Showing 60001 words to 63000 words out of 403653 words

Chapter 21 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

50

dik wasu sassasa da mutum zai iya zuwa a cikin kingdom ɗin nan sai da suka je suka duba.

Kowa ya tashi daga barci har da su Mummy, King ya tashi kowa, commander Zafar kam shi ne mutum na uku da King ya fara tasa daga barci bayan uncle Abbas da uncle Taheer.

In short Akka ce kawai ba'a sanar da ita abin da yake faruwa ba, ita ma saboda bata da lafiya ne kada ciwon ya kara tsananta suna iya rasata a kan hakan, shi ne yasa suka ki sanar da ita.

Jigum jigum suka zauna cikin parlourn King, su commander Zafar kuwa sun gama kewaye kota ina da warrios a cikin kingdom ɗin anata kai komo wajen nemanta.

Lokacin da commander ya zo sanar da Hoorain ga halin da suke ciki gimbiya Zunaira ta ɓata, sai ya tarar da shi da zazzaɓi mai tsananin zafi, jikinsa ta yi zafi jaw kamar wuta, hakan yasa ya fasa gaya mashi halin da ake ciki, ya ɓoye mashi, ya ce ya zo duba shi ne kawai.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Gabaɗaya family hankulansu in ya kai miliyan ta ya tashi, harta maman Yah Ramish ta shiga damuwa matuƙa, mummyn Chuchu har kusan kwallah ta yi, Momma kam ba'a magana, tana tsaye taki zama, kamar wanda aka sassaƙa.

Kamar yadda suka ga rana haka suka ga dare zaune a cikin parlon King, lokacin da aka yi kiran sallar asuba ta farko King ya fito waje hararbar kingdom ɗin, dan yana zargin warriors da commander zafar ya wakilta wajen nemanta a dik wasu lungu da saƙo na kingdom ɗin basu duba da kyau ba, so sai ya fito da kansa dan ya duba.

Momma ta so binsa, sai dai kunsan a doka irin tasu ba zata fita waje ba, killacesu ake yi, matan sarki bayi da warrios basu da damar ganinsu, suna da ƙaidoji da dokoki masu karfi.

So Mummyn Chuchu ta riketa ta hanata fita.

Dik yadda King yake tinani abin ya wuci nan, dan babu in da basu duba ba babu ita babu labarinta, da kyar uncle Abbas ya rarrashesa suka koma ɗakunansu dan su shirya zuwa masallaci.

Yau gabaɗaya zargin Momma a kan maman Yah Ramish yake, dama ta jima tana zarginta, kawai tana dannewa ne saboda bata san tashin hankali, amma yau a kan ɓatar Zunaira wlh ba zata ragawa kowa ba, dole ta fito da zarginta ta ɗaura a kan wanda zuciyarta take raya mata!!.

Lokacin da su King suka dawo daga masallacin sallar asuba, babu ɓoye ɓoye suka sanar da matan cewa Auta fa bata cikin kingdom ɗin nan, ta ɓata, dan haka kowa ya zage da yin addu'ar Allah ya bayyanata.

King yana sanar da su gabaɗaya parlourn ya dauki shiru mai tsananin girma fiye da kowanne kuka. Momma zube gwiwowinta a kasa ta yi, nan take hawaye suka fara gudu ba kakkautawa kamar ruwan kogin da ya ketare iyaka a saman face ɗinta.

"Ba zan iya yarda ba! Ba zan yarda cewa Zunaira bata cikin kingdom ɗin nan ba! Ba zan iya yarda ta ɓata ba!"....... Haka ta fara sambatu, muryarta na kara tsananta kuka.

King da aka san shi da jarumta, yana tsaye a gefe kamar wanda ya rasa hanyar tunani. Idanunsa cike da hawaye da ba ya so su zubo, amma ba zai iya hana su ba. Ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa, yana kallon momma ya kasa yin magana.

Guyson ne ya ce. " Dad Momma wai me na yi wa duniya har za'a kashe ni da irin wannan bakin azaban ciwo mai tsananin zafin? Da a ɗauke Zunaira ai gara ni a kasheni!"............ Ya tambaya da muryar da ta nuna karayar zuciyarsa. Guyson mai saurin kuka yau dai hawaye taki fitowa, sabdoa azabar dake cikin ransa ba zata iya baiwa hawaye gurbin fita ba!.

