Showing 345001 words to 348000 words out of 403653 words
ido.
Bayan gaisuwar sarauta sun gudanar da raye-raye na gargajiya wanda ƴan'matan family ne suke gudanarwa bisa al'adar. Sun yi rawa irin su Ardah. Maza na sarauta sukan tsaya da takubba suna wakar girmamawa da rawar alfarma ana buga daff da tabl, kayan kiɗa na gargajiya. Sai dai fa Jawad ya yi, amma Jaish dik yadda yake san Auta yaki yi, dan ya ce shi fa bai ga amfanin yin al'adar nan ba, King kuwa ya ce auran Autarsa ce dole ayi dik al'adun da suke yi, kunga haɗuwar da guyson ya yi cikin warriors wears ɗin nan kuwa? Ya yi bala'in kyau sosai, ya riko takobi a hannunsa, a tsakiyar hall na gidan aka gudanar da wannan biki, Omaid and Obaid dik sun yi, Jaish ne dai ya ki yi, shi kuwa Smart ko in da suke bai leƙo ba, yana cikin bedroom ɗinsa. Shi ma Abdussalam ya yi, kuma dik sun yi masifar kyau sosai, uncle Taheer, Uncle Jahiz dik sun yi, su Ramish kam ko bikinma basu zo ba, sun ce sai bikin ta dawo Dubai kawai, idan an gama a kingdom of power aka miƙe masu amaryar su zasu tarbeta a Dubai, tin da abin dik family ne sai suka kasa kansu gida biyu
A daren ranar da aka gama wannan bikin raye-rayen sai suka gudanar da Gidauniyar Alkhairi. Wasu sarakuna na amfani da bikin aurar da ƴaƴansu dan buɗe asusun tallafi, bayar da gudummawa ga marasa galihu ko yin aikin alkhairi da sunan amarya, sai dai shi King ita kanta Auta daga cikin ɗinbin dukiyarta ta buɗe wannan, shi ya jagoranta ta buɗe wannan gidauniya, shi kuma ya yi kyautar motoci, gidaje da kuma kujerun makka, Jaish ma ya yi kyaututtuka da sunan Auta tamkar dukiyarsa zata kare, sai dai ko kaɗan bai girgiza ba, shi ma uncle Abbas ya yi kyaututtuka, ya taka ya je prison da kansa ya yi freeying masu ƙananan laifuka, ya yi belinsu sannan ya basu kuɗi dan nemawa kansu aikin yi, baya ga haka yasa anyi girke girke da dama aka kai gidan prison ɗin dan ciyar da waɗan da suke ciki. Shi kuma uncle Jahiz gidan marayu ya je, nan ya bada millions dan tallafa masu, dik da sunan Auta suka yi suna fatan Allah ya bata farinciki da kwanciyar hankali mai ɗorewa a gidan aurenta, su kansu sun san zama da wanda baka so ba kara mun abu bane, shiyasa dik suke wannan, kowannensu da abin da ya yi, Dr Raj ma yana nan, ya yi kyaututtuka da dama, Ramish, Bilal and Yah Rizwan suma sun yi mata kyaututtukan da baki ba zai iya faɗa ba. Abubuwa dai sai wanda ya gani, sai dai wacce ake yi dominta ko kaɗan bata a tare da su, umarnin daddynta kawai take bi yasa ta ja bakinta ta yi shiru.
DINNER NIGHT.🔥
Ango ya sha kyau cikin bisht wato kayan sarauta na maza, rawani da takalmin fata na alfarma, dukiya ya yi mubaya'a a wanna waje, komai nasu very luxury. Su Aunty MieMie sun shirya amarya a cikin wasu haɗaɗɗun p-k, wani shegen gown ne mai bala'in kyau da tsada, tana jan kasa, ga alkyabba mai kwalliyar lu'ulu'u, takalmar kafanta kawai ya isa yasa ku fahimci auren ƴar gata ake yi. Babu karya, ko makiyi yasan Zunaira ta yi kyau sosai, sai dai ko kaɗan babu walwala a saman face ɗinta, alamar tana cikin tsananin tashin hankali, a haka ta shigo cikin hall ɗin, mc yana ta faman zuba kirari a gareta, Chuchu tana rike da hannunta, ɗayan side ɗin kuka Aneesa ce ta riketa, su Khadija dik sun shirya sun halicci dinner ɗin bisa umarnin Aunty MieMie, Pretty ce kawai taki zuwa, ta dai cewa Momma ba zata je ba dan bata san hayaniya, shiyasa ta yi zamanta a parlourn Momma tana kallan tv.
