Showing 195001 words to 198000 words out of 403653 words
a saman shoulder ɗinsa".
Kafin guyson ya gama yin magana Hoorain ya tako cikin jarunta ya nufi cikin fadar. Sai dai yana zuwa tsakiya wasu zaƙwaƙuran warriors dake cikin fada su huɗu suka zare takubansu tare da yi mashi zobe, saboda sun san hukuncin da King ya yanke mashi shi ne hukuncin kisa. So sai suka kewayesa suna jiran King ya bada umarni su datse mashi kai.
Cikin fushi da kakkausar uncle Taheer ya ce. "Kai ƙasƙantacen bawa har ka isa ka ɗauki Zunaira da dattin hannunka? Baka san doka irin na masaurar nan bane? (Dokar dik wanda ya taɓa jikin wata gimbiya hukuncin sare hannu ne ya hau kansa) Ko ka manta da dokar ne kare kawai?". Ransa ta sosu ne matuƙa.
Ko kaɗai Hoorain bai yi kamar ya ji abin da ya faɗa ba, haka zalika ko kaɗan bai ji tsoron warriors da suka kewayesa ba, hasalima bai dakata daga tafiyar da yake yi ba, kai tsaye ya nufi King. Sai binsa warriors ɗin suke yi suna jiran umarnin King da ya tsaresu da idanu yana ganin ikon god.
Su commander Zafar dik sun rasa bakin magana, kowa King yake jira kawai. Hoorain bai dakata ba har sai da ya isa gaban King, a nan ya sauke Auta da idanunta biyu amma azaba ya gabata koda motsawar kirki. Allah sarki, a yau Hoorain ya sha azabar wahala wajen cetarta ita da Pretty, mayakan da suke neman su Pretty ne suka kawo masu hari a dab hanyarsu na dawowa gida, an gwabza yaki ba karya, da kyar ya iya kashesu, wani mayaki ne ya ture Auta ta faɗa saman wani dutse ta fama ciwonta. Almost mayaƙa 30 ya yi faɗa da su, ya sha wahala sosai.
Yana sauke Auta cikin fushi uncle Taheer yasa kafa ya takesa a kirji da karfi har sai da ya ɗan yi baya baya kamar zai faɗi, bawan Allah a gajiye yake, bai shi da kuzari sosai shiyasa uncle Taheer ya iya turesa ɗin.
Wani irin zabura commander ya yi, tamkar shi uncle Taheer ya ture, har wani girgiza ya yi, wlh idan kuka ga commander sai kun tausaya mashi, saboda yadda idanunsa suka yi jajir ganin irin abin da aka yi wa Hoorain.
Uncle Taheer cikin ɗaga murya ya sake cewa. "Kai kare ba da kai nike magana bane?".
Shiru Hoorain bai yi kamar yasan da halittarsa a cikin fadan ba, sai ma juyawa da ya yi yana san sauka kasan stage ɗin dan ya isa ga Abbonsa.
King dai ya rasa bakin magana, banda kallansu babu abin da yake yi, yana ƙoƙarin gane gaskiya ne shiyasa ya yi shiru, kun san dama yana zargin Hoorain shi ya saceta, to ga shi kuma shi ya dawo da ita, abin ya sanyasu a ruɗani, shiyasa King ya yi shiru yana ƙoƙarin tantance gaskiya.
Ran uncle Taheer ne ya kara baƙanta matuƙa, cikin fusata ya umarci warriors da suka kewaye Hoorain ɗin da su yi mashi dukan mutuwa har sai ya durkusa a saman gwiwonsa. Da yake suma sun jima da takaicin Hoorain a ransu, sun jima suna bakincikin yadda ya zama shugaba a garesu, shi ne mai basu umarni kuma sun fisa shekaru, so hassada na cinsu sai basu tsaya jiran umarnin King ba, a hanzarce suka fara kai mashi duka wai dan ma kada King ya dakatar da su basu daka shi yadda yakamata ba.
