Showing 66001 words to 69000 words out of 403653 words
faɗa mata komai, da zarar ta kawo zancen Jaish Mahnoor zata doje taki yarda su yi ta.
Daga karshe Jumma ta fahimci Mahnoor fa ba zata faɗa mata ba, sai kawai ta hakura, a tinaninta iya kunya ce kawai tasa Mahnoor bazata sanar da ita ba, bata san ba haka bane, Mahnoor tasan wannan sirrin mijinta ne shiyasa taki yarda ta faɗa, sai dai su yi hira na iya labarin da ya shafi kauyen, amma Mahnoor bata yarda a shigo da hiran Jaish ba, da Jumma ta sako maganarsa bakin Mahnoor zai fara haila ta ki bata amsa, sai ta yi kamar bata ji me ta ce ba, daga karshe ta kawo wani zancen ta ɗaura a kai.
Har sai da mangariba ta kawo kai, sannan Jumma ta tafi ita kuma Mahnoor ta fito ta kama aikin da ta saba.
A tsakar gida ta isko Mahreen tana zaune ta buga uban tagumi kamar dai ɗazun a gona, shi kuma bappa ya wuce masallaci daga nan ya wuce gidan Arɗo dan su yi magana a kan Mahnoor ɗin.
After some days. Bayan wasu kwanakin.
An ɗaura auren bappa da Mairo tamkar yadda aka ce, yanzu saura tarewa, kwana uku kenan yau da ɗaura auren, babu wani biki da suka gudanar saboda na faɗa maku ita ba budurwa bace, so iya ɗaurin aure ne kawai sai kuma wannan al'adar tasu da suke yi nahawa dutse dan a rubuta sunan ma'aurata, wannan dole ce a wajensu, sannan sai al'adar da suke yi na yanka shanu ayi ta gashi, a can gidansu Mairo kuma an yi al'adar da iyaye da makota suke yi wato a tara nono da fura dayawa ayi ta sha, kowasu makota ranar ba zasu sayar da nono da furansu ba, zasu haɗosa a kawo gidansu Mairo, shi ne nasu gudumawar.
Dik bakin da zasu zo sai su yi ta sha babu kakkautawa.
So iya abin da aka gudanar a bikin kawai, Mahnoor dai bata je wajen bikin ba, tana wajen Inna kakarta, Mahreen kuwa da bata ga abin da zai hanata zuwa wajen biki ta ci uwar sabada ba ai sai da ta je, ta ci uwar kyalliyar powder gora guda ta zazzage a face ɗinta abinta, kamar aljanar asuba, amma saboda bala'inta kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau sosai, kuma karya suke yi ba wani kyan da ta yi, kawai suna tsoron bala'inta ne yasa suke yabata ɗin munahikai. Kaki yabata ka shiga uku.
Har da su Jumma sun je bikin, sun kuma yaba kyan Mahreen ƴar amarya kenan, dan ita ta gama shaidawa kauye yanzu ita yar Diddi Mairo ce ba ƴar Nenne ba, wato a duniya yarinta ma fa duniya ce, ba abin da ya kai shi daɗi, ta dai ce ita ƴar Mairo ce, ta koma tsagin amarya.
Kwanaki uku ana ta hidima, yau za'a kawo Mairo ɗakinta ko in ce zata tare a ɗakinta, bappa bai yi mata wani ɗaki na daban ba, ya ce a ɗakinsa zata zauna, so nan kawai ya gyara mata, yaki yi mata wani bukkar.............. Ni Princess Teema na ce anya bappa ba ɗan duniya bane kuwa? Wato so yake bakinciki ya kashe Nenne ko? In ba tsabar minahinci ba ita ma ya yi mata ɗakinta daban kamar Nennen mana! Me na wani ta sauka a nasa ɗakin?.
