Showing 36001 words to 39000 words out of 403653 words
suka yi, yadda ta yi masu magana kamar tana basu umarni, kallon mamaki Ronnie ya bita da shi ita kuma Floris kallan takaici! Sai dai basu furta uppan ba, ita kuma ko a jikinta.
"Idan na gama bayanai da nike son yi sai ku tambayeni in kuna da tambaya, amma yanzu ku yi shiru ku saurareni tukun nan, zan gaya maku komai game da hujoji!".
Kasa yin magana Ronnie ya yi, amma ba karya ransa ya sosu, ta wani ajisu kamar wasu ƴaƴanta tana kora masu kashedi, wlh Sweetie akwai balai'n karfin hali yarinyar nan!.
Sai a lokacin Ronnie ya kula da kamar wani abin ya faru a room ɗinsa bayan tafiyarsu church, amma bai yi magana ba, ya yi shiru bisa umarnin hajiya Sweetie!.
Mirrornsa da ya fashe Black Tiger ya mayar da shi yadda yake, chandelier ta koma mazauninta tamkar bata taɓa motsawa ba, amma a haka Ronnie ya fahimci akwai abin da ya faru a ɗakin!.
Cigaba da bayani Sweetie ta yi kamar haka. "Al-Qur'ani littafi ne wanda Allah ya saukar wa Annabi Muhammad (SAW) ta wurin Mala'ika Jibril. Shi ne kalmar Allah tsarkakakke ba tare da canji ba tun lokacin da aka saukar da shi, kuma ya kasance jagora ga dukan al'umma".
"Injila. Asalin Injila da Annabi Isa ya kawo an saukar da ita ne da harshen Aramaic, wanda shine yaren Annabi Isa. Amma Bible na yau an rubuta shi ne da Greek da Latin kafin a fassara shi zuwa wasu harsuna. Wannan ya haifar da bambance-bambance masu yawa da kara tsaurara banbanjin tsakanin injila da Bible".
"Al-Qur'ani an saukar da shi da harshen Larabci na asali, kuma har yanzu yana nan daidai kamar yadda aka saukar. Wannan yana tabbatar da tsaronsa ba tare da canji ba!".
"Injila ta kunshi wa'azi na Annabi Isa, da alheri, da darussan soyayya, da imani, da sanin girman Allah da ranar kiyama. Amma rubuce-rubucen Bible na yanzu sun haɗa tarihin Annabi Musa, annabawan da suka gabata, da wasikun manzanni da su irin su Bulus, wanda ba sahabi ba ne na Annabi Isa (A.S.) Wannan ya sanya kiristoci suna samun akida mai ɗan rikitarwa".
"Al-Qur'ani ba wai wa'azi kawai ba ne, cikakken tsarin rayuwa ne wanda ke jagorantar Musulmi wajen ibada, mu'amala, siyasa, dokokin shari'a, da zamantakewa, hukunci kan lahira, mutuwa haɗe da kwamciyar kabari, hisabi da dai sauransu. Ya kunshi hukunci masu ma’ana da shawarwari kan dukkan bangarori na rayuwa, Alqur'ani mai girma ya haɗe komai da komai".
"Injila ta asali (Injil) an yi mata canje-canje da yawa bayan Annabi Isa. Bible na yanzu an rubuta shi shekaru da dama bayan barin Annabi Isa duniya, kuma kiristoci suna da nau'o'i daban-daban na Bible, misali, Catholic Bible da Protestant Bible, wanda ya nuna rashin tabbaci kan ainihin littafin, Alqur'ani mai girma shi kaɗai ne babu wani kala daban daban, kai ko suna ba'a sake mashi ba, yana nan a Alqur'aninsa kamar yadda ya sauka!".
"Al-Qur'ani ya kasance tsarkakakke tun lokacin da aka saukar da shi har yanzu, ba tare da wani canji ba. An adana shi a kwakwalwa da rubuce-rubuce daga lokacin Annabi Muhammad (SAW). Wannan ya tabbatar da tsaronsa daga duk wani ruɗani".
"Annabi Isa ya kira mutane zuwa tauhidi, wato bauta wa Allah shi kaɗai a cikin injila ta ainahi Mark 12 verses 29. Amma a cikin Bible na yanzu akwai akidun Triniti (Trinity) da suka bayyana Yesu a matsayin Ɗan Allah ko wani ɓangare na Ubangiji. Wannan yana da saɓani da asalin saƙon Annabi Isa a Musulunci!!".
