Showing 219001 words to 222000 words out of 403653 words

Chapter 74 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

88

motsa. Kasa gaba ya yi ya shigo cikin toilet ɗin, ya kuma kasa yin baya ya fita, ya tsare yar mutane da ido, yasata jin kunya in ban da rashin kunya irin na jikokin Akka.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



Love page, yauwa kwana biyu mun sha gwagwarmaya sosai, to yau kam bari mu ɗan yi nishaɗi mu leƙa duniyar masoya kafin mu ɗaura da surprises ɗinmu.


Ita kuwa tana ganinsa ta saki kara tare da juya mashi baya. Ɗan ɗaure fuska ya yi tare da jan siririn tsaki, wai irin shi zai basar kada a rai'na shi ɗin nan, sai ya wani tsare gida, cikin dakiya ya ce. "Ke bana ce kada ki bari mu sake haɗuwa ba?". Yana maganar kuma yana karewa halittar jikinta kallo dan tabbatar rashin kunya irin na jinin Akka.

Shiru ta yi, ta ƙasa amsa mashi, ji ta yi tamkar ta nitse ƙasa saboda kunya. Wani siririn tsaki ya sake ja kafin ya juya da sauri ya fice yana haɗiyar yawu, wai shi a dole zai basar ya danne.

Saman bed ɗinsa ya haye ya kwanta, janyo wayarsa ya yi domin ya ɗan rage lokaci kafin ta fito. Sai dai kuma yana taɓa wayar tamkar ya kunnawa ƙwaƙwalwarsa tinaninta ne, gabaɗaya ya nemi sukuninsa ya rasa, har wani zufa ne ya fara keto mashi a gefe da gefen face ɗinsa, gabaɗaya a matse yake amma ya nuna zai danne hakan.

A hankali ya jefar da wayar tasa ba tare da ya farga ba, wasa wasa ya ɗan fara juyi a saman bed ɗin ƙwaƙwalwarsa na kara tinano mashi kyan surar jikinta, ga shi sai glowing take yi, hasken fatarta ya ƙara fitowa sosai, har wani yellow yellow ta yi. Haba tini notikan ƙwaƙwalwarsa suka fara kwancewa.

A haka ta fito ɗaure da towel ɗinsa a kirjinta ta same shi, yana jin motsin fitowarta sai ya danne juyin da yake yi, ya kwanta ya kifu tsit kamar wanda ya yi barci, ɗan rainin wayo kuma abar tana damunsa sosai, amma wai irin kada ta rainasa ɗin nan, sai ya dake.

Ita kuwa baiwar Allah, bata wani kallesa sosai ba, saboda kunyar babu kaya a jikinta, da sauri ta shiga dressing room dan ta shirya.

Yana ganin ta shiga ya yi saurin miƙewa ya nufi toilet wai dan ma kada ta dawo ta same shi a haka har ta gane halin da yake a ciki, sai ya gudu cikin toilet yana matse bananar tasa dan ya samu sauki.

Cikin ɗaya daga cikin kayan da momma tasa mama Haulat ta kawo mata na barci ta shirya. Ta yi wani irin kyau da in dai namiji lafiyaye ne ya ganta to fa ba zai iya hakura ba. Hijabin da take sallah ta ɗauka ta ɗaura a saman kayan, sannan ta fito ta nufi part ɗin momma dan ta ɗauko mashi cappuccinon, Allah sarki sam bata gajiya da kyautata mashi dan tana san kayanta, shi kuma sai sinki sikin iskanci da iyashege cike da ƙwaƙwalwarsa.

Mama Haulat ce kullum take kara karfafa mata gwiwa a kan ta cigaba da matsar da kanta a garesa tabbas watarana zai waiwayeta, shiyasa kuka ga har yanzu take shiga bedroom ɗinsa bata dai'na ba, ita kuma Chuchu tana kara koya mata yadda zata narka zuciyarsa a soyayyarta, yanzu ta ɗauki darasi sosai abinta, jira take yi kawai wani abin ya haɗasu yaga zallar madarar soyayya.