Da ganin yadda suka rufesa da jibga zaka iya fahimtar dukan huce takaici suke yi mashi. Wani mayaki ne ya taka shi a kirji da karfi har sai da ya yi baya baya zai faɗi ɗayan mayakin ya sake taka shi ta baya ya yi gaba gaba ya faɗi ƙasa ya buga kansa da jikin bakin stage ɗin.
Ko kaɗan bawan Allahn nan bai yi yunƙurin zai rama dukan da suke yi mashi ba, saboda yasan koma me ya faru laifinsa ne, shi yake ƙoƙarin kai kansa in da Allah bai kaisa ba, so a ganinsa ya cancanci wannan hukuncin. Amma ku kunsan da Hoorain zai motsa dik waɗan nan mayaka sai sun gaza tafiya a kan kafafunsu ko? Dan dai ya barsu ɗin ne.
Sosai suka shiga jibgarsa kamar waɗan da aka saukarwa da wahayin yin hakan.
A hankali Auta ta motsa, da kyar ta miƙe tsaye a kan kafafunta, idanunta har sun rine saboda kuka, ta ƙasa iya buɗan baki ta yi magana. King yana kallanta ta fara lallaɓawa zata sauƙo kasan stage ɗin, amma kuma King ɗin bai dakatar da ita ba, ya bita da kallo kawai kamar dai babu shi a fadan.
Anya ba wani abin King yake shiryawa ba kuwa, irin wannan shirun?.
Cikin mayaƙan ta keta ta isa gaban Hoorain dake kwance suna dukansa, da kyar ta iya buɗan baki maganarta can ƙasa bata fita ta fara faɗin. "Ku kyale shi, ku barmun kayana, kada wanda ya sake dukan mun shi, ni ku dake ni a madadinsa, ku kyale mun shi".
Su uncle Abbas dik an rasa mai bakin magana, shiru kawai suke binsu da kallo. Sai da suka ga Auta ta nufi wajen nasa ne uncle Abbas ya yi yunƙurin sauka ya kamata kada su jimata ciwo. Sai dai bai kai ga sauka ba uncle Taheer ya rigasa sauka cikin zafa, yana wani huci na kishi kamar zai haɗiyi zuciyarsa.
Ita dai Pretty tana tsaye a bakin kofar shiga fada. Commander Zafar tamkar zuciyarsa zata fashe saboda tsananin tashin hankali, ga shi kuma babu halin ya yi magana bawan Allah, dole ya daure ya ɗauki dik hukuncin da aka yankewa Hoorain. Ta wani ɓangaren kuma fa commander ya sha jinin jikinsa ya kuma shiga ruɗani na ganin Hoorain da Auta, shi dai yasan sun yi yaki da Hoorain da mayakan Queen Zarina, to ta ya aka yi yanzu kuma Hoorain ya dawo tsaginsu, shi fa wannan abin ya ɗaure mashi kai...... Na tabbata kuma my people's kanku ya ɗaure sosai a kan wannan al'amari, kada ku damu alkalamin princess Teema taku ta amana zan warware maku komai dallah dallah.
Uncle Taheer yana saukowa ya damko hannun Auta, da karfi ya ɗan jata ya mikar yana mai daka mata tsawa a kan wani dalili zata je wajen Hoorain dake matsayin bawa ƙasƙantacce mai gadinta.
Fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, soyayyarsa ya rufe mata idanu, bata ji bata gani ta sake komawa zata tsugunna a kusa da Hoorain ɗin dan ta hana warriors ɗin nan dukansa.
Kunsan jinin Modarawa da balai'n kishi, to haka larabawa ma suke da kishi, kishi bala'i ya rufe idon uncle Taheer, cikin fushi ya sake fisgo hannunta, da karfi ya fincikota, yana san janta su bar wajen. Ƙoƙari kwace kanta ta fara yi tana kuka hawaye bibbiyu. Ransa ne ya kara ɓaci cikin zafa ya cire hannu ya dalla mata mari a kumatu, shi kansa bai san ya yi wannan mari ba, kishi ce kawai.
Wannan mari tamkar zuciyar uncle, uncle Jahiz, Guyson, King and Jaish ya mara, barema Jaish da sai da ya wani ja dogon numfashi a lokacin da marin ya sauka a kumatunta, a take idanunsa suka rikiɗe suka yi jajir, gabaɗaya gashin jikinsa har wani mimmiƙewa suke yi saboda ransa ya ɓaci.