Yah Jawad wanda idanunsa yake yi mashi gizon Auta tana tsaye kusa da guyson tana murmushi ne ya kasa iya furta word. Kamar ma baya cikin hayyacinsa sosai.

Su uncle Taheer sun kasa yin magana, sai kawai kukan zuci da suke yi. Fanan da ta manne da Chuchu ce a cikin ranta ta ce. "Auta ta kasance mai kawo dariya da farinciki a kan fuskar kowa dake gidan nan, ta sanya zuƙatan kowa a nitsuwa, sanyi idaniyar kowa, yanzu ace babu ita? Kai anya zasu iya ɗauka kuwa? Gurbin ta tamkar rami ne mai zurfi wanda babu abin da zai iya cikawa a zuƙatansu".

Kowanne daga cikin su yana tuna abubuwan da ta yi na alkhairi, irin murya mai daɗin da ke jansu cikin farinciki, yadda take cika gida da rayuwa da ƙauna.

Chuchu dai ganin abin kamar mafariki take yi, hakan yasa bata iya furta word ba, tana dai binsu da ido, gata nan gata nan kamar wadda aka sassaka ta kasa motsawa.

Momma kuwa kara fashewa da kuka mai sauti ta yi, hakan ya ja hankalin mummyn Chuchu a kanta, da sun afka duniyar tunanin ina Auta take? Jin kukan Momma yasa suka yi saurin karisowa in da take.

A tare Mummyn Chuchu da Maman Yah Ramish suka tsugunna a gabanta, a tare suka kai hannu suka rungumota.

Cikin ɗaga murya momma ta ce da mama kada ta sake taɓata!. Tashin hankali.

Nan fa kallo ya koma kansu a cikin parlourn, yadda Momma ta yi maganar ya girgiza kowa. King da yake tsaye kaman wanda aka sassaƙa ma sai da ya ji gabansa ta faɗi ya dawo cikin hankalinsa.

Mama da bata gane me Momma take nufi ba, a tunaninta saboda raɗaɗin rashin ƴar tata ce yasa take sambatu, sai bata saketa ba, sai ma ta yi ƙoƙarin goge mata hawaye dan ta rarrasheta.

A tsananin fusace momma ta kwace kanta daga riƙon mama, take ta fara huci kamar zakanya tana jin yunwa, cikin zafa ta ce. "Idan kika sake taɓani dik abin da na yi maki ke kika nema!!". Babbar magana!.

Ganin hakan yasa su Jawad gabaɗaya suka matso kusa da su, so suke yi su kwantarwa da Momma hankali da kalamansu, amma dikkansu babu wanda yake da kalmar da zai iya tinkarar momma da shi.

Dan haka sai dai suka matso suka tsaya jugum jugum kaman wasu gumaka.

Allah sarki Chuchu da ta ɗauki abin matsayin mafarki ba gaskiya ba, dik da haka hawaye ne yake gudu a saman face ɗinta kamar ruwan pampo, tana tsaye kamar wadda aka sassaƙa, da alama bata a cikin hanyacinta.

Wai a haka sun ɗauka sace Auta aka yi, to idan suka san ta bar duniya mai gabaɗaya me kuke tinanin zai faru? Akwai bala'i gaskiya.

Da kyar King ya iya motsa laɓɓansa da suka yi mashi masifar nauyi ya furta kowa dake cikin parlourn nan ya je su kyale shi daga shi sai Momma bari su yi magana.

Babu musu kowa ya nufi waje, Mummyn Chuchu ta saki momma ta miƙe, a babban parlour suka haɗu suka zauna jugum jugum.

Chuchu ta kasa motsawa har sai da Yah Jawad ya tallaɓota ya ja suka fita.

King da Momma kawai aka bari a cikin parlon King, harta Guyson mummyn Chuchu ta ja shi sun fita wajen, kamar ba mutum ta rike ba, dik ya sake mata jiki kaman wanda ya sume, Allah sarki bawan Allah, da alama ya fita hayyacinsa ne.

