Showing 90001 words to 93000 words out of 403653 words

Chapter 31 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

64

ta turo ba tare da ta bashi amsa ba, saboda ita dai magana ta Allah bata san zaman cikin nan.

Jin ta yi shiru yasa ya sake cewa. "To ku wuce mu tafi". Ya faɗa ba tare da wasa ba.............. Ran Pretty bai so ba ta wuce gaba tana tura baki, Auta ta rufa mata baya. Haka suka wuce izuwa ma kwancinsu.

Ko da suka shiga sai da ya jima tsaye a wajen yana satar kallon Auta kamar bakinsa da magana, kamar yana san amayar da ita kuma, sai dai kamar yana tsoro, wato dik zafin kan mutum da izzarsa abu guda ɗaya tana ɗarsa mashi tsoro a cikin zuciyarsa, wannan abin kuma ba komai bane face soyayya, wlh in dai namiji soyayyar gaskiya ce a ransa yana ɗarsa mashi tsoro da ɗarɗar a kan ua faɗa ko kada ya faɗa, yana jin matuƙar tsoron ya furta bai yi nasara ba, tinanin abin da zata je ta dawo da abin da rashin nasararsa zai haifar masa yasa yake dasa mashi tsoro a zuciyarsa.

Haka ya rufesu, ya ɗan jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya tafi. A wannan karon ma yana tafiya suka buɗe suka fito, wlh ita dai Pretty Allah ya gani ba iya zama a wannan waje take yi ba, burinta ta fito waje, gara ma lokacin da Auta take jinya a cikin wajen, a wannan lokaci kullun tana ciki, saboda tana kula da Auta.

Sadauki ne ya tsinto Auta a cikin ruwa ya kawota wajen Pretty, shi kuma ya yi jinyarta tsawon lokaci, shiyasa kuka ga ta shiga ransa sosai, dan dik wasu magunguna shi yake saka mata a ciwon, Pretty kullum tana manne da ita, ko nan da can bata san matsawa, suna tare, kusan a tare ita da sadauki suka yi kinyarta.

A ranar da Auta ta buɗe idanu da Pretty ta fara yin arba, shiyasa take balain jinta a ranta sosai.

Ga dikkan alamu Auta ma bata san zaman cikin ramin nan, saboda da Pretty ta ce tazo su je waje zata ce to, ta bita su tafi, ga shi ita bata gama samun lafiya ba, har yanzu akwai sauran magani a jikinta da ba'a ɓare shi ba.

Kuma ita Auta bata san cewa akwai waɗan da suke farautar rayuwar su Pretty tsawon lokaci ba, bata taɓa kawo hakan a ranta ba, a dik tinaninta fita ne kawai sadauki baya san su yi yasa kullun yake yi masu gargaɗi a kan fita, basu san cewa abin ya wuci haka ba.

Fitowa suka yi, suka jero kusan tsawonsu ɗaya, Pretty ce ta ce. "Zo mu canza waje tun da nan wajen yasan muna wajen, zo mu je ta can baya akwai wani wajen korama ba zai san muna wajen ba, sai mu zauna mu yi hiranmu a wajen sai can yamma mu koma.

Da to kawa Auta ta bita suka cigaba da tafiya. Sun yi tafiy mai nisa sosai har Auta ta fara dafe cikinta wajen ciwon nata, kunsan bata gama samun sauki ba, so sai ya fara yi mata ciwo.

Tun tana ji a hankali hankali tana daurewa har ya fara fin karfinta, karkashin wani bishiya ta samu ta zauna tare da dafe wajen tana ƙoƙarin fara kuka. A tsorace Pretty ta dawo kusa da ta zube gwiwowinta, kamar zata yi kuka ta fara tambayarta lafiya? Meyake damunta.

Auta bata kai ga buɗe baki ba suka sinkayo sukuwan dawakai masu karfin gaske. Kafin su yi wani ƙwaƙƙwaran motsi dawakan sun bayyana a wajen. Waɗan nan warriors ɗin na ɗazun da sadauki ya biyo bayansu su suka kewayesu.

