Showing 159001 words to 162000 words out of 403653 words

Chapter 54 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

48

Khadijah da ta afka yasa bata ji shigowarsa bama, sai jin sautin muryarsa ta yi yana faɗin. "Zee lafiya kika zauna a nan?".

A ɗan razane ta ɗago ta kallesa. Kallo ɗaya ta yi mashi ta yi saurin kawar da kai, ta tsani maza dama idan baku manta ba, da shi kaɗai ta ɗan saki jiki ashe shi ma ɗan iska ne, wani tsanarsa ce ta ratsa zuciyarta, sai ta ji kamar ta gudu ta bar gidan, amma ina zata je to idan ta gudu?.

Kanta a ƙasa ta amsa mashi da babu komai. Ko kaɗan bai kawo aransa da wata matsala ba, dan shi yana ganin ai normal ne kallan da ya yi mata.

"To tashi muje Dr na jiranmu". Ya faɗa idanunsa a kan kirjinta dik da ta sanya kaya.

Da yake bata ma san fita zasu yi ba sai ta ji zancen wani irin, a ranta ta furta yanzu haka zata jera da wannan ɗan iskan? Sannan su shiga mota ɗaya a gidan baya, bayan haka su je hospital? Wlh ba dan Khadijah ba bata ga abin da zai sa ta sake ɗaga idanu ta kalli mutumin nan har ta jera a tare da shi ba.

Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufo shi, a maimakon ya wuce gaba sai ya ce mata ta yi gaba zai rufa mata baya, aikuwa nan fa ta ce babu wannan magana, kar ta fito ta ce mashi ita a'a sai dai ya wuce gaba ko ta fasa zuwa ta hakura da ganin Khadijah ɗin. Jin hakan yasa bai yi mamaki ba ya wuce gaba, da harara ta bishi tana jin kamar ta dallah mashi mari amma babu dama, zai wani ce ta wuce gaba dan ya ji daɗin kalle mata baya tana tafiya, to wlh ba zata yiwu ba, ta faɗa a cikin ranta tana harararsa.

Sai da ma ya ɗan yi nisa sannan ta rufa mashi baya. Ko da suka shiga mota taki ɗagowa ta kalli in da yake, shi kuwa a da idan sun shiga mota latse latsen wayarsa yake yi baya wani kallanta, yau kuwa zura wayar a aljihunsa ya yi yana cigaba da kare mata kallo da kyau kamar wanda ya samu tv. Dannewa ta yi kamar zata yi kuka, amma haka ta hakura har suka isa hospital ɗin.

Kai tsaye ɗakin da Khadijah take suka nufa, special room ne da aka ware mata ita kaɗai dan kula da ita sosai, a gaskiya ba karya ta samu kulawar da ta dace matuƙa. Tana kwance shiru idanunta biyu tana kallan sama, da yake ta yi ta shan drip sai bata wani rame ba, har wani haske ta kara yi sosai, ta kusa kamo Zee hasken fata, jikinta ya yi fresh sosai.

Tana ɗaura idanunta a kan su ta wani zabura ta miƙe zaune, idanunta a kan uncle Jahiz ba a kan Zee ba, ita kuwa Zee tana ganin ta farfaɗo ta tafi da gudu ta rungumeta tana ambatar sunanta. Tamkar ba Khadijah bace a wajen, ta kafe uncle Jahiz da kallo mai wuyar fassaruwa, lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka fara wanke kata fuska.

Hankali a tsakanin tashe ta furta. "Zee a ina kika samo wannan mutumin............". Sai kuma ta dakata da yin maganar, a hanzarce ta kai hannu ta fara goge hawayenta da suka fara zubowa, a take ta shanye kukan nata.

Jin furucinta yasa Zee ta yi saurin raba jikinsu da juna, a tsananin matse da san jin kan zance Zee ta ce. "Khadijah kenan da gaske shi ne a jikin wancan hoton ko? Dama na ce maki shi ne kika ce ba shi bane, kullun sai na kalli hoton nan in kuma kallesa idan mun haɗu da shi, har yau ban taɓa ganin banbancinsa da na cikin hoton ba, amma kuma kin ki ki faɗa mun gaskiya".