Kiɗan larabawa mai shehen daɗin mc ya bada umarnin a saki da shigowar tauraruwar amarya, tana shigowa wasu jakadun mata suka hau fesheta da turarruka wasu suna watsa mata furanni. Dama sai zuba kamshin turarukan larabawa su oud, musk, sandalwood take yi, dik wanda yake cikin hall ɗin nan sai da dandatsetsen sarkar zinarin dake wuyarta ya ɗauke mashi hankali, kai kyau fa iya kyau Auta ta yi, walwalar ne dai da babu shi ne matsalar. Abdussalam dake tsaye yana jiran ƙarisowa dik ya kotsa ta iso ya ji me yake damunta da ta haɗe rai haka, shi ya rigata zuwa, a tsarinsu ba tare suke shigowa ba, shi zai shigo da abokansa, ita ma tare da kawayenta.
Kun san menene babban abin takaicin my people's? Hoorain yana wajen wannan dinner, yana gab da bakin kofar shigowa, sai dai kuma zuciyarsa bata yarda mashi abin da kunnuwansa suka ji yo a masallaci ba, yana ganin kamar bikin Aneesa ake yi bana Auta ba, yaki yarda, shiyasa bai nuna damuwa ba, kuma King ne ya wakilta shi a kan tsaron kofar shigowa dinner, yana tsaye yana aikinsa yana ta faman tinaninta, a ransa yake faɗin ya yi mata uzuri na rashin ɗaukar call ɗinsa da bata yi ba, kila saboda jama'a ne yasa busy ya yi mata yawa, amma dik a dame yake da ta ɗauki waya su gaisa.
Suna isa bakin stage ɗin Abdussalam ya yi saurin matsawa ya riƙo hannunta a in da ya taimaka mata ta hauro sama, dik da kanta a ƙasa, kuma tana cikin alkyabbarta sai da gaban Hoorain ya faɗi lokacin da ya ga Abdussalam ya riƙo hannun amarya, wai a haka ma bai san hannun waye ya riko ba, da ya san hannun Hoonairarsa ce me kuke tinanin zai faru?....... KAI WHAT A HEART TOUCHING PAGE 💔😥
Saman haɗaɗɗen King seat da aka tanada masu suka zauna, suna zama mc ya yi umarni da a juya kiɗar zuwa karatu dan a buɗe taron da addu'a. Haka kuwa aka yi, suratul Fatiha suka sanya bisa tsarin musulunci da kuma tsarinsu, sannan aka buƙaci manya suka gudanar da addu’a dan yi wa amarya albarka. Dik dai wani al'adunsu suka yi shi suka gama, saura sanyawa amarya ring and kiss, sai cin abinci da abin sha kafin a fara sake kiɗa dan yin nishaɗi.
Mc ya buƙaci da ango yasa wa amaryarsa zobe, sai tambayarta yake yi meyake damunta, amma taki ta yi mashi magana, shiru tin da ta zo wajen. Ya shiga damuwa matuƙa, amma a haka ya daure zuwa a gama taron, wani dankareren diamond ring kusan shigen wanda ta sanyawa Hoorain a hannu daren jiya ɗaya daga cikin abokan Abdussalam ya miƙo mashi, Ring ɗin yana cikin box ɗinsa. Unboxing ɗinsa ya yi tare buɗewa, wani irin kyalli yake yi yana ɗaukar ido. Miƙewa tsaye ya yi tare da riƙo hannunta ya miƙar da ita, ya tsayar da ita suna fuskantar juna, sannan ya kama ƴan yatsunta ya zura mata ring ɗin, take hannun nata ya kara wani irin kyau na musamman. Tafi rap, rap, rap, gabaɗaya cikin hall ɗin ya ɗauka, abin ya ƙayatar. Muryan mc suka ji yana faɗin yanzu Ango zai sumbaci amaryarsa kamar yadda suka saba yi!.
