Showing 381001 words to 384000 words out of 403653 words
sai ya yi ƙoƙarin tuba ya koma ga Allah, kaga kenan dama yasan ALLAH kenan".
"Cikin suratul Yunus, sura ta 10 aya ta 90 zuwa 92. ALLAH ya ce. Mun tsallakar da Banu Isra'ila daga cikin teku, sai Fir'auna da sojojinsa suka biyo su da zalunci da girman kai, har da ruwan ya rufe shi, sai ya ce. Na yi imani, lallai babu abin bautawa sai wanda Banu Isra'ila suka yi imani da shi, kuma ni ma ina daga cikin musulmai. Allah ya ce. Yanzu? Bayan kuwa a da ka kasance mai ƙi, kuma daga cikin masu ɓarna? To yau za mu cece ka da jikinka, domin ka zama alama ga waɗanda ke zuwa bayanka, kuma lallai mutane da yawa sun kasance gafalallu daga ayoyinmu. Wannan ayar ta nuna cewa Fir'auna ya tuba ne a lokacin da ya ga hallaka, amma Allah bai karɓi tubarsa ba".
Uhm dik iskancin mai iskanci ba zai taɓa kai Fir'auna ba, amma shi kansa da ya kira kansa da ALLAH da ya ji azabar fitar rai ya shaida babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH har ya yi ƙoƙarin tuba, wannan kawai bai ishi mutane ishara da su kama ALLAH gam du rike ba? Me kake nema a duniya da har zaka yi bautar mutum irinka ko wata dabba? Wai ni har Fir'auna ma ya shaida ALLAH ALLAH ne to kai kuma a suwa da ba zaka damki hanyar gaskiya ba! Ku duba iskancin Fir'auna a bayan kasa fa? Amma da yaga mutuwa har da su zuba! A wasu ruwayanma cewa suka yi Mala'ika ya toshe bakinsa ya hanasa tuba, amma ni wannan ruwaya ban tabbatar da ingancinta ba, abin da na sani daga Alqur'ani da ayoyinta shi ne ya ce ya tuba ya shaida ALLAH ALLAH ne kuma ya zama musulmi daga ranar, ALLAH yaki karɓar tubansa!!.
Darussa daga rayuwar Fir'auna
"Dik wani mulki ko iko ba shi da wani amfani idan ba ayi amfani da shi ta hanyar da ALLAH ya umarta da adalci ba. Girman kai da zalunci suna haifar da hallaka!!. ALLAH yana iya jarrabtar mutane da iko dan ganin yadda za su yi amfani da shi. Tuba tana da muhimmanci, amma idan mutuwa ta zo, ba za a karɓa ba!. Wannan shi ne tarihin Fir'auna a taƙaice daga Alqur'ani da binciken tarihi". Ta kai karshen maganar tana kallonsa!.... MASU KARATU DIK WANDA YA KARANTA NAN YA DAURE YA FURTA ASTAGFIRULLAH KO DA SAU UKU NE, TUBA TANA DA KYAU SOSAI, DAGA NAN A DAURE A JEFA TEEMA TAKU TA AMANA A ADDU'A KUN JI MY PEOPLE'S!.
"Mu je mu yi dinner". Ta faɗa tana miƙewa................ Hakika ya ji a gaskiya lokaci ya yi da yayansa zai daina mulkin zalinci kada ALLAH ya hallakasa, yanzu ya fahimci zalunci bata da wata amfani face halaka mai muni!.
Ganin bai amsa mata bane yasa ta ja dogon kyakkyawan shap nose ɗinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe ya sauko ƙasa. Ta fahimci halin da yake a ciki, dan haka sai ta ce mashi. "Kada ka damu, Big Bro ya kusa zama adalin sarki mai jin ƙan mutanensa, da zarar ya musulunta shikenan komai zai canza, kuma zamu yi nasara, ina jin hakan a jikina, ban taɓa jin cewa lokacin samun saukinmu ya gabato ba sai a ƴan kwanakin nan, tabbas da izinin mai dikka zamu yi nasara Bro".