Da Hausa suke maganar, hakan yasa uncle Jahiz sam bai fahimci me suke faɗe ba.

Murya a raunace, da alamar karyewar zuciya a tattare da ita, da kyar ta iya cewa. "Zee kada ki sake yin magana a kan wannan hoto kamar yadda na faɗa maki a baya, na faɗa maki ba shi bane ya tsaya a iya hakan!! Idan kuma ɓacin rai'na kike so to bismilla ki cigaba, and in kuma ban isa in yi maki magana bane nan ma ki cigaba kasa ki dai'na".

Kalaman Khadijah sun taɓa zuciyarta, haka zalika wannan abin da ya faru yaja ta kara jin tsanar uncle Jahiz, lallai ba shakka a yanzu ta yarda Khadijah ta ɓoye mata babban al'amari fiye da wanda ya faru da ita abaya, tabbas akwai wata a ƙasa, wlh ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba uncle Jahiz ne a cikin wannan hoto, kuma tana kan bakarta babu gudu ba ja da baya. Tashin sense, wai wani irin ruɗanine wannan? Mekuke tinani? To dai ku kwantar da hankulanku, komai bala'in ruɗani da zaku shiga alkalamina zai warware maku gaskiya, zan zaƙulo maku meyake tsakanin uncle Jahiz da Khadijah and meyasa Zee ta ce shi ne a jikin hoton, shi kuma ya nuna kamar ba hakan bane? To mu dai je zuwa, lokaci ne zai warware mana.

Saman chair dake kusa da bed ɗin ya zauna, a tinaninsa kukan da Khadijah take yi na murnar ganin Zee ne, dan ya ga ita ma Zee ɗin tana ruwan hawaye, sai ya zuba masu idanu yana kallansu.

Massage ne ya shigo wayarsa, hakan yasa wayar ta ɗan yi ƴar ƙara. Zarota daga aljihunsa ya yi kallansa a kan Khadijah, shi dai yasan wlh ya taɓa kallan wannan fuska, kuma shi bai taɓa zuwa Nigeria ba sai wannan zuwan nasu, to a ina ya taɓa kallanta kenan? Ya jefawa kansa tambayar da bashi da amsarta.

"Ka samemu a meeting room". Shi ne sakon da ya shigo wayarsa, uncle Abbas ne kuma ya turo mashi wannan sako. Yana gama karantawa ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce masu su kasance a tare da yamma zai dawo ya ɗauki Zee. Dik cikinsu babu wadda ta iya amsa mafi, basu da bakin magana.

Bai wani damu ba yasa kai ya fice da sauri, yana fita Khadijah ta hau jerawa Zee tambayoyin a ina ta haɗu da wannan mutumi? Yadda take jera mata tambayoyi zaku fahimci hankalinta a tashe yake.

"Khadijah ki faɗa mun gaskiya, dan girman Allah ki fitar da ni duhu, ni ban ce karya kike yi mun ba, amma dan Allah ki sanar dani abin da yake a ɓoye a karkashin zuciyarki, ki sanar dani alaƙar Jahiz da wannan hoto na cikin akwatinmu, dan girman Allah ki faɗa mun shi ne baban baby Junior?".

Jin karshen zancen Zee yasa ta yi saurin kai hannunta saman cikinta, sai a lokacin tasan ma babu cikin a tattare da ita, a tsorace ta kai kallanta a kan Zee. "Zeezee ina cikina? Ina yake?".

Zama a gefenta Zee ta yi, cikin nitsuwa ta fara kora mata bayani yadda komai ya wakana har suna tsinci kansu a wannan hospital ɗin. Shiru Khadijah ta yi tana jinjina al'amari na ubangiji, idan Allah ya tashi amsa addu'arka sai ya haɗaka da bayinsa da baka taɓa zatan haɗuwa da makamantansu ba, kuma su taimaka maka, lallai ne ba shakka addu'a bata faɗuwa ƙasa banza, sai dai jinkirin amsawa, wannan jinkirin kuma shi ake kira da jarabawa ta Ubangiji, Allah zai jarrabaka da jinkirin amshi yaga zaka cigaba da yarda da tawakkali da shi ne ko dai imaninka bai yi karfi ba?! Lallai ba shakka su Khadija sun yi hakuri, sun kuma ɗauki wannan jinkiri a matsayin jarabawa wanda a yanzu Allah yake basu sakamakon hakurinsu cikin ruwan sanyi, tun da momma ta ce sai an bi masu hakkinsu hakika ba makawa sun san ikon Allah ne da ya amsa addu'oin da suka jima suna yi.

