Showing 78001 words to 81000 words out of 403653 words

Chapter 27 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

84

da alama wani mugun abin ta kullah.

Da gudu ta shige cikin ɗakinta, kamar ba ita ta fito yanzu ba, har da kwanciya ta lulluɓa da zaninta.

Bappa kuwa ya fito ya shiga banɗaki dan yin wanka. Ita kuma Mairo ta hau sharan ɗakin, da alama Mairo tana da tsabta sosai.

Mahnoor kuwa bayan ta gama, a kusa da Mahreen ta zo ta zauna tare da buga uban tagumi, a hankali ta fara jin faɗuwar gaba kaɗan kaɗan kamar wani abin yana shirin faruwa da ita, jingina bayanta da jikin bango ta yi, a hankali ta fara maimaita Hasbunallahu wani'imal wakil domin Allah ya saukaka mata koma menene yake shirin faruwa da ita!.

A wani irin haukace bappa ya fito daga cikin toilet ɗin nan, ihun da yake kurmawa da karfi sai ya razana dik wanda kunnuwansa zasu saurara. Cike da tashin hankali da firgici ya faɗo tsakar gidan yana ihu.

Mahnoor tamkar bata ji su ba, sam bata fito ba, dan tasan shi da matansa ne, sai ma kifa kanta ta yi a saman gwiwowinta ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Da gudu Mairo ta fito daga cikin ɗakin dan taga menene yake faruwa, Nenne kuwa sam taki fitowa tana ciki kamar bata ji shi ba, sai dai tana can tana zuba uban dariya kamar wata zararriya.Ta toshe baki da pillow dan kada sautinta ya fita tana ta tikar dariya.

Mario tana fitowa ta iskosa kwance rashe rashe a kasa yana ta birgima yana ihu kamar wani zararre, daga shi sai kajeran wando a jikinsa, ita ma bai gama sanyata da kyau ba, ga kuma ruwa a jikinsa, da alama ya fara wanka ne ya fito, dik kasa ta buɗe shi saboda ruwan dake jikinsa.

Ganin haka yasa Mairo ta fita waje da gudu neman taimako dan taga kamar wani mai ciwon aljanu ko farfaɗiya haka, so ba zata iya ba sai ta yi waje dan neman taimako.

Kai tsaye gidansu Arɗo Mairo ta nufa, ko mayafi bata ɗauka ba, hankalinta ne a tashe.

Takuwa yi sa'a Ibrahim kawun Mahnoor yana nan, dan haka sai suka taho a tare da shi da Arɗo.

Dik ƙasa ya farfasa fatan jikin bappa, saboda yadda yake ta dirza jikinsa a kasa yana ihu, kafin Mairo ta dawo wlh har jiki ne yake fitowa daga fatar tasa, bawan Allah.

Ashe ƙarara Nenne ta je ta zuba mashi a cikin ruwan wanka, muguwa saboda tasan Mairo ce ta kai mashi ruwan wankan, kunga yanzu zai ce Mairo ce ta yi mashi mugunta, Allah sarki daga zuwan amarya bappa zai fara ganin laifinta. Wato wlh Nenne da gwaggo anya akwai shaiɗanu irinsu kuwa? Dik abin da Nenne take yi gwaggo take shirya mata shi dallah dallah yadda zata yi komai, shiyasa kuka ga ta dawo gidan bappa da confidence ɗinta.

Sun lura aikin bokaye baya kama bappa, shi ne suka dawo ta munafurci da kisisina, komai Mairo ta yi su ɓata, tin bappa baya ganin laifinta har ya zo ya fara gani ya fara jin haushinta, har ma ya saketa, shi ne burinsu, to yanzu Nenne ta fara fito da makaman yakinta, muje zuwa dan ganin yadda wannan wasa zata kaya.

Ƙoƙarin kama shi Arɗo dattijon arziki da Ibrahim suka yi dan su kai shi ko da ɗaki ne kada ƙasa ta cigaba da fasa fatarsa. Sai dai ina, sun kasa kama shi, saboda wani irin zillo da yake yi, burinsa kawai a sosa mashi jikinsa, wani irin bala'in kaikayi na musamman yake ji, Allah sarki bawan Allah.

