Showing 375001 words to 378000 words out of 403653 words

Chapter 126 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

99

Da yake momma tasan hali, sakalcin Pretty ya wuci tinani, sai ta ce mata. "Ke da waye kuma babyn Yah Omerish? Yau ba'a kai mashi kara ba sai aka kawo mun?". Momma bata san yau shi ya yi laifi ba, yau kararsa aka kawo ba na mutane da aka saba kawowa or kai mashi ba.

Ita dai momma ba ruwanta, ta fita daban, dama a ko'ina akwai na kirki dana banza, ita dai bata nuna kabilanci da kyamar wasu da ba nasu ba, kowa nata ne da hannun bibbiyu take rungumesa!!.

Cikin kuka ta ce. "Momma Yah Omerish ne ya sa bakinsa a cikin nawa, kuma yasa mun yawunsa da babu zaki babu daɗi a cikin nawa, ya kuma sha mun nan". Ta kai karshen maganar tana nuna lips ɗinta da hannu!. Ajiyar zuciya momma ta sauke, dama tasan za'a yi hakan one day one time, saboda su jaraba gadonta suka yi, ita kuma Pretty ga ɗan banzan kyau kamar ita ta yi kanta, ai keɓewarsu waje guda abu ne mai haɗari sosai, shiyasa take ta lallaɓa Smart ɗin ya aureta kawai sai ayi dik wacce za'ayi, wlh ita Momma ta san cewa Smart yana bala'i kaunar Pretty, dan kuwa ita ce mace ta farko bayan ita da mom ɗinsa and Auta da taɓa shiga rayuwarsa har ta zauna kusa da shi, abin gaskiya yakamata ta ɗauki mataki.

Tana can tana tinani sai ji ta yi Pretty ta miƙe zata bar jikinta tana faɗin. "Bari in je in faɗawa Zunaira abin da Yah Omerish ya yi mun"..... Ita fa Pretty bata ma san dik gurmin da ake yi a kan Auta ta mutu ba, dan tana waya da ita idan ta je wajen Smart, so dik bala'in da ake yi a kingdom ɗin ko a slippers ɗinta, hankalinta a kwance..

A hanzarce momma ta rikota tare da cewa. "Ba sai kin faɗawa kowa ba kin ji my baby? Kada ki faɗawa ko Zunaira ɗin ce ma, ki bari iya ke da ni zan rama maki abin da ya yi maki!". Girgiza kai ta yi. "Ni Momma ki bari in faɗawa Zunaira, ai ita ma ta faɗa mun da Hoorain ɗinta ya sha bakinta"....... Ai momma bata san lokacin da ta zaro idanu waje ba, bala'in can, yaushe Zunaira ta iya dikka wannan abin? Yaushe aka yi hakan? Innalilahi wa inna ilahir rajiun! Gaskiya King ya yi kuskure da ya hanasu mallakar juna, abin har ya kai haka?.

Tana can tana tinani Pretty zata gudu, kuma fa wajen Smart ɗin zata koma dan yarinta, shi ne kawai zai kira mata Auta a waya ta kuma faɗa mata ya sha mata baki, kai kuruci dangin hauka.
"Zo mana my baby, baki san shi Yah Omerish ɗin mijinki bane? Shi zai aureki ai! Kada ki faɗawa kowa abin da ya yi maki, ki rufe sirrinku". Momma ta faɗa mata hakan ne dan ta samu ta yi mata wayo kada ta faɗawa kowa, sai dai ina, taki fir, ta ce babu wannan magana, ita wlh sai ta sanarwa da Zunaira abin da yake faruwa.

