Showing 9001 words to 12000 words out of 403653 words

Chapter 4 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

117

"Saboda biye maku da nike yi mana, kullum nine karshe".

Floris ce ta karɓi zancen da cewa. "And you're a winner everyday ba".

Kashe mata ido ɗaya ya yi alamar haka ne zancenta. "To kuzo mu je".
Ya faɗa yana miƙa masu hannu.

Kusan a tare suka kariso gabansa, wayarsa dake hannun Sweetie ya fara karɓa ya zura a aljihu kafin ya kama hannayensu, suka nufi waje.

Sai daɗi Sweetie take ji yau, hakika tana da karfin tawakkali da imani da Allah Sweetie, ta yadda da kaddara mai kyau ko maras kyau, bata sanyawa kanta damuwa ko kaɗan, idan ta tuna kuncin dake cikin rayuwarta, cikin sauri take tunano girma da niimomin da Allah ya yayi mata, hakan yakesa ta mance ƙuncinta, mu koya daga gareta domin mu ji daɗin gudanar da al'amuranmu cikin nutsuwa, mu kuma kara karfafa imaninmu!!.

Sosai filin wasan skaternsu yau ya cika, matasa sai gwada baiwarsu suke yi, ga ƴan gasa sun shirya tsaf, tsabar kaunar wasan da Ronnie yake yi, yanzu haka yana kammala karatunsa zai shiga wasannin duniya gabakiɗaya bisa yardar Black Tiger, ya yi mashi hakan ne dan ya faranta mashi ransa sosai.

Kowani matashi yana gwada baiwarsa, babu nuna ragonta, dik sun tsaya tsayin daka dan nuna jarumtarsu.

Saman ƙayatattun kujeru na musamman ya zaunar da Floris and Sweetie wanda tun shigowarsu wajen idanun kowa yake a kansu.

Saboda kaunar wasannin Ronnie yasa Black Tiger ya gina masu wannan stadium ɗin, dik dan farincikin kanin nasa.

Tin da ya sako kafafunsa cikin wajen jama'a suke ihun sunansa da ɗaukar tafi da hannayensu, ji kake fito ya karaɗe ko'ina, da alama suna murnar zuwansa sosai. Ya saye zuƙatan kowa!.

Sai da ya sumbaci kumatun Sweetie and Floris sannan ya juya ya shiga fili, nan fa tafi da fito ya kara yawaita sosai.

Master Devil ne ya bashi skatersa ya sanya a ƙafafunsa, dik wajen nasa takalmar ce kawai ta fita daban, dan haɗuwa da tsadarta ya wuci tunaninku, dik takalmar wasanninsa da ɗanyar gold Black Tiger yasa aka kyara mashi su, kunga kuwa ai bazama ayi zancen tsada ba, dan akwai kuɗi kam.

Zuba mashi idanu su Sweetie suka yi suna ta kallonsa, shi ma idanunsa yana a kansu. Ƴan wasa gabaɗaya sun tsaya layi kowa jira yake yi su fara, sai fito ake yi.

Wani katon warriors wanda ya ji horo ya ƙoshi ne ya hura masu usir dan a fara wasa. Tafi da karfin sautin fito ne ya kara karaɗa wajen.

Floris ma tafi ta fara yi tana faɗin Ronnienta ne winner. Ganin tana tafi yasa Sweetie ma ta fara yi, yanzu dik abin da Floris ta yi ita ma sai ta yi.

Kun san wasan skater kusan yana tafiya ne da zuciyar mutum, kamar gudun doki ne, idan kana a kan doki, to gudunsa ya ta allakane da yanayin bugawa da gwazon zuciyarka, shi ma haka yake.

====================💘🔥

Ko gargada Ronnie bai taɓa yi a wasan skater ba, sai ga shi yau saura kaɗan ya yi wani mummunar faɗuwa Black Tiger ya tare mashi da magic ɗinsa, ba komai ya haifar da hakan ba kuma face Sweetie.