"Al-Qur'ani yana nan daidai da saƙon tauhidi na Annabawan da suka gabata, yana tabbatar da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Suratul Al-Ikhlas 112. Ya kuma kawo bayani kan matsayin Annabi Isa da sauran annabawa".
"Injila sakon tauhidi ne ga bani Isra'ila daga Annabi Isa, amma Bible na yanzu ya haɗa da bayanan da suka sha bamban da asalin saƙon Allah".
"WANNAN SHI NE BANBANCIN ALQUR'ANI DA INJILA DA KUMA BIBLE INA FATAN KUN GAMSU SOSAI?".
Ta yi tambayar tana rarraba idanunta a kansu. Babu wanda ya iya furta uppan a cikinsu.
Sai dai a lokacin da ta zo wannan gaɓar Ronnie ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi, saboda shi kansa yasan suna da Bible kala daban daban wanda rubuce rubucen cikinsu ma yake kala daban daban! Kamar yadda ta ce akwai Catholic Bible da Protestant Bible, yasan da hakan, so sai ya ji kamar ta ɗan faɗi gaskiya a wannan gaɓar.
Ganin kamar zuciyar Ronnie ta ɗan sanyaya ne yasa ta kara jin kwarin gwiwar zata iya cin nasara a kansu, dan haka sai ta cigaba da bayaninta.
Tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Ronnie ya katseta da cewa. "Shekara nawa ne tsakanin rasuwar annabi isa da kuma bayyanar Bibles na yanzu da kiristoci suka kaddamar a matsayin injila?".
Zaro idanun Floris ta yi haɗe da mamakin Ronnie, ta ji kamar ya gamsu da zancen Sweetie ne.
Sosai Sweetie ta ji daɗin wanna tambaya da Ronnie ya yi mata, dan tana ganin kamar ta fara cin nasara ne, dan haka cikin farinciki da zumuɗi ta amsa mashi da.
"Tarihin rubutun Bible, musamman Sabon Alkawali (New Testament), yana nuna cewa akwai babban tazara tsakanin lokacin da Annabi Isa (A.S.) ya bar duniya da lokacin da aka rubuta kuma aka tattara wannan littafi. Bari dai na yi maku dallah dallah dan ku fahimta".
Kara nutsuwa Ronnie ya yi dan ya saurareta da kyau, da alama zuciyarsa ta fara yarda da maganganunta, dan komai ta faɗa tana kawo hujja mai karfi wanda dole ka yarda, kamar a baya yadda ta faɗi ayayon Alqur'ani da za'a je a duba dan tabbatar da gaskiyarta, hakan yasa ya fara gasgatata.
"A tarihin Kiristanci, ana tsammanin Annabi Isa ya bar duniya, daga hangen nasu an ce an kashe shi, amma a Musulunci ba a kashe shi ba, Allah ya ɗaukaka shi zuwa sama kamar yadda na faɗa a baya. Wannan lamarin ya faru kimanin shekarar 30-33 AD".
AD wato Anno Domini yana nufin bayan haihuwar Annabi Isa ne, BC wato before Charist yana nufin kafin zuwan Annabi isa duniya kenan, to shekarun ake kira da BC, bayan zuwansa kuma AD.
Cigaba da bayani Sweetie ta yi cikin sani da kuma kwarin gwiwa. "Bayyanar Sabon Alkawali (New Testament). Rubuce-rubucen farko na Sabon Alkawali, waɗanda aka ce wasikun Bulus ne (Paul), sun fara bayyana kusan shekaru 20-30 bayan ɗauke Annabi Isa daga duniya da Allah ya yi, kimanin shekarar 50 AD bayan zuwansa duniya kenan".
"Injiloli guda huɗu ko in ce Bible ɗinkuna yanzu guda huɗu wato Matthew, Mark, Luke, John. An rubuta su kusan daga 60 AD zuwa 110 AD. Injila na Markus wato Bible mark ana ɗaukar shi mafi tsufa, an rubuta shi kusan shekarar 60-70 AD. Sauran injiloli (Bibles) suna tafe daga bayansa".