Cigaba da lallaɓata momma ta yi, dan ta samu ta yi shiru, tasan idan ta ce zata yi abu to wlh sai ta yi ne, idan kuma ta ce ba zata yi abu ba ko me zaka yi mata ba fa zata yi ba, ai abin da kunya ta faɗawa Auta ga babban yayansu ya yi mata kiss, haba zata zubawar da Smart mutunci................😅

To shi ɗan air me ya kai shi dama, ko da yake ba laifinsa bane, laifin Prettyn ce, ƴar rainin wayo sai ta rinƙa yi mashi abubuwa, ta godewa Allah ma da abin ya tsaya a iya kiss, badan yana da dauriya ba yadda suke da gadan abar ai wani canza ake ba wannan ba, in ba iskanci irin nata ba ina ruwanta da cibiyarsa? Dan ta saba yi wa Kamran haka, shi Kamran a lokacin da take yi mashi ai kunga bai ma san me feeling ba, time da ya fara jin feeling ya sanar da mammarsa kuma ai kunga kashe mashi sha'awar ta yi da magunguna, ko kun manta lokacin? Saboda ma kada ya shiga haɗari ya yi ciwo tasan babu mata a forest ɗin shiyasa take bashi magungunar kashe sha'awa, wannan yasa dik abin da Pretty take yi mashi baya jin komai bawan Allah, amma Smart fa? Ai kunga da banbanci, dole idan ta yi mashi ya yi mata...........🥱😅

Da kyar momma ta shawo kanta ta hanyar yi mata alkawarin cartoon na kayan zaƙi, sannan ne ita ma ta yi alkawarin ba zata faɗawa kowa ba, ajiyar zuciya momma ta sauke kafin ta miƙe haɗe da riko hannun Pretty ɗin ta ce da mom tana zuwa bari ta duba Smart. Da okey mom ta amsa, bata jin larabci bata ji me suka tattauna da Pretty ba.

Bedroom na Smart momma ta nufa da ita, a parlourn ta ce mata ta zauna bari ta zo, da okey ta amsa tare da zama saman sofa tana turo baki ita kaɗai kamar wadda aka yi wa wani abin. Ciki momma ta wuce, yadda Pretty ta bar shi haka momma ta shigo ta samesa, idanunsa a lumshe, da alama tashi jarabar ta fi ta kowa, har sallama momma ta yi mashi amma bai jita ba, hankalinsa ya yi nisa sosai.

A saman bedside drawer ta zauna tare da kai hannu ta ɗan shafi lallusan gashin kansa. Nisawa ya ɗan yi ba tare da ya yi magana ba, sai dai ya waro idanunsa da suka kaɗa suka yi jajir kamar wuta. "Omerish". Momma ta ambaci sunansa cikin sanyin murya, bai iya amsa mata ba, sai dai ya ɗan juyo da kallonsa a kanta, sai a lokacin ya farga da Pretty bata a cikin ɗakin, a hanzarce ya yunkura ya gyara zamansa yana ɗan wawwaigawa nemanta!.

"Bata nan ta fita". Momma ta bashi amsa, dawo da kallonsa a kan mommar ya yi, da yake shi ba kunya ne da shi ba, renon masu jajyen kunnuwa sai ya ce. "Momma ta je ta faɗa maki na yi kissed ɗinta ko?"....... Jinjina mashi kai momma ta yi alamar e, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To ina take ta zo muci abinci". Ya faɗa yana kawar da kallonsa daga kanta.

"Tana parlour, amma yanzu dai ba wannan ba, idan kun kammala cin abincin sai ka ɗauketa ku je ka siya mata cartoon na kayan zakin da na yi alkawari, sannan ina da magana da kai". Juyowa gareta ya yi. "Kayan zaki kuma a daren nan?". Kai ta jinjina mashi alamar e kafin ta ɗaura da cewa. "Sai da na yi mata alkawarin kayan zaki sannan ta yarda ba zata sanar da kowa abin da ka yi mata ba".

Da mamaki ya ja ɗan siririn tsaki haɗe da cewa. "To me a ciki momma dan ta sanar da na yi kissing ɗinta?"......... Momma bata yi mamakin jin hakan ba, dan tasa daga ina ya fito, ba ruwansa da wani kunya. Kawar da zance ta yi da cewa. "To ni dai ina san kuje ka saya mata kayan zaki". Ita dai momma tasan kunya, kuma tasan wannan ba magana ce da za'a fitar da shi ba, yana matsayin Prince ace Pretty ta fitar da wannan magana ai sam bai yi ba!
"Momma zakin nan fa cuta ce a gareta, baikamata take sha ba". Yana ɗan ɗaure fuska ya yi maganar. "For today dai ka saya mata". Shiru ya yi yana tinanin yadda zai yi ya rabata da zakin nan ya huta. "Omerish ". Ta ambaci sunansa tana kallansa.

