Showing 69001 words to 72000 words out of 403653 words

Chapter 24 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

63

Tiger a gefe, wanda shi tuni ya shirya aje a durkusar mashi da kingdom of power a kawo mashi King Zuhair gabansa ya zo ya yi mashi sujjada ya lashi kafafunsa, batun fitarsa fada ya dakatar da shegun wayakan Robbot ɗinsa ba su afka kingdom of power ba, amma yana nan da shirin a ransa, kuma zasu aiwatar, yanzu so yake ya shiga fada.

Hankalinsa ta ɗan kwanta, ya nitsu, bayan haka ya ɗauki mataki a kan Sweetie, idan ta bashi Spender sai su ruguje kingdom of power, wannan ne shirinsa a yanzu.

••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Yau hospital cike yake da ahalin King, Jawad da bai san Jaish ya dawo ba yana hospital zaune kusa da gadan da aka bawa Chuchu, su uncle Taheer dik suna cikin hospital ɗin.

Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsu a cikin asibitin, sai dai da ya tambayi me yake faruwa? Basu faɗa mashi Zunaira ta ɓata ba, sai suka ce mashi rashin lafiya ne na guyson da Chuchu.

Ya yarda da hakan, dan haka ya je ya duba jikin Chuchu kafin ya fito ya nufi ɗakin da guyson yake kwance. Bawan Allah tamkar babu rai a jikinsa.

Uncle Jahiz ya yi mamakin ganinsa a haka, sai ya yi tunanin ko ciwonsa ne ya tashi, dan haka sai ya yi mashi addu'a sosai tare da tofa mashi, sannan ya fito ya shiga wajen su Khadija.

Harda mai keken napep ɗin nasu dik aka taho da shi, idan baku manta ba na faɗa maku shi ma ɗan arewa ne, ɗan Kano ne, so da su uncle Jahiz aka ce masu babu kowa nashi da ya zo, sai suka haɗa da shi kawai suka kawo su ana jinyarsu.

Dik wannan bidiri da ake yi fa Sarina da Mammiensu suna part ɗinsu hankalinsu a kwance suna shabgar gabansu, sai kulla wani minahincin suke ta faman yi, da alama wannan karan mugu mugun abu Mammie take shiryawa wannan ahali!!.

Dai'dai lokacin da uncle Jahiz ya sako kafarsa cikin ɗakin dai'dai wannan lokacin Zee ta fara motsi numfashinta yana fita da karfi karfi.

A hanzarce ya ƙariso gaban bed ɗin nata, ɗakinta daban da na Khadija, iya kaɗai ne nan.

Ganin tana buƙatar taimakon likitoci ne yasa uncle Jahiz ya yi saurin juyawa ya je ya kira likita.

Oxygen suka zo suka sanya mata dan numfashinta ya dai'dai, a saman kujerar da aka tanada dan masu jinya uncle Jahiz ya zauna yana tinanin ina ahalin su Zee suke?.

Tsananin tausayinsu ne ya kama shi sosai.

Oh ta ko'ina ba sauki fa, to bari dai mu leƙa Dubai muga me ake ciki ne wai!.

•••••••••••••••••DUBAI•••••••••••••••••🔥

Tuni Ramish ya miƙawa jami'ansa Leesharh, dama sun jima suna neman kamata, sai yau dubunta ya cika. Sai dai fa ni da ku dik munsan halin Leesharh da ɗan banzan taurin kai, yadda aka rinƙa fama da ita a court ta yi magana lokacin da ta kashe mamarta ta ki buɗe baki ta yi magana haka yanzu ma ta yi.

Dik wani azabtarwa sun yi mata amma taki ta yi magana, har ya kai ya kawo bata iya takawa da kafafunta saboda azabtarwa Ramish, amma dik da haka taki basu haɗin kai, daga karshe ma da suka matsa mata sai ce masu ta yi dan Allah su kasheta kawai ta huta, dan ita dai bata ma san a kan me suke tukumarta ba.

