Showing 216001 words to 219000 words out of 403653 words

Chapter 73 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

57

ne to hakan ne babu shakka a wannan al'amari".

Kirjin mama and Mammie ne suka bada dum dum da karfi!!. Hankalinsu ne ya kara tashi, lokaci guda suka fara haɗa gumi, momma ta jiƙa masu aiki, mama kam kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Ta ya aka yi ya zama ɗansa shi ne zaki yi mana bayani!".

Momma bata bi ta kanta ba ta cigaba da cewa. "Dama ba mutuwa ya yi ba, a lokacin da ka kafe lallai sai na dawo maka da shi, na yi magiya kaki saurarona, dik kunki fahimtata, kun ki fahimtar abin da nike faɗe, har daddy a wannan karan bai fahimceni ba, su Yah Rahab kowa yaki fahimtata, Yah Muhammad ne kawai ya iya fahimtata, a wannan lokacin ne dan Omerish ya tsira da ransa ya kuma rayu sai muka haɗa baki da Yah Muhammad a kan mu shirya maka ya mutu sai ya tafi da shi kasar France in da babu wanda zai sake ganinsa domin ya rayu............"

Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani tsawa da Akka ta daka mata. "Rahilarh dama ba gaskiya bane mutuwarsa? Amma kika jefamu cikin tashin hankali? Kina ji kina ganin mahaifinsa ya rinƙa ciwo kaman zai mutu dalilin mutuwarsa, amma kika share kamar babu zuciyar tausayi a kirjinki, e lallai".

Kasa da kai momma ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Goggo ki yi hakuri, wlh a kullum ina kukan ciwon da Yah Zuhair yake yi a kan mutuwar Omerish, na shiga damuwar da ban taɓa shiga ba, har na karaya na yanke shawarar zan dawo da Omerish in yaso a kashesa da gaske kowa ya wuta, amma Yah Muhammad ya ce a'a in daure komai zai wuce, wlh goggo ina tsananin san Omerish shiyasa na yi hakan, amma dan Allah ki yafe mun, kai ma Yah Zuhair ka yafe mun, nasan na yi kuskure............"

Wai me ya faru a baya ne da yasa har aka so kashe Omerish ɗin?. To mu je dai zuwa, wanda zata bada labarin abin ya faru a baya bata bayyana ba tukun nan, idan ta bayyana zaku ji komai.

Katse mata magana King ya yi da cewa. "Kin cuceni Rahilarh, kin cuceni wlh". Yana kai karshen maganar ya miƙe da sauri saboda wani irin zafi da zuciyarsa take yi mashi, yasan zai iya faɗuwa a wajen idan ya cigaba da tsayawa saboda zafin zuciya.

Bedroom ɗinsa ya shiga da sauri yana huci, da sauri momma ta miƙe ta bi bayansa, Aunty MieMie ce ta yi saurin sake miƙewa ta rufa mata baya. Nan fa parlon ya koma kallon kallo, su Mammie da suka san abubuwan da suka faru a baya sun gane kan maganar da momma take yi, su kuma su Sarina da basu san tarihin baya ba sai basu gane kan maganar momma ba bayan cewa Smart ɗan King ne.

Bari in kara maku wani haske kaɗan kafin mu wuce gaba. Tabbas Smart ɗan King ne, kuma shi ne babban yayansu, ya fi su Ramish dikka.
Ya aka yi ya fi su Ramish?. Mu je dai zuwa, kada ku manta ita ma mummyn Chuchu tana da babban yaro da ya fi Ramish amma ya rasu, kada ku manta na faɗa maku hakan a baya.
Akwai wani abin da ya taɓa faruwa a kingdom ɗin a lokacin da momma ta haifesa bai wuci kwana uku a duniya ba, so a lokacin momma ta gudu Dubai ba tare da sahalewar King ba, saboda ta ce zata tafi ya hanata, ita kuma tana ganin ɗanta zai mutu ne idan tana Kingdom of power, shi ne ta gudu bai sani na.
Time da ta koma Dubai, ta yi ta yi ta zauna iyayenta suka ki yarda saboda King ya ce bai aminta ba, ya ce ta dawo, ta yi ƙoƙarin yi masu bayani a kan in ta koma tabbas ɗanta zai mutu, amma suka ki fahimtarta, hakan yasa ta yanke shawarar shirya masu cewa Smart ya rasu. Ta kuma yi nasarar yin hakan tare da taimakon yayanta wato daddyn Smart na Faransa kenan, sai da kowa ya aminta da Smart ya mutu, sannan daddynsa ya tafi da shi France.