Dawo da kallonsa a kanta ya yi. "Na'am Momma".
Tattara natsuwarta ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Omerish kana son Pretty, meyasa ba zaka yarda ka aureta ba kawai tin da ire-iren waɗan nan abubuwa sun fara shiga tsakaninku?".......... "Momma saboda na yi kissed ɗinta ba shi ne zai nuna ina santa ba, kiss daban soyayya daban that's all!".

Shiru momma ta ɗan yi, yana neman goge mata hadda, wato kiss ba wani abin bane, e lallai ma Smart, wato zai gaji babansa kenan!!.

"Na yarda kiss daban soyayya daban, amma kuma ai kasan haramun ne ka yi mata hakan ko?". Shiru ya yi bai bada amsa ba, babu kuma alamar zai yarda da zancen momma ɗin ma.

"Please ka yarda ka aureta ga ji my son? Ina san yarinyar sosai, na tabbata zaka ji daɗin zama da ita, kuma nasan kana sonta kai ma......." Saurin katseta ya yi da cewa. "Ni bana sonta momma, ki dai'na faɗa mun haka".... Murmushi irin nasu na manya ta saki kafin ta ɗan girgiza kai, a ranta ta ce ta yaro kyau take bata ƙargo, a fili kuma sai ta ce. "Na yarda baka sonta, amma nikuma ai ina sonta ko?".

Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, can kuma sai ya ce. "Momma please ki bari in yi dinner, am feeling hungry, ta ya za'ayi ki fara cewa in auri wannan ƴar yarinyar da na kai in haifeta". (Ku ji iskanci, wai ya kai ya haifeta amma a haka ya sha mata baki.🤔)

"Amma kuma ai dik da ka kai ka haifeta ɗin zaka iya kissing ɗinta ko?"........ Wani irin kallo ya wurga mata haɗe da cewa. "Mommaaaaaaa, zaki fara ko? Shiyasa jiya naki zuwa wajenki, saboda kada ki cigaba da kawo mun zancenta, ga mom ta dameni da zancen Heleena, so kuke yi in daina zuwa wajenku ko?.........." "Mom ɗinka ai bata san ka rabu da ita ne shiyasa take son ka auri Heleena, kaga zaku kasance a tare, nima bana son ka rabu da ni shiyasa nike son ka da Pretty, please ka duba mu mana my son". Cikin tausasawa ta faɗa.

"Momma mata mayaudara ne, please ku kyaleni haka, ni bana da sha'awar wata mace ta shiga rayuwata a yanzu, Please kada ku katsa mun farincikina". Ya kai karshen maganar yana saukowa kasan bed ɗin. Riko hannunsa ta yi da sauri, hakan yasa ya dakata a bakin bed ɗin ba tare da ya karisa sauka ba. "My son meyasa yanzu baka son farincikina sosai ne?".
"Mommaaaaaaa, zaki fara ko?". "Gaskiya na faɗa ai". Kai ya girgiza. "Kenan kin san ina sanki kuma ina san farincikinki, kawai so kuke ku wahalar dani"....... "Haba my aboy".... "Mommaaaaaaa wai ba zaki manta da wannan suna ba?". Ya faɗa yana binta da kallon kauna.

"Sai ranar da matarka ta haifa mun jika zan daina ce maka sunan in mayar kansa, idan kana son na dai'na faɗa to ka yi aure ka haifa mun jika". Ta kai karshen maganar tana shafa kansa. Cikin sanyin murya ya ce. "Dik abin da kike so kin san shi nike yi mommata, kuma farincikina, this time ki ɗan bani lokaci zan yi tinani, zan yanke hukunci"........... Jinjina kai ta yi tare da cewa. "Okey tom amma ka yanke hukunci mai kyau, sannan ka rinƙa kulawa a zamantakewar da Pretty, kada ka zurfafa abubuwa"...... Ya gane nufinta, wato kada ya rinƙa taɓa Pretty har a kai ga kiss, ya gane in da ta dosa, sai ya miƙe kawai ba tare da ya sake yin magana ba ya nufi wajen abincin nasa. Miƙewa momma ta yi ta nufi waje tana sanya mashi albarka.