Ga shi kararar ta damuna ce ba ta rani ba, irinta ta fi bala'in zafi, kaikayi kamar zai kashe mutum, ga zafi idan ka sosa, wlh Nenne muguwa ce ta karshe, tana ɗaki tana ta dariyar mugunta hegiya.

Mairo kuwa kuka kawai take yi da hawaye bibbiyu, Mahnoor ma tana jin dik abin da yake faruwa, amma taki leƙowa, saboda bata san ganin wani tashin hankali a kan wanda take ciki a halin yanzu.

Sai da Ibrahim ya fita ya samo wasu manyan maza su biyu, sannan suka zo da kyar suka iya kama bappa. Allah sarki abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya, dan yadda yake birgima sai ya baka dariya, hannunsa dikka biyu a kansa, dan daga kai ya zuba ruwan, tamkar zai ɗaye fatar kansa saboda sosawa, ji yake yi kawai ya yi ta dirje kan nasa a ƙasa ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji.

A yanzu ma bai san su wanenen a kansa ba, wlh kuka yake yi sosai, hawaye dik ta wanke mashi fuska. Mairo dik tinaninta yana da wani ciwo ne da bata sani ba.

Arɗo da ya gane menene sai ya ce da Ibrahim a kawo mashi ɗanyar kashin shanu, dan shi ne maganinsa.

Jin Arɗo ya ce a kawo ɗanyar kashin shanu yasa Ibrahim ya fahimci karatun, ransa ne ya yi mummunar ɓaci, a kule ya ce. "Waye ya saka mashi karara kenan?". Ya yi maganar yana kallon Mairo, da yake akwai zuciya da saurin fushi sai nan take idanunsa suka yi ja ransa ya ɓaci.

Mairo da hawaye sun gama wanke mata fuska ne ta fara girgiza mashi kai tana faɗin wlh ba ita bace kuma bata san wacece bace. Ibrahim zai sake yin magana Arɗo ya umarcesa da ya yi sauri ya kawo ɗayar kashin shanun nan da wuri kada su rasa bappan.

A fusace ya fice daga gidan, a ransa ya kudurta babu abin da zai hana shi cin uban koma wanene ya saka wa bappa wannan abin........... Lallai Nenne zata sha duka a hannun yayanta kenan.

Da kyar suka kama bappa suka kaisa ɗaki, a saman batarman amarya Mairo suka kwantar da shi.
Sanya waɗan nan maza biyun Arɗo ya yi da su danne mashi bappan da karfi, haka suka danne hannunsa da ƙafafunsa, Allah sarki yana jin kaikayi sosai hakan yasa da suka danne shi babu halin sosawa sai ya fara zaro idanunsa da suke jajir kamar wuta yana wani irin miƙa yana san kwace kansa, azaba yake ji Allah sarki, wlh dik wanda ya gansa a wannan hali sai ya tausaya mashi, abin akwai azaba ne sosai.

Wlh ko leƙowa Nenne taki yi, tamkar bata a cikin gidan. Suna ɗauke bappa izuwa cikin ɗaki ta samu hanya ta fita gidan a miliyan sai gidan Arɗo. Ta je gwaggonta ta ɓoyeta a cikin ɗakin, wato waɗan nan biyun anyi mugaye, kamar waɗan da suka fita daga tsatson Black Tiger............🤔

Da kyar su Arɗo suka iya ceto bappa ta hanyar yi mashi wanka da ɗanyar kashin shanu, suna tsaka da yin wannan aikin ne tamkar saukar aradu suka fara jin kukan jirage a sararin samaniya.

Ai a miliyan Mahnoor ta fito waje daga cikin ɗakinta, dan tasan waɗan nan jirage su suka rabata da mijinta, ta manta ma bata goge hawayen fuskarta ba, dama Mahreen ma ta tashi daga barci tin lokacin da bappa yake ihu, Mahnoor ɗin ce ta hanata fita, so yanzu sai suka fita waje da gudu a tare.