Wannan magana ya matuƙar konawa Ramish rai da har yasa bindiga zai harbeta ɗin da gaske, Bilal ya dakatar da shi ta hanyar kwace bindigar ya ce dan Allah Ramish ya barshi da case ɗin a hannunsa, zai sakata ta yi bayani cikin ruwan sanyi, Ramish zafin zuciyarsa ta yi yawa, abu kaɗan ya hasala, dan haka ya bar mashi case ɗin kawai.

My people's kun yarda Ramish ya barwa Bilal wannan case ɗin? Kada ku manta Leesharh ta ce ta taɓa ganin Bilal a gidan masu nikaf, sannan kada ku manta Bilal shi ya fara nunawa Leesharh kauna da tausayawa a gidan, meyasa Bilal ya hana Ramish ya kasheta? Kai bari dai na barku haka kada masoya Bilal su yi mun zanga zanga, amma dai bani na faɗa ba, Leesharh ce ta ce ta taɓa ganinsa a gidan masu nikaf, dan haka dole mu zargesa!!.

Tsabar rainin wayo irin na Leesharh ma, har da ce masu ita fa wannan ba wayarta bace, kuma bata san a kan me ma suke magana ba.

Wato masu nijaf sai da suka yi binciken wacece Leesharh kafin su bata wannan aiki, irin wannan taurin kai haka? Dama irinta ƴan ta'addan suke so.

Ramish bai so barinta a raye ba, amma Bilal ya ja shi suka bar ɗakin da ake horata a ciki ɗin, sai daɗin baki da kalamai masu daɗi Bilal yake yi mashi dan zuciyarsa ta huce ya mance da batun Leesharh.

Yasan wanenen Ramish sarai, yasan idan ransa ya ɓaci ya ce zai yanke hukunci a kan abu to fa sai ya yi, shiyasa yake mashi daɗin baki dan ya mance da komai.

(Ni kuwa nace da a yadda yake cikin ɓacin rai yanzun nan King ya yi mashi waya ya ce an sace Zunaira mana😂 me kuke tunanin zai faru?🤔 Tab na yi nan babu ruwana😂🥱)

A can gefe kuwa, wuni kuka kwana kuka Sharifat take yi, ta gama shiga tashin hankali da damuwa, Allah sarki, tana kaunar Leesharh tamkar ranta, bata taɓa zaton cin amana daga gareta ba, yau tsawon kwana uku tana kuka a kan rashin Leesharh, har ƴar rama ta yi.

Abu Abdussalam ya yi rarrashi har ya gaji, shi ma Leesharh ta kariyar mashi da zuciya, ya ji baya san sake jawo wani jikinsa kuma, hakika ya shiga tashin hankali.

Ita kuwa Ummie, wlh ranta fes, sai addu'a ma take yi Allah yasa Ramish ya kashe Leesharh kowa ma ya huta.

Ramish da kansa ya yi wa Leesharh azabar da sai da ta zaɓi mutuwa a kansa, irin azaban da yake ganawa manyan ƴan ta'adda da jami'ansa idan suka yi laifi ya rinƙa gana mata, amma Leesharh ta daure ta shanye wannan dukka.

Ko sa yake ai ta saba da wahala tun da ta yi zaman gidan AAJ, yarinyar da ake tuhuma da kashe mahaifiyarta ai kunga dole ma zata yi fin hakan.

Hmmmm wato fa Dubai ma ta kama da wuta, ta ko'ina dai ba sauki, to bari dai mu leƙa France muga ko da ɗan sauki sauki can.

•••••••••••••••••FRANCE••••••••••••••••🔥

Sosai Smart ya sha barcin na good 4 hours, sannan ya farka. Misa call ɗin mom ya kai 10 a wayarsa, sai kiransa take yi yaki ɗagawa, da ƙoƙari irin nata wai so take yi ya zo su yi bankwana da iyayen Heleena zasu koma England, har suka tafi ba'a samu ya ɗaga call ba.