Sosai ya ji daɗin kalamanta har ya samu zuciyarsa ta yi sanyi ya iya cin abinci mai ɗan yawa, ba dan kalamanta ba da wuya yau ya iya cin abinci sosai, ko da suka je wajen cin abincin ma, suna ci tana jansa da tsokana tana kara kwantar mashi da hankali har suka kammala, sannan suka miƙe suka nufi bedroom na Black Tiger.
🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥
Zaune suke a cikin room ɗinsu ita da Leesharh, yanzu Leesharh ta samu abokan zama, wato Guyson and Auta, kullum suna tare, yanzu Ramish yana iya fita bata da matsala, dan akwai mahaukatan tsaron da Smart ya zuba masu tamkar ba zasu bar mutuwa ya shiga ya ɗauki ransu ba, ga jami'ai guda biyu dake gadi a cikin gida waɗan da suke parlour, ɗayan jami'in shi yake yi masu girki, so yana kasancewa ne a cikin kitchen, ɗayan kuma yana zama ne a parlourn kuma shi yake kai masu abinci har cikin bedroom ɗinsu idan sun buƙata, tsuhuwa ta dai'na yi masu girki sai dai ta yi wa kanta, a tinanin Ramish suna jin daɗin zama da tsohuwar ce ma shiyasa bai mayar da ita gidan Abbie ba!
Yanzu tsohuwar burinta kawai taga ta bar wannan gida, dan a tsorace take kada asirinta ya tonu a kamata, tun ranar da ta ɗaura idanunta a kan Smart ta shiga tashin hankali da fargaba, abin dariyar kuma wai zuciyarta ta kamu da son Ramish matuƙa!!.
---------------------------------------🔥🔥🔥
Sai hira suke yi Leesharh da guyson, amma ita Auta tana zaune ta jingina kanta da jikin bango, hannunta riƙe da wayar da Smart ya saya mata sabo, ta fara warwarewa baiwar Allah, amma ba karya ta ji jiki matuƙa. Sai ƙoƙarin janta da hira suke yi amma taki kulasu.
Wayar tata ce ta ɗan yi kara alamar shigowar sako, ɗan nisawa ta yi kafin ta kai kallonta a kan sakon. "My Queen yanzu kin manta da ni tsawon lokaci, na sha wahala kafin na samu numberki, meyasa baki nemeni ba? Ko dai yanzu baki san kalamaina ne?". Shi ne abin da yake rubuce a jikin sakon. Shin kun tuna lokacin da wani guy yake turo mata saƙonni? A lokacin da take tare da uncle Taheer? Kun tuna lokacin tin kafin ma ta fara soyayya ta zahiri da Hoorain! To wannan guy ɗin ne, kun san ta canza wayoyi har sau uku, shiyasa ya rasa numberta, sai yanzu ya samu sabon da Smart ya bata last week, kuma wannan sabon number mutane biyar ne kawai suke da shi. Daga Smart, Ramish, leesharh, guyson sai Jaish, ko Momma bata da shi, ko daga ina ya samo number? Ko da yake mai san abinka ya fika dabara.
Siririn tsaki ta ja wanda yasa Leesharh da guyson dawo da kallonsu a kanta, har suna haɗa baki wajen tambayarta lafiya kuwa. Kai kawai ta girgiza masu alamar babu komai. Kallo juna suka yi, guyson ne yasa hannu ya karɓi wayar tata domin ya duba me ta gani take yi wa tsaki!.
Daidai lokacin ɗaya daga cikin jami'an ya yi masu sallama a kofar room ɗin tare da shigowa. A tare Leesharh and guyson suka kai kallonsu a kansa haɗe da amsa mashi sallamar, ita kuwa Auta ta lumshe idanu tana san yin kuka, ta tina kalaman guy ɗin, idan baku manta ba a da can ta ce tana bala'in son kalamansa.
"Akwai wani abin ne?". Guyson ya tambayi jami'in. With full respect ya ce. "Abinci ne is ready, in kawo maku ne?". Jinjina mashi kai guyson ya yi alamar e ya kawo. Juyawa ya yi cike da jarumta ya fice daga ɗakin. Miƙewa Leesharh ta yi tana faɗin. "Yah Omer bari in yi wanka kafin muci abincin". Da okey ya amsa mata, kofar bedroom ta nufa dan fita, har ta kai wajen muryarsa ya dakatar da ita. "Aunty Aesh kada ki manta da yi mun Nigerian tea anjuma fa".
