Showing 147001 words to 150000 words out of 403653 words
tada kai da cinyar Mammie suna shirya muguntarsu.
Ai a haukace ta shigo tana ihu, har ta razana Sarina ta yunkura zata gudu. Saman bed ɗin ta haye ita ma, Mammiensu ta rungumo tana faɗin. "Na shiga uku Mammie, shi kenan rayuwata ta zo karshe, ki taimakeni kada na mutu Mammie".
Sarina dai baki ta saki galala tana kallon ikon god.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=======🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Rungumeta Mammie ta yi tana faɗin. "Ya isa haka, yi shiru ki faɗa mana menene yake faruwa?".
Ƙasa yin shiru ta yi, sai ma wani irin shessheka take yi tamkar zata haɗiyi zuciya ta mutu.
A kule Sarina ta ce. "Ke bama san hauka, dalla rufe mana baki ki faɗa mun me yake faruwa?". ........... Sanin bakin halin Sarina yasa ta haɗe malaman jikin waje guda ta nitsu, cikin muryan kuka ta fara kora masu bayanin yadda Aneesa ta kora mata.
Wata iriyar zabura Mammie ta yi, dan kuwa tasan da cewa Queen Zarina tana san Jaish, kuma tana san shi ne a matsayin saurayi ba wanda ya taɓa aure ba, in kuwa ya yi aure akwai matsala, dan haka dole su yi saurin kawar da Mahnoor tin kafin ya rasa samartakansa, samartakan nasa Zarina take so, shiyasa kuka ga a yanzu Mammie ta daina goyan bayan Fanan a kan soyayyar Jaish.
HMMM BABBAR MAGANA.
A baya ta so Fanan ta mallaki Jaish, amma da Zarina ta nuna kwaɗayinta a kansa sai Mammie ta janye, shiyasa kuka ga ta dai'na bawa Fanan dik wata gudunmawa, ita kuma Fanan lokacin da Mammie take matsa mata ta rinƙa zuwa wajen Jaish dan ta samu soyayyarsa, a lokacin bata wani feeling a kansa sosai, daga baya sonsa na gasken gaske ya shigeta, a lokacin ne kuma Mammie ɗinsu ta zare hannunta a lamarin,........................... Tashin hankali, lallai akwai cakwakiya.
Mahnoor ta ko'ina sai tarin makiya kike da su, Allah dai ya fiddaki, amma akwai matsala, Mahnoor zata yi kishi da Queen Zarina and Fanan, kai my people's shin kuna ganin wannan abu ne mai ɓullewa ga Mahnoor kuwa? Babban abin takaicin ma shi ne mijin da ake ta wannan bura uba a kansa ɗin ma bai san suna yi ba, hasalima dikkansu ba wanda ya ke kalla da mutunci, dik ya tsanesu, akwai bala'i a kingdom of power wlh, ga dai can Zarina ta tura a ɗauko mata shi, wayyo Allah Jaish yaron Mommarsa zaka yi bayani dan gidanku in ka jika a komar Zarina, ina dai Mahnoor ce baka so? Mu je zuwa zaka so Zarina dan dole ai.
Wani irin matsiyacin tsaki Sarina ta ja. A walaƙance ta dallawa Fanan wani tsinannen harara wadda sai da tasa Fanan haɗiyar yawu mai wuyar wucewa.
"Shashasha kawai, ke yanzu a kan namiji kike wannan kuka Fanan? Me aka yi aka yi Yah Jaish? To ko mata dubu zai aura cikin minti nawa zaki ci uban shegu ki kaɗasu hanyar yamma? Ke sai kace ba jininmu bane a jikinki! Ni kam anya Mammie Fanan ƴar ki ce kuwa?"........... Cewar hajiya Sarina almasifatu rasa kunya.
Bata jira amsar Fanan ba ta ɗaura da cewa. "Ko ƴar autar sarkin aljanu ya aura karshe kenan ko? To ubanta zaki ci kawai, zan yi supporting naki ba dan komai ba sai dan kina sansa, dole in tayaki mu kwato maki shi". Tana magana tana dallah mata wannan makirin hararar.