My people's kuzo mu yi gulma, anya ba maman Mahnoor bawan Allahn nan yake gani a tattare da Mairo ba kuwa? To mu dai yanzu zamu koma team uwar gida Nenne dan mu taya Nenne faɗa, haba wannan wani irin bala'i ne, yar cikinta ma ta gujeta ta komawa amarya, to mu ba zamu yi lamurje ba.🙄
To izina garemu mata, shi dai bakin hali yana raba ka da kowa, ciki harda ƴaƴan da ka haifa a cikinka, ya rage naku ku kyautata zamanku da kowa, ku zaku ji daɗi idan kuka iya zama, kai in fa kuka zauna da kowa lafiya wlh sai kunfi abokan zaman nakuma cin ribar zaman, ina fatan kun ɗauki darasi?!!.
Wato akwai dirama a gidan bappa fa, dan kuwa ko da ƴan uwan Mairo suka kawota basu kwashe ta daɗi da Nenne ba, dan kuwa irin wanna nasiha da ake yi ace an kawowa uwar gida amana nan da suka zo zasu bawa Nenne amana ta yi masu wankin babban bargo, har da cewa su dai kaiwa bappa amana tin da shi ya rakitimowa kansa ita kuma yake ganin zai iya, dan haka a kai mashi ba dai ita ba!!!.
Ta ci masu mutunci fes, dik da haka kuma bai isheta ba, da taga basu kulata ba sun nufi cikin ɗakin bappa sun kai Mairo suna karisa mata jeren da basu gama na.
Sai Nenne kam ta fito da tanadin da ta ɗauki sati guda tana shirya masu, wato wuta ta hura yana ci sosai, sai ta banka barkono mai bala'in zafi da yawa a cikin wutar, ai ba iya ƴan kawo amarya ba, gabaɗaya unguwar rikicewa ya yi da tari mai sauti, kun san yadda barkono yake a cikin wuta.
Haba ai ba yan kawo amarya ba, harta ita kanta amarya bata tsaya ba, tuni suka ari kafar kare suka cikawa zannuwansu isa. Binsu da barkono da toka wanda ta daka barkonon ta tanƙaɗe toka ta haɗe su wajen guda ta rinƙa ɗaurawa a leda, to shi ta rinƙa binsu da shi tana harbinsu da shi, yana da bala'in zafi ga shiga hancin mutun.
Idan ta harba shi ya faɗi kasa ya fashe sai tokan ya tashi sama da garin barkonon, ya yi masu dai kamar guguwar turɓaya yana shiga hanci. Balai'n zafi ne da wannan abin.
In short pata pata Nenne ta yi masu, ta zama kamar mahaukaciya, dik wasu abubuwan da aka kawowa amarya sai da ta ta dawo ta watsa shi kaca kaca, abubuwan fashewa dake cikin kayan kuma dik ta bi ta fashesu rugu rugu, kwaryar dama nono da su ludayi da aka kawowa amarya masu bala'in kyau har da kwalliya a jikinsu, dik ta takesu ta fashe, dik wasu tulu na jere sai da ta fashe shi!.
Abin dariyar kuma tana gama yin wannan aika aikan bata tsaya ba sai ta gudu gidan Arɗo ba tare da Arɗo yasan ta zo ba, ta gudu ta je gwaggonta ta ɓoyeta a ɗaki ta yadda ko annemeta a yau dai ba za'a ganta ba. Ashe maras kunyar karya ce ita.
Idan ran bappa ya kai dubu to ya ɓaci, yana ji da kansa an kawo mashi amarya kawai Nenne zata wani rakasu a guje!. Wlh bata isa ba.
Cikin ɓacin rai bappa ya dawo gida domin ya ɗacaca mata kamar yadda ta ɗacaca mashi, ta korar mashi amarya, yau Nenne ta kuresa ta kawo shi har wuya, hakan yasa ya shigo a fusace, sai dai kash, bai sameta ba, wlh yau da ya sameta a gidan da bakaramin duka zai yi mata ba, saboda ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci.
Cikin kunan rai ya juya ya fita, kai tsaye gidan Arɗo ya nufa dan ya dubata. Sai dai ko da ya je can Arɗo ya ce mashi bata zo ba, dan bai san tana ciki ba.
Da kyar bappa ya iya haɗiye ƙuncinsa ya koma wajen Mairo dan ya basu hakuri ya kuma ɗauko amaryarsa su koma gida a tare.