A miliyan ta juyo da kallonta a kansa. "Yah Omar wacece kuma Aunty Aesh?". Signal da gera guda ya yi mata kafin ya kashe mata ido ɗaya. "Kece Aunty Aesh namu mana, ko kin ɗauka ban san Yah Ramish ɗinmu na ƙoƙarin tsaraki kekuma kin ki bada haɗin kai bane? To ni narigada na bashi ke shiyasa ma nike kiranki da Aunty". Hararar wasa ta wurga mashi. "Ni Yah Ramish yayana ne kawai, bayan haka babu wani abin". Ta kai karshen maganar tare da juyawa zata cigaba da tafiya.
"Uhm mun san komai fa Aunty Aesh, shiru kawai nike yi, sai wahalar mun da yaya kike yi, ya yi ta faman lallaɓaki yana san ganin kina farinciki, sai ki ta wani sha mashi kamshi kina nuna ke bakya sonsa bayan kuma nasan sonsa kike kamar hauka, dik ina ganinku ai, sai kuma na faɗa mashi kina sonsa kawai ja mashi rai kike yi".
A miliyan ta sake juyowa dai'dai lokacin da ta kai bakin kofa. "Yah Omar fisabilillah a yaushe ka ji na ce ina sonsa ni?"........ Harara ya wurga mata shi ma tare da cewa. "Uhm me hotunansa suke yi a sabuwar wayar da ya saya maki? Wayar nan ko sati bata yi a hannunki na amma har kin cikata da hotunansa da kika rinƙa ɗaukarsa ba tare da ya sani ba, idan ya zo nan dik in da ya yi kallonki a kansa kamar yadda shi ma dik abin da yake yi yana satar kallonki, dik fa nasan komai, kawai idan zaki bada kai ki rungumo mun yayana ki kula mun da shi gara ki bada kai, idan ba haka ba kuma wlh basu mutuwar sonsa Allah ya yi yawa da su, kina ji kina gani wata zata kwace maki shi". MY PEOPLE'S KU TAFAWA KAIFIN ƘWAƘWALWA IRIN MA ƳAƳAN MOMMA, ASHE GUYSON YA HARBO JIRGINSU, YASAN KOMAI!
Rasa bakin magana ta yi, dan ya faɗi komai, bata da wani sauran kalami. Auta ce ta katsesu da cewa. "Aunty Aesh ki ja ajikinki hai, rabu da Yah Omar ɗin nan, ki tabbatar kin wahalar da Yah Ramish kafin ki yarda, amma fa ki rinƙa yi mashi kwalele sosai saboda ya kara rikice maki yana cigaba da sunkuyar maki da kai yana neman amincewarki, ki wana shi ki ja mashi rai sosai". Cikin sanyin murya sosai ta yi maganar. Ba kara mun daɗi suka ji ba yau Auta tasa baki a maganarsu, har suna rige rigen amsa mata.
Guyson ya ce mata. "Aww haka zaki ce ko Auta? Yah Ramish ɗin namu za'a wana, to sai na faɗa mashi!". Ita kuma Leesharh cewa ta yi "That's my lovely sis, shiyasa nike sonki, kin iya bada shawara, kanki na ja"................Ɗan yake Auta ta yi wanda aka ce ya fi kuka ciwo, cikin sanyin murya ta ce. "Yah Omar hakan shi ne maganinku, kai ma ai naga kana san wannan yarinyar da kake yawan cewa Yah Jaish ya haɗaku a waya, ina komawa gida zan hure mata kunne ta tabbatar ta baka wahala kafin ta amince maka". Kun san ita Auta bata san su Mahnoor ba, lokacin da suka zo kada ku manta ta tafi Paris, da ta dawo kuma tana cikin zulumi, ita totally bata cikin natsuwa, kunga ta ɓata zuwa forest, ta dawo ba jimawa ta wuce Paris, yanzu kuma tana nan Dubai, so bata san su waye su ba tukun nan!!.