King da momma sun ɗauki a kallah 30 mins suna tattaunawa ta sirri, kafin daga bisani King ya rarrasheta tare da gaya mata wanda yake zargi da sace Auta wato king Al-Mustapah kenan, kuma ta kwnatar da hankalinta cikin ƙanƙanin lokaci za'a dawo mata da Auta lafiya lou In Sha Allah, yanzu za'a shirya dakarun yaki domin tinkarar Daular Qahtaniyawa, tun da sun tsokalo yaki dole a yakesu.

Aunty MieMie dai bata da labarin dik abin da yake faruwa, tana can ɓangarenta tare da mijinta. Tsabar tashin hankali yasa suka manta da ita ba'a sanar da ita ba!.

Momma da kyar ta hakura ta yi shiru, hakan ma dan King ya yi mata alkawarin dawo da Auta cikin kwana ɗaya ne.

Cikin bedroom ɗinsa ta shiga ta kwanta, shi kuma ya wuce toilet, wanka ya yi tare da shirin tafiya fada, nan ya buƙaci Commander Zafar da ya kira mashi Hoorain ya kuma haɗa kan mayaƙa tawagar farko.

Me zai yi wa Hoorain kuma?.

===========================🔥

Karfe 9 daidai gabaɗaya manya manyan jiga jigan masu faɗa a ji a cikin fada suka haɗu, hankalin kowa in ya kai miliyan a tashe yake, dik sun nitsuwa tsit suna cikin alhini, dik wanda ya ɗaga idanu ya kalli fuskar King ba zai so ya sake ɗaga idanu ya kallesa ba, saboda fuskar a ɗaure take, uban kwarjininsa ta kara bayyana, zarra ga marasa adalci da san gaskiya kenan.

Yana dake saman kujerarsa, yau babu wargi bare wasa, su commander Zafar dik sun shiga taitayinsu, kowa yana nan bisa ƙaida, dik sun tattaro hankulansu a kan King Zuhair, shi kawai ake jira da ya yi magana.

Dai'dai lokacin da Hoorain ya dimfaro babbar kofar fada da nufin ya shigo ciki dan amsa kiran da King ya aika ayi mashi, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan baya a cikin hayyacinsa sosai, dik ya firgice, tamkar wanda aka zarewa laka, yana yafiya yana jan kafafu tamkar ba sadauki Hoorain assistant commander ba, jarumi mai tafiya cike da zarra da kwarjini mai razanar da zuƙatan dik wasu warriors dake cikin kingdom ɗin, amma yau ya taho tamkar mace yana wani jan kafa.

Masu gadin kofar fada har sun bashi hanya, ya matsa gada da su kaɗan har ya kusa shiga fada, kunsan dai'dai in da suke tsaye domin gadin kofar akwai ɗan tazara tsakaninta da kofar, a kasar stage na hawa suke tsayawa, kofa kuma tana sama.

So sun bashi hanya zai wuce, ya haura saman step ɗai ɗai har uku zai taka na huɗu kenan ya tsinkayo muryar King ya fara magana cikin kakkausar murya da zafa, dama ga voice ɗinsa da kaifin bala'i, hakan ya yi gaggarumin ɗaga hankulan su commander.

"Kaiconku! Kun bani kunya kuma na raina kwarewarku! Commander kana da shekaru sama da talatin kana matsayin mai jan ragamar warriors da suke cikin kingdom ɗin nan, amma yau har a samu wani mai karan kwana da zai iya keta tsaronka ya shigo har cikin kingdom ɗin nan ya ɗauki Zunaira ya fita da ita! A gaskiya ka gaza dayawa Zafar!"............ Shi ne abin da King ya faɗa a kan kunnen Hoorain da ya dakata da yunƙurin shiga fadar ya kasa kunne yana sauraronsu.

Kasa da kai commander ya yi, bashi da bakin yin magana tun da ba'a bashi izini ba, sai kawai ya yi ƙasa da kai yana sauraron faɗar King.

Cigaba da faɗa cikin zafa King ya yi.

