokacin zai bayyana domin ruguje zalincinsu ya zama jagora ga musulmi. Tsakanin bayyanarsa da bayyanar dijjal. A hadisan Annabi (SAW), ya nuna cewa Imam Mahdi zai bayyana ne kafin bayyanar Dajjal, kuma zai yi wa Dajjal tawaye tare da taimakon Annabi Isa (AS) lokacin da Dajjal ya bayyana, Imam Mahdi zai jagoranci musulmi su yi gwagwarmaya da shi. Sai Annabi Isa (AS) ya sauka daga sama, sannan shi ne zai kashe Dajjal a ƙarshe. Hadisin Bukhari da Muslim. An ce Annabi Isa zai sauka a lokacin da Imam Mahdi ya riga ya kasance jagora, sannan su biyu za su haɗa kai wajen yin maganin Dajjal. Annabi Isa zai sauka a kusa da minar Madina mai farin haske (minaratul bayda) a Syria, Bayyanar Dajjal. Fitowarsa ita ce mafi girman fitina ga al’umma, wanda zai zo tare da ƙarya da sihiri mai ƙarfi. Saukar Annabi Isa. Annabi Isa zai zo domin taimakawa Mahdi wajen kawo ƙarshen Dajjal, sannan ya jagoranci sauran al’umma. Zai zo ne bayan Mahdi ya fara gyara duniya. Wannan shi ne ainahin cikakken bayani a kan bayyanar Imam Mahadi".

Ta kai karshen maganar tana kallansa. Shiru ya yi yana jinjina girma irin na Ubangiji, wato Alqur'ani ya tabbata ba abin wasa bane, lallai ne ba shakka dik mai tinani ba zai bijire maganar Allah ba.

Buɗe baki ya yi domin ya yi magana sai gani suka yi anturo kofar ɗakin an shigo. A tare suka kai kallansu a kan kofar shigowa tana zare hannunta daga rikon da ya yi mata. Ɗan zaro idanu Sweetie ta yi tana kallansa, shi kuwa ƙarisowa ciki ya yi ba tare da ya kalli in da suke ba.

Gaban mirrorsa ya karisa ya tsaya, ya gama shirya komai domin cire ƙwaƙwalwarta kamar yadda ya tsara, yau kuma yake sa rai zai yi wannan aiki, shi ne dalilin dawowarsa yanzu kenan.

Silent talk ya yi wajen cewa Ronnie ya fita daga ɗakin ita kuma ta same shi a wannan ɗaki da ya yi treating ɗinta last time. Kallon juna suka yi ita da Ronnie, miƙewa Ronnie ya yi ya sauko kasan bed ɗin, sannan ya nufi kofar fita, yana san tambayar yayan nasa me zai yi mata ko dai bata da lafiya ne? Amma sai ya ji tamkar an ɗaure mashi tongue ɗinsa, ya kasa magana, haka ya nufi fita waje.

Ita kuma dirowa kasan bed ta yi, idanunta a kansa, shi kuma sam sam baya kallanta, ita kyansa na musamman da ya yi ma take kallah, kowani kaya yasa kyau yake yi wa kayan, ita jacket ɗin jikinsa ma take balai'n kauna, rigar ta yi mata kyau, ga shi har gwiwonsa ya kai, kamar long coat haka jacket ɗin yake.

Kafafunsa dake sanye cikin wasu irin armor sandal ta bi da kallo, takalma bakake ne hakan yasa hasken fatarsa ta kara fitowa sosai, kafafunsa kyawawan gaske, faratunan yatsunsa kamar madara, zaka ce bai taɓa taka ƙasa ba.

Ganin ta sauko kasa yasa ya juya zai nufi hanyar zuwa wannan ɗakin dan su je ya yi aikin, ba ruwansa da zata mutu, shi dai buƙatarsa kawai ta biya.