Kai my people's Nenne ƴar duniya ce wato.
===============≠===========🔥
••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••🔥
Kwance momma take a saman bed ɗin a cikin bedroom ɗinta, ta baro room na King, da kanta ta kaiwa Jaish abinci cikin bedroom ɗinsa, a lokacin ta isko shi yana wanka, sai ta koma room nata dan ta ɗan huta.
Sallama mama Haulat ta yi mata a bakin kofar shigowa, tana da kwance ƙasa ƙasa ta amsa sallamar haɗe da bata izinin shigowa.
Turo kofa ta yi ta shigo, a ƙasa gaban bed ɗin ta zube gwiwowinta, cikin girmamawa ta ce
"Barkanki da hutawa ranki ya daɗe".
Shiru na ƴan sakanni momma ta yi kafin ta amsa da. "Akwai wani abin mai muhimmanci ne?".
"E dama uncle Jahiz ne yake parlour yake san ganinki".
Jinjina kai ta yi ba tare da ta sake magana ba ta nunawa mama Haulat hanyar fita da hannu alamar ta je tana zuwa.
Miƙewa ta yi ta nufi waje tana yi mata addu'ar a fito lafiya. A cikin ranta ta amsa addu'ar da Amin, Allah sarki, damuwa ne kamar zai kasheta, shiyasa King yasa a ɓoye mata Guyson ya suma yana gadon asibiti, ga Chuchu ma kwance rai a hannun Allah, dik saboda tashin hankalin ɓatar Zunaira, tun fitar da su Mummyn Chuchu suka yi da shi ashe tin lokacin yake a sume, yanzu haka yana hospital ɗin cikin kingdom ɗin ana duba lafiyarsa, ita ma Chuchun an bata gado.
So King ya ce a ɓoyewa Momma da Jaish hakan kada a bari su sani, sannan a ɓoyewa Jaish batun ɓatar Zunaira, a ce mashi tana Dubai, dan in ba haka na za'a samu gagarumin matsala, kun dai san bai jima da dawowa cikin hayyacinsa ba, so a cewar King kafin Jaish ya damu ya fara nemanta har ya ce zai bita Dubai to su kuma sun yi gaggauwar gano in da take!........... My people's shin kuna ganin hakan zata yiwu kuwa?!.
Miƙewa momma ta yi, dik sai ta ji jikinta ya kara mutuwa sosai, Allah sarki ciwon Guyson ne yake ratsa jininta ba tare da ta sani ba.
Alkyabbarta ta ɗauko ta ɗaura kan kayan jikinta, ta nufi parlourn.
Ba karamar mamaki ta sha ba ganin uncle Jahiz rike da jariri a hannu, yaron ya kwanta luf a jikinsa, idanunsa kuma a buɗe sai dai bai yi kuka ba, yana ta faman buɗe baki alamar yana jin yunwa sosai.
Tsuma da san jin daga ina ya samo jajiriri yasa momma ta kasa iya zama kafin ta tambayesa, cike da mamaki ta ce.
"Jahiz....... Ina kuma ka samo baby?".
Zama ya yi saman mai zaman mutum ɗaya sofa kafin ya bata amsa da. "Zauna mama sai ma baki labari, dama kuma hakance ta kawoni wajenki".
Idanunta a kansa ta samu waje ta zauna saman two seater.
Dik a ƙage take da san jin in da wannan yaro ya fito, ta tsare yaron da kallo, lokaci guda ya shiga ranta, dama ta jima rabonta da jariri a hannu, shekaru wajen 14 fa yanzu, tin kan Zunaira, ai kunga zata so jariri sosai a yanzu.
Miƙa mata babyn ya yi. Ba musu ta yi saurin karɓa tana kallon babyn cike da kauna, har da sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Dawo da kallonta a kan uncle Jahiz ta yi tana jiran ta ji bayanai.
Ɗan gyaran murya ya yi kafin ya fara bata labarin haɗuwarsa da su Khadija, yadda suka bugesu da mota da kuma halin da suke ciki a yanzu.
A ɗan hanzarce ta ce. "To yanzu ina suke?".