Robbert kuma mamaki yake ta yi a kan ya aka yi wannan nuclear da aka gwada bata dawo ba, kada ku manta shi bako ne a wajen, yanzu yake koyan aiki. Batu na gaskiya makamin nuclear ba'a harba shi sama kuma ya dawo, idan aka saita shi in da ake sam ya je aka harna shi ya tafi shikenan, ba zai dawo ba, wannan shi ne nuclear na gaskiya.

So already a cikin takekken teku Smart ya saita shi, dan haka yana tashi barci ya je ya duba computersa dan yaga yadda makamin ta tarwatse a cikin ruwa, dama so yake yaga karfin aikinta, idan ta yi yadda yake da buƙata sai su cigaba da haɗa irinta, wannan shi ne gaskiya.

Robbert dai kasa hakura ya yi har sai da ya tambayi Smart ya aka yi makamin bata dawo ba.

Iska Smart ya bawa ajiyarsa, dan bai amsa mashi ba, ya wuce ya yi wanka tare da sauya kayan jikinsa, ya fito ya umarci yaransa da su cigaba da haɗa irin wannan makami dan ya yi mashi yadda yake so hundred over hundred!.

Daga haka ya nufi gidansa.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





•••••••••••••BLACK WORLD•••••••••••••🔥

A hankali jiki dik a mace Ronnie ya hau saman escletor domin ya haura izuwa parlourn Black Tiger, jiya kwana suka yi suna cashewa, yanzu haka idanunsa dik barci, kuma yana da Exams a school da zai rubuta yau, kamar wanda aka hana shi yin barci jiya, wato shi dik in da sharholiya take yana nan wajen abinsa, bashi da wata damuwa.

Allah sarki jiya Floris ta rufe mashi kofan ɗaki hakan yasa ya je ya yi rawa a tare da Angela, kun san jiya ta yi fushi ai, ta kwana kuka Ronnie ya kwana taka rawa abinsa, yo dama shi me ya damesa? Ai sai dai ta kashe kanta da bakinciki, shi bai taɓa cewa yana san ta ba, infact Ronnie bai san menene soyayya bama, kunga kuwa babu fushin wata mace da zai hana shi yin abin da yake da ra'ayi!!.

Ko Sweetie tausayinta kawai yake ji, bai taɓa cewa yana santa ba, hasalima wlh a yanzu kam babu soyayyar kowace mace a ransa, Sweetie ma shakuwa da kauna ce irinta kanwa da ya ɗauketa, ita kuma Floris kyanta yake burgesa, that's all.

Yanayinsa idan kuka ga yadda yake treating ƴan'mata sai ku yi zatan sansu yake yi ko wani abin makamancin haka, ainahi zuciyarsa tana da rauni a kan halittar macece sosai, amma kuma ai kunga jarumi ne a kan maza sosai, yana zubar da maza a wajen Wrestling, mata ke cin riba a kansa.

Yana san zuwa room ɗinsa duba Sweetie, amma ya fi san ya fara zuwa wajen yayansa.

Yana zuwa ya buɗe kofar ɗakin da password ya shiga ciki. Ɗan jujjuya koreans eyess ɗinsa ya yi yana neman ta ina yayansa yake? Dan ɗakin tana da girma sosai.

Like wow he was so surprised na ganin alamar babu mutun a cikin ɗakin, shiru ya ɗan tsaya tamkar mai nazarin wani abin, yau kwata kwata baya san zuwa school, dik san shi da karatu yau dai baya jin zai je.

Calmly ya fara takawa dan ya ƙarisa ciki ya tabbatarwa da kansa da gaske yayansa baya nan. A bakin bed ya zauna yana cigaba da bin ɗakin da kallo, shi ko tsoron ɗakin ma baya ji.

Hamma ya fara dakawa alamar barcin tana san a biyata bashin da aka ci daren jiya da ba'ayita ba, ɗan yamutse fuska ya yi tamkar guyson a gabansu Yah Ramish.

Shi da zai je ya yi shirin tafiya school sai ga shi ya gyara ya karkata ya kwanta a saman bed ɗin abinsa............ Kafin ƴan mintina barci ta yi awon gaba da shi.