Tamkar dai a baya yadda suka zo suka ɗauki Jaish, haka yanzu ma jirage ta sama motoci ta ƙasa, kuma a kusa da kofar gidan bappa suka faka motocin.

Waje Mahnoor da Mahreen suka fita, yau Mahnoor babu tsoro, dan zuciyarta mijinta kawai yake san gani, burinta ta sanya idanunta a kansa, shiyasa bata tsorata da jirage da motocin ba.

Gabaɗaya mutanen kauyen a wannan karon ma fitowa waje suka yi dan ganin su wanene suka zo. A lokacin su Arɗo sun kammala shafe bappa da kashin, hakan yasa bappa ya nitsu tsit kamar wanda ya yi barci, tabarman Mairo kam ya lalace da kashin shanu.

Fitowa Arɗo suka yi, dan suma su je suga su wenene?. Kowa a kauyen sai rarraba idanu suke yi, yau shine ganin motonci na biyu a kauyen.

Manya manyan bodyguards ne suka fara fitowa daga cikin motocin, da yake dikkansu larabawa ne, sai su Mahreen suka yi masu kallon mutane guda, wai suna kama sosai.

Gabaɗaya yan kauyen sai da suka ja da baya lokacin da bodyguards ɗin nan suka bayyana, wasu jiga jigai da su.

Bubbuɗe kofofin motocin suka yi gabaɗaya. A hankali uncle Jahiz ya fara fitowa daga cikin motar. Ya zo ya tsaya a kusa da ɗaya daga cikin motocin, yau yana shirye cikin Arabs dressing, har da alkyabbarsa ya ɗaura saman shigar tasa, ya fito a balarabensa sak.

Like wow unexpected momma ta fito daga cikin ɗaya daga cikin motocin wanda uncle Jahiz yake tsaye a kusa da shi, tana fitowa guyson ya biyo bayanta, da kallo ɗaya zaka yi mashi in dai kasan shi ka gane bashi da cikakken lafiya sosai.

Mahnoor tana ɗaura idnaunta a kan momma da guyson nan take ta gane dik yadda aka yi ƴan uwan Jaish ne, dan jini ba wasa ba, ita kuwa Mahreen da hankali bai gama isarta ba kallon Jaish ta yi wa guyson, kun san na gaya maku guyson yana da tsawo sosai, amma bai kai Jaish ba, kuma Jaish ya fisa cika gaskiya, amma ita kallon Hamma Jaish ta yi mashi.

Kowa ya zaro idanu waje yana kallon waɗan nan kyawawan taurarin, barema guyson da kusan rabin ƴan kauyen suke yi mashi kallon Jaish, har sun fara manta yadda Jaish yake. Dik hankalin kowa a tashe, wasu sai kuskus suke yi suna gulmar bappa, wai bappa ne dik ya fara ɗauko masu wannan annoba dangin aljanun ya kawo masu kauye, da bai ɗauko Jaish ba ai da hankalinsu a kwance, yanzu ga shi sai zirya motoci suke yi a kauyensu suna ɗaga masu hankali.

Wasu kuwa addu'a suke yi Allah yasa bappa aka zo kashewa tin da shi bashi da aiki sai yayuɓo mutane ya kawosu gidansa ya ajiye. Sai mugun fata suke yi mashi.

Jama'a ku tafawa mata......... Meya kawo Momma Jimeta? Mu koma baya mu leƙa KINGDOM OF POWER mu ji ta ya aka yi suka zo kafin mu dawo muji dame suke tafe.

Jama'a nace ku kara tafawa mata........

Bayan dawowar Jaish da kwana biyu, sai da suka barshi ya huta, sannan ne momma ta buƙaci da tana san sanin in da ya afka tsawon wannan watanni da ba'a gansa ba, King ne ya ce mata e gaskiya hakan kam yakamata, yakamata su san in da ya je.