A tsorace Pretty ta fara binsu da kallo tana mamakin ganinsu. Hannun Auta ta riko tare da janta tana faɗin ta tashi su gudu su koma ma kwancinsu.

Auta da ciwo ya ci karfinta ne ta kasa motsawa ne yasa ta saki wani wahalallen ihu, janta Pretty ta cigaba da yi tana faɗin ta tashi su gudu. Sai dai ina Auta ba zata iya tashi su gudu ba, haka suna ji suna gani waɗan nan warriors ɗin suka ɗaukesu suka saɓasu saman dawakansu.

Sai kuka Auta take yi saboda ciwonta, ita ma Pretty sai kuka take yi saboda an rabasu kowacce warriors daban ne ya ɗauketa. Haka suka juya kan dawakansu suka kutsa da su cikin daji.

To nima dai na juya na kama hanyar gida dan maltina ta ta yi sanyi dai'dai sha. Good bye my people's.

Wani fata zaku yi wa Auta! Pretty! Leesharh da kuma Sadauki a halin yanzu?.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






Sai kuka Auta take yi saboda ciwonta, ita ma Pretty sai kuka take yi saboda an rabasu, kowacce warrior daban ne ya ɗauketa. Haka suka juya kan dawakansu suka kutsa da su cikin daji.

Sosai dawakan suke gudu, dan a tunaninsu Auta da Pretty ƴan uwana ne, dama in baku manta ba Sweetie and Pretty suke nema, so sai suka ɗauki Auta a matsayin Sweetie kenan.

Suyi nisan zago a tafiyar tasu, dan sun yi tafiya a kallah na good 20 mins a cikin wannan dajin, kuma basu kusa fita ba, sai a lokacin Pretty ta gane ashe fa dajin nan duniya ce guda mai zaman kanta, da a tinaninta iya wajensu ne kawai.

Waɗan nan mayaƙa sun kware wajen iya sarrafa dawakai sosai. Dai'dai tsakiyar wasu manya manyan dogayen bishiyoyi masu tsayin da kaurin gaske, basu da cikar ganye sosai, sun yi sama sai suka yi runfa hakan ya haifar da inuwa mai daɗin gaske a wajen, wajen yana da faɗi sosai, waɗan nan dogayen bishiyoyi ne suka yi wa wajen zobe, kasan wajen kuma wani irin tashi ne mai laushin gaske, idan ka matsa gaba kaɗan akwai wani irin yashi mai bala'in laushi wanda ya fi na wannan wajen da suke, shi har lumewa bawa zai yi a cikinsa idan ya shiga, irin wannan yashin da ake iyo a cikinsa ne, idan ka iya ka fitar da kanka in ka faɗa, idan kuma baka iya ba ka lume ƙasa ka mutu.

Kunsan dawakai basa iya gudu a cikin yashi mai yawa ko? Hakan yasa dawakansu gabaɗaya suka dakata a wajen suka ki yin gaba suka kuma kin yin baya, kunsan idanun doki daban yake dana sauran dabbobi, shi da kare sun banbanta da sauran dabbobi, su suna iya kallon masifa, misali suna iya kallan shaiɗanu da abin cutarwa, so sun hango yashin dake gabansu mai lumar da mutane ne yasa suka ki yin gaba, dan sun hango mutuwa.

Waɗan nan warriors sun yi sun yi waɗan nan dawakai su yi gaba, amma ina sun ki tafiya, sun tsaya a wajen. Dan dole ya tilastawa kowannesu ya sauko kasa daga kan dawakan.

Cike da jarumta suke taka kasa, haka suka fara kewaye arear wajen suna duba me dawakansu suka gani da yasa suka ki tafiya gaba suka tsaya a in da suke?.

Sauke Auta da Pretty ma suka yi, da gudu Pretty ta zo ta rungume Autar dake ta faman kuka kamar ranta zai fita, har jini wajen ciwonta ya fara yi.