Suna tsaka da tafi ita da Floris suna kallonsu suna nishaɗi, kwatsam sai ta nuna takalmar ƙafarsa da yatsanta tana tambayar Floris amma takalmar Ronnie na gold ne ko?. Dan ta gansa yana kyalli sosai.

Wannan nuna shi da yatsa da ta yi unexpect magic ɗinta ya fita, baiwar Allah sam bata ma san yadda zata sarrafa magic ɗinta ba, dan bata san da shi a tattare da ita ba, in dai zata nuna abu da hannu to da wuya idan magic ɗin bai fita ba, kuma a iya hannun hagunta ne abin.

Wani ɗan siririn haske ne ya fita daga hannun nata kai tsaye sai kan takalmar Ronnie da ta nuna hasken ya nufa, hakan ya haifar mashi da tuntuɓe, da yake Black Tiger yana ganinsu ya ga magic ɗin nata, ya kuma yi sauri ya tare shi, amma dik da haka da yake nata yana da karfi sosai sai da ya sa Ronnien tuntuɓe kamar zai kifa ƙasa, da ya faɗi kuma za'ayi mummunar faɗuwa, saboda ƴan wasa dayawa suna biye da shi a baya, da dik zasu faɗi, wasu su faɗi a kan junansu.

Dayawan mutanen dake wajen sun sha madarar mamakin ganin Ronnie ya yi tuntuɓe, sai dai ba wanda ya ga dalilin hakan, shi kansa ya ɗan yi mamaki, dan dai wajen flat yake babu wani gargada, to me ya sanya shi wannan tuntuɓe? Ya jefawa kansa tambaya.

Yana can yana wannan tunani har wasu ƴan wasa biyu suka tsere mashi ba tare da ya farga ba, sai da ya ji ihun Floris tana ambatar sunansa ne ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka.

Cikin tafasar jini ya fara gwabza wasan, kafin wani ɗan lokaci ya wuce waƴan can.

A lokacin da ƴan wasan can suka wucesa har sai da damuwa da rashin jin daɗin hakan ya bayyana a saman face ɗin sweetie, Allah sarki bata san ita ce sanadi ba.

Shiru Black Tiger ya yi yana tunanin meyakamata ya yi domin cire magic dake jikin Sweetie? Dan in ba haka ba watarana zata iya zama ajalin Ronnie ba tare da sun sani ba, ko da bai rabata da magic ɗin ba ya zamana shi yake sarrafa magic ɗin nata, dan tsaro, ita bata san da shi a tattare da ita ba, zata yi ɓarna sosai a dalilin hakan.

Can wani zuciya ya ce mashi. "To ai kila saboda magic ɗin nata ne yasa aka ce ita ce zata kawo karshenka!".

Tuna hakan yasa ya kara ɗaur wanna fuska mai kama da hadarin, dan in kuwa hakan ce da wuya ya iya sarrafa magic ɗinta, tunani ya fara yi a kan wacece ita ma tukun nan ? Ina asalinta yake? Wani shafaffe da mai ya bata magic?. Waɗan nan sune tunanin dake ransa!.

Ni dai bana tunanin mahaifiyarsu Sweetie ce ta bata magic, domin kuwa mom ɗinsu baiwar Allah ce mai riƙo da addini, ga shi har ta koyar da su karatun addini da har suka koyawa Kamran ga shi yanzu tana karantar da Ronnie girman Allah, kun ga kuwa mom ɗinsu mutuniyar kirkice, da wuya ta koya masu tsafi.

Dik yadda aka yi ko dai mahaifinsu ne ko kuma wannan sadauki mai taimaka masu ɗin, akwai dai cakwakiya da sarkakiya mai ɗaure kai, to Pretty ma tana da shi ne ko dai iya Sweetie ce kawai?.

Da alama kuma ita ma Sweetie sai da ta haɗu da Black Tiger ne magic ɗinta ya bayyana, dik yadda aka yi magics ɗinsu yana da alaƙa ko dai wani abin makamancin hakan!!.

Lokacin da Ronnie ya matso kusa da su sai da ya kashe masu ido ɗaya. Fito mai sauti Floris ta saki, ita kuma Sweetie da bata iya fito ba sai kawai ta sakar mashi murmushi tana cigaba da yi mashi tafi.