Guyson bai san lokacin da ya ce. "Uncle Taheer who the hell are you da zaka mareta? For what reason ma?".
Uncle Taheer da yake cikin fushi ai bai ma san ya yi ba, kuma bai san guyson yana magana ba, sake cire hannu ya yi zai kara mata mari sai ji ya yi cak an damki hannunsa, ita kuma sai kuka take kara yi, a take yatsunsa biyar suka fito ruɗu ruɗu a face ɗinta.
Wani irin zufa ne yake ketowa Hoorain a gefe da gefe face ɗinsa, jikinsa na wani irin tsuma, wasu zara zaran jijiyoyi ne suka bayyana a wuyarsa, da karfi ya damki hannun uncle Taheer, zuciyarsa na tafasar marin da ya yi wa kyakkyawan face ɗin Hoonairarsa. Ita kuwa dakatar da kukanta cak ta yi ganin Hoorain ya miƙe, sosai ta ji daɗi, dama ita bata san ya kwanta ya bari su yi ta dukansa ɗin nan.
Da karfi Hoorain ya murɗe hannun uncle Taheer baya, ji kame kass ya karya mashi kashi, cikin ɓacin rai ya ɗauke fuskarsa da wata azababbiyar mari mai sanya mutu zuwa duniyar shaiɗanu a mafarki ya dawo. Take uncle Taheer ya gansa a wata iriyar duniya mai cike da wasu dodanni masu ban tsoro, marin assistant commander yasa ya bar duniyar mutane ya rasa hankalinsa.
Sake kara mashi wani marin Hoorain ya yi take uncle Taheer ya zube ƙasa tamkar fawa, da alama sumewa ya yi. A hankali ya dawo da kallonsa a kan Auta, har lokacin huci yake yi kamar me.
Su kuma warriors dake dukansa cak suka dakata suna binsu da kallo, har lokacin King bai yi magana ba, bai ma yi niyar yin magana ba, uncle Jahiz nema ya ɗan yi ƙoƙari wajen buɗe baki yana san cewa kowa ya samu waje ya zauna su jira umarnin King, sai dai bai iya yin magana ba sakamakon nufar su Hoorain ɗin da Jaish ya yi cikin zafa.
Miƙa hannun Hoorain ya yi ya riko hannun yana ce mata sorry, a hankali ya ɗaura ɗayan hannunsa a saman lallausan kumatunta in uncle Taheer ya mareta, yana ƙoƙarin rarrashinta sai gani suka yi Jaish ya sanya kafa ya taka shi da karfi, sai wani huci shi ma yake yi tamkar wani zaki.
Shi ma Jaish ba dukan uncle Taheer da Hoorain ya yi bane ya bakanta mashi rai har yasa ya taka Hoorain ɗin, a'a shi dan me Hoorain zai taɓa Auta da hannunsa a matsayinsa na mayaki? Wannan shi ne ya bakanta mashi rai har yasa ya takasa.
Baya baya Hoorain ya yi saura kaɗan ya faɗi, amma abin ku da jarumi sai ya rike kansa yana mai ɗago da kallonsa a kan Jaish ɗin. Cikin fushi Jaish ya yi kansa, zaro takobi daga ƙugun ɗaya daga cikin warriors dake wajen jaish ɗin ya yi da nufin y sare hannun Hoorain dan ya taɓa Auta.
Allah sarki rashin sani ya fi dare duhu, basu san irin gwagwarmayar da Hoorain ya sha wajen kare Auta ya ceci ranta har suka samu damar sake iya ganinta ba, ai ba dan shi ba da sai dai wata ba dai ita ba, amma saboda basu sani ba har ƙoƙarin datse mashi hannu suke yi.
Ganin Jaish ya zaro takobin mayakin nan ne yasa Auta yin zafin namar shiga tsakaninsa da Hoorain, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita ta fara ƙoƙarin bawa Jaish hakuri muryarta na sarkewa. Ina ai bai saurareta ba, dan ransa ya ɓaci sosai shi ma, hannu yasa ya tureta gefe da karfi ta tafi zata kifa.