Mammie cikin karayar zuciya ta ce. "Fanan da gaske son Jaish kike yi?". Yadda ta yi maganar zaku fahimci wlh zuciyarta ya karaya matuƙa, tana san ƴaƴan nata sosai, bata jin zata iya marawa Zarina baya ta mallaki Jaish in dai har da gaske Fanan tana san shi, kuma ba zata iya rabuwa da shi ba, ba zata cutar da ƴaƴanta ba gaskiya, dan tasan ya zafin so yake.
"Zaki iya hakura da shi?". Cike da tsoron amsar da zai fito daga bakin ƴar tata ta sake jefa mata wannan tambaya.
Wasu zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Fanan, cikin murya mai ban tausayi ta amsa da. "Mammie wlh mutuwa zan yi idan har na ce zan hakura da Yah Jaish, wlh ina sansa so mai tsanani, ban taɓa san wani abin kwatankwacin jin sautin muryarsa kawai bama.........."
Katseta Sarina ta yi cikin tsiwa. "Ke dallah ki dai'na jero mana wasu sambatu, ni natsani jin kalaman soyayya a bakin mace, idan kin ga dama ki dafa shi ki cinye, amma kada ki faɗa mun, kina son shi e kina son shi ya wadatar, ba sai kin kara mana da yadda kike ji a ranki ba"........... Wai Sarina sai shirin Allah, wannan yarinya da ba dan ma jinin Akka na gudu a jikinta ba wlh ina ga shaiɗancinta sai ya wuci yadda ake tinani.
Shiru Fanan ta haɗiye sauran maganganunta tana shessheka haɗe da kawar da kallanta daga kan Sarina.
Mammie kam shiru ta yi kamar wadda ruwa ya cinyeta, ta rasa abin faɗe, iya abin da ta sani shi ne lallai a wannan gaɓa ba zata taɓa taimakawa Queen Zarina ba, tun da Fanan ta kamu da san Jaish dole yarta ce zata mallake shi............ Bala'i can, kai my people's me kuke tinanin zai faru? Jaish shi kaɗai mata uku, dik bama wannan ba, ya mammie zata kaya da Queen Zarina?.
Riko hannun Fanan Sarina ta yi. "Zo mu je ɗaki in baki lecture yadda zaki yi maganain Yah Jaish ya dawo tafin hannunki, a wannan karon bama buƙatar Mammie, dan ita bata san salan zamani ba, na da can ta sani, Mammie ke kuma mun baki aiki kawar mana da matar da aka aura mashi ɗin koma wacece".
Tana magana tana janyo hannun Fanan har ta sauko kasan gadon. Cikin shessheka murya a hanzarce Fanan ta ce. "Aunty Sarina bafa wata matar azo a gani bace, wlh tantagaryar ƴar kauyece wadda bata da banbanci da dabbobi, kuma kin ganta yar datti, amma kuma wlh tana da kyau sosai, dan ya fini kyau".
Ɗan taɓe baki Sarina ta yi tana ɗaure fuska. "Kin san matar tasa ce? Kin taɓa ganinta ne?".
Da sauri ta amsa da. "E jiya fa a ɗakina momma ta kawosu suka kwana, sai kin gansu wasu kucaku da su ƴan datti, ɗakina ya yi ta wari sai da nasa aka kwashe bedsheet da suka taɓa da dik wani abin da suka yi amfani da shi aka zubar da su, na sa aka zuba tirarika sannan na iya kwana".
"What?!!" Sarina ta faɗa cikin ɗaga murya. Jinjina kai Fanan ta yi alamar tabbatarwa.
"Muje in gansu". A gadarance ta yi maganar.
Banda idanu babu abin da Mammie take binsu da shi, ta rasa abin faɗe, tinanin balai'n dake tinkarota kawai take yi a kan wannan case ɗin.
"Aunty Sarina yanzu kam sai dai mu je mu tambayi Neesha ta bamu labarin in da matar tasa take, dan Haulat ta zo da safe ta ɗaukesu". Cewar Fanan.