"Dole hukunci zata hau kan Hoorain! Saboda shi na ɗaurawa alhakin kula da Zunaira! Shi na ɗaurawa alhakin kada ya bari ko guda ya taɓa mun ita, dan haka idan wani abin ya samu Zunaira dole in hukunta shi!!"..........

A dai'dai wannan gaɓa sai da commander Zafar ya yi hanzarin ɗago kansa da kallonsa izuwa kan King, ya ji zazzafar magana da baya jin zai iya jure hakan, wato hukunta Hoorain, yasan hukuncin King bata da sauki, bare kuma a kan Auta, ai ina abin ba zata yi kyau ba.

Sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi, gaban maza sai da ta bada dukan uku uku, Hoorain shi ne farincikinsa, sannan ace za'a hukunta shi da laifin da bai sani ba? Gaskiya a wannan gaɓar baya jin zai iya ɗaukar wannan hukunci na King, to amma ya zai yi? Ya jefawa kansa tambaya. Sai sake sake yake yi a cikin zuciyarsa ya daina sauraron abin da King yake faɗa.

Kamar daga sama ya ji warriors dake tsaye a kusa da shi ya kai hannu ya taɓa shi yana faɗin. "Master King yana magana".

A ɗan zabure ya miƙe tsaye, bawan Allah ya afka duniyar tunani ne bai ji King yana tambayarsa ina Hoorain ɗin yake ba?.

Ran King ne ya kara ɓaci na ya yi magana commander bai jisa ba, kun san idan mutum yana cikin ɓacin rai da zarar an mashi abu kaɗan zai tashi ya hau bala'i, to haka abin take.

Ɗan risinar da kai ƙasa commander ya yi alamar girmamawa.
"Kayi hakuri ranka ya dade, tun ɗazun da kace in kira Hoorain ɗin na faɗa mashi kana kiransa, ban yi tsammanin zai kai har iyanzu bai iso ba!".

Sosai ran King ya kara bakanta, a ɗan fusace ya umarci ɗaya daga cikin warriors dake cikin wajen a kan su kira mashi Hoorain yanzun nan, sannan kuma dole ya fuskanci wani hukuncin a kan jinkirin da ya yi bai amsa kira ba.

Dik maganganun da suke faɗa a kan kunnunsa suka yi ta, ya ji komai! A maimakon ya shiga cikin fadar ko hakurine ya bawa King ko zai samu sassaucin hukunta shi da za'ayi, sai ya juya ya fasa shiga, cikin sassarfa ya bar wajen. Masu gadi kuwa basu ce da shi ko uppan ba!.

Kai tsaye bedroom ɗinsa ya koma. After 5 mins da shigansa cikin ɗakin ya fito ya nufi katafaren wajen dawakansu, dik da yana sanye cikin kayan yaki ya ɗaura jacket mai girma a jikinsa, ya kuma sanya hular jacket ɗin a kansa, hakan ba zai hana ka gane yana cikin tashin hankali na kin karawa ba!.

Saman wannan ƙosasshen jibgegen dokin nasa ya hau. Da karfi ya bawa dokin wuta, kai tsaye babbar gate na Kingdom ɗin ya nufa.

Tun daga kan gate na farko har izuwa babba na karshe babu wani warriors da ya dakatar da shi ko ya ce zai hana shi fita ko dai ya tsaya a bincikesa, saboda dik wanda ya kwana ya tashi a cikin kingdom ɗin yasan wanenen Hoorain kuma me matsayinsa, dan haka basu yi gigin dakatar da shi ba, sai ma hanya da suka bashi cikin girmamawa ya danna waje a miliyan.

Ina kuke tunanin zai je? Meyasa yaki amsa kiran King? Meyake shirin faruwa ne? Guduwa ya yi ne ko menene?....................

=======================🔥

Dai'dai lokacin da wannan warriors da King ya aika da ya kira Hoorain ya dawo cikin fada dan ya isar da sakon Hoorain baya nan bai gansa ba, a dai'dai wannan lokacin uncle Jahiz ya danno kai cikin fada, ta kofar da zata sadaka da cikin gida kenan.

Sun jero a tare shi da Jaish, tin ɗazun suka shigo cikin kingdom of power, yanzu haka basu fara isa ga kowa ba sai da suka iso ga King.