Wani dakakken warrior ne ya tinkaresu da nufin ya rabasu, wasu warriors biyu suka rufa mashi ba. Suna zuwa suka kamasu suka ɓallesu, ma'ana suka rabasu, sai ihu yaran nan suke yi, amma ko kaɗan basu tausaya masu ba.
Wani tsawa mai sauti wannan warrior ɗin ya daka masu a kan su yi mashi shiru. Ƙoƙarin kwatar kansu daga hannunsu suka fara yi, hakan ya bawa warrior ɗin haushi har ya ɗaga hannu zai dallawa Aura mari, da yake shi ya riketa su kuma warriors guda biyun nan suka rike Pretty, kunsan Pretty ta fi Auta lafiya, so sai fisge fisge take yi yasa su biyu suka riketa.

Auta kuma a nitse take sai dai kuka da take ta fama, kuma kukan ma wlh na ciwonta da ya fama take yi. Tsabar rashin imani irin na wannan warrior ɗin da gashi kan Auta ya riketa, ta rasa da wanne ɗaya zata ji, da zafin da gashin kanta yake yi mata na rikonsa ne ko kuma da ciwon dake cikinta?.

Da karfi ya ɗaga hannu zai mari bakinta dan su yi mashi shiru, sauran warriors ɗin suna ta kewaye a wajen suna diba menene ya hanasu cigaba da tafiya.

Lokacin guda wajen ya ɗauki wani irin shiru na unexpext haka, irin shirun na ban mamaki wanda kamar an datse komai da sauti zai iya fita. Nan take wani irin iska ya fara kaɗawa da karfi karfi. Wani irin haniniyar ƙosasshen jibgegen doki ne ya karaɗe ko'ina a yankin wajen, ya doɗe masu dodan kunnuwa, haka zalika ya razana dawakansu da suke hawa.

Wannan warrior da zai mari Auta ne ya fara janyo numfashinsa da karfi sannan ya kurma wani irin ihu mai amsakuwar da sai da gabaɗaya arear wajen ta amsa. A miliyan sauran mayakan suka yi kansa suna tambayar meya faru yake ihu haka?.

Kowannensu bai iya kai kashen tambayarsa ba idanunsu suka sauka a kan hannunsa da baya tare da jikinsa. A miliyan suka kai kallonsu kan jikinsa, tabbas babu hannunsa an datse mashi shi. To waye ya datse mashi? Yaushe kuma aka yi hakan? Ba yanzu ya ɗaga hannun zai mari Auta ba? Meyasa hannnun ya fita daga jikinsa?.

Wannan shi ne tambayoyin da suke jefawa kawunansu. Kururuwan wannan doki ne ya sake dakar dodannin kunnuwansu, hakan yasa suka ɗaga kai sama suna neman ta ina ne? Ita kuwa Auta da taga abin da ya faru kuma taga lokacin da aka datse mashi hannu sai abin ya yi mugun rikitar da ita da har yasa ta haɗiye kukanta diff, ita ma Pretty shiru ta yi diff.

•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Can suka hango wani namijin gaske a saman wannan doki dake ta zuba uban haniniyar. A miliyan suka mimmike tsaye suna kallonsa. Yana zaune zaman cikar jarunta a saman dokin, ya rike linzaminta da kyau da hannunsa ɗaya, da alama dokin nasa ma ɗan yi ne, dan kuwa ga shi sai ɗaga kafafun gaba sama yake yi yana wani haniniyar ƙasaita.

Wannan namijin gasken rike yake da zabgegiyar takobinsa mai bala'in kaifi wanda jini ya gama wanketa har ɗiga yake yi a ƙasa. Da gani ba tambaya zaka san jinin wannan warrior da zai mari Auta aka datse mashi hannu ne, ga jinin jajir da shi.

Mamaki waɗan nan mayaka suka shiga yi a kan yaushe wannan namijin gasken ya zo ya datsewa wannan mayakin nasu hannunsa har ya wuce basu gansa ba?. Kunga a iya nan kawai ya gwada masu fifikon kwarewa a fannin yaki da jarumta, dan kuwa shi ba tsayawa ya yi ya datse hannun nashi ba, yana kan dokin tsabar yana da saiti mai karfi, a miliyan ya tsaga tsakiyarsu ya wuce tare da wucewa da hannnun mayakin da takobinsa, kafin su ankara kamar kiftawa da bismilla ne ya wuce.