"One mint big bro". Ta faɗa tana ɗaura hannayenta dikka biyu a saman kugunta. A tare suka dakata shi da Ronnie, dama Ronnie bai kai ga fita waje ba. So jin maganarta yasa suka dakata

Dakarawa ya yi da tafiya amma bai juyo ba, ya nuna alamar dai yana sauraronta....... Ko kaɗan babu tsoron abin da zai iya aikata mata kawai ta nufesa, a hankali take takawa har ta isa garesa, ta zago ta gabansa suna fuskantar juna, da kyau ta kara rike kugunta.

Slowly ya ɗaura idanunsa a kan face ɗinta, sai da ya ji gabansa ta ɗan faɗi, ita kanta sai da ta ji wani irin shock kamar an jona mata wutar lantarki, amma haka ta daure, cike da kwarin gwiwa zuciyarta na dukan uku uku ta ce.
"Why do you want to remove my brain?" She threw the question at him, her face hardening as if to make it clear that she was not joking.

Ɗan zaro idanunsa a kanta ya yi, a wannan gaɓar sai da ta ɗan kawar da kallonta daga cikin idanunsa, saboda da ya zaro idanu sun kara kaifafa sosai da ba zata iya ganinsa ba.

Ko waye ya faɗa mata zai cire mata ƙwaƙwalwa kuma? Kai Sweetie duniya.

When he didn’t respond, she spoke again. "So, you mean to tell me that you can’t retrieve anything from me unless you take my brain? Don’t you think that’s a sign of your failure?"

He stood motionless like a statue, showing no intention of answering her.

She fell silent, her eyes trailing down to his feet, watching how he slightly shifted them a subtle sign that her words were getting to him. Slowly, she lifted her gaze back to his face, slightly tilting her hips before freeing one hand from the grip she had on her waist. Then, with her heart pounding hard in her chest from fear of him, she forced herself to lift her hand, positioning her fingers right in front of his face. Her chest felt like it was about to burst from fear, but she suppressed it.

Shiru ta ɗan yi tana kallan yatsun kafafunsa yadda yake ɗan motsasu kaɗan kaɗan alamar maganganunta suna taɓa mashi zuciya. Slowly ta ɗago kallanta a face ɗinsa, ɗan jijjiga ƙugunta kaɗan ta yi kafin ta zame hannunta ɗaya daga rikon da ta yi wa kugun nata, sannan ta ɗaga hannun nata dai'dai saitin face ɗinsa, kirjinta tamkar zai fashe saboda tsoronsa, amma haka ta danne.

Kiyasta mashi yatsunta a saitin face ɗinsa ta yi. Her voice was sharp as she spoke, "I challenge you. Find Spender using only the brilliance of your own mind, without my help, without hurting me to get to him. Find it on your own. If you can, then I will acknowledge that you are truly a man. And I want you to understand something, when it comes to the story of your fate, I am the first page and the last. I am your destiny, and there’s nothing you can do about it!!. If you truly are a man, find Spender yourself." Babbar magana, lallai Sweetie jinjina gareki gaskiya, eyye yarinya ta ƙalubalance Black Tiger, tashin hankali, ya kuke tinanin wannan wasa zai kaya? Mu je zuwa.

She ended her words with her fingers still pointed at him, her gaze unwavering.

Tin da ta fara magana bai motsa ba yana sauraronta har sai da ta kai aya, sannan ne ya ɗan nisa kaɗan, cikin zafa ya kai hannunsa zai capki wuyarta, dan ya lura bata azabtu bane shiyasa har yanzu take da kwarin gwiwar yi mashi magana, bai san karin gwiwar ya samo asali ne daga dogara da Allah da ta yi ba, ba wai dan bata azabtu bane, ta dai rike Allah ne kawai.

Wani irin zulle mashi ta yi, ƙasa ta sunkuya sai ta tafi da karfi ta faɗa saman lion chest ɗinsa, dama ta yi wa kanta alkawarin ba zata taɓa bari ya sake taɓa mata lafiyar jikinta ba, sai dai ayi wacce za'ayi.