Allah sarki momma uwa ta gari, dik da tana cikin damuwa a kan abin da ya faru a tsakaninta da King, hakan bai hanata ta shiryawa ƴaƴanta abin da suke so ba, ta shiryawa Jaish and Omerish cappuccino kamar yadda suka saba sha a kowacce dare kafin su kwanta.

Mahnoor tana zuwa ta ɗauki cappuccinonsa kamar yadda ta saba, a lokacin momma tana cikin toilet tana wanka dan ta koma wajen dearlyn love ɗinta ta rarrashi kayanta......🤭👀

Bata tsaya jiranta ba ta ɗauki cappuccinonsa ta fito. Har lokacin da ta koma bedroom ɗin yana cikin toilet bai fito ba....... Wai me ya tsayar da Jaish a cikin toilet ne?........👀🥱

Ɗan ƙaniya yana can yana ƙoƙarin controlling na kansa ya haɗiye kwaɗayinsa ya danne abar gadon, sai dai ya gaza iya yin hakan, sai ma kara tashi hankalinsa yake yi ta sanadiyyar tinano mashi surarta da ƙwaƙwalwarsa yake ta yi, dik ya kiɗime, abin tausayi kuma abin dariya.
Saman table ta ɗauka cappuccinon, sannan ta ɗauko perfume da Chuchu ta bata mai sanyin kamshi ta feshe jikinta da shi. Kamar zata fice waje izuwa bedroom ɗinta, sai kuma ta tina da kalaman mama Haulat da kuma Chuchu ɗazun in da suke ce mata ta dai'na kwana a wani waje in ba a saman bed ɗinsa ba, komai zai ce mata kada ta damu ta daure watarana zai wuce kuma zata yi nasara.

Tina waɗan nan kalaman yasa ta cire hijabin jikinta ta mayar da shi d-room ɗinsa, sannan ta dawo ta haye saman bed ɗin, kwanciya ta yi haɗe da rufe idanunta tana tinanin abin da zai faru idan ya fito ya sameta kwance a saman bed ɗinsa.

•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A gefe guda kuwa, Dr Raj da ya bi Akka yaga babu wata matsala, ga kuma su uncle suna tare da ita, sai ya yi saurin ficewa daga ɗakin, dan dik hankalinsa yana a kan yarinyar da suka yi karo ɗazun. (Zee) Burinsa kawai ya sake sanyata a idanunsa dik da bai san wacece ita ba.

A karon farko yau ya yi wa garden sallama da ɗan sauti. A lokacin Zee tana kwance saman sofa ta takure jikinta waje guda, har barci ya fara ɗaukarta, dama kun san ta ce ba zata koma part ɗin mama ba, gara mata ta kwana a waje, so shi ne ta yi kwanciyarta a nan har barci yana shirin ɗaukarta.

Ganin alamar bata ji sallamarsa bane yasa ya sake yi mata sallama cikin natsuwa. A ɗan razane ta waro idanunta. Da yake ta fara barci sai bata iya gane wanene bane dik da hasken dake wajen. Ganin mutum yasa ta yi saurin miƙewa zaune idanunta a kansa, tana san tantance wanene?.

Wucewa ya yi izuwa saman sofa ya zauna yana kallanta shi ma, sai yanzu ta iya gane ashe mutumin da take mafarki ne a yanzu, wannan ɗan barci da ya ɗauketa har mafarkinsa ta fara yi. Ƙasa ta yi da kanta tare da cewa. "Good evening".

Kallanta da yake yi irin kallan nan ne na ke special ce da kika sace zuciyar jinin Zuhair lokaci guda. Ta tafi da imaninsa ta yadda kunnuwansa suka ƙasa iya jiyo mashi sanyayyar muryarta tana ɗaga mashi gaisuwa. Sai da ta sake ɗaga mashi gaisuwar sannan ne ya fahimci ashe magana take yi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya amsa mata.