Faɗuwa ƙasa wannan mayaki ya yi azaba tana ratsa kashi da ɓargonsa. Su kuma sauran mayakan zaro takubansu suka fara yi daga kwankwasonsu. A guje suka dimfari in da yake a saman dokin nasa.

Bai bari sun kariso garesa ba ya sauko ƙasa daga saman dokin nasa, kan dokin ya ɗan shafa kafin cikin harshen larabci ya ce da dokin ya je bari ya ɗan buga wasa da waɗan nan ƙananan kwarin. Da gudu dokin ya matsa gaba, wato dokin nan ya horu iya horuwa, gudun bala'i ne da shi na wuce misali, ga karfin gaske, sannan yana jin maganar ogan nasa idan ya yi mashi, da alama sun yi sabo sosai.

Mayar da takobinsa mazauninta ya yi, a cewarsa waɗan nan ƙananan kwarin warriors ɗin ba sai ya taga hankalin takobinsa wajen faɗa da su ba, hannunsa ya wadatar, cikin ƴan mintuna zai murkushesu a wuce wajen.

Su kuwa da karfin gaske suka dimfaresa, sai wani ihu suke yi suna wani irin haki kamar waɗan da suka je babban filin daga mai cike da mayaƙa dubu zasu yaka.

Dikkansu da takobi shi babu komai a hannunsa suka fara gwabza faɗa babu kama hannun yaro. Pretty ta taso da gudu ta zo ta rungumi Auta tana yi mata sannu da jiki. Ganin ciwon na jini yasa Pretty ta kara tsorata, nan take ta kara sautin kukanta, ni da ku dik mun san halinta da balai'n tsoro, bare kuma taga jini, ai tsoro ninkuwa ya yi.

Ƙoƙarin tallafawa Auta ta yi da ta tashi su gudu su bar wannan waje. Ina ai Auta ko motsawa daga in da take durkushen saman gwiwowinta nan ba iyawa zata yi ba, dik Pretty ta rikice, ta rasa me zata yi mata sai kawai ta rungumeta suka cigaba da kuka.

Su kuwa waƴan can suna ta gwabza yaki har suka isa ga wannan yashi mai lumar da mutum ɗin nan. Namijin gaske ya kashe mayaka biyu, su kuma ko kwarzane basu samu damar yi mashi a fatarsa ba, da alama yasan irin wannan yashi sosai, hakan yasa suna kaiwa wajen ya tura mayaka biyu ciki.

Nan take suka fara ƙoƙarin yin iyo dan su fitar da kansu, sai dai ina, ba zasu iya yi ba, suna ji suna gani ga azaban zafi cikin yashin haka suka lume can kasa sai gawarwaki.

Haka suka cigaba da gwabza yaki suna gwada mazantaka................... A hankali Auta ta fara ganin dishi dishi sakamakon jinin da ta zubar, jiri ne mai karfin gaske ya fara ɗibarta, kanta yana sara mata da karfi kamar zai fashe. Pretty tana rike da ita sai ta ji ta sakar mata nauyinta gabaɗaya.

Kasancewar Pretty ba iya riketa gabaɗaya zata yi ba sai suka tafi gabaɗaya zasu zube a ƙasa............... Kamar daga sama suka ji an taresu, gabaɗayansu ya haɗesu ya capko suka faɗa jikinsa.

A tsorace Pretty ta juyo garesa dan taga wenenen? Cikin ranta tana tinanin Sadauki ne, dan ta san shi kaɗai ne mai taimaka masu a dik time da suka shiga matsala. Sai dai kash a wannan karon tana juyowa sai taga bashi bane, dik da shi ma wannan yana cikin shigar mayaka kuma fuskarsa a rufe, tabbas ba Sadauki bane, dan ko da bata san fuskar sadauki ba ta san kirar jikinsa, kuma ba zata kasa iya ganesa ko cikin millions masu rufe da fuska ba!.