A fujaje ya zaro idanunsa waje. "Please my pleasure kada ki zuga Mahreen, wlh yanzu ma haka azabtar da zuciyata take yi, Chuchu na can ta kara lalata mun ita da banzan shawara, ki rufa mun asiri, yanzu haka ni a matsayin ɗan iska nike a idanunta"........... Zaro idanu Auta ta yi, a hanzarce ta ce. "Yah Omar ɗan iska kuma? Kai ɗin ne ɗan iska?"
"No Auta, kome ya faru ni naja take kirana da hakan, kuma yarinya ce, so ba yadda kika ɗauka bane, manta ma da maganar waye ya turo maki wannan sako?". Ya yi maganar tare da nuna mata wayarta........ "Ban san wanenen ba ne". Ɗan jinjina kai ya yi kafin ya ce zai yi bincike a kan number ya ga wanenen, daga haka ya ciro wayarsa ya ɗauki number sannan ya miƙa mata nata wayar. Ita kuma Leesharh ta wuce ta nufi bedroom ɗinta.
Wanka ta tsara a gurguje, ta shirya cikin wani haɗaɗɗen abaya mai shegen kyau, ta yi rolling veil a kanta, ta fito so Masha Allah, sai tashin kamshi take yi. Waje ta nufo cikin hanzari. Har zata koma wajen su Auta sai wani zuciya ya ce mata ta je ɗakin Ramish, haka kawai ta tsinci kanta da san zuwa can, wucewa ta yi ta nufi can tana jin gabanta na faɗuwa, Hasbunallahu wani'imal wakil ta furta a cikin zuciyarta kafin ta ƙarisa wajen door ɗinsa.
Knowking ta ɗan yi dan a tinaninta kila yana a ciki. Sai dai kuma shirun da ta ji ba'a amsa mata bane yasa ta fahimci babu kowa a ciki. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya zata bar wajen, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi, har ta yi step biyu na taku sai kuma ta dakata tare da juyowa ta kalli kofar, a hanzarce tasa hannu ta tura kofar tare da afakawa ciki....... Shiru babu kowa sai sanyin Ac da niimantaccen kamshi dake tashi. Ajiyar zuciya mai ɗan sauti ta sauke tare juyawa zata fita. Unexpected ta hango kafar mutum a bayan labule wanda ko ba'a faɗa mata ba tasan kafar dattijuwa ce!.
Mamaki ne ya kamata na ganin dattijuwa a cikin bedroom ɗin, wato knowking da ta yi a farko ne yasa ta farga ta ɓuye kenan, to me ya kawota ɗakin? Me take yi mashi a ciki? Shiru ta natsa cikin thinking ɗinta, can kome ta tina sai ta saki ƙayataccen murmushi tare da juyawa ta nufi waje. Bedroom ɗin ta murzawa key ta baya sannan ta nufi bedroom na dattijuwar. Bincike ta hau yi mata babu kakkautawa kamar an aikota, ta kuwa yi nasarar samun wasu hotuna na mutane daban daban. Sannan ta yi nasarar gano cewa wannan matashiyar budurwa ta jima tana son Ramish, hakan ba karamun daɗi ya yi mata ba ta samu hanyar tunzura tsohuwar nan har sai ta tona asirin kanta da kanta!!.
Bata ɗauki komai a cikin ɗakin ba, sai dai ta yi snaping na wasu pic a wayarta, sannan ta mayar da komai yadda ta samu kafin ta dawo ta nufi bedroom ɗinsa, murza key ɗin ta yi ta buɗe, ba tare da tsoro ba ta shiga ciki, har lokacin dattijuwa na laɓe a bayan labule.
Ciki ta shige tare da zama a gefen bed tamkar tana jiransa, da alama akwai abin da ta shirya a ranta wanda bata bawa kowa damar ya sani ba. Da zamanta a gefen bed ɗin da shigowarsa room ɗin dik bai wuce ratar mintuna biyar ba, tana jin motsin zai shigo ta yi gaggawar kwanciya tamkar wadda barci ya ɗauka, irin kwaciyar da ta yi kamar unexpected barci ya ɗauketa haka, ta dunkule waje guda.