Kamar walkiya haka Hoorain ya tareta ta faɗa jikinsa, hakan ba ƙaramin kara kona ran Jaish ya yi ba, zuciyarsa ce ta ƙara fusata, gadan gadan ya nufesu, yana zuwa ya sanya hannu ya damki wuyar Auta zai sake tureta gefe guda.
Kankame Hoorain ta yi tana faɗin. "Yah Jaish dan Allah ka yi hakuri ka rabu da shi, wlh bashi da laifi......"
Bata ƙarisa maganar ba Jaish ya saukar mata wani marin a gefen ƙuncinta, abin da bai taɓa yi ba bai kuma taɓa sa ran zai yi ba a rayuwarsa sai ga shi yau ya yi, ko a mafarki bai taɓa zatan akwai wata rana da zata zo ya ɗaura hannunsa a jikin Auta ba, sai ga shi yau ɓacin rai yasa ya yi hakan.
Haba ai yana sauke mata wannan marin ran maza ta ɓaci, a miliyan Hoorain ya kai hannu ya danki wuyar Jaish, sai wani irin huci yake yi yana furzar da wani irin numfashi mai tsananin zafi daga bakinsa.
Yana damkar wuyar Jaish sai da King ya miƙe tsaye, gabaɗaya waɗan da suke cikin fada sun yi wani irin zaro idanu tamkar idanunsu zasu faɗi ƙasa, commander Zafar yau sai da hantar cikinsa ta ƙaɗa, mayaki da capkar wuyar Prince da kansa, tashin hankali, lallai yau akwai bala'i.
Warriors dake cikin fada gabaɗaya suka zari takubansu suka yi kan Hoorain, da karfi shi ma ya zaro takobinsa da hannu ɗaya, hannunsa ɗaya kuma ya shake Jaish da shi. Mamaki ya hana Jaish motsawa.
Ɗaga takobinsa Hoorain ya yi ya sauketa a in da ja layi a floor na fada, cikin kakkausar murya yana huci ya ce. "Dik wanda ya matso kusa da ni sai na datse kansa na rantse!!!".
Tashin hankali, da yake dikkan warriors sun san halinsa sun kuma san fin haka zai aikata idan ransa ya ɓaci, sai dikkansu suka ja suka tsaya tamkar an sassaƙasu.
Ido cikin ido Hoorain ya kalli Jaish, cikin kakkausar ya ce. "Dik ranar da ka sake ɗaura hannunka a jikinta, na ratse sai na datse hannunka, ba kai ba dik wanda ya sake taɓata tabbas zai iya rasa ransa, ni ka dakeni iya dukan da zaka yi mun, ai ni na yi maka laifi, ita kuma me ta yi maka? Meyasa zaka taɓata?".
Yadda kuka san babu Jaish a cikin fada, tamkar ba shi Hoorain ya shakewa wuya ba, idanunsa sun yi jajir kamar wuta, mamaki yana shi ya gwada kwanji da Hoorain ɗin ma.
"Hoorain kana da hankali kuwa? Kasan kuskuren da kake san tabkawa kuwa? Ka manta a ina kake ne? Kasan bala'in da kake san jefa kanka a ciki kuwa?". Cewar commander, cike da tsananin tashin ya yi maganar.
Ɓacin rai dai shi yasa idanun Hoorain suka rufe, baya ji kuma baya gani, a yadda yake ji yanzun nan ko King ya zama shamaki a tsakaninsa da ita ko kuma ya taɓa lafiyarta to fa zai iya kawar da shi. Tashin hankali!!.
"Umarni nike baka da ka gefar da takobinka kasa kuma ka zube ƙasa a saman gwiwonka ka bawa Prince hakuri". Cewar commander Zafar again, yana magana tamkar ya manta wanene Hoorain, ya manta ya ɗan nasa yake idan ya fusata.
Guyson ne ya matsa ya riko hannun Auta domin ta bar wajen kada wani abin ya sake samunta. Sai dai ina, fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, kuka sosai ta ke yi.