Zame jikinta daga nasa Pretty ta yi, ta barshi da Auta kawai, cikin nitsuwa ya ɗauki Auta cancak. Ya gama kashe waɗan can warriors ɗin gabaɗaya, kisan walaƙanci wanda ko kare ba zai ci ba ma ya yi masu,

Fito ya yi da ɗan karfi, Pretty na ta binsa da kallo tana san sanin wanenen shi?......... A guje dokinsa ya danno zuwa in da suke, wannan fito da ya yi kiran dokin ya yi. Da gudu Pretty ta juya zata bar wajen, dan a tinaninta wajenta dokin zai zo. Cikin zafa yasa hannunsa ɗaya ya riko hannunta bai bari ta gudu ba. Ihu ta saka mashi tana ƙoƙarin kwatar hannunta dan ta gudu.

Sai dai ina, bata iya yin hakan ba, yana tsaye har dokin ya ƙariso gabansa, saketa ya yi tare da gyara Auta a jikinsa sosai, sannan ya haye saman dokin da ita. Pretty tana kallonsa tana san guduwa, bata hankara ba sai ganinta ta yi a saman bayan dokin, da hannu ɗaya ya ɗagata sai saman dokin, sannan ya umarci dokin da su tafi............

Shin wanenen shi ɗin?.ina kuma zai kai su?.

============================🔥
•••••••••••KINGDOM OF POWER••••••••••🔥

Kwace rikon da Jawad ya yi mashi ya yi, da sauri ya nufi hanyar fita waje dan ya je ya cire kayan jikinsa dan ta taɓa, in baku manta ba mugun kyankyani Jaish yake da shi, kun tuna farkon zuwansa garinsu yadda ya rinƙa kwarara amai saboda bappa ya taɓa shi? To yanzu ma hakance.

Binsa da kallo suka yi har ya fice daga ɗakin, momma bata yi magana ba, dan ta lura ransa a ɓace yake sosai, kada ta shiga hakkinsa. Da sauri Jawad ya rufa mashi baya dan ya je ya ji menene dalilinsa na shiga ɓacin rai haka? Ya kuma rarrashesa, kunsan su ɗin amanan juna ne.

Mahnoor ta rungume Mahreen, sai a lokacin ita ma ta samu damar sakin kukan da tun shigowarta arear kingdom of power take san yi amma ta danne.

Ƙarisowa wajensu momma ta yi da nufin ta rarrashesu, hakan ya yi dai'dai da shigowar Aunty MieMie da kuma Fanan a tare da ita.

Cike da mamaki Aunty MieMie ta fara binsu da kallo, taga yan kauye jiki dik datti, zaro idanu ta yi lokacin da ta ga momma ta ɗago Mahreen ta rungume tana rarrashinta, kasa hakura ta yi har sai da ta ce. "Momma waɗan nan fa daga ina?".

Fanan ma mamaki ne ya kamata, sai dai bawai kyamarsu take ji ba, kawai dai mamakin ganinsu take yi.

"Fanan ɗaukesu ku je ɗakin Zunaira da su, ki taimaka masu su yi wanka ina zuwa da kaina na basu kaya da kuma abinci". Cewar momma da ta dawo da kallonta a kan Fanan.

Fanan yarinya mai biyayya, bata yi wani magana ba ta ce su zo su tafi, sai dai taki matsawa kusa da su dan tana ganin datti a jikinsu. Mannewa da juna suka yi, dikkansu sai kuka suke yi, sun ki motsawa bare a sa ran zasu bi Fanan.

"Mahnoor ku yi hakuri ku je tare da Fanan kun ji?". Cewar Momma.

Kin motsawa suka yi, Mahnoor ce ma ta yi ta mazan cewa. "Mu kam a mayar da mu wajen bappanmu, ba masan nan". Tana magana tana wani irin kuka mai tsuma zuciya.

Take momma ta ji tausayinsu ya kamata, Allah sarki dole su yi kuka basu taɓa zuwa irin wannan waje ba.

Matsawa kusa da su Aunty MieMie ta yi, dan kun santa da fahimta, ta fahimci koma su wanene su ba shakka momma ta ɗaukesu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login