A ƙagare da san ganin Mahnoor Sarina ta amsa da su je wajen Aneesa ta basu labarin ina Mahnoor take. Da wannan shawara suka nufi waje hannunsu cikin najuna, har wa yau dai Sarina tana cikin wannan ɗan iskan shigar tata mai tada hankalin maza.
Mammie da ta afaka duniyar tinani sam bata san lokacin da suka fice daga ɗakin ba, mafita kawai take tinawa kanta.
Basu zame ko'ina ba sai part ɗin King, ɗakin Aneesa kai tsaye suka nufa. A lokacin ta fito daga wanka ɗaure da towel a kirji, tana tsaye a gaban mirro, sai tashin kamshi ɗakinta yake yi.
Zee tana zaune a saman sofa ta buga uban tagumi tana bin Aneesa da kallo, tana cikin shigar abaya mai bala'in tsada na Aneesa launin ash colar, ta yi matuƙar kyau sosai, ta yi rolling veil a kanta.
Tun sako kafarsu a cikin ɗakin Sarina take bin Zee da wani matsiyacin kallo da in aka yi wa mutum sai ya ji kamar shi ƙasƙantace ne. Ganin haka yasa Zee ta kawar da kanta daga kallonsu, ga shi kuma tana bala'in san kallan nasu, saboda larabawan ainahi suna da tsananin kyau sosai, amma ta lura kamar gabaɗaya familyn King daga mazan har matar dikka tacaccun ƴan duniya ne masu jiji da kansu, babu mai saukin kai da za'a ɗaga idanu a gani ya ɗan tarbi mutum da fuska mai sauki sauki koda ba fara'a ma, gabaɗayansu daga matan har mazan fuska kamar an aiko masu da saƙon mutuwa. Allah sarki bata samu Zunaira da Chuchu bane shiyasa take wannan tinani.
Sarina na ƙoƙarin ambatar sunan Aneesa dan ta tambayeta sai Aneesa ta yi saurin katsesu da cewa. "Aunty Sarina nasan bai wuce amaryar Yah Jaish kuka zo tambayata ina take ba, ai dama nasan sai kin so ganinta, to ba fa wata shegiya bace, ku kwantar da hankulanku, yar kauye ce mara gata wanda ko a ƴar aiki ba zan ɗauketa ba, banza ya fi mun ita muhimmanci, dan haka ni ban ga abin da zaku nemi gani a wajen bama, sai dai fa tashin hankalinku ɗaya ne"....... Dakatawa ta yi da magana tana wurga masu kallo ta cikin mirror.
Aneesa wlh karshe ce yarinyar nan, wannan idan Allah ya taimaketa Yah Rizwan ya shiga hannunta shikenan kuma sai abin da ta so, yarinya ta iskance tun bata kai ko'ina ba, Allah ya ceci Yah Rizwan.
Cike da fadanci Sarina ta amsa da. "Mecece matsala gudan?"..... Shiru Aneesa ta ɗan yi na kamar one min, sannan ta amsa da. "Momma, momma tana bala'in kaunar yarinyar dik da take kazama maras gata".
Siririn tsaki Sarina ta je. "Wannan ba matsala bane, ke dai yanzu faɗa mana in da take?".
Cikin halin nuna ko in damu Aneesa ta faɗa masu Mahnoor suna ɗakin gyara. Sai dai tasan su Sarina basu isa faɗa da momma ba, dole su gama dik iskancinsu su dawo lallaɓa momma kam, dan ta gagari kowa a gidan, kafun Allah ce ita.
Sai binsu da kallo a sace Zee take yi, dan kyansu take san kallansu ba dan komai ba.
Juyawa Sarina ta yi, har lokacin hannunta rike da Fanan dake ta sauke ajiyar zuciya saboda kukan da ta sha. Har sun kai tsakiyar ɗakin zasu nufi waje Sarina ta dakata, juyo da kallanta a kan Zee ta yi. Wani irin kallan walaƙanci ta watsa mata up and down kafin ta ce.
"Neesha wacece kuma wannan?".
Aneesa na cigaba da gyaran gashin kanta ta amsa masu da. "Bakuwar second dad ne".