Izuwa yanzu jikin Ronnie ya yi sanyi, saboda jin yadda take zayyano tsawon shekaru baya, ko mai san zuciyar mutum ya ji wanna bayanai nata dallah dallah sai ya san gaskiya take faɗi, sai dai idan yaki aminta da hakan dan san zuciyarsa ne! Amma irin wanna shekaru da take ambata ai babu karya!.
"A lokacin shekaru 325 AD bayan haifar Annabi Isa kenan, a taron Council of Nicaea, a karkashin Sarki Constantine, aka fara tsara da tantance irin waɗanda za su shiga cikin Bible na yanzu, kuma wannan ya ƙarfafa canje-canje na ra'ayi da tsarin Kiristanci, kun dai ji Bible naku na yanzu sarakunar da ne suka shirya abubuwan da za'a rubuta a ciki, so ni nasan ba laifinku bane zamanku kiristoci, laifinku a nan shi ne rashin faɗaɗa bincike da neman sanin gaskiya bayan Allah ya baku dama da baku yi na shi ne laifi, kun dogara da littafi guda ɗaya wanda tsara maku shi aka yi ba zancen Allah bane!".
"Injila ta gaskiya da Annabi Isa ya kawo ta ɓace na tsawon lokaci, hakan yasa saƙon Allah bai isa ga mutanen yadda yakamata ba. Wannan ne yasa Allah ya saukar da Al-Qur'ani Mai Girma don ya zama tabbataccen jagora wanda ba zai taɓa sauyawa ba, wasu gungun kafurai sun jima suna shuka tsiya da rashin son gaskiya a duniya, amma Allah ba'a yi mashi wayo, da suka ɓatar da injila ta gaskiya sai ya sauko da Alqur'ani wanda wane mutun ya iya canza rubutun cikinsa, karya mutum yake, tsawon shekaru har yau yana nan yadda aka sauke shi!!".
Ta kai karahen maganar idanunta a kan Ronnie tana kuma sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai fatan take yi Allah yasa su gane gaskiya.
Floris ta rasa abin faɗe, sai idanu kawai take binsu da shi, ta ji abin da ya girmewa shekarunta.
"Shin kana da wata tambaya dan kara tabbatar da gaskiya ta da gaskiyar addinanina ne ko dai ya isa haka?".
Ta jefawa Ronnie tambaya idanunta a kansa.
Zuciyarsa ta gama yarda da zancenta dikka, amma dik da haka dan kara tabbatarwa sai ya ce.
"Shekara nawa Annabi isa ya yi a duniya.............. and tare da mahaifiyarsa ya yi rayuwa? Sannan akwai wani dalilin da yasa bai yi aure bane?. And ya rayuwarsa ta kasance a cikin al'umma a lokacin da ya bayyana bai da uba? Ya fisakanci kyara ko tsangwama ne daga mutane? Ko dai a addininki Annabi isa yana da baba ne ɓoye mana aka yi kamar yadda aka canza mana komai?".
Ta ji matuƙar daɗin jin wanna tambaya tasa, ranta ya yi sanyi sosai.
With full confidence ta ce. "Tarihin Musulunci da Kiristanci ya nuna cewa Annabi Isa (A.S.) ya rayu a duniya na kimanin shekaru 33 zuwa 34 kafin Allah ya ɗaukaka shi zuwa sama. Wannan yana nufin bai mutu ba a hannun mutane, kamar yadda Musulunci ya bayyana Surat An-Nisa shafi na 4 aya na 157-158 Allah ya yi wanna bayani".
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗaura da cewa.
"Annabi Isa ya taso ne a ƙarƙashin kulawar mahaifiyarsa, Nana Maryam, wacce Allah ya zaɓa kuma ya tsarkake ta daga zunubi. Ya zauna tare da ita yayin ƙuruciyarsa har lokacin da ya fara wa'azinsa. Mahaifiyarsa ta kasance ginshiƙi da gatansa, musamman ganin cewa ba shi da uba".
Ronnie fa ya ji abin da bai taɓa ji ba, ga shi maganganunta dai ba zasu karyatu ba, shi kansa yasan gaskiyar take faɗe, saboda idan ba gaskiya bane taya tana karamarta haka ace zata tsara irin wanna dogon karya? Ai ba zata taɓa yiwuwa ba.