Ganin alamar zama ya zo yi a wajen yasa ta miƙe tsaye domin ta koma ciki, sai satar kallansa ta kasan ido take yi, taga ɗan kyakkawan mamansa kani a wajen Ramish namu na amana.
Step biyu ta ɗan taka zata taka na uku kenan ta tsinkayo sexy voice ɗinsa yana faɗin. "Ina kuma zaki je?".

Cikin natsuwa ta juyo, dik da bata san wanenne shi ba tana respect ɗinsa sosai. "Ciki zan koma". Ta bashi amsa tana ɗan ɗago kallanta dan ta saci kallansa da kyau, tana san ganin face ɗinsa sosai amma bata san su haɗa ido. ........... "Ciki kuma?". Ya maimaita maganar da alamar mamaki a saman face ɗinsa. Kasancewar da turanci ta ɗaga mashi gaisuwa sai kawai ya cigaba da yi mata magana da English ɗin.

Kai ta gyaɗa mashi alamar e ciki. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "To kafin dai ki shiga cikin z ki bani abata da kika sace kada ki tafi da ita". Ya yi maganar yana kara gyara zama haɗe da ɗan wasa murya.
Zaro idanu sosai ta yi, take tsoro ya bayyana a saman face ɗinta, a ɗan ruɗe ta ce. "Wani abu kenan? Ni ban ɗauki komai ba wlh". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka.

Miƙewa tsaye ya yi, a hankali ya yi step biyu ya matsa kusa da ita sosai, ƙasa ya yi da murya kafin ya ce. "Kawai ki bani abata tin kafin kowa ya jimu, kin san da cewa a wannan masarauta dik wanda ya yi sata cire mashi hannu ake yi ko?".
Kai ta girgiza alamar bata sani ba tana zaro idanu.
Kara taka step ɗaya ya yi ya sake matsawa kusa da ita sosai, kashe muryansa kaɗan ya ɗan yi, kun san doctors da shegen iya soyayya da iya magana. Da sauri ta ɗan ja baya ganin ya matsota sosai, har cikin ranta ta ji tsoron kalamansa, dan ta ɗauka da gaske an sace mashi wani abin ne zai kala mata sharri.

"To in baki sani bama yau kin sani, dik wanda ya yi sata datse idanunsa muke yi, ga shi ke kuma kin mun sata, amma babu komai ki dawo mun da abata da kika sace zan rufa maki asiri ba zan sanar da kowa ba bare a cire maki hannu". Yana maganar yana kara matsawa kusa da ita.

Kara tsananta tsorata ta yi, a hankali ta fara ja da baya tana san matsawa daga kusa da shi, dan yadda ya matsota ɗin nan kwarjininsa ya kara yi mata yawa. Sai dai kuma dik in ta taka taku ɗaya ta matsa baya, shi kuma zai taka taku ɗaya ya matsa kusa da ita, a haka suka rinƙa yin baya baya tana ce mashi ya yi hakuri ita wlh bata yi mashi satar komai ba, shi kuma yana ce mata a'a bai yarda ba sai ta bashi abarsa da ta sace kafin ta tafi.

A haka har suka kurewa bangon wajen, a ɗan tsorace ta juya taga sun isa wall glass dake wajen rumfar, a tsorace ta juyo da nufin ta kallesa sai ta ga ya matsa dab da ita sosai, har suna iya jiyo numfashin juna, ya kuma yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa yana kallan face ɗinta. Lokaci guda ta ji ta yi nadamar fitowarta, gara mata ɗakin mama ashe a kan wajen nan, dik sai ta shiga tashin hankali, a tinaninta wani abin zai yi mata.