"Zee yanzu dai ki kyaleni na huta, idan na kara samun sauki sai mu yi magana". Cewar Khadijah. Na'am da hakan Zee ta yi suka cigaba da jinjina girman Allah.

•••••••••••••••••••••••••🔥

A ɓangaren Jaish kuwa, gobe Monday zai koma bakin aikinsa, sai dai fa har yau kudurinsa na bincike a kan wannan ma'aikata da suka tsunduma shi cikin wahala yana nan a ransa, bai janye ba!!.

After one day. Aneesa, Fanan, Chuchu ne suka shirya cikin uniform ɗinsu na school. Chuchu ta sha kukan rashin Auta, da farko har ta ce ita ba zata je school ɗin bama, daga baya da Yah Jawad ya rarrasheta sai ta shirya suka tafi, da kansa ya kaisu, sannan shi ma ya dawo ya shirya zuwa office. A tare da Jaish suka tafi kamar yadda suka saba.

Sarina kuma bata da class,.tana guda. So gidan ya rage daga Sarina, uncle Jahiz, uncle Taheer, uncle Abbas, su momma, King, Guyson yana nan, su twins, sai Zee da suke asibiti. Aunty MieMie tana part ɗinta.

••••••••••••••••••••🕊️

Momma da Mama Haulat ne zaune a bedroom na monma suna tattaunawa a kan irin dressing ɗin da yakamata su yi wa Mahnoor a lokacin da zasu kaita gaban su King.

Mama Haulat ta kawo jerin kayayyaki na alfarma masu bala'in kyau da tsada da yakamata su shiryata a ciki domin kaita, momma tana dudduba hotunan kayan ne, dikka cikin waɗan da ta yi oder su daga Dubai ne, tun jiya aka kawo kayayyakin kusan mota guda.

Mammie da Sarina kuwa, suna nasu shirin dan su zo part ɗin King su kalli Mahnoor, su kalli dame ta fi Fanan? Sun san cewa King ya ce nan da karfe 8 na safe dai'dai a kawo mashi ita ya ganta kafin ya fita fada, shi ne suma suke sauri dan su zo su ganta, saboda sun san idan King ya aminta da ita yadda momma ta kwallafa rai a kan sonta ba lallai su rinƙa samun damar ganinta ba, kunga in King ya aminta da ita zata koma part ɗin Jaish ne, to da ni da ku dai mun san dik rashin kunyar mai rashin kunya baya tinkarar part ɗin Jaish, bayan Auta da Guyson, King and Yah Jawad, sai momma da mama Haulat ne kawai suke iya shiga part ɗinsa, ko su Omaid basa kaunar dosar wajen, dan kun san dalili.

So sun san tana shiga part ɗinsa ba zasu taɓa samun damar ganinta yadda yakamata ba.

Uncle Jahiz, uncle Abbas, King, Akka su ne zaune a cikin parlon King suna jiran momma, King ya buƙaci da Mummyn Chuchu da Mama and Mammie dik su zo. Akka ta samu lafiya yanzu, jikin ya yi kwari, sai dai fa masifa ya karu, yaseen kana taɓota kaɗan yanzu ka shiga talatin, sauke haushin rashin Spender zata yi a kanku.

To King ya bata labarin Jaish ya yi aure, shi ne ta ce wlh bata yarda ba, dan haka dole a warware wannan aure, da kyar autanta uncle Jahiz ya shawo kanta a kan ta yarda ta kalli Mahnoor ɗin ko sau ɗaya ne, taga idan bata dace da Jaish ba sai a warware auren, to shi ne dalilin hallararta a parlourn King, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya cikin shiga ta alfarma, eh mana uwa ga manyan kai ba, ta dake cikin alkyabbar na girma, sai wani kafafa take yi, har da cewa ko ta ga Mahnoor fa ita ba zata taɓa yarda da wannan aure ba, uncle Jahiz da yake yana bin bayan Momma dan tana rufa mashi asiri bakinsu ɗaya, sai ya ce da Akka e dai su bari Mahnoor ɗin ta zo aganta.