Momma bata taɓa yin kwana biyu bata yi video call da yayan nata ta ga ɗanta ba, hakan yasa Smart ya tashi da sanin ita ce mahaifiyarsa, yana yawan tambayarta ina daddynsa, kullun sai ta ce mashi sai ta zo ɗaukarsa zata zo tare da daddynsa. Time da ya kai 20 years sai ya matsa mata a kan lallai yana san ganin daddynsa, a lokacin ne ta kira shi video call ta juya camera ta shiga ɗakin King, so a lokacin ya fara sanin daddynsa shi kuma King bai lura da video call take yi ba, so bai ga ɗan nasa ba, da yake yayan momma ɗin yana yi mashi komai yasa bai damu da yazo ga iyayensa ba, dan suma sun ɗaukesa kamar ɗa dama Allah bai taɓa basu haihuwa ba.

Kun ji a in da Smart ya samo kamanninsa da daddynsa na France ko? Daddyn nasa yayan momma ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya wato King Badeen kenan, kunga dole a samu kamanni ai.

Shi kuwa daddyn nasa tun yana yaro ya tafi kasar France, a can ya yi karatu ya kammala, har ya samu aiki sannan suka fara soyayya da mom ɗin Smart ɗin, suka yi aure, a dalilin haka ya samu takardar ƙasa ya zama ɗan ƙasa har ya iya shiga siyasarsu.

Momma kuwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen nunawa Smart ƴan uwansa gabaɗaya, dan bata san kan ƴaƴanta su tashi a wargaje, tana san su tashi kansu a haɗe, su kaunaci juna, ta kuma yin nasarar samun hakan, tabbas sun tashi cike da kaunar juna dikkansu, sun san juna.

Sai dai shi kuma Smart ba iya kannensa kawai ya sani ba, a lokacin da ya girma ya gama karantu sai ya fara bincike a kan ƴan uwansa, a nan ne ya san su Ramish dikka, dik kuma yana kau taimakawa su Ramish a bakin aikinsu sosai, domin dayawan lokuta da taimakonsa Ramish yake samun karin girma har ya zo matsayin da yake, amma su basu san shi ba, kuma basu san yana taimaka masu ba.

In short shi ne ma ya binciko in da Jaish yake time da ya ɓata, sannan ya turawa Ramish address ɗin, so dik abin da suke yi yana gani kuma yana sane da su, momma take hana shi zuwa ga kingdom of power, ta ce ba yanzu ba sai ya kara girma, dan tsaro.

Harta gidan Smart dake France in da yake yawan zama in ya bar gidan daddynsa, wannan gida da sunan Zunaira ya ginata, gidanta ne da ya mallaka mata, yana da nasa na daban, ya zaɓi ya rinƙa zama a nata ne kawai, yanzu haka yana nan yana kan bincike a kan masu nikaf dan ya taimakawa Ramish ba tare da sanin kowa ba, shi ɗin garkuwan gabaɗaya familyn marigayi King Abdul Malik ne, dan yasan kowa su ne basu san shi ba, kuma yana taimaka masu ta hanyoyi daban daban wanda mutum ba zai taɓa zata ba idan dai ba faɗa mashi aka yi ba.