Narai narai da idanunta da suka ciko da kwallah ta yi zata yi mashi kuka, dik zafinta dai shi ta kasa zazzaga mashi masifa ko ta faɗa mashi san ranta, ya yi mata kwarjinin da ba zata iya yin hakan ba. Yana tsaye ya dafa hannunsa ɗaya a jikin bango ta bayanta, ɗayan kuma yana rike da wayarsa yana kallnta.

Sai da ya ga hawayenta sun fara salwanta a banza suna bin saman kuncinta ne ya ɗan waro idanu kaɗan, calmly ya furta. "Ashe haka kike da tsoro da saurin kuka?". Ya yi maganar ba tare da ya zare kallansa daga kanta ba.

Cigaba ta yi da kukanta bata bashi amsa ba, dan bata da abin faɗe. Ɗan nisawa ya yi tare da furzar da iska mai ɗan ɗimi daga bakinsa, sannan ya ce. "To ai ke bama ki tambayi abin da kika sace mun ɗinba da kika tsaya kina mun asarar hawayenki".

Sai a lokacin ta ɗago manyan idanunta kaman na kawunta Sadiq, a cikin nasa idanun ta sauke kallanta, lokaci guda sai ta ji kukan nata ya tsaya cak sakamakon wani irin kallo da ya wurga mata mai narkar da zuciya, bata san time da ta shanye kukan ba, sai ji ta yi hawayen sun dai'na zuba. Da sauri ta yi ƙasa da kanta, kun dai san mu Nigerians da kunya kamar me muke.............🥱

Zira wayarsa a cikin aljihun wandan sleeping dress dake jikinsa ya yi, sannan ya sanya hannunsa ya riƙo hannunta ɗaya, ƙasa ya yi da murya cikin wani irin salo mai kwantar da hankali ya ce. "Malama wadda ban san sunanta ba, kuma ɓarauniyata maza bani abata da kika sata, dan babu in da zaki je sai kin bani kayana". Yana magana yana ɗaga gera guda kamar wani...................🤫

Muryarta na sarkafewa saboda kuka, ga wani shessheƙa da take yi, kun san mutuniyar akwai zuciyata, so sai shessheƙa take yi alamar zuciyar tana a kusa, da kyar ta ce. "Allah ni ban sace maka komai ba, dan Allah ka yi hakuri ka barni in ta fi ciki". Ta yi maganar cike da san ta kwace hannunta daga rikon da ya yi mata, saboda a takure take, bata saba ba.

Shi kuwa kara rikota da kyau ya yi, a karo na biyu ya sace cewa. "To ai baki ma tambayi abin da kika sata mun ɗin ba"........ Kawar da kallanta daga kansa ta yi tare da cewa. "Me na sace maka to?".
Ɗan rankwafo kanta kaɗan ya yi, dan ya fita tsawo sosai, a dai'dai saitin kunnenta ya kawo ɗan bakinsa, kasa kamar mai raɗa ya ce. "Zuciyata kika sace mun, kuma sai kin bani ita kafin ki tafi daga nan".

Abin ku da ita ba soyayya ta taɓa yi ba, hasalima kunga ta tsani maza, so bata san komai ba, sai ta zaro idanu sosai, cike da ruɗani ta ce. "Zuciya kuma?". ......Kai ya jinjina mata alamar e.
"Ta yaya ake satar zuciya kuma shi da yake cikin jikin mutum?". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kansa...... Ya fahimci tabbas wannan yarinyar bata san me soyayya ba, infact bama ta taɓa yin soyayya ba, ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba, dan dama kun sansu da bala'in kishi, sun fi dik wasu nau'i na larabawa kishi, so sai ya ji daɗin ya yi sa'a shi zai fara koya mata soyayya kuma ya aureta da wuri dan ma kada wani ya ganta ya ce yana so.

Tab kuna ganin King zai aminta Dr Raj ya auri Zee kuwa? Kun dai san shi da kabilanci ko? Ya aka yi na Mahnoor da Jaish ma? Kuma kun ji ya ce dikka ƴaƴansa a cikin ƴaƴansu uncle Rahab zasu yi aure ko? To muje dai zuwa, zamu gani yadda za'ayi.