"Wannan kucakar? Daga ina ya samota?".Sarina ta sake tambaya........... Tara gashin kanta Aneesa ta yi ta ɗaure, sannan ta juyo garesu da kyau, ta ɗan jingina bayanta da jikin mirror kaɗan, sillent talk ta yi wajen cewa.
"Wannan ne kuma zaki iya tambayarsa, bani da alaƙa da hakan kuma bana san yin alaƙa da hakan shiyasa ban nemi sanin labari a kan meyake tsakaninsu ba". Tana kai karshen maganar ta wuce dressing room ɗinta.
Harara Sarina ta bi Zee da shi kafin tasa kai ta nufi waje, kai tsaye ɗakin gyaran suka nufa. Sai dai ko da suka je mama Haulat ta hanasu shiga, saboda doka ce momma ta saka bata yarda ta bawa kowa daman ya shiga wannan ɗaki ba har sai su Mahnoor sun fito.
Tatas Sarina ta yi wa mama Haulat, rashin kunya tas ta yi mata wanda ko kare ba zai sinsina ba, sannan ta ja hannun Fanan suka ta fi tana faɗi ko mama Haulat zata mutu yau ba sai gobe ba sai sun shiga ɗakin nan sun ga Mahnoor, ta jira dawowansu a karo na biyu.
Ko sannu mama Haulat bata ce masu ba har suka fice, wucewa ta yi ta rufo kofar da Mahnoor suke ciki ɗin, ta zo ta ɗauko kayan marmari dan ta kai wa Jaish yana lambu.
Allah sarki mama Haulat baiwar Allah ƴar amana, matar nan tana da ƙoƙari sosai, ba ƙaramin fama ta sha da Mahreen ba kafin Mahreen ta yarda a shafa mata haɗin gyaran jiki a jikinta, har zagin mama Haulat ta yi, amma dik da haka bata tuna ta wani damu ba, sai ma hakuri da ta rinƙa bawa Mahreen ɗin.
Abin dariya kuma shi ne Mahreen bata taɓa yarda ta shiga toilet ita kaɗai har sai mama Haulat ta rakata, wanka ma ita ta yi mata yau, dan tsoron toilet ɗin take ji, sai su manne waje guda ita da Mahnoor saboda tsoro. Dik da haka mama Haulat ta jure bata wani damu ba.
A ɓangaren uncle Jahiz kuwa, yana barin wajen su Zee ya dawo in da momma take ya karɓi babyn Khadija wanda ya sanya mashi suna da Junior, haka yake kiran yaron, Allah ya saka mashi kaunar babyn nan sosai. Yana ɗaukansa ya wuce wajen King a fada da shi, a nan suka je rabon zakka.
Sai dai fa dik hankalinsa yana a kan Zee, tinaninta kawai yake yi, yana jin kamar ya tashi ya zo ya sake dubata, dan yana ganin kamar bata jin daɗin zama da Aneesa, saboda yasan halin ƴaƴan nasa, haka dai yake ta sake sake ya kasa tsayar da abu guda.
Da yamma ta yi cikin nitsuwa ya yi wanka ya canza kaya, ya bawa mama Haulat junior ta yi mashi wanka ta shirya shi cikin shiri na musamman, sannan ya koma ya karɓesa, ya nufo wajen Zee a ɗakin Aneesa.
Babu kowa a cikin ɗaki, ita kaɗai, ta takure jikinta waje guda, tana kwance saman sofa barci ya yi awon gaba da ita. Ciki ya kariso, a gaban sofar ya tsaya yana kallan face ɗinta, har sai da ya ji faɗuwar gaba lokaci guda, ji ya yi kamar kada ya tasheta, amma kuma ya tina tana san ganin ƴar uwarta, hakan yasa ya fara ambatar sunanta a hankali hankali.
Da yake bata da nauyin barci sai ta farka. Ganin shi a kanta yasa ta yi saurin miƙewa zaune tana janjayo kayan jikinta ta gyara. Ɗan kawar da kallansa a kanta ya yi yana faɗin. "Sorry na tasheki daga barki ko?".
Kanta a ƙasa ta amsa mashi da ba komai. Sai wani gyara jikinta take yi tana takure kanta bayan komai nata a rufe yake.