Aikuwa kamar jira Abdussalam yake yi, Mc na bada dama ya yi saurin sanya hannunsa ya ɗago haɓarta da tin da ta zo wajen bata ɗago kanta ta kalli kowa ba. Ɗago kanta ya yi tare da matsar da face ɗinsa dab da ita, cikin salon nuna mata soyaya da kauna ya kai bakinsa zai sumbaceta. Daidai lokacin ta ɗago kallonta kai tsaye sai saman fuskar Hoorain da ya yi mutuwar tsaye yana kallanta, tin da ta miƙe Abdussalam ya sanya mata ring ya gane ita ce, shiyasa ya yi mutuwar tsaye!!.
Dik da cewa akwai hular warriors a face ɗinsa, hakan bai hanata ta hango tashin hankalin dake cikin idanunsa ba, kwayar idanunsa tamkar wuta saboda ja, kuma kallanta kawai yake ko kyaftawa bai yi ba, Ansar na tsaye a gefensa ya ɗaura hannunsa a saman takobin dake waist ɗinsa. Abdussalam yana dab da zai haɗe bakinsa da nata sai gani ta yi Hoonaira ya tafi gabaɗaya ya yi ƙasa, take a wajen numfashinsa ta ɗauke ɗiff.
Ai bata san lokacin da ta zunduma ihun sunansa har sai da ta razana dik abokan ango da su Chuchu dake wajen ba, lokaci guda kuma zancen King ya dawo mata cikin kwakwalwarta na sharaɗin da ya gindaya mata idan har tana son ya yafe mata, ya ce to kada ya sake jin sunan Hoorain a bakinta, ko da sunan wasa kada ta sake ɗaga idanun ta kallesa, Allah sarki da farko ta yi niyar ta zumduma a guje ta yi kansa, amma da ta tina maganar King sai kawai ta kara zunduma wani ihun da bata kai karshen yinsa ba ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a wajen. A miliyan Abdussalam ya yi kanta yana ambatar sunanta, su Chuchu dik kanta suka yi kamar yadda su Ansar suka yi kan Hoorain da suka tabbatar da baya numfashi, babu rai a jikinsa!!. Cike da tashin hankali Ansar da Anwar suka ɗaukesa, haka ita ma Auta Abdussalam ya ɗauketa ya sauko kasan stage ɗin da ita, da gudu su Chuchu suka rufa mashi baya, nan fa taro ya hargitse, hankula sun tashi sosai.
Hospital suka wuce da Hoorain a in da gwajin farko Dr ya tabbatar masu da babu rai a jikinsa, ita kuma Auta wuce suka yi da ita cikin family part, King ya umarcesu da su kaita part na bayan fam part ɗinsa a in da babu kowa a wajen, babu hayaniya babu ribibi, su kai ta can Dr's su zo su duba lafiyarta, sabon part ne da ba'a buɗe ba, dama na uncle Jahiz ne in da idan ya yi aure zai zauna kamar yadda uncle Abbas yake da part ɗinsa. Nan aka wuce da ita, a take aka kira likitoci guda uku suka dukufa a kanta dan ceto rayuwarta, ita dai bata mutu ba, amma zuciyarta na dab da bugawa, shi kuma Hoorain zafin kishi da soyayya yasa ya haɗi zuciya take rai ya yi halinsa! Lallai ba shakka Hoorain ya kurɓu gabar soyayya mai zafin gaske!!. Wlh a lokacin da Dr yake sanar da su Hoorain ya rasu Ansar yanke jiki ya yi ya faɗi sumamme, shi kuma Anwar capko wuyar rigar Dr ya yi, kamar wanda ya rasa hankalinsa ya fara faɗin wlh Dr ya tasan masu ɗan uwansu ko kuma ya kashe shi shima, abin dai very very heart touching, heartbreaking.......😥💔