Jama'a nace ku zo mu haɗu mu tsinewa tsafi, tsafi karyar banza ne da na wofi, idan ba karya ba ne meyasa dik tsafin Mammie bai iya gane mata Smart ba? Meyasa ta kasa iya gane cewa yana raye har ma ya girma? Kullum sai dai ta kare a hasashe shegiya, karyar banza da wofi, wlh idan mutum zai koma ga Allah ma da ya fi mashi, tsafi dik surkullen banza ne shegu.

Wannan dalilin yasa kuka ga Smart and his dad musulmai ne, saboda dad ɗinsa yayan momma ne, balarabe ne, mom ce baturiya kuma krista, kuma tana da kyan hali, dan ita ta makale lallai tana san daddy.

To in short dai kun ji yadda labarin Smart ya kasance ko? Nasan a iya wannan bayanin kun fahimci in da na dosa, ba zan tsaya dogon bayani sosai ba, dan akwai labari a gaba sosai, gaba zaku ji karin bayani dai. Mu cigaba da labarinmu.

••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

Tsaye momma ta isko King a tsakar ɗakinsa, sai huci yake yi, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci, zuciyarsa sai tafasa take yi, momma bata kyauta mashi ba, tasa Smart ya taso baya ganin girmansa, bai ma san shi ba, wannan ai zalinci ne.

Da alama King ya samu ɗan da zai iya sanya shi ya gane yadda zafin kaunar ɗa yake da yasa commander Zafar ya hukunta ɗansa ɗaya tilo a duniya, dan ga dikkan alamu King yana tsananin kaunar Smart over, dan shi ne first born ɗinsa, har ciwo ya kwanta lokacin mutuwar Smart na karya da momma ta shirya. Wato fa idan Allah ya tashi kama mutum wlh baka isa ka iya canka ta wace hanya zai kamaka ba, ga shi dai cikin ruwan sanyi ya kama King bama aje da nisa ba, zakuwa muga yadda wannan cakwakiya zata kaya.

A gabansa momma ta zube gwiwowinta a ƙasa, cikin sigar ban hakuri ta ce. "Dan Allah ka yi hakuri Yah Zuhair, wlh ban yi abin da na yi dan na cutar da kai ko wani abin makamancin hakan ba, na yi ne kawai saboda san da nike yi wa Omerish, ba zan iya jurar rashinsa ba, kuma kai da kanka ka shaida da tabbas zai iya mutuwa a wannan lokaci, ba kai da kanka daga baya ka ce in dai'na haihuwa a nan in rinƙa komawa Dubai in haihu a can ba? Kaga da ban yi mashi hakan ba da mutuwa zai yi, kana ganin yadda Jaish ya tsira da kyar fa, kasan komai, dan Allah ka mun afuwa ka ji?".

"Kin cutar dani Rahilarh, cuta mafi munin da ba zan taɓa mantawa da shi ba!! Ki duba yadda ɗana ya taso, ya taso cikin kafurai, bai san darajar manya ba, ki kalli yadda yake magana da ni tamkar ɗansa ne ni, gaskiya kin cuceni". Cikin zafi ya yi maganar, bai taɓa shiga ɓacin rai irin na wannan rana ba, abin da ciwo matuƙa wlh, dan ma tana matsayin ƴar kawunsa ne, kuma Akka na bala'in kaunarta, da wlh sai ya hukunta hukunci mai zafin gaske.

Aunty MieMie da take binsu da kallo ne ta samu waje saman sofa ta zauna, bata taɓa kallan daddynsu a cikin irin wannan yanayi ba, gaskiya ko mafarki ta yi akwai ranar da zata zo King da momma su samu gagarumin matsala irin wannan idan ta tashi daga wannan mafarki sai ta yi sadaka kuma ba zata taɓa yarda da hakan ba, sai ga shi a zahiri ya faru, ita dai tasan sosai King yake bala'in san momma.

Mummyn Chuchu da ta shigo tun ɗazun ne ta matso tare da rike Momma dake durkushen tana ƙoƙarin faɗuwa, ƙoƙari buɗe baki ta yi dan ta taushi King.