Kai jama'a wato akwai tashin hankali a Kingdom of power, HOORAIN YA SHAKE JAISH SABODA AUTA! BABBAR MAGANA, WANI IRIN HUKUNCIN KUKE TINANIN HOORAIN ZAI IYA FUSKANTA? NA FARKO ANA ZARGINSA DA SACE GIMBIYA, NA BIYU YA SUMAR DA UNCLE TAHEER, NA UKU YA TAƁA JIKIN GIMBIYA HAR YA RUNGUMETA, NA HUƊU UWA UBA YA SHAKE WUYAN PRINCE JAISH DA KANSA, ME KUKE TINANIN ZAI IYA FARUWA NE WAI?.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
======🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Guyson ne ya matsa ya riko hannun Auta domin ta bar wajen kada wani abin ya sake samunta. Sai dai ina, fisge hannunta daga rikon da ya yi mata ta yi, kuka sosai ta ke yi.
Shi kuwa Hoorain cigaba da daka masu warning ya yi a kan taɓa Zunaira, ɓacin rai ta yi ɓacin rai........ Da sauri Auta ta matsa kusa da Hoorain, dan taga kamar bashi da niyar sakar mata Yah Jaish ɗinta, shi kuma Jaish ɗin yana tsaye tamkar wadda aka sassaƙa, to ta ji tsoron kada Jaish ya mutu dan taga idanunsa kamar wuta.
Kusa da Hoorain ta isa, ɗan hannunta ta kai saman nasa tana ja tana faɗin. "My Hero ka sake shi mana, Yah Jaish ɗina ne fa, please ka sake shi, kada ka illama mun shi". Tana magana voice ɗinta baya fita sosai, muryarta ya dashe sosai saboda kuka.
Hoorain da ya yi nisa sam baya jin kira, ko kaɗan bai ji kalamanta ba, sai ma ƙara shake Jaish da ya yi. Uncle Jahiz ne ya sauko kasan stage ɗin, da sauri ya matsa in da suke, dan hankalinsa ya tashi sosai na ganin jinin dake zuba daga cikin Auta wanda ba kowa ne ya lura da shi ba, har ta fara ganin jiri jiri saboda ta rasa jini sosai.
Yana zuwa ya ɗauketa cak ta baya ya nufi hanyar fita da ita. Ihu ta fara zunduma da voice ɗinta da baya fita sosai, sam bai saurara mata ba sai da ya fice da ita, bai kuma zame ko'ina da ita ba sai parking space, pretty ta bi bayansu, cikin motarsa ya sanyata, da kansa ya kunna motar, da gudu ya figeta suka nufi hospital na kingdom ɗin.
Hannu Jaish yasa ya damki hannun Hoorain ɗin, da karfi ya ɓanɓarota daga wuyarsa, Hoorain sam bai yi ƙoƙarin hanasa ba, saboda dama shi idan da shi zasu daka ba zai tanka ba, saboda sun kai su dakesa ɗin ne, amma su taɓa gimbiyarsa flowers zuciyatsa kam wlh ba zai bari ba.
Dan haka yana ganin Jaish ya ɓanbare hannunsa daga wuyarsa, cikin fusata sosai Jaish ya kai mashi wani duka mai firgitarwa a kumatu har sai da ya yi tangal tangal kamar zai faɗi ƙasa, amma ya yi ta maza wajen rike jikinsa ya tsaya cak.
Uncle Abbas ne ya yi saurin tasowa ya matso ya rike Jaish ɗin, dan idan ya barsu abin ba zai yi kyan gani ba. Commander Zafar gwanin ban tausayi, har idanunsa sun ciko da kwallah dik jaruntar nan tasa, kowa yana da rauninsa, tabbas ba shakka Hoorain shi ne raunin commander Zafar.
Jan hannun Jaish uncle Abbas ya yi suka nufi kofar fita fada ta kofar shiga cikin gida. Da karfi Jaish ya kwace hannunsa daga hannun uncle Abbas, ransa in ya kai miliyan to ya ɓaci, har kamar Hoorain ne zai rike mashi wuya? Lallai yau bai ga mai iya dakatar da shi ba daga yi wa Hoorain illah ba!!.
Shi