Wlh uncle Jahiz da momma bakinsu ɗaya, ita ke goya mashi baya, harta batun tafiyarsa kwallan kafa ita ta tsaya mashi, da Akka taki yarda, amma da momma tasa baki sai suka fi karfin Akka dole ta yarda, so in short dik abin da ya ɗebo rufewa suke ita da shi abinsu, shiyasa kuka ga suna mugu mugun shiri da juna, ya fi santa fiye da sauran matan King.

Saida momma ta tsaya ta hantse ta zaɓawa Mahnoor wani haɗaɗɗen gown mai kama da weeding gown, daga ta sama daidai da ita zuwa waist ɗinta, kasa ya yi bala'in buɗewa kamar umbrella, rigar launin pink ne da ratsin golden, ga wasu ƙayatattun duwasun alfarma masu kyalli da suke walwali suka kara ƙawata kayan rigar, sannan ga wasu manyan zanen flowers a jikin kayan, rigar ta haɗu, ga tsada kamar me.

Wasu half cover masu kwalliya da duwatsun lu'ulu'u momma ta zaɓa mata, takalmar launin golden kalar kwalliyar jikin rigar, ai ku daga jin kwalliyar dutse mai daraja wato lu'ulu'u a jikin takalmar kun san kuɗinsu ya wuci baki ya faɗa.
Dankareran alkyabbar launin golden kalar takalmarta momma ta fidda mata, alkyabba ce wanda King Badeen wato mahaifin momma ɗin ya saya mata a lokacin da za'a kai ta gaban King Abdul Malik mahaifin King Zuhair kenan, a lokacin ya saya mata su guda shidda, to da guda ɗaya ta yi amfani sauran biyar ɗin sunan sabbi gal, a lokacin da tasa wannan alkyabbar sai da kowa yasan e lallai ƴar the most powerful King ta fito, alkyabbar ce wanda ba'a samunta a ko'ina, kwalliyar jikinta da duwatsun lu'ulu'u aka yisu, haɗuwar alkyabbar baki ba zai iya faɗarsa ba.

Mama Haulat sai da ta sha jinin jikinta jin cewa momma zata bawa Mahnoor wannan alkyabba mai dajara tasa, domin kuwa ita tasan darajar waɗan nan alkyabbars ɗin, momma kuwa dama matan ƴaƴanta ta ajiyewa, sai kuma Allah yasa tana kaunar Mahnoor ɗin, kunga kuwa fin haka ma zata iya yi mata.

Dik jikin mama Haulat ya yi sanyi ganin kyautar momma ga Mahnoor, amma haka ta miƙe ta karɓi alkyabbar, nauyi sosai yake da shi, saboda duwasun lu'ulu'u da aka kawata kyalliyarsa da shi. Haka ta nufi waje da shi, kai tsaye ta je ta ɗauko kayanda momma ta zaɓa za'a haɗawa Mahnoor ɗin da su.

Kai tsaye ɗakin gyara ta wuce da su. Momma ma wanka ta je ta yi ta shirya, sam babu faɗuwar gaba a tattare da ita a kan wannan matsala, domin ita ɗin macece mai jajircewa a lamuranta, bata san faɗuwa ba, tana da yakinin zata yi nasara.

Su mummyn Chuchu dik sun hallara a parlourn King momma kawai ake jira, Sarina da shegen gulma har da wani zuwa ta zauna kusa da uncle Abbas, ta wani kwanto a jikinsa dik dan gulma, kamar da gaske haka take jinsa a ranta, kawai tsabar san kallan Mahnoor ne. One funny thing kuma shi ne yau sai ga Sarina da alkyabbar, saboda su King suna wajen, sai ta yi shigar mutunci, ni ko na ce ashe rashin kunyar tata ta karya ce ƴar ƙaniya.