Cigaba da bayani ta yi. "Dalilin da yasa bai yi aure ba, Allah ya aiko Annabi Isa (A.S.) da takamaiman manufa, isar da saƙon tauhidi ga Bani Isra'ila da warkar da zukatansu daga zalunci da ruɗi. Rashin yin aurensa ba tare da shakka ba ya haɗu da wannan manufar, don ya mai da hankali kan aikin annabci ba tare da wata tangarda ba!".
"Al'ummar da Annabi Isa ya fito daga cikinta tana cike da tsangwama da adawa ga saƙon Allah, kuma rayuwarsa ta kasance cike da ƙalubale. A irin wannan yanayi, yin aure ba zai yiwu ba, domin tsangwamar mutane za ta iya shafar iyalinsa idan ya kasance da su".
"Allah yana aikawa da annabawa tare da yanayi daban-daban, don su zama abin koyi ga al’umma. Rashin aurensa wata hanya ce ta nuna cewa rayuwa mai cike da ibada da sadaukarwa na yiwuwa ba tare da iyali ba, musamman idan mutum yana da babban aiki na isar da saƙon Allah".
A dai'dai wanna gaɓa Ronnie ya samu karin haske sosai, wato hikima ta Allah tana da yawa, rashin yin auren Annabi Isa wani haske ne ga al'umma. Nan take ya kara jin lallai wannan Allah da Sweetie take magana a kansa shi ne Ubangiji na gaskiya.
Cigaba da bayani Hajiya Sweetie tamu yarinya ƴar baiwa mai cike da ababen ban mamaki ta yi.
"Rayuwarsa a cikin al’umma lokacin da ya bayyana ba tare da uba ba. Fitowarsa ta musamman ce, Annabi Isa ya fito cikin mu'ujiza rashin uba........ Wannan lamari ya haifar da jita-jita daga wasu mutane, suna zargin mahaifiyarsa Maryam da aikata abin da bai dace ba. Amma Allah ya kare Maryam da Annabi Isa ta hanyar da ya sa Annabi Isa ya yi magana tun yana jariri, cikin Surat Maryam shafi na 19 daga aya ta 29 zuwa 34. Wannan mu'ujiza ta tabbatar da tsarkin mahaifiyarsa da cewa shi annabi ne daga Allah".
"Wasu daga cikin Bani Isra’ila sun karɓi saƙonsa saboda sunga mu'ujizarsa da kyawawan halayensa. Amma yawancin shugabannin addini da manyan masu mulki a lokacin sun tsangwame shi saboda ya ƙalubalanci mulkinsu da karairayinsu, so sai suka yi ƙoƙarin karyata shi a idan duniya, suna ƙara yaɗa jita-jita kan asalinsa (ba tare da uba ba), wanda ya kasance babban kalubale ga rayuwarsa a cikin al’umma".
"Duk da tsangwama, Annabi Isa ya kasance mai rahama, tawali’u, da juriya. Ya yi wa mutane wa'azi, ya warkar da cututtuka, ya kawo zaman lafiya, kuma ya ci gaba da kira ga bauta ga Allah Shi kaɗai, ya jure ya kuma cije".
"So a takaice Annabi Isa ya fuskanci tsangwama sosai daga shugabannin addini na Yahudawa, waɗanda suka yi ƙoƙarin halaka saƙonsa saboda yana yi musu tsawa kan zaluncinsu!. Amma talakawa, marasa galihu, da masu buƙatar taimako sun karɓe shi, suna girmama saƙonsa na tausayi da gaskiya, a iya nan zaku iya gane cewa Allah Ubangijin talikai shi ne Allah na gaskiya, dan shi ne mai jin ƙan bayinsa, ya umarci annabi isa da ya wanzar da adalci, ya daraja kaskantattun bayin da aka kaskantar, waye zai yi maku wannan idan ba mahaliccinmu na gaskiya ba? Ko malamanku sun taɓa kwatanta maku irin hakan ne?".
Ta jefa masu tambaya tare da tsayar da idanunta a kan Ronnie ta kuma dakata da yin magana tana jiran su bata amsa.