Ita kuwa Floris ta sha kuka har kamar ranta zai fita, daga karshe barci ya yi awon gaba da ita zaune a bakin gado, sai da ta kwala kanta da jikin headboard na bed ɗin ne, da ta ji zafi sai ta karkata ta kwanta haɗe da rungumo pillow tana jin kunan rai tana kuma sauke ajiyar zuciya har barci ya yi awon gaba da ita.

After some hours.

A hankali Sweetie dake kwance s saman bed ɗin Ronnie ta fara motsa idanunta da suka yi mata bala'in nauyi, zara zaran eyelashes ɗinta a jike suke da hawaye, alamar kafin ta yi barcin nan hawaye sun zuba daga idanunta sosai.

Jikinta dik tamkar an girka dik wasu gaɓɓai ɗinta, tsokar namar jikinta dik sun yi mata tsami tamkar wadda aka yi wa luguden duka da sandina, harta tongue ɗinta ji ta yi tamkar an sanya igiya an ɗaure mata shi, taci bakar wahala daren jiya a hannunsa ne, yarinya ta ji kamshin mutuwa, Allah ma ya taimaketa yana san Spender a hannunta yasa ya yi ƙoƙari ya yi mata magani ta tashi bata mutu ba, da jefar da ita zai yi.

Gashin kan nan nata tamkar wanda aka sanya kum aka baza mata shi, dik ya cukurkuɗe kamar kayan wankin da aka kwato daga bakin kura, idanunta har sun kumbura sun yi jajir da su, har ta kara hasken wahala yar ƙaniya.

Ta sha madarar mamaki matuka a lokacin da ta waro idanunta ta ganta a cikin ɗakin Ronnie, bata yi tsammanin hakan ba, ta yi zaton ganin kanta a wata duniyar kamar yadda ya nuna mata tun farko zata yi, ya aka yi ta dawo nan? Ta jefawa kanta tambaya.

Allah sarki, ta yi zaton ta yi bankwana da su Ronnie kenan, ashe ba haka abin yake ba, gata ta dawo garesu.

"Good morning sarkin barci"............ Kamar daga sama ta jiyo sautin muryar Ronnie ta bayanta.

Da sauri ta juyo da kallonta ta wajen. Yana tsaye gaban mirrorsa, sanye yake da wando three quter jeans sky blue, da round neck polo shirts black color, ya yi masifar kyau cikin bakin rigar, tamkar ka sace shi ka gudu.

Yana tsaye yana ƙoƙarin sanya ɗan kunne a kunnuwansa, ta cikin mirror ya hango ta farka yasa ya yi mata magana. All his though since yesternight da suka rabu take barci up till now, shiyasa ya ce mata sarkin barci, bai san ita ɗin ma dik kanwar ja bace, ai kusan a tare suka yi barci wato da safe kenan, and ita daga suma ne ta farfaɗo ta zarce da barci.

Ajiyar zuciya a bayyane ta sauke mai matuƙar sanyin gaske wanda yasa Ronnie juyowa gareta da kyau. A yau dai ƙaƙalo murmushin dole ta yi ta sakar mashi, dan bata taɓa tinanin zata rayu ba, ta sha bakar wahala, so babu walwala a tattare da ita, infact bata ma jin daɗin jikinta, dik wani sassa na jikinta kamar na nata ba.

Bayansa ta kurawa kallo sosai kafin ya juyo, idan ka gansa a yanayin yadda yake tsaye ɗin nan sai ka ji gabanka ya faɗi, ko ta baya ka gansa kasan ya cika cikar halitta sosai, ga faɗin baya sosai saboda wrestling ɗin da yake yi, sexy body kamar na yayansa.

Gashin dake kwance a bayan wuyarsa ta zubawa idanu tana kallo, sai a lokacin ta lura gashin kan Ronnie fa kamar combination ne na two colors ba zallar white bane, dan daga tushen gashin nasa zaku ga kamar ruwan toka toka mai haske haka.

Ɗan runtse idanunta ta yi tana ƙoƙarin tunani ina ta taɓa ganin irin wannan gashin? Tabbas kafin idanuwanta su dai'na gani a lokacin da take forest wlh ta taɓa kallan mai irin wannan gashi.