"Suna hospital na cikin Kingdom ɗin nan, naga a Abuja ba wani kula da su sosai za'ayi ba, kuma kinga dik wani abin da ya samesu alhakin a wuyarmu zai rataya, shiyasa na nemi takarda daga hospital ɗin can dan mu samu damar zuwa da su nan a dubasu da kyau".
Jinjina mashi kai ta yi alamar tabbas haka ne, dik abin da ya faru da su Khadija a wuyarsu ya rataya, sannan ta dawo da kallonta a kan babyn dake ta faman buɗe baki.
"Jahiz yaron nan ai yunwa yake ji". Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe mashi fuska da kyau ta yadda zai samu damar ganin haske da kyau!.
"Yeah tun jiya babu abin da aka bashi, mahaifiyarsa tana kwance bamu da tabbacin tana raye ma".
Sosai momma ta ji tausayi ya kamata, sai ta ji tana san zuwa ta gansu, amma babu hali, bata da damar fita, dan haka sai ta ce da shi.
"Ba damuwa, zan kula da yaron, kai kuma ka kula da marasa lafiyan har zuwa su samu sauki".
Miƙewa tsaye ya yi, cikin nitsuwa ya ce. "Yauwa momma ina godiya, dan Allah ki kula da yaron nan sosai, saboda ina kaunarsa, ya shiga rai'na da kallon farko, yanzu dai bari in je hospital ɗin ma in duba su, dan tun da muka miƙasu ga likitoci ban sake komawa ba".
Jinjina kai ta yi kafin ta amsa da. "In ka fita ka turo mun Haulat, dan wannan yaron ɗanyen jariri ne da ko wanka ba'ayi mashi ba".
Da okey ya amsa mata, sannan ya nufi waje.
Kurawa yaron idanu ta yi yana ta kallonsa, kyakkyawa kamar a bata shi kyauta, ga idanunsa a buɗe dara dara.
Da fitarsa bai fi minti ɗaya ba sai ga mama Haulat ta shigo cikin hanzari. A gaban momma ta zube gwiwowinta.
Miƙa mata babyn momma ta yi tare da miƙewa tsaye.
"Ki yi mashi wanka, sabon haihuwa ne, sannan ki bashi madara mai ɗumi, ki yi mashi dik abin da ya dace".
Tana kai karshen maganar ta wuce izuwa bedroom ɗinta, dan jikinta babu kwari, alamar zazzaɓi mai zafi ma take ji.
Wucewa da babyn izuwa ɗakinta mama Haulat ta yi, ita ma sai kallon yaron take yi, da alama babyn Khadija yana da farin jini matuƙa, dan kowa ya kallesa sai ya kama zuciyarsa da kauna.
•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
A can cikin fada kuwa, ran King ya gama ɗacaca matuƙa, hankalinsa a tashe, ga guyson da Chuchu rai a hannun Allah, ga Zunaira ba labari, Hoorain ya gudu, dan haka sai ya yanke hukunci cikin fushi, ya ce da commander Zafar a je a yaki Daular Qahtaniyawa, a kashe dik wanda ya gwada gardama, a tattaro mashi mata da maza yara da manya dik a gurfanar mashi da su a gabansa, daga yau sun zama bayi a kingdom of power..... Tashin hankali. Cikin fushi ya yanke hukunci fa.
A dai'dai wannan lokacin da King yake umartan commander Zafar da a ruguje Daular Qahtaniyawa, ya yi dai'dai da lokacin da Queen Zarina take tsaye a saman kafafunta cikin wani irin ƙasaitacciyar shiga na ban mamaki, gaba da bayanta dikka dakakkun warriors ne da suke gadin lafiyarta ta yadda ko guda ba zasu bashi damar taɓata ba.
A saman wani stage take tsaye wanda ƙasan stage ɗin wasu irin mahaukatan manya manyan warriors ɗinta wanda ta gina masu jikinsu da tsafi ne, ganinsu da ido kawai sai yasa zuciyar mutum ta buga ya mutu, basu da kyan gani ga bakar mugunta a fuskokinsu, babu rahma ko ɗigo a tattare da su.