Wlh page ɗin nan ya yi mugu mugun taɓa ni, Allah sarki, ashe da rabon kafin ya mutu zai yi kissing Zunairarsa, to King yanzu dai Hoorain ya bar maku duniyar, sai ku dafa Zunaira ku cinye, amma my people's kuna tinanin Commander Zafar zai yafe jinin Hoorain ya tafi a banza kuwa? Baku ganin kamar commander zai juya masu baya ya yakesu? Kada ku manta commander shine kaso sittin cikin ɗari na karfin kingdom ɗin, warriors dik umarninsa suke bi, ya kuke gani idan ya juya masu baya?!. Wlh akwai case ba na wasa ba, ni dai bari in je in kora Maltina ko zan samu sassaucin abin da nike ji a cikin zuciyata!!!.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
54
Sai da kingdom of power ta tsaya cak na ƴan wasu ɗakinku a lokacin da labari ya karaɗe kunnuwar mutane Hoorain ya mutu, shi kansa King sai da ya yi zazzafar razana, ai Commander Zafar cewa ya yi karya ne, ba Hoorain bane ya mutu sai dai wani, amma shi ɗansa yana raye, dik yadda aka so a fahimtar da shi Hoorain ya mutu ya zo su gana da gawarsa ya yi mashi addu'a kafin a je a rufesa, amma commander ya ƙaryata, ya ce wlh shi babu gawar da zai zo ya yi sallama da ita, dan shi ɗansa na raye. Ansar ya lura lallai commander ya zaune ce, ba kuma zai taɓa fahimtarsu ba, dan haka sai ya ce su sanar da King ko zai iya sanya commander ya fahimtar har ya sami damar yin bankwana da ɗansa.
Haka kuwa aka yi, suka sanar da King ga abin da yake faruwa, suna san yin jana'izar Hoorain amma commander ya ki yarda ya zo ya gansa ma bare har ya yi mashi addu'a. Cike da alhinin abin da ya faru King yasa a kira mashi commander. Babu kunya babu tsoron Allah King ya iya kallan commander ido cikin ido ya sanar mashi da ya ɗauki dangana Hoorain dai ya mutu.
Murmushi commander ya yi kafin ya ce. "Allah ya kara maka tsahon rai, na tabbata ba Hoorain ɗina ne ya mutu ba, wani Hoorain ɗin ne, Hoorain ɗina yanzu na barosa a waje". Jin waɗan nan kalamai yasa King ya fahimci commander fa ƙwaƙwalwarsa ta shiga cutar da ake kira da I-M-R-S, lallai ko zasu shekara suna faɗa mashi Hoorain ya rasu ba zai taɓa yarda ba, dan shi Hoorain yana yi mashi gizo, yana kallansa da idanun da babu mai kallansa sai shi. INNALILAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL!! KENAN YANZU COMMANDER YANA KALLAN HOORAIN KOWA BAYA KALLANSA? YANA YI MASHI GIZO? BABBAR MAGANA!! LALLAI KUWA BA ZAI TAƁA YARDA DA HOORAIN YA MUTU BA!!.
Yana tsaye a tsakiyar fada yana kallan King, sai kuma ya juyar da kallansa izuwa kofar shigowa, gwanin ban tausayi ya fara faɗin. "Yauwa my lion, wai cewa suke yi ka mutu, na ce masu baka mutu ba, zo ka gwada masu kanka!". Ya kai karshen maganar yana riko iska a matsayin Hoorain da ya shigo fada a yanzu.
Wlh a dai'dai wannan lokacin gabaɗaya ƴan majalisar fada sai da idanunsu ya ciko da kwallah, shi kansa King sai da zuciyarsa ta karaya, gaskiya bai taɓa ganin soyayyar uba da ɗansa irin tsananin soyayyar dake a tsakanin Commander da Hoorain ba.