A karo na biyu ta sake cewa Floris. "Amma skater kafar Ronnie da gold aka yi ta ko?".

Kai Floris ta gyaɗa tare da cewa. "Yeah, da gold yaya yasa aka yi mashi".

Ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin yadda suke facaka da gold, bayan kuma Ronnie ya gaya mata irin tsada da darajar da gold yake da shi, amma a haka suke abin da suka ga dama da shi, bata san arzikinsa Allah ya yi masu ba, a tunaninta saya suke yi, hakan yasa take kara jinjinawa karfin arzikinsu.

Da gudu Floris ta miƙe ta nufi cikin wajen wasa, da idanu Sweetie ta bita tana mamakin ina zata je to?.

Tana zuwa ta daka tsalle ta faɗa jikin Ronnie dake tsaye, abin ku da babu Muslunci a waje, iyayen Floris suna wajen suna ganin wasan, amma ko kaɗan basu damu ba dan Floris tana yawan rungumar Ronnie, shi ma kuma yana ɗaukarta, wani lokaci har goyata yake yi, babu ruwansu......... Kai wato musulunci fa ya yi a rayuwar nan, Allah dai ya bar mu a cikin addininmu har karshen rayuwarmu, samun kanka a cikin addinin musulunci ba karamar ni'ima bace da Allah ya yi maka, yakamata a kullum bawa ya rinƙa yawaita godiya ga Ubangijin taliƙai!!.

Da hannu ɗaya Ronnie ya ɗaga Floris, a saman shoulder ɗinsa gabaɗaya ya zaunar da ita, ta ɗaga hannayenta jikka biyu sama ya fara playing skater da ita, dama idan da sabo sun saba yin haka, dik cikin ƴan wasan babu wanda yake da karfin iya ɗaukar wata ya kuma yi playing wasa da ita sai Ronnie, shi kaɗai ne yake iya goya Floris ko ya zaunar da ita a saman shoulder ɗinsa, ta zauna tamkar tana zaune a saman kujera, ya yi ta wasa da ita, shi ya fita daban da sauran ƴan wasa.

Da hannu ya yi wa Sweetie alama a kan ta zo. Ba musu ta taso cikin nutsuwa ta ƙariso in da yake. Nan fa kallo ya koma kanta, sun ga madarar kyau.

Haka kawai yau Ronnie ya tsinci kansa da jin haushin mutanen wajen dan suna ta ganin Sweetie, bai taɓa damuwa dan sun kalli wani ko wata ba, idan baku manta ba ya taɓa faɗawa Sweetie cewa sai mace tana da kyau ake kallonta, idan ma jama'a basu kallonta ai bata cika mace ba, to sai ga shi yau Sweetie ta cika mace ana kallonta kuma yana jin haushi.

Gabaɗaya idanun jama'a ya dawo kanta. Tana zuwa ta tsaya a kusa da shi, dik sai ya ji wasan ta fita a ransa, ji ya yi su koma cikin gida kawai.

Amma haka ya daure ya sanya ɗayan hannunsa ya ɗagata sama sai saman shoulder ɗinsa ta ɗayar gefen, ita da Floris suka haɗe hannaye suka ɗaga sama suna sakin murmushi.

Nan take wajen ya ɗauki ihu da fito, haƙiƙa Ronnie ya samu horo mai kyau, ko nauyinsu bin ji ba ya fara rolling da su a saman shoulders ɗinsa, abin ya yi matuƙar ƙayatarwa ya kuma ɗauki hankular jama'a, basu taɓa ganin irin hakan na. Su Sweetie kamar wasu ƴan baby.

Allah sarki Delisha kuwa tana can tana fama da dogara sanda. Dik abin da suke yi master Devil yana ganinsu, dan yana wajen.

Tabbas wasan yau ya kayatar matuƙa, wasa ne da ba'a taɓa yin irinsa ba, Ronnie ya kawo sabon salo ya kuma kara tafiya da zumatan mutane dayawa.