"Kin taɓa yin soyayya?" Ya jefa mata tambayar cike da fargabar amsar da zata bashi, dan in ta taɓa yin soyayya Allah zuciyarsa zata yi ciwo sosai saboda kishi, dik da yana ganin alamar kamar bata taɓa yin soyayyar ba, amma dai gara ya tambaya ya ƙara tabbatarwa. Sai harbawa zuciyarsa take yi kamar wanda zai shiga court kuma yana sa ran hukuncin kisa za'a yanke mashi, dik saboda fargabar amsar da zata iya fitowa daga bakinta ne fa.

Kai ta girgiza mashi kafin ta buɗi baki ta amsa da. "No, ban taɓa yi ba kuma bana sha'awar in yi".................... Wani irin daɗi da ya lulluɓe zuciyarsa ne har bai san time da ya ɗan matse hannunta da yake rike da shi a cikin nasa ba, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke a bayyane har sai da yasata kallansa a cikin ido.

Kara yin ƙasa da murya sosai ya yi, cikin salo mai tafiya da imani sosai ya ce. "Har da ni baki sha'awar yin soyayya ko kuma ban da ni?". Ya kai karshen maganar tare da ɗaga mata gera guda saboda yaga tana kallansa............... Ya subhanallah, Zee bata san lokaci da ta kara waro idanunta haɗe da afkawa duniyar tinani ba.
Hannunsa dake saman wall glass ɗin ya dawo da shi saman face ɗinta, a hankali ya ɗan goge mata hawayen da ya yi saura a face ɗinta, wato Dr Raj ba iya Dr bane kawai, shahararren ɗan love ne, kawai dama bai samu wadda ta sace zuciyarsa bane yasa yake wani jiji da kai, yanzu ba ga shi ya yi la'asar har da rarrashi ba.

"Answer me mana, har da ni baki sha'awar yin soyayya?". Yadda ya yi mata maganar cikin wani irin salo sai da yasa Zee ta yi saurin girgiza mashi kai alamar a'a ban da shi, shi kam za'a iya yin soyayya da shi, bata san ta girgiza mashi kai ɗin ba, kawai salon maganarsa cikin natsuwa mai kwantar da hankali yasa ta bashi wannan amsa.

Wani irin sanyi ya ji ta ratsa zuciyarsa. Matsawa kusa da kunnenta sosai ya yi, cikin raɗa yana rike da hannunta yana kuma kallan face ɗinta ya ce. "Kina so na?". Ya yi maganar yana kashe mata idanu ɗaya yana ɗan canza yanayin face ɗinsa, dan yana fargabar amsar da zata iya bashi, ba zai iya ɗaukar ta ce bata san shi ba, dik da yasan mawuyacin abu ne ta ki yin accepting ɗinsa, dan jinin Akka fa sai dai mata su kawo kansu garesu, basa tambayar soyayya su, a karon farko ya roki soyayya a hannun ƴar Nigeria, yo to mu Nigerians dama wasa ne? Haba dole ka roki soyayya malam Dr Raj, dan mu ɗin na daban ne malam.

Shiru Zee ta yi ta kasa magana, da alamu kamar suman tsaye ta yi, wato a duniyar nan idan Allah ya kaddara ga mijinka fa shikenan babu wanda ya isa ya canza, idan ba wata kaddara ta Ubangiji ba fisabilillah ina Zee ina Dr Raj? Mutanen da ƙasa ba ɗaya ba, babu abin da ya haɗa, babu dangin iya bare na baba, kaddara kawai ya kawo ƙasar, shi kansa Dr Raj kun san suna shafe shekaru 6 zuwa sama basu leƙo kingdom of power ba, amma da Allah yasa dole a kaddararsa akwai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login