Cikin zafa ya ɗaga mata hannu alamar baya da buƙatar jin komai daga garesu, infact su fita mashi a ɗaki baya san ganinsu. Ganin ya ɗauki zafi sosai hakan yasa mummy ta miƙar da momma tare da ce mata. "Rahilarh ki yi hakuri mu je, zuwa da safe idan ya huce sai muyi magana ko?".

Hawaye sosai momma take yi, dan ita kanta tasan bata kyautawa King ba, haba wani irin zalinci ne wannan? A lokacin da ya samu labarin rasuwar Smart yana zaune a saman kujerar mulkinsa sai da ya miƙe tsaye, bai san lokacin da ya cire crown ɗinsa daga kansa ba, ya jijjiga sosai, kwana uku bai fita fada ba yana jinyar zuciyarsa, da taimakon Allah da addu'ar iyaye da abokan arziki ya samu zuciyarsa ta iya ɗaukar wannan kaddarar, shi ma ya kusa mutuwa, ashe dik shirin momma ne, gaskiya abin akwai ciwo, babban abin da ya fi kona ran King ma shi ne yadda Smart bai ɗaukesa da daraja ba, yanayin tarbiyarsa kaf ta sha banban da tarbiyar jikokin Akka, dik ya damesu a komai ya shanye, King ya yi takaicin hakan matuƙa.

Waje gabaɗayansu suka fita, suka kyale King shi kaɗai a cikin ɗakin yana ta huci. A bakin kofa mummyn Chuchu ta tsaya ita da Aunty MieMie suka hau sharewa momma hawaye suna tausanta har sai da ta yi shiru, sannan suka rakata ɗakinta.

A parlour kuwa kowa ya yi mutuwar zaune da jin abin da momma ta faɗa, su uncle Abbas an rasa abin faɗe, Akka kuwa ta kara ɗaukar zafi, abin ya bakanta mata rai, momma ta yi masu ba dai'dai ba, a fusace ta miƙe ta nufi part ɗinta domin ta je ta kira Husaininta wato King Badeen ta sanar da shi abin da ƴaƴansa Momma da baban yayanta wato daddyn Smart suka aikata.

Da sauri Dr Raj ya miƙe ya bi bayan Akka, a cewarsa kada ciwon zuciyarta ya tashi ta sume, bari ya yi saurin bin bayanta......................... Sarina kuwa, dik abin da ake faɗa baya shiga kunnuwanta, hankalinta na'a kan Smart, sai kallansa take yi kamar zata cinyesa da ido, taga kyau iya kyau, tini ta yi rantsu da Allah ga mijinta nan ya bayyana.

Mammie ma alkawari ta yi wa kanta a kan lallai ne wannan shi ne mijin Sarina, dama ta ce first born na King yarta zata aura, to ga shi ya bayyana.

Uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka yi gaggawar bin bayan Akka da Dr Raj. Miƙewa Jaish ya yi tare da cewa Smart ya zo su je part ɗinsa ya kwanta ya huta zuwa da safe zasu sake zama, dan case bai kare ba, yanzu ma aka fara.

Jawad da shi ma already ya san da Smart saboda shi ɗin kamar ɗan momma yake, shi ma miƙewa ya yi tare da riko hannun Chuchu yana faɗa mata ta tashi su raka Yah Omerish part ɗin Jaish kafin su dawo su tafi nasu dare ya yi.

Smart rike da hannun guyson and Auta da ta yi shiru ya miƙe tsaye, Jaish ya yi gaba ya rufa mashi baya. Miƙewa Obaid and Omaid suka yi, har zasu wuce su fita Omaid ya juyo da kallansa a kan Sarina, ƙasa ƙasa ya ce. "Aunty Sarina kinga Yah Omerish ɗin yanzu ko? Ko dai har yanzu a mafarki kika san shi?".