__________AFTER SOME MINUTES🔥

Yamma ta yi, rana ta yi sanyi irin bayan la'asar ɗin nan. Barci mai nauyin gaske ne ya ɗauki Sweetie, tana kwance saman bed ɗin Ronnie, dan yaki yarda ta bar room ɗinsa, saboda yana ganin kamar idan ta bar room ɗinsa Black Tiger zai iya cutar da ita, yana ganin kamar zamanta a nan ne zai hana Black Tiger taɓa lafiyarta.

Floris tana tare da Angela suna buga triangle game kamar yadda suka saba, Angela ɗaya daga cikin yara marayun Black Tiger ne, kyakkyawar yarinya mai farar zuciya, zubinta sak na ƴan Black world ɗin.

Sanye yake da swimming short, babu riga a jikinsa, yau ainahin wrestling surarsa ta bayyana, idan ka gansa a cikin kaya sai ka gansa ɗan siriri zubin Koreans ɗin, ashe ba haka bane, murɗaɗɗen mutum ne sosai, daga wanka ma ya fito.

White hairnsa a ɗaure ya busar da ita. Part na Black Tiger ya shiga, a maimakon ya shiga master room na yayan nasa sai ya wuce izuwa gym, ta wani glass way mai matuƙar burgewa da ɗaukar hankali ya bi.

Yanayin hanyar idan ka hau kana iya ganin kasa, sai kaga kamar zaka faɗa idan baka saba bi ba, dan zallar glass ne.

Like wow, sai dai mu ce masha Allah, amma wanna waje ya amsa sunansa gym ɗin da gaske, ya kawatu da abubuwan motsa jiki kala daban daban masu bala'in kyau.

Cikin shigar da ya saba ganin Black Tiger da shi yau ma ya gansa.

Kusa da shi ya tsaya, a ɗan shagwaɓe ya ce. "Brother open your face, because you look so beautiful, I want to see you again, Please stop covering your face".
Kamar zai yi kuka ya kai karshen maganar, kamar wani ɗan yaro, ashe haka yake magana da Black Tiger, sai dai kada ku manta cikin harshen koreans suke magana!.

Wasu irin mahaukatan barbell mai ɗauke da weight plates masu bala'in nauyin da zasu iya kai goma goma ta kowani ɓangare ne a hannun Black Tiger yana ta ɗagasu yana saukewa.
Da kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci ya jima a gym ɗin yana motsa jiki, ga wani care luxury glass a idanunsa, hakan yasa ba'a iya ganin kwayar, gaskiya Black Tiger hege ne, ganinsa kawai yana firgita hantar manya da ƙananan halittu.

Bai tankawa Ronnie ba yana cigaba da ɗaga wannan barbell ɗin kamar bai san da halitta a wajen ba.

Ɗan zunɓura baki Ronnie ya yi tare da ƙarisawa wajen, DUMBBELL ya ɗauko ya fara ɗagawa yana kallon kwanjin hannunsa, ga wasu layukan guraye a cikinsa kamar wanda ya zana da gangan, kuma dik horo ne ta yi mashi yawa, cikin nan nasa a shafe manne da baya.

Cigaba da ɗaga dumbbell ɗin ya yi yana kara zunɓura baki shi a dole Black Tiger bai kula shi ba ya ɓata rai.

Ya kai a kallah 10 mins yana ɗaga dumbbell kafin ya ajiyesu ya nufi gaban yayan nasa wanda tin da ya zo wajen bai kalli in da yake ba, aikinsa kawai yake yi yana ta haɗa uban zufa saboda wahala, wajen kuma gabaɗaya kewaye suke da A.c dake busa sanyi, amma bai hana shi zufa ba.

Wlh ba dik kai ba iya ɗaga barbell mai weight plates guda biyar ma, sai a tara maza dubu ba a samu biyu masu iya ɗaga mai biyar ba, shi kuma Black Tiger mai goma kuma manya manya yake ɗagawa, har yau Ronnie a iya mai huɗu kawai yake iya ɗagawa, shi ma sai da Black Tiger ya tsaya tsayin daka sannan ya iya jajircewa.