Sosai ya yi mamakin ganinta a room ɗinsa, har lumshe idanunsa ya ɗan yi ya sake warosu a kanta dan ya babbatar ba gizo mane ba!. Samun tabbacin hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya tare da ƙarisowa ciki, ko kaɗan bai game dattijuwa tana cikin room ɗin ba!. Gaban bed ɗin ya iso, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da sanya hannunsa ya gyara mata kwanciya da kyau, wlh har ya rame saboda damuwa a kan masu nikaf. A fili ya furta. "Ɗaukarki fa nazo yi Aesh". Ya yi maganar tare da zama a kusa da ita.
A hankali ta ɗan motsa wai irin mai barci yana son farkawa ɗin nan! "Aesh". Ya ambaci sunanta a hankali. Sake motsawa ta yi haɗe da cewa ummm irin mutum a cikin barci ya ji an kirasa ɗin nan. "Zaki iya tashi yanzu ne ko dai in kyaleki sai zuwa gobe mu je?". Jin ya kira batun fita ta yi saurin sake cewa ummm, an ji yawo ba, har da juyawa wai irin ta farkan nan, ita ma fa Leesharh A ce wlh. Cikin dabara ta ɗan buɗe idanunta, a lokacin yana bin surar jikinta da kallo, yadda ta kwanta mashi a saman bed ɗin nan yau da ita mallakinsa ne da ta sha mamakinsa, ya kwaɗaitu da ita sosai yanzun nan, idanunsa a kan kirjinta da suka fito sosai saboda yanayin yadda ta kwanta.
Ita kuwa ganin ba face ɗinta yake kallah ba yasa ta yi gaggawar satar kallon bayan labule, aikuwa nan ta ga dattijuwa tana leƙosu, ta ji daɗin hakan sosai, zata shaƙa mata bakinciki, a cewarta tin da ta gano yarinyar tana son Ramish soyayya na gaskiya to ba shakka da kishi zata amfani wajen sanyata ta tonawa kanta asiri.
Mai da idanunta ta yi ta datse gam tare da juyawa ta ɗaura kanta a saman laps ɗinsa, irin wai tana gigin barcin nan. Har cikin zuciyarsa ya ji ta amsa, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. Hannunsa ya kai saman lallausan kumatunta, cikin sanyin murya ya ce. "Aesh zaki iya tashi kuwa?". Ya yi maganar idanunsa a kan shape na HP ɗinta, tin da ya shigo bai kalli idanunta bane da zai gane barcin karya take yi, gabaɗaya hankalinsa a kan surarta. Marairace murya ta yi irin muryar barci, cike da shagwaɓa ta ce. "Yah Ramish barci nike ji sosai amma ka tashe ni"............... 🤔🥱
"Sorry to cigaba da yin barcinki kin ji?". Kai ta ɗan girgiza tare da juyawa ta yi kwanciya ruf da ciki, dan ta ga ya kurewa kirjinta da HP ɗinta idanu, sai abin ya bata kunya sosai, kun san mu fa Nigerians da kunya aka sanmu, mu ɗin ma arewaci ne masu kunyar, so Leesharh dai da sauran kunyarta...... "Yah Ramish ai ka rigada ka kori barcin tin da ka tasheni". Ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa game da waro idanunta. Dawo da kallonsa saman face ɗinta ya yi, dai'dai lokacin ta miƙe zaune tana kallon kasa. Kallo ɗaya ya yi wa idanunta yasan ba barci ta yi ba, ya ɗan yi mamaki, a ransa ya ce ko dai kewata Aesh take yi ne yasa ta zo bedroom ɗina ta kwanta da ta ganni kuma dan kada in ce me ya kawota shi ne ta yi acting kamar barci ne ya ɗauketa a wajen? Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya yi wannan tinani, sai ya ji daɗi, ko ba komai yau ta damu da shi.
"Yah Ramish yaushe ka dawo?". Ta yi maganar tana bin ɗakin da kallo, wai irin ta nuna kamar bama ta san nan ta shigo ta kwanta ba. "Kai me yakawoni bedroom ɗinka kuma? Kai innalilahi barcin nan bai mun dai'dai ba!". Ya faɗa tana ƙoƙarin sauka bed ɗin, wai tana son nuna mashi barci ne ya yi mata yawa