"Kin shirya mu tafi ne?". Da sauri ta gyaɗa mashi kai. Sannan ta ce. "Dan Allah ka ɗan bani yaran in rike".
Ba musu ya miƙo mata shi naɗe cikin kyakkyawan abin rike yaro fari kal mai tsada. Hannunta har kerma yake yi tasa ta karɓesa, ya yi barci, bawan Allah da mama Haulat ta bashi badara ya sha, ta yi mashi wanka shikenan sai ya hau barci abinsa, bashi da kukan banza.
"Muje ko?". Ya faɗa yana nuna mata hanya. Gaba ta wuce ya rufa mata baya yana ta kallanta. Kasa hakura ya yi har sai da ya ce. "Zee kayan nan sun yi maki kyau sosai, kin yi kyau".
Hankalinta a kan baby ta amsa da ta gode, daga haka bata sake yin magana ba suka wuce izuwa parking space na gidan. Gidan baya na ɗaya daga cikin motocinsa suka shiga, driver ya jasu zuwa hospital na cikin Kingdom ɗin.
•••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥
Bari mu leƙa wani part.
Katafaren gida ne irin contemporary Glass Architecture ne, gini ne na gilashi mai kauri da tsari mai ban sha'awa don bayar da haske da kyau.
Hawa biyu me mai amfani da escalator mai amfani da lantarki don tafiyar da mutane sama ko ƙasa cikin sauƙi. Manyan ɗakunan barci guda uku a sama da karamar parlon, sai main parlour mai girma a ƙasa wanda aka kawata shi da kayan alatu launin pink and milk.
Akwai wajen wasanni, shakatawa, da filin motoci, grand Living Room, lambun waje furanni masu kyau da kamshi, ga shuke shuke masu ƙawa na musamman.
Babban Kitchen na Zamani (Modern Kitchen) mai ɗauke da kayan girki na zamani (smart appliances) Dining Room wajen cin abinci mai ɗauke da fitilu na alfarma. Guest Room, ɗakunan baki guda biyu masu zaman kansu. Restroom, tare da kayan zamani.
Hawa Na Biyu (First Floor)
Master Bedroom. Babban ɗaki mai ƙunshe da toilet, wardrobe na zamani, da balcony haɗe da kayan alatu na more rayuwa. Mini Library. Wurin karatu da nazari. Gaming Room. Wurin wasanni da na’ura masu ban sha’awa. Cinema Room. Wajen kallon fina-finai na zamani. Office Space. Wajen aiki ko haɗuwa da abokan ciniki. Guest Lounge. Wani parlour na musamman ga baki. Indoor Pool. Ruwan wanka na sama mai gabaɗaya mai ɗumi na musamman. Barbecue Space. Filin girke-girke na musamman, sune a sama.
Waje hararbar gida (Outdoor)
Swimming Pool. Babban ruwan wanka mai kyau. Garden. Lambun shakatawa da kujeru. Playground. Wurin wasan yara da manya. Parking Lot. Wajen ajiyar manya-manyan motoci, har guda 8. Shake yake da motoci irinsu, Rolls-Royce Phantom, Bentley Bentayga, Lamborghini Urus, Mercedes-Maybach S-Class, Ferrari Portofino. Gidan ya haɗu matuƙa.
Sai dai dik girmansa da ƙawatuwansa mutane biyu ne kawai suke rayuwa a cikinsa, daga wata dattijuwa sai jikarta. Tsohuwar dattijuwa mai cikar kamala, da ƴar matashiyar jikarta da ba zata wuci 18 to 19 years ba a duniya.
Kyakkyawar gaske ce yarinyar, gata so sillent haka, tin da ta taso a tare suke da wannan kakar tata, da farko rayuwa suke yi a cikin wani kango wanda da shi da banu dik ɗaya ne, dik ya rurrushe babu kofa, gini ne na laka da ya jima ya sha wahala, ci da kyar sha da kyar, idan sun samu cin safe basa sanya ran zasu samu cin rana, basu da gata basu da galihu.
Ga jikar tata kuma Allah ya yi mata basira sosai, akwai ilimi da