A karo na farko a tarihin kingdom of power yau King bai san lokacin da ya miƙe tsaye daga kan kujerar mulkinsa a zabure ba lokacin da ya ɗaura idanunsa a kan Jaish.

Tun da King yake bai taɓa jin wani abin na tashi hankali ko na farinciki or al'ajabi da zai sanya shi ya zabura ya miƙe tsaye daga saman kujerarsa ba sai dawowar Jaish unexpext, Ramish ya iya bazata kam gaskiya.

Sun jima suna dakon wannan rana shi da Momma, kullun addu'arsu Allah ya bayyana masu ɗansu farincikinsu, sai ga shi Allah ya bayyana shi a lokacin da basu tsammata ba, lokacin da suka fidda rai suka yanke kauna, suna cikin wani tashin hankalin kawai ya dawo garesu unexpext, kai Allah abin godiyane matuka, ya baka wani lokaci, wani lokaci kuma ya hanaka, dik cikin ikonsa da kyautatawansa ne!!.

Dik da commander yana cikin tashin hankali da damuwar furucin King a kan Hoorain zai karɓi hukunci hakan bai hana shi ya zaro idanu yana kallan Jaish ba.

Gabaɗaya su salama sun zuba mashi idanu, suna san yi mashi sannu da dawowa, amma babu hali, dan King bai bada damar ayi magana ba.

King ɗin kuwa, ya tsaya ne tamkar wanda aka dasa. Idanunsa sun zaro waje sosai, kallonsa a kan fuskar jaish ɗinsa da ya ke kallan abin tamkar a mafarki ko kuma zuciyarsa ce take yi mashi gizo.

Karisowa gabansa Jaish da uncle Jahiz suka yi, shi Jaish mamakin irin kallansa da King yake yi mashi ya yi, saboda in baku manta ba a baya ya yi loosing memorunsa ne, yanzu ne ya dawo dai'dai, so shi bai san da cewa ya jima baya gida ba, ya mance da rayuwarsa ta baya wato na gidan bappa kaf.

Har sai da Jaish ya tsugunna a gabansa domin kwasan gaisuwar ban girma wanda kun san yin hakan dole ce a sarauta matuƙar masu gudanar da mulkin irin King Zuhair ne masu ƙarfin izza.

Jin bugun numfashin ɗan nasa a kurkusa da shi ne yasa ya gasgata abin da idanun nasa suke gane mashi, amma dik da haka sai da ya ce.
"My Jaish kai ne? Hakika kai ne ɗana, tabbas kai ne!"............. Ya yi maganar cikin murya mai sanyi, amma cike da rawar jiki.

Bai jira amsar Jaish ba, ya yi sauri duƙawa ya ɗagosa ya jawo shi jikinsa ya rungume.

Rungumar tasa tana da ƙarfi, cike da kewar watanni da suka wuce. Ya rike jaish gam kamar kar ya sake barinsa ya motsa ko nan da can, kamar kada ya raba jikinsu tsantsar so da kauna.

"Na jima ina jiran wannan rana, mun jima muna neman ka........... ba zan sake rabuwa da kai ba!".
Ya furta cikin farinciki wanda ke haɗe da murmushi mai bayyana farincikin sosai.

Jaish da bai gane me King yake magana a kai ba sai ya ce. "Dad ba zamu rabu ba ai dama".

Kara kankamesa sosai King ya yi tamkar zai mayar da shi cikin cikinsa. Sai murmushi uncle Jahiz yake yi. Gabaɗaya fada sai da suka ɗan murmusa ban da commander wanda dama shi baya yin murmushi, sannan kuma ya kara haɗuwa da yana cikin damuwa King zai hukunta mashi ɗan gold ɗinsa.

Dawowar Jaish ya sanya su farinciki ya kuma sanyaya masu zuƙatansu akan raɗaɗin da suke ciki na rashin gimbiya Zunaira.

Yanayin ya cika da farinciki mara misaltuwa, kamar duniya ta tsaya domin wannan lokaci na musamman. Kowannensu yana jin tamkar zuciyarsa tana kara kaunar juna. Wannan haɗuwa ta koma alamar soyayya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login