Tana fita ta turo mashi Pretty, babu ko sallama ta afka mashi cikin ɗaki, alamarta ya gani ta wutsiyar idanunsa, bai ce mata ko uppan ba, a kusa da shi ta zauna tana kallan abincin. Tana zama ya kai hannu ya capki shoulder ɗinta haɗe da cewa. "Saboda na yi kissed ɗinki shi ne zaki kai karata wajen momma?". Harara ta dallah mashi kafin ta ce. "Saboda me zaka saka mun yawunka da babu zaƙi kuma babu daɗi? Kuma na goge bakinka da ya taɓa nawa tas, na tufar da yawun naka ma".

"Da gaske?". Ya tambaya. Kai ta gyaɗa mashi alamar e tana yamutse fuska. Ɗan ciza laɓɓansa ya yi, alamar ya ji haushin abin da ta yi wai ta tofar da yawunsa kuma ta goge bakinta in da nasa ya taɓa. Hannunsa ɗayan yasa ya janyota jikinsa, da karfi ya matseta tare da kai ɗayan hannunsa ya matse mata ɗan bakinta, lips ɗinsa ya kai saman tata, sai da ya tsotsa son rana, sannan ya cika mata yawunsa sosai a bakinta, ya kuma matse hancinta yasa dole sai da ta haɗiye kafin ya saketa tare da ɗaukar spoon da nufin ya fara cin abincinsa, yawa wani irin sauke ajiyar zuciya, shi kaɗai yasan me yake cikin zuciyarsa!!.

Kuka ta saka mashi mai sauti yana faɗin Allah ya isanta, ta yi maganar tana kai hannunta saman lips ɗinta ta hau gogesu dana dirzasu da karfi karfi. Shi kuwa abincinsa ya cigaba da ci ko a jikinsa, yana ganinta ta wutsiyar ido tana ƙoƙarin goge bakinta. Sosai ya ji daɗin hakan, koba komai ya haɗiye yawunsa sosai, har zata ce yawunsa babu daɗi ta tufar, to ai ga shi yanzu ta haɗiye. Miƙewa ta yi da gudu zata fita daga ɗakin, da sauri ya kai hannu ya rikota tare da mayar da ita ya zaunar.

"Ina kika fita daga ɗakin nan yau ba sai gobe ba tare da tiger zaku kwana a ɗaki guda, in kuma kin ce ba haka ba fita ki gani". Ya kai karshen maganar tare da sake mata hannu. Kuka mai tsuma zuciya ta fashe da shi tare da kwantawa a saman carpet ɗin ta juya mashi baya. Banza da ita ya yi ya cigaba da cin abincinsa kamar bai san tana yi ba!.

A can gefe kuma, uncle Abbas yana sanar da Mammien ya yi wa Sareena miji wato Smart, haƙiƙa Mammie ta ji daɗin wannan haɗi, dama burinsu kenan, yau zata zuba ruwa bisa ƙasa ta sha, har ta kira Sareena a waya a kan ta zo ta ji daddaɗar labari!!.. Shi kuma King yana nan damuwa sai kara ninkuwa a ransa take yi, ya yi zaton ya rufe sirrin da bawan da zai iya sani, ya aka yi Smart ya sani to?. Shi fa King a tinaninsa idan ya yi wa Smart aure shikenan zai koyi sanin darajan mutane da girmamasu, shiyasa ya nema mashi auren Sareena!. Kun san aure yana canza abubuwa sosai.

A ɗayan ɓangare kuwa uncle Jahiz sai ƙoƙari shiga zuciyar Zee yake yi, while ita kuma ta rigada ta kamu da soyayyar Dr Raj, shi kaɗai take gani, dik in da uncle Jahiz zai je suna a tare da baby Ahmad, wato yaron Khadijah, yaro ya yi wayo yanzu, har rarrafe yake yi, Allah sarki mai keken napep ɗinsu dai ya samu sauki ya koma Nigeria, sun karɓu numbersa a zuwan idan sun dawo zasu nemesa su gana, uncle Jahiz ya yi mashi kyautar makudan kuɗaɗe.