Dik cikinsu babu wanda ya iya buɗe baki ya yi magana, dik ta sare masu gwiwa ta kuma sanya sun ji zuƙatansu ya fara karaya da addinin Kiristanci, sun ji sun kwaɗaitu da san Allah da take ambata mai adalci da kuma jin kan bayinsa, ga tausayawa marasa gata, tabbas zuƙatansu sun ji tausayin hakan matuƙa, sai dai da kamar wuya Black Tiger ya bar hakan ta cigaba da yin tasiri a zuƙatansu, saboda kada ku manta jinin kiyayya haɗe da yakar addinin musulunci yake gudana a cikin jikinsa, burin babansa kenan kafin ya bar duniya, kada ku manta babansa ya kaddamar da Duniyar shaiɗanu, kunga kuwa raya Musulunci a cikin Black world abu ne wanda yiwuwarsa tana da matuƙar wahala!!.
Floris baki ya mutu, ta rasa abin faɗe, saboda ta ji tsagwaran gaskiya.
"Ronnie ku bani amsata, shin a cikin malamanku akwai wanda yake faɗa maku da kuji tausayin na kasa da ku? Ku kyautatawa marasa shi, ku taimakawa gajiyayyu marasa karfi, ku jikan mata da yara?! Akwai waɗan da suke gaya maku hakan?".
A karo na biyu bai amsa mata ba, binta da kallo kawai yake yi dan yasan ba'a taɓa gaya masu hakan ba, sai dai tongue nasa ta mashi nauyi ta yadda ya kasa amsa mata. Idanunsa sun yi jajir kamar wuta, kamar ba lafiya ba.
Ganin haka yasa Sweetie ta kawar da tambayar da cewa. "Akwai wani tambaya da kuke san sake yi mun dan tabbatar da gaskiya?".
Jinjina mata kai Ronnie ya yi, da kyar ya iya furta.
"A cikin malamullah ɗinku (Alqur'ani mai girma) a wace sura da wace aya ce Allah ya umarci annabi Isa da ya yi magana a lokacin da yake jariri? And a wace aya da wace surace Allah ya umarci mahaifiyarsa Maryam da ta yi azumin magana?".
Nisawa Sweetie ta yi kafin ta ce. "A cikin Al-Qur’ani Mai Girma, Allah ya yi bayani kan waɗannan abubuwan biyu a Surat Maryam, inda aka kawo lamarin Annabi Isa (A.S.) da mahaifiyarsa, Maryam a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya na 29 zuwa na 33".
"Lokacin da Nana Maryamu ta haifi Annabi Isa, ta damu sosai game da abin da mutane za su ce game da ita. Sai Allah ya umarce ta da ta yi azumin magana (wato ta yi shiru kuma kada ta ce komai ga mutane), domin Annabi Isa zai yi magana da kansa don ya bayyana gaskiya. Wannan umarni yana cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya na 26".
"Lokacin da ta dawo cikin mutane da jariri goye a bayanta, sai suka fara zarginta suna ƙoƙarin cin mutuncinta a kan ina ta samu yaro? A lokacin sai ta nuna masu shi goye a bayanta ba tare da ta yi magana ba, har sun fara yi mata izgili da iyashege suna dariya a kan ta ya za'ayi su yi magana da jariri?!".
"Kwatsam ba zato ba tsammani cikin umarnin Allah Annabi Isa ya buɗi baki a in da ya ce. Lalle ni bawan Allah ne, Allah ya ba ni Littafi, kuma Ya sanya ni matsayin Annab, ya albarkace ni, kuma Ya yi wasiyya da ni game da salla da zakka matuƙar ina da rai, kuma ni mai kirki ga uwata ne, bai sanya ni mai girman kai ba, ni annabi ne ba kamar yadda kuke tunani ba, aminci ya tabbata a gare ni a ranar da aka haife ni, da ranar da zan bar duniya, da ranar da zan tashi da rai".
(Fassara maku ayar fa na yi dan ku ji me annabi Isa ya faɗa time da ya yi magana a jaririnsa.)
"Ina san wanna Alqur'ani dan na duba wanna aya da kuma sura da kika faɗa". Cewar Ronnie kenan.
"Tabbas in na bar wannan gari na koma forest zaka zamu Alqur'ani a wajena, yanzu dai babu yana wajen Pretty".
Floris ce ta katsesu da cewa.