Isar Ronnie gabansa ke da wuya ya sauke barbell ya mayar da shi mazauninsa, sannan ya duka ya yi shirin fara press up.

Hayewa saman tsakiyar bayansa Ronnie ya yi yana cigaba da zunɓura baki. Bai kula shi ba ya fara press up da shi babu kama hannun yaro, da yake gwarzon namiji ne ya saba, sai da ya yi press up 200 babu hutawa, shi ma Ronnie yana tsaye a kan kafafunsa a tsakiyar bayan nasa kamar wadda aka sassaƙa, ko gezau bai yi ba.

Abin dai gaskiya da mamaki, sun kware kam wajen yin wanna zallar madarar jaruntar.

Dikkansu sai da suka yi sharkaf da zufa, gabaɗaya fuskar Ronnie kamar wanda aka watsawa ruwa, shi kuma big man da yake face ɗinsa a rufe sai ya zamana ba'a gane halin da yake ciki.

Wucewa ya yi ya nufi room ɗinsa bayan sun kammala. Da sauri Ronnie ya bi bayansa yana saka mashi kukan shagwaɓa a kan lallai ya buɗe fuskarsa ya gani, dan shi gaskiya Black Tiger ya yi mashi kyau, kuma ba zai iya tafiya ba tare da ya gansa ba, in baku manta ba kaunar kyau a jinin Ronnie yake, dik wani abu mai kyau to yana kaunarsa sosai.

Tamkar Black Tiger kunnuwarsa sun doɗe, sai ya nuna kamar bai san da wani Ronnie ba, ya shige cikin room nasa. Har ciki Ronnie ya bisa.

Toilet Black Tiger ya nufa cikin wani irin tafiya mai matuƙar ban mamaki da al'ajabi, kamar wanda baya taƙa ƙasa.

Saman wannan DAULAR bed ɗin nasa Ronnie ya haye ya kwanta, shi fa ya rantse ba zai fita ba sai ya ga face ɗin yayan nasa, ga shi by 5:30 zai tafi church, yanzu kuma 5:06.

_____________ SWEETIE ___________🔥💘

Kamar a mafarki ya tsinkayo sanyayyar voice ɗinta tana faɗin.
"Where are you Ronnie? Why are you leaving me alone in the room? Do you want the man who made me suffer that day to come back and take me away again?"
Idanunta sun yi jajir sun ɗan kumbura, jikinta dik a mace alamar barci bai isheta ba, golden white hair nan nata a watse kamar wadda aka kwato daga bakin kura, sanye take da kayan barcin Floris riga da wando masu dogon hannu launin sky blue, ba karya ta yi kyau sosai, tin da ta yi sallar la'asar take zuba barci.

Tana magana tana nufo master room ɗin, dan tasan a nan kaɗai zata same shi, saboda ta je parlourn kasa baya nan, Floris and Angela ta samu, Floris ta ce mata yana wajen yayansa, ko tsoro bata ji ba shi ne ta biyosa, akwaita da karfin halin bala'i yarinyar nan.

Haba ai a miliyan kamar wani walkiya haka ya diro kasa daga saman bed ɗin, kafin ƙiftawa da Bismillah har ya kai bakin door room, jikinsa har yana ɗan kerma wajen buɗe kofar ya fito da gudu kamar wanda aka koro.

Yana sanyo kai suka yi karo da ita, dan tsabar karfin hali irin nata tana ƙoƙarin buɗe kofar ne ta shigo ciki.

Ai bai dakata ɓata lokacin duba in da ta buge ba, hannunsa na kerma ya ja nata suka nufi hanyar barin wajen, ya mance da cewa kuka yake yi wa yayansa a kan ya buɗe fuska, tuni ya wuce.

Kamar waɗan da aka rako ya banke kofar room ɗinsa ya shiga da sauri yana sauke ajiyar zuciya.

Ita da sam babu tsoro a tattare da ita kuma bata ga abin da zai bata tsoro bane ta ce.

"Are you okay?"

Bata jira amsarsa ba ta ɗaura da. "Why're you running like that? And why

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login