Ta fahimci gatse ya yi mata cikin maganar, amma sai ta danne ta ce e ta gansa, a cikin zuciyarta kuma mamakin Omaid take yi, dan lokacin da tambayesu wanene Omerish shi Omaid bai yi magana ba, ya yi ma kamar bai jita ba, ashe ya ji ɗan kaniya, rashin kunya yasa ya yi banza da ita.
Wucewa suka yi suka nufi waje abinsu. Mammie ce ya miƙe tana cewa Sarina su tashi su tafi dare ya yi. Miƙewa suka yi suka fita, parlourn ya rage mama, uncle Taheer da kuma Aneesa, mama ta gaza motsawa daga in da take zaune, tamkar ruwa ya cinyeta, ta rasa ganewa kanta, momma ta rusa mata plan, a ranta ta kuduri niyar wlh ba zata hakura ba, ba zata bari ba gaskiya, sai ta ɗauki mataki.

Bedroom dake kusa da nasa Jaish ya kai Smart, cike da kauna ya ce mashi. "Yah Omerish wannan bedroom ɗin ya yi maka ko dai na canza maka wani?".

Hannu Smart ya ɗaga mashi bayan ya saki hannun guyson, sannan ya ce. "Is okey, Omar ku zauna bari in yi take bath ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sake hannun Auta. Juyo da kallansa a kanta ya yi, cikin sigar rarrashi ya ce. "Sorry our baby, daddy sai ya biya wannan marin da ya yi maki, bari Allah ya kaimu wayewan gari kin ji?".
Ya yi maganar yana ɗan shafa kumatunta in da shatin hannun King suka fito ruɗu ruɗu.

Kai ta jinjina mashi tana kara shagwaɓe fuska.
"Hau saman bed ki kwanta ina zuwa". Ya faɗa yana nuna gadan da hannunsa. Ba musu ta haye har lokacin tana ɗan sauke shessheƙar kuka a hankali hankali.

"Yah Omerish ni ma bari in je in yi wanka sai in sa a kawo maka abinci". Cewar Jaish.
Jinjina kai Smart tiger ya yi, kafin ya ce. "No need anything now, ka dai je ka yi wankarka, ba sai kasa an kawo mun komai ba". Ya kai karshen maganar tare da ɗan rungumar Jaish ɗin kamar yadda suka saba a al'adarsu ta France, sannan ya nufi toilet.

Matsawa kusa bed ɗin Jaish ya yi, cike da kauna ya kara rarrashin Auta da guyson kafin ya wuce ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin. Yana fita kai tsaye nasa bedroom ɗin ya nufa. Wani irin daddaɗar kamshi na daban ne ta dokin hancinsa ba wanda ya saba ji ba, alamar an canza mashi room freshener kenan. Shakar kamshin ya yi haɗe da ɗan lumshe idanu, alamar kamshin ta ratsa shi sosai, akwai daɗi kam.

Mamaki ya yi a kan waye ya canza mashi room freshener kuma?. A bakin bed ya zauna tare da rage kayan jikinsa, short and singlet kawai ya bari a jikinsa, miƙewa ya yi ya nufi toilet yana tinanin wannan cakwakiya na.

Tura kofar toilet ɗin ya yi tare da yin addu'ar shiga ya sanya kansa. Tura kofar da ta ji anyi ne yasa ta juyo a miliyan dan taga wenenen? Tana tsaye a gaban jacuzzi wajen shower, ta kunna ruwa ta cika boket tana wanka, dan ita bata san shiga cikin jacuzzi, tafi yarda da ta tara ruwa a boket sai ta yi wankanta.

Ta gama sanya kumfar sabulu a gabaɗaya jikinta ta juyo gatesa. Ɗan zaro mata idanunsa ya yi yana binta da kallo kamar ba shi ne ya ce kada ta bari su sake haɗuwa ba, ya ga kaya ɗan rainin wayo, dama da guntun jarabarsa ta kwanaki uku da suka wuce da ya sameta tana barci a parlournsa, to bai gama watsakewa daga wancan bama sai ga shi yau ya sake yi babban kallo wanda da wuya ya iya tsallekawa ko kuma ya ce zai kwantar da wannan tarzoma dake shirin tashi

Saboda da alama abar ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login