Ai tana faɗawa jikinsa sai da ya ji komai nasa ya tsaya cak na wucin gadin. Lokacin guda ya ji har ɗan juyi ɗakin ya yi mashi, ita kanta sai da ta rasa nitsuwarta, wani irin azabbabben shock da ta ji wanda bata taɓa jin irinsa ba, sai da ta ji gabaɗaya gaɓɓan jikinta sun mutu.

Ronnie dai mutuwa tsaye ya yi tamkar wanda aka dasa, dan kalaman Sweetie sun fi karfinsa, ƴar yarinya da ita wai ta ƙalubalance Black Tiger, wannan bala'i dame ta yi kama?.

Cikin zafa yasa hannu zai ɓanɓareta daga jikinsa ya yi wurgi da ita, ina ai bata bashi wannan dama ba, hannu tasa ta riko waist ɗinsa da karfi, dan dolensa ya lafa da yunkurinsa, barema yadda take kara shigewa jikinsa da karfi.

Shiru ya ɗan dakata yana tinanin irin hukuncin da zai yi wa wannan yarinyar. Jin ya yi shiru yasa ta sakesa tare da ɗago kanta daga saman lion chest ɗin nasa.

Da yake ya fita tsawo sosai sai ta ɗan ɗaga kafafunta sama, a hankali ta kai hannunta ta shafa gefen lallausan kumatunsa, ƙasa sosai ta yi da murya wajen furta. "I am your destiny, hakuri zaka yi da ni fa big bro, I challenged you, kada ka ɗauki zafi sosai mana, ko ka manta a sharaɗinmu babu batun cutarwa ne? Ba zaka cutar da ni ba kuma zaka yi nasarar samo Spender, ka yi hakan zan sara maka kuma na yarda kai namiji ne". Ta kai karshen maganar tare da ƙara ɗaga kafanta sosai, sumbata ta manna mashi a lallausan kumatun nasa sannan ta juya cikin wani irin tafiya mai nuna cike take da confidence ta nufi hanyar fita waje kirjinta tamkar zai fashe saboda tsoro.

Ya subhanallah, yadda kuka san an dasa Black Tiger a wajen, ta gogewa Ronnie haddar dake kansa gabaɗaya, nasan ba Ronnie kawai ba, har da ku masu karatu ta goge maku hadda ko? Wannan yarinya Sweetie nan gaba ban san ya zamu yi da ita ba, da alama idan Black Tiger bai yi da gaske ba fa zai rasa bakin magana a gabanta.

Tana zuwa kusa da Ronnie ta kyasta mashi yatsu a saitin face ɗinsa kafin ta wucesa, tana taku kamar wata hawainiya, tafiya mai matuƙar ɗaukar hankali, dik wasu albarkatu na jikinta suna motsawa a dik san da ta taka kafafunta ta yi taku ɗaya.

Har ta isa kofar room ɗin Ronnie da Black Tiger babu wanda ya iya motsawa daga in da yake tsaye, ita kuma bata juyo ba ta sanya password na kofar kamar yadda Ronnie ya koya mata.

Take kofar ta buɗe ta nufi waje abinta. Tana fita ta zube gwiwowinta a kasa a wajen tare da dafe saitin zuciyarta tana sauke numfashi da sauri sauri. Ƙasa ƙasa ta furta. "Allah na gode maka da ka bani ikon da kwarin gwiwa na iya aikata hakan a garesa, Allah Alhdulillah da baka bari bugawar da zuciyata take yi a lokacin da nike gabansa ya kasheni ba, Allah ka cigaba da dafa mun kana kareni, Allah kaga zuciyata jahadi nike san yi, Allah ka cigaba da ɗaurani a kansu, astagfilullah, astagfilullah, astagfilullah, Allah na tuba, Allah ka jiƙaina ka cigaba da karamun kwarin gwiwa kana bani ikon daurewa na yi magana yadda yakamata a gabansa".