While shi ma uncle Abbas yana can yana fama da tinanin Khadijah a cikin kwakwalwarsa, yarinyar tana burgesa sosai. Ita kuwa Akka tana can tana fama da tashin hankali, dan King ya sanar da ita batun da ake ciki, dik yadda aka yi ita ma ta san wasu sirrikan da suke ɓuye.

Mammie kuwa ta sako Mahnoor a gaba yanzu, burinta ta rabata da Jaish wanda banda wahalar da ita babu abin da yake yi dama, yana sonta, amma sai ja maga rai yake yi, yasata ta yi ta abubuwan wahala dik saboda iskanci irin nasa. Chuchu na can tana fama da jinya, dan har yanzu bata warware daga ciwon rashin Auta ba, Aneesa ma jinya take yi. Mama kuwa tana nan tana raba jaraba na wanna hali nata, ta ki yarda Smart ɗan King ne har yanzu, ta matsawa Ramish sai ya yi mata bincike, ya dai ce mata to kawai, dan shi ma yanzu abin da yake kansa kawai ya ishesa.

A gefe guda kuwa, guyson da yake Dubai kullum sai ya kira Jaish video call ya ce ya haɗa shi da Mahnoor, idan ya haɗasu sai ya roketa ta haɗa shi da Mahreen, sai dai Mahreen ɗin bata karɓar wayar, sai Mahnoor ta rike mata suna hira, masifa take zazzaga mashi amma shi daɗi yake ji, Mahnoor tana yi mata faɗa sosai a kan masifar da take yi mashi, amma taki dai'na wa, ta ce ai ɗan iska ne shi, shi dai kome take faɗa murmushi kawai yake yi, dan burgesa take yi, kuma burinsa ya cika idan ya ganta.

Daga gefe guda kuwa Sareena da team ɗinta ne suke ta shirya munafurcin da zasu yi wa Pretty. Ta ce su zuba mata Acid, Omaid ya ce. "Amma ke Aunty Sareena kanki baya ja, ai kina zuba mata acid ko zaki mutu cikin minti ɗaya Yah Omerish zai kamamu, hmmm baki san shi ba ko? Shegen kwarone in faɗa maki, yana ganin idonmu zai san mu muka aikata!. Ke da zaki kawo shawarar da zaki sanya ya tsaneta ko ta tsanesa! Baki san soyayya bako? Ai ko kin zuba mata acid idan sonta yake yi da gaske ba zai dai'na sonta ba, dan soyayya babu ruwanta da kyau or muni".

Obaid ne caɓi zancen da cewa. "Haka ne, acid ba zai sa Yah Omerish ya rabu da ita ba, kuma wlh in dai acid ne zamu zuba mata to watan cin ubanmu ne ya tsaya, abin da zai sa ta tsane shi ko ya tsaneta shi zamu kirkira". KAI WATO GASKIYAR SMART, ƳAƳAN MOMMA BA DAI KAI BA, UHMM SU TWIN'S SHEGUN KWARI NE YARAN NAN, AKWAI BASIRA, A MAIMAKON SU YI AMFANI DA BASIRAR DAN TAIMAKO, SAI SUNA KARAR DA SHI A MUGUNTA DA SHIRYA TUGGU, KAI WAƊAN NAN YARA SAI SHIRIN ALLAH.

Shiru Sareena ta yi, sai yanzu ta ɗauki haske da suka faɗa mata, cikin zaƙuwa da zan jin meyakamata su yi mata ta ce. "To ku bani idea, kai'na dik ya kulle, ban iya tina komai".

Omaid ne ya ce. "Zamu faɗa maki abin da zamu shirya amma ba yanzu ba, bari mu yi tinani da shawara". ....... Sosai ta ji daɗi, dan bata taɓa kawo kukanta garesu basu share mata hawaye

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login