A lokacin su commander Zafar sun shirya tsab zasu tafi yaki, ba yadda Aunty MieMie bata yi ba a kan King ya dakatar da wannan yakin su yi tsastsauran bincike tukun nan, amma ina ransa a ɓace, zuciyarsa taki sauƙa, hankalinsa baya jikinsa, ya ce babu ja da baya, umarni yake badawa ba shawara ba, kada ya sake jin bakinta a cikin wannan magana, hakan yasa ta ja gefe ta yi shiru, amma wa King kawai, ta nuna mashi ta bar zancen, amma bata bari ba, ta dai umarci su commander Zafar a kan ta basu nan da kwana biyu dik in da Zunaira take su nemota, idan ba haka ba kada su dawo kingdom ɗin nan, shi ne abin da ya faru.

A tinanin king umarninsa suka tafi aiwatarwa, amma neman Zunaira suka tafi, saboda dama dan Zunaira za'a je yakin ai, idan aka dawo da ita ba shikenana ba zance ya mutu, idan kun lura ita Aunty MieMie bata san yaki sam sai in ya zama dole, dik da taurin zuciyarta akwai imani da tausayi a cikinsa, tasan yaki yana haifar da matsaloli sosai, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya rasa rayukansu.

Guyson ya farfaɗo daga doguwar sumar da ya shiga, sai dai baya magana, dik yadda suka so ɓoyewa Momma rashin lafiyarsa sai da ta gane, dan ta rasa sukuninta, ta shiga damuwa, hakan yasa King ya sanar da ita cikin nitsuwa ta hanyar da yasan ba zata ji raɗaɗi sosai ba.

Aikuwa faɗa mata ɗin ya yi amfani, ta buƙaci a dawo mata da shi gida ta yi jinyarsa, a turo nurse su zo su rinƙa kula da shi a gabanta tun da ita babu halin ta je hospital. Hakan aka yi, dan dik abin da zai faranta mata shi King yake yi a yanzu, baya san ganinta a cikin damuwa, dan ma dawowar Jaish ya rage mata abin da take ji a ranta sosai.

Jinyar guyson da ta fara yi ne tana faɗa mashi kalmomi masu karfi dan nuna tawakkali da godiya ga Allah, sai Allah ya taimaketa ta fara shawo kansa, kunga kuwa faɗa mata rashin lafiyarsa ya yi amfani, tin da ga shi ta dalilinta ya ɗan samu lafiya har yana iya yin magana.

A daren rana na huɗu da dawowa Jaish Tunisia, dama ya yi kwana ɗaya a Nigeria, so a rana ta huɗu da dawowarsa momma ta buƙaci da su zauna su yi magana a kan daga ina su uncle Jahiz suka ɗaukosa, dik ta damu tana san jin hakan, kun san mufa mata batu na gaskiya muna da sanin yakamata ato, taga yakamata ta san daga ina yaronta ya fito ne?.

Uncle Jahiz ne ya fayyace masu komai yadda ya kasance da yadda Ramish ya gano in da yake har suka je suka ɗaukosa. Dik cikin parlourn wanda kowa da kowa yana cikin except Jawad da Chuchu da har yanzu Chuchu jikinta bai warware ba, suna hospital, sai kuka take yi taki dainawa, ita dai a dawo mata da Autarta.

A gabaɗaya parlourn nan babu wanda ya gane aibi a cikin abinda su uncle Jahiz suka aikata, kowa sai godiya yake yi wa Allah, sai murna suke yi, shi ma Jaish yana zaune kusa da Momma, sai satar kallonsa Fanan take yi, tana san yi mashi sannu da dawowa, amma tana tsoronsa sosai.

•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

"Amma Jahiz wani irin abu ne wannan zaku je ku ɗauke shi ba tare da kun nemi waɗan da suka rikesa kun yi masu godiya ba?".

Muryar momma ce ta dakatar da dikka wannan godiya da murna da suke yi ɗin.

Mummyn Chuchu ce ta amsa da. "Gaskiya nima naga abin bai kyautu ba sam".

Aunty MieMie dake zaune a gefen King ne ta amsa da. "Gaskiya kam ba'ayi masu adalci ba, bai kamata ayi masu haka ba".

Miƙewa Jaish ya yi ya nufi hanyar fita daga parlon. Aunty MieMie ce ta tambaye shi ina zai je.