Karfe takwas yana bugawa dai'dai wani irin daddaɗar kamshin perfume mai kwantar da hankali ya fara dukan kofofin hancin kowa dake cikin parlourn King, turaruka masu tsadar gaske da shegen kamshi momma ta sa aka kawo mata, sai Allah yasan daga ina ta samo waɗan nan zafafa turarukan ta feshe sirikarta da shi.

Tin su momma basu kai ga shigowa ba kamshin Mahnoor ya aiko masu sallama. Dikkansu sai da suka shaki kamshin suka ɗan lumshe idanu. Kowa ya fara rarraba idanu a kan hanyar shigowa, suna jiran suka ɓullowarta.

Like wow lokacin da suka sako kafafunsu a cikin parlon, gabaɗaya kallo ne ya dawo kansu. Momma na ɗan rungume da Mahnoor ɗin suka shigo, suna takawa cikin natsuwa.

Like wow tamkar wata tauraruwa haka Mahnoor ta haska, shigar kayan jikinta kawai suke kallah, Sarina alkyabbar kawai take kallah ma tukun nan, bata taɓa kallan irin wannan alkyabbar ba.

Mummyn Chuchu ce ta yi saurin miƙewa ta taro momma, dik da basu san wacece momma ta riko ba, amma suna da haɗin kan taimakawa junansu a irin wannan yanayi. Gefen Mahnoor ta zo ta rungumo suka karisa da ita ciki.

Mammie da tin da suka sako ƙafafunsu take ta faman leƙo fuskar Mahnoor tana san ganinta amma ba dama, dan alkyabbar ya yi mata yawa, hularsa ya fi kanta sosai, kunsan na faɗa maku na momma ce, dik da lokacin bikin momma ita ma da kaɗan ta fisu, amma dai ya yi mata yawa, hakan yasa hular alkyabbar ya sauko mata sosai, kuma ya haɗu da ta sunkuyar da kanta ƙasa, so ba'a iya ganin face ɗinta.

Ita kuwa Sarina bata kai ga batun face ɗin amarya ba, tsadaddun kayan jikinta kawai take kallah, ta mutu da san alkyabbar, sai dai ba samu zata yi ba, dan na manyan mata ne wannan.

A gaban King suka kawota, mama sai binsu da kallo take yi, bare Mammie da ta saki baki ta rasa abin faɗe kamar wata gaula.

Dama King, uncle Abbas, uncle Jahiz a saman kujerar ɗaya suke zaune mai zaman mutun uku kenan, so a gabansu Mahnoor ta zube gwiwowinta kanta a ƙasa.

King ne ya fara cewa Momma ta kaita wajen Akka tukun nan, su fara gaisawa da Akka. Ƙara ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya da kyau Akka ta yi, Queen mother zata yanke hukunci e mana, Akka tamu ta amana.

Rikota mummyn Chuchu ta yi, ita ta kaita gaban Akka ta durkushe gwiwowinta. Sannan suka koma saman sofas ɗinsu suka zauna. Ɗago idanu Akka ta yi ta karewa su Momma kallo kamar na mintu biyu, sannan cike da izza ta ce.

"Ina Zunaira?"........ Dum dum kirjin kowa dake cikin parlon ya buga except Mammie and Sarina, babu wanda ya taɓa expecting Akka zata nemi Auta a yanzu, nan fa parlon ya koma kallon kallo a tsakaninsu, an rasa mai iya bawa Akka amsa, dan sun san dik amsar da zasu bata ba zai taɓa gamsar da ita ba, babbar magana.

Tsit parlourn ya yi tamkar uwar gulma ta yi cikin shega. Can dai uncle Jahiz ya yi ta mazan cewa. "Zunaira bata nan, sun koma school".

Shiru Akka ta yi na ƴan mintuna da zasu kai uku haka, sannan ta ce. "Amma kun san a bisa al'ada Zunaira ce take da damar buɗe fuskar amaryar ko?".......... Jinjina mata kai suka yi alamar tabbas sun sani. Ita dai momma shap ta mance da wannan al'ada, tabbas tasan kanwar miji

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login