Sai dai dikkansu dik da wannan horo da suka samu ga kuma tsafi suna tsaye ne a bayan wani dakakken warriors guda ɗaya wanda shi ne a gaba da su yake jagorantar wannan runduna.
Ko baka san fuskar Hoorain ba idan kaga wannan mayaka tabbas zaka iya alakanta shi da Hoorain assistant commander na kingdom of power......... Tashun hankali.
Dan daga yanayin tsayuwarsa cikin jarumta da daki zai iya tabbatar maka da basu da banbanci da Hoorain...... Tashin hankali.
Kai Hoorain ne ma, dan wannan irin abu haka ba zai taɓa zama waninsa bane, shi ɗin ne!! Tab akwai matsala, kenan Hoorain dama Queen Zarina yake yi wa aiki? Menene yasa ya ci amanar kingdom of power har da mahaifinsa haka? Kenan ya zaɓi wasu a kan mahaifinsa? Ya aka yi Zarina ta san Hoorain? Tin yaushe ya fara yi mata aiki? Aiya mahaifinsa ma zai iya kasancewa abin yarda kuwa? Anya shi ma ba maciyi amana bane kuwa? Kada ku manta a baya alkalamin princess Teema taku ta amana na gaya maku cewa bayan mammiensu Sarina akwai waɗan da suke cin amanar Kingdom of power suke aiki da Queen Zarina, kuma mutane da suke da kusanci sosai da King Zuhair, yardaddunsa ne, in baku manta ba na taɓa faɗa maku zaku sha mamaki a lokacin da gaskiyar zata bayyana, zaku sha mamaki idan kuka gane maciya amanar kingdom of power, ku dai muje zuwa, akwai tashin kai a gaba.
________________________________🔥
Yana tsaye ne tamkar wanda aka sassaƙa, dik da yana cikin hular mayaƙa, hakan ba zai hana ka fahimci babu rahama da imani a tattare da shi ba.
Cike da izza da zallar madarar zalinci Queen Zarina take basu umarnin kalar kisar da take da buƙata zasu yi wa kingdom of power, har da cewa su ɗauko mata Jaish su kawo mata shi, dan a duniya idan akwai wanda take so to ya biyo bayan Jaish yaro ɗan Mommarsa, dan haka a kashe kowa a ɗauko mata Jaish, a shekaru fa ta kai ta haifi Jaish, amma kuma zuciyarta ta kamu da kaunarsa dan tabbatar matacciyar zuciya.
Allah sarki yaro ɗan Mommarsa, yana can yana sha'aninsa ana mutuwa a kansa bai da labari.
Cikin girmamawa waɗan nan bakaken azzaluman mayaƙan nata suke karɓar umarninta, zaluncin mutanen nan ya kai su iya zaro jariri daga cikin uwarsa su kashe shi su jefar da gawar babu abin da ya damesu, basu da tausayi ko ɗigo a ransu, ko da yake zukatan da ake sarrafawa da tsafi yaushe suka ga imani da tausayi?.
Akwai cakwakiya, King Zuhair ya bada umarni ga mayakansa da su je su ruguje Daular Qahtaniyawa su kashe kowa su haɗo mashi kan mayakansu da bayinsu su zo su zama bayi a kingdom of power ba tare da ya tabbatar da cewa King Al-Mustapah ne ya ɗauki Zunaira ko ba shi bane, kawai ya yanke hukunci cikin fushi babu bincike. Ita kuma Queen Zarina ta bada umarnin a zo a kashe mata kowa a Kingdom of power a kama Jaish a kai mata shi su yi aure. Me kuke tinanin zai faru?.
A gefe guda kuma evil kingdom suna can suna ta gagatumin shirin da idan suka dinfari kingdom of power dole su rugujeta su shafeta a doran duniya, wani irin mummunar kafurin shiri suke shiryawa.
Ga shi shi kuma King Zuhair yaki yarda ya karɓi tuban King Al-Mustapah bare ma har su haɗa kai wajen ganin bayan Queen Zarina da su King Abdul Aziz, shi kaɗai kuma ni da ku mun san wlh ba zai iya yin faɗa da waɗan nan masarautu har ukun ba, ga ubansu Black