"Ranka ya daɗe ba ga shi nan ba! Ai dama na faɗa maka bai mutu ba, ga shi ka gani ma da idonka". Allah sarki, daga yadda yake magana zaka fahimci sambatu ne kawai, dik yana rikice, gwanin ban tausayi, ya yi maganar yana nunawa King iska a matsayin Hoorain dake gabansa. Aunty MieMie dake zaune a kusa da King wacce bata jima da shigowa bace ta miƙe tsaye, wani irin kuka ne mai karfin gaske ya kwace mata, dama ta shigo ne ta ɗan taushi zuciyar baban nata, dan ta ga ya ɗauki zafi sosai, tana zaune aka kawo labarin mutuwar Hoorain, ta ji hakan a ranta sosai, sai yanzu kuma ta ga abin da ya fi mutuwar tasa zogi, ba zata iya zama ba, da gudu ta ruga cikin gida alkyabbarta na jan ƙasa tana hawaye.
Allah sarki commander dattijon arziki, cike da damuwa ya ce. "Lafiya ranki ya daɗe ta tafi tana kuka? Ko wani abin ne yake faruwa?". A ruɗe ya yi maganar.
Dik cikin fada babu wanda ya iya bashi amsa, sai sharan kwallah da kowa yake yi, bare ma sarkin hatsi da tuni hawaye sharɓa sharɓa sun gama jiƙa fuskarsa har sun jiƙa wuyar rigarsa. Da mamaki commander yake binsu da kallo, cikin ruɗu ya fara faɗin. "Malam liman lafiya kuke kuka? Ko dai akwai abin da yake faruwa ne? My lion ka ji labarin wani abin yana faruwa ne?". Ya yi maganar yana kallan gefensa a zuwan yana kallan Hoorain.
A gizon da yake gani girgiza mashi kai Hoorain ɗin ya yi yana ce mashi babu wani abin da yake faruwa, watakila kukan farinciki suke yi. Jinjina kai commander ya yi tare da mayarwa gizon nasa amsa da. "E ina ga kukan farinciki suke yi, suma suna murnar biki ne, to shikenan jeka abinka ni bari in zauna a nan mu gama magana kan yakin da zamu tafi jibi". Jinjina mashi kai gizon nasa ya yi tare da juyawa ya bar wajen ya nufi waje.
Wlh dik taurin zuciyar king sai da idanunsa suka kawo kwallanh, bai taɓa zatan zai shiga damuwa a mutuwar Hoorain ba sai da commander ya shiga cikin wanna hali, amma kuma fa dik da haka sam bai yi danasanin abin da ya aikata na raba masoyan ba, shi yana ganin yana a kan dai'dai!!
-------------------------------🔥🔥🔥
Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci suka yi nasarar shawo kan Auta har ta farfaɗo, sai dai kuma, Dr ya sanar da in dai basu bata abin da take so ba, to wlh zuciyarta tana gab da bugawa, yanzu haka ta samu babban rauni a zuciya. Sosai ƴan uwan suka girgiza da jin wannan labari, a in da suka ce kada a kuskura a sanar da ita Hoorain ya mutu, King kuma ya ja Abdussalam gefe a in da ya sanar da shi ya san dik ta yadda zai yi ya maye gurbin Hoorain a cikin zuciyarta gudun kada su rasata, sai dai abin da King bai sani ba shi ne, soyayyar Auta and Hoorain daga Allah ne, babu wanda ya isa ya maye gurbin Hoorain a cikin zuciyarta kamar yadda babu wanda ya isa ya maye gurbinta a cikin zuciyarsa!. Abdussalam ya tambayi wanenne Hoorain kuma, sai King ya ɓoye mashi, ya ce dai ya yi ƙoƙarin janyota a jiki ya kwantar mata da hankali, King baya san Abdussalam ya san komai!.
-----------------------------🔥🔥
Tin da momma ta samu labarin mutuwar Hoorain ta shiga tantama da tashin hankali, zuciyarta na ayyana mata akwai wata babbar dalilin da yasa King ya gwammaci gara Hoorain ya mutu a kan ya auri Zunaira, sosai momma take zargi da biyu ma King ya saka Hoorain ɗin gadin hall ɗin dinner dan zuciyarsa ta buga a lokacin da zai ga Auta da wani, abin ya tsayawa momma a rai, shiru ta nutsa cikin tinaninta tana tariyo rayuwar baya, ɗauko tinanin