Tana kai karshen maganar ta fashe da kuka saboda yadda kirjinta yake duka tara tara ya wuce tinaninku, a tsananin tsorace sosai take fa, kawai shegen karfin ne. Ta ɗan jima a wajen tana hawaye kafin ta miƙe da gudu ta nufi ɗakin Ronnie, tana zuwa ta faɗa saman bed tana ƙara rushewa da kuka mai tsuma zuciya.

Kamar kuma wadda aka dakatar ta yi saurin miƙewa tana gogewa hawayenta, dan ta tuna Black Tiger zai iya ganin tana kuka, ita kuma bata san bashi wata kofar da zai fahimci tana jin tsoronsa. Babbar magana, yanzu za'a fara buga wasa a Black world, my people's Black Tiger fa ya ji sumbata ya yi sumar tsaye ɗan ƙaniya, ina da ya ce baya ji, yanzu Sweetie zata yi mana maganinsa ai. Ku dai muje zuwa.

🔥🔥🔥 KINGDOM OF POWER🔥🔥🔥



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



🔥🔥🔥KINGDOM OF POWER.🔥🔥🔥

Gabaɗaya barci ya kauracewa idanunsa, banda kyakkyawan surar jikinta da ya gani lokacin da ta fito wanka ranar da zasu je wajen Khadijah babu wani abin da yake tunawa, haƙiƙa idan ya ce zuciyarsa ta kamu da san Zee to bai yi karya ba, sai dai kuma yana jin zuciyarsa bata kyauta mashi ba, dan shi yana da ra'ayin auren mace mai 25 years ne ba yarinya kamar Zee ba, dik tinaninsa ya kulle a kanta, sai dai kuma ta wani ɓangare ya fi yarda da cewa ya kwaɗaitu ne da surar jikinta kawai, dan shi ne abin da ya tsaya mashi a ransa.

Sai safa da marwa yake yi a cikin tsakiyar parlournsa, kwanciya wannan ya gagara yi, kirjinta daya kurawa idanu wancan ranar kawai ƙwaƙwalwarsa take hasko mashi a idanunsa, gabaɗaya ya gaza iya rike kansa.

Time ya duba a wayarsa dake hannunsa. 11:00pm dai'dai, gabaɗaya sai ya ji zuciyarsa tana fusgarsa a kan ya je ya ganta a daren nan, ya yi ƙoƙari wajen ganin ya tursasa zuciyarsa ya hakura da zuwa ganinta, amma ina abin ya fi karfinsa, dan haka dole a cikin wannan dare ya fito sanye da sleeping dress a jikinsa.

Kai tsaye part ɗin mama ya nufa, yana tafiya tamkar wanda yake tsoron taka ƙasa, can ƙasan maƙoshinsa ya yi sallama kafin ya tura kofar ɗakin a hankali ya shigo, light na ɗakin a kunne yake, suna kwance saman bed suna zuba barcinsu, Aneesa na gefe ita ma Zee tana gefe, gadan nasu yana da matuƙar girma sosai.

Ji ya yi tamkar ya juya gudun kada Aneesa ta farka ta gansa a kansu, amma kuma zuciyarsa ba zata iya hakura ba muddin bata ga fuskar Zee ba.

Daurewa ya yi ya ƙarisa ciki yana ji tamkar ba shi ba, wai yau shi ne ya folawa mace under 18 years, gaskiya zuciyarsa dai bata yi mashi adalci ba, shi ne abin da yake ta faɗa yana maimaitawa.

Ta side ɗinta ya zo, duƙawa ya yi a saman gwiwowinsa a gaban bed ɗin. Tana kudundune a cikin bargo, tun daga kan yadda Zee take barci mutum

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login