Ba tare da ya dakata daga tafiyar ba ya amsa mata da nitsuwa yake so, baya san hayaniya, zai je ne ya kwanta. Miƙewa ta yi ta bi bayansa dan tana san yi magana da shi. A wannan lokacin ne suna fita ya wuce hospital wajen Jawad dan yau tun da rana da ya je asibitin suka gaisa bai sake zuwa ba, Jawad kuma baya fita ko nan da can sai masallaci, so a tare suka je da Aunty MieMie.

Sosai momma ta nuna rashin dacewan abin da suka yi, ita ma mummyn Chuchu ta nuna hakan, mama dai bata ce ko uppan ba, ta dake a kan kujera tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya.

Momma ce ta nemi King da ya yarje mata zata je ta ga mutanen nan da suka rike mata yaro, har ta ji kaunarsu ya ka mata, uwa kenan, ko yaya ka yi wa ɗanta abu bata mantawa da kai.

King yasan condition da take ciki na rashin nitsuwa a kan ɓatar Auta, a yanzu farincikinta suke nema ba ɓata mata ba, dan haka sai ya ce to za'a shirya mata tafiya nan da gobe ta je ta gansu ɗin, wannan shi ne dalilin zuwanta Jimeta, bata ma san Jaish yana da mata ba, bata san irin rayuwan da ya yi a can ba, ita dai ta zo da kanta ne ta yi godiya na riƙe mata yaro da suka yi, to kun ji yadda aka yi, taso su zo a tare da Jaish, amma yaki yarda, ya ce shi gaskiya babu a gajiye yake, kuma baya san zuwa ne kawai. Yauwa ku kara tafawa mata jama'a.......

••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Da gudu Mahreen ta tafi ta rungumi guyson, dan a tunaninta Jaish ne, securitys ɗinsu sun so hana Mahreen isa gare shi, amma kafin su tareta tuni ta isa gare shi, kun santa da iya gudu.

Ita dai Mahnoor ta san ba Jaish bane, dan suna da banbanci da guyson dik da cewa guyson ɗin ke binsa a wajen haihuwa, amma suna da banbanci.

Momma bata yi mamakin ganin Mahreen ta rungume mata yaro ba, saboda tana ganin Mahreen yarinya ce, sannan kuma hakan da ta yi yasa momma ta kara jin daɗi a ranta, dan alamu sun nuna sun yi sabo da Jaish sosai shiyasa ta rungumi guyson matsayin Jaish.

Uncle Jahiz ne ya wuce gaba wajen isa gaban Arɗo dake tsaye a kofar gida yana kallansu, sun ga shi ne dattijo a wajen sai suka nufesa.

Sarautar nan dai tana nan, badan momma bama da su uncle Jahiz ba zasu zo nan ba, dan haka cikin isa ya ce da Arɗo suna neman gidan da ɗan uwansu ya yi rayuwa a ciki kafin suka zo suka ɗaukesa kwanaki shidda zuwa bakwai da suka wuce!

Arɗo ya ɗan yi mamakin jin yadda Uncle Jahiz ya yi mashi magana kamar wani ɗansa, yana mashi magana ba girmamawa, bai san haka suke magana cike da izza ba su kam.

Da hannu ya nuna masu gidansu Mahnoor dake bayansa, dan yasan a kan bakonsu Jaish suke magana.

Momma da guyson kuwa, sun yi tsaye suna kallan Mahreen da ta rungume guyson tana zuba mashi surutai haɗe da ɗauki game da sambatun ta san zai dawo garesu dama, har da cewa ta yi kewarsa, ta fara bashi labarin irin kukan da Adda Mahnoor ɗinta ta yi a lokacin da baya nan.

Guyson da momma dik babu mai jin yarenta, dan haka basu san me take faɗe ba, sun dai yi shiru suna sauraranta ne.

Jin basu yi mata magana bane yasa ta raba jikinta da guyson ɗin ta riko hannunsa ta fara jansa wai ya zo su je su ga bappa, bappa ma yana can yana kewarsa. Ita dai Mahnoor idanunta a kansu ko kyaftawa ta kasa yi, tana kuma tsaye, fuskar mijinta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login