Wani irin juyawa da wani sadaukin warriors ya yi da karfi ne yasa gashin kansa ya pyaɗeta a wuyarta, da sauri mum ɗinsu ta ɗauketa daga wajen................... Da karfi ta sauke ajiyar zuciya, tabbas ta tuna in da ta taɓa ganin sak irin wannan gashi, tun mum ɗinsu tana a tare da su a forest, akwai wani lokaci da wasu warriors suka kai masu hari zasu ɗauki mum ɗinsu, tabbas a nan cikinsu ta taɓa ganin mai irin wannan gashi, to ko waye shi? Kuma a yanayin girman jiki da kira ba zai wuci kamar Ronnie ɗin ba!.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Ɗan ciza laɓɓanta ta ɗanyi kafin ta motsa jikinta zata miƙe zaune. Sai dai kash, ta ƙasa iya motsawa bare har ta miƙe zaune, gaɓɓanta tamkar an ɗaure mata su.

Ronnie ya lura da ita kamar ba lafiya take ba, dan tin daga kan yanayin yadda ta sakar mashi murmushi ya fahimci lallai akwai matsala, dan wannan ba ƙayatattcen murmushin da ta saba sakar mashi bane.

"Sweetie are you okey?"................. Da mamaki sosai a saman face ɗinsa ya yi maganar.

Ita kuma kyan da ya yi mata a lokacin da ya juyo gareta kawai take kallah.

Cikin kasala da nitsuwa ya tako zuwa in da take, jikinsa dik a mace. A gefen bed ɗin ya zauna yana kallon fuskarta, sai a yanzu ya lura da kumburin da idanunta suka yi, da kuma shi kansa face ɗinta.

Da yake Dr ne shi ɗin sai ya yi tinanin barcin da ta yi ta zubawa ne yasa idanunta suka ɗan yi ja suka kumbura, bai dai yi tinani maras kyau ba.

Ganin ta kafe shi da kallo ne yasa ya ɗaga mata gera guda irin ɗan duniyar nan. Bata san lokacin da ta ɗan wurga mashi hararar wasa ba sai ji ta yi ya ce.

"Laifin me kuma na yi yau kike hararata?".

Blinking eyes ɗinta ta ɗan yi tare da kawar da kallonta daga kansa, cike da takaicin abubuwan da yake yi wanda suka saɓawa Allah amma a wajen mutanen birnin Black world hakan normal ne, ranta yana ɓaci a dik time da taga Ronnie zai aikata saɓon Allah, saboda tana san shi da rahama tana san ya tsira daga azabar lahira.

Ranta ya sosu sosai na ganin ya kara zana zanen tattoo a gefen wuyansa na dama, sannan wannan uban ɗankunnaye da yake sakawa sam bata san ganinsu.

Cikin takaicin hakan ta ce. "Ronnie meyasa kake san aikata ba dai'dai bane?".

Idanunsa a kanta ya amsa da. "Menene kuma ba dai'dai ɗin da na aikata ba?".

Dawo da kallonta kansa ta yi, kamar ta kama kunnen nan nasa ta ja da karfi take ji, bashi da aiki sai zane jiki ya kuma bi fuska da karafuna kaman wanda bashi da mafaɗi, ko da yake kusan bashi da mafaɗin ne ai, tin da dik abin da yake so shi yayansa yake yi mashi, kunga kuwa ai babu mafaɗi.

"Meyasa kake zane a jikinka kuma kake san saka waɗan nan karafuna a face ɗinka?".

Fuskarsa ce ta sauya izuwa na mamaki, shi bai taɓa sanin hakan wani abin azo a gani bane, ya ɗauki hakan a matsayin kwalliya ne kawai, bai ɗauki hakan wata tsiya ba, dan haka with full of surprise ya ce.

"Hakan yana da aibi ne?"..............

Jinjina mashi kai sosai ta yi, kafin ta amsa da. "Babban aibi ma kuwa, kuma yana ɗaya daga cikin kananun alamomi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login