Showing 267001 words to 270000 words out of 403653 words

Chapter 90 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

21

sun marawa waɗan da suka kawo masu harin baya, saboda kowa dai yasan matan wannan birni sun tsani Black Tiger da RAWANIN ZALINCI da ya ɗaura a kansa yake mulkarsu, dan haka sai suka yi mashi tawaye, dik suka rufawa waɗan can baya, harta wasu daga cikin bara gurbin warriors ɗinsa sun juya mashi baya wannan dalili ya kara tada hankalin Ronnie fite da tinanin kai tinani.

A yau dai Allah ya nunawa Black Tiger karfin ikonsa dik na banza ne, wato idan Allah ya ga dama ya tashi kamaka cikin minti ɗaya zai yi maka kamun da dik danginku zasu taru a rasa mai kawo komai ƙanƙantar mafita a lamarin.

Hannu Sweetie tasa ta tallabo kumatun Ronnien, idanunsa sun tsananta ja sosai, jikinsa dik ya yi sanyi, kamar zata yi kuka ta ce. "Menene yake faruwa Ronnie?". ...... Ajiyar zuciya ya sauke, bai ɓoye mata komai ba ya zayyana mata dik abin da yake faruwa da cinsu da yake da ake shirin yi, ga shi mayakansu sun yi wa Black Tiger tawaye, bugu da kari matan birnin dik sun juya mashi baya sai ƙalilan masu tsoro azaba da izayar Black Tiger ne suka ki kwaye mashi baya, amma kusan rabin birnin sun bi bayan waɗan can, yanzu maganar da ake yi ma sun dinfaro cikin empeir na Black Tiger domin su fitar da shi su gurfanar da shi a gaban kowa su kashe shi su kwaci CROWN OF INJUSTICE ɗinsa su ɗaurawa kansu, sannan su zauna a saman powerful seat ɗinsa.

My people's me kuke tinani a wannan yanayi? Kun dai ga irin aya da Allah ya ajiyewa Black Tiger, dan haka yakamata bawa ya sani dik wani karfin iko da mulki da yake ji da shi second ɗaya ta yi wa Allah yawa ya yi watsa watsa da rayuwarsa ya mayar da shi abin tausayi, dan haka aikata ba dai'dai ba dan Allah ya baka wata dama sam ba mafita bace a gareka, dan zaka faɗa hanyar da ba zaka iya fita ba, Allah dai yasa mu fi karfin zuƙatanmu yasa mu dace.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️




"Ronnie ka dai'na saurin sarewa daga samun rahamar Ubangiji, In Sha Allah Allah zai kawo mana mafita, yanzu dai mu yi shawarar meyakamata mu yi?"....... Muryarsa a rautace sosai ya ce. "Dama ɗaya muke da shi Sweetie, dama ɗaya ta rage mana, idan har muka saka wannan password na karshe ba dai'dai ba shikenan laptop ɗin zai rufe kansa sai after 24 hours za a sake gwadawa".

Tashin hankali, zaro idanunta waje ta yi, lokaci guda kuma sai ta sauke ajiyar zuciya, domin ta tina maganar Allah a cikin suratul baqara, sura ta biyu aya ta 153. Allah Madaukakin sarki yana cewa. "Ya ku waɗanɗa kuka yi imani! Ku nemi taimako, natsuwa, hakuri da sallah ga Allah. Lallai Allah na tare da masu hakuri".

Wannan aya na koyar da cewa a dik lokacin da mutum ya shiga cikin wahala ko tashin hankali, to ya nemi taimako ta hanyar haƙuri, natsuwa da sallah, domin Allah yana tare da masu waɗan nan sifofi. Haka zalika a cikin suratul baqara aya ta 155 Allah ya sake cewa. "Kuma lallai ne za mu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da rashi daga dukiya, rayuka da ƴaƴa". Wannan yana nuni da cewa kowane mutum zai fuskanci jarabawa, kuma mafi dacewa a yi haƙuri da dogaro ga Allah.

A cikin muslim, hadisi mai lamba 223 Manzon Allah (SAW) ya ce. Hakuri haske ne.
Wannan yana nuna cewa hakuri yana da haske mai nuna hanya a cikin duhun matsaloli. Dan haka yana da kyau su yi hakuri su kuma natsu sosai dan samo mafita mai kyau ba wanda za su yi danasani ba.

Karar da mirrorsa ya yi ne ya kara firgitasu, dan alama ce ta tashin hankali sosai. Miƙewa tsaye suka yi a tare, a gagauce Ronnie ya kai kallansa a kan mirror, idanunsa ne suka ciko da kwallah tab, dan ana cinsu da yaki babu karya, abin ya mugun ɗaga mashi hankali. Sosai Sweetie ta ji ta karaya a wannan lokaci, dan ganin hawaye a idanunsa, dik sai ta ji ta tausaya mashi over. Matsawa kusa da shi sosai ta yi, cike da tsoron abin da zai je ya zo ta ce. "Ronnie bari in gwada saka wani password ɗin mu gani".

Bawan Allah yana cikin ɗimuwa sam bai ji kalamanta ba ma. Ganin bai amsa mata ba ne yasa ta miƙe ta kai hannunta saman madannan laptop ɗin, jikinta na kerma ta fara ƙoƙarin dannawa, bata ta san abin da zata rubuta ba, kawai dai ta sanya a ranta Allah ba zai taɓa mata kunya ba dan da shi kawai ta dogara.

Hannunta na kerma sosai ta kai saman later R zata danna sai ganin wani hannun daga bayanta ta yi ya rigata da danna later R ɗin, ai a miliyan ta zabura ta juyo, dan tasan wannan ba hannun Ronnie bane, hannun Black Tiger ne, saboda yanayin hasken skin ɗinsa shi da Ronnie akwai banbanci sosai. Tana jiyowa sai ganinsa ta yi a tsaye a bayanta, ko yaushe ya farfaɗo? Ta jefawa kanta tambayar, jikinta na rawa ta kai kallanta a kan face ɗinsa. Wani irin razana ta yi ganin yadda ya canza, fuskar nan tasa babu imani babu annuri, wlh ko mai taurin zuciyarka ka gansa a wannan yanayi sai ka ji wani irin ajijiya ya ɗebeka, sai hantar cikinka ta ƙaɗa. Take ta sha jinin jikinta.

Ronnie ma a milyan ya miƙe tsaye, dan shi ma bai ga time da Black Tiger ya miƙe ba, kawai ya gansa ne a bayan Sweetie. Tsuru tsuru suka tsaya an rasa mai iya magana, ita Sweetie ma jikinta har ɓari yake yi, saboda yankar da ta yi mashi a kirji, tsoronta ɗaya irin hukuncin da zai yanke mata, ta shiga zilimi a kan hakan.

Shi kuwa bai bi ta kansu ba ya cire password na laptop ɗin wanda ya kasance sunan Ronnie ne, dik wahalar da Ronnie ya sha ashe sunansa ne password ɗin, wato da gaske ne fa rashin sani ya fi dare duhu. Cikin ƴan mintocin da basu gaza uku ba ya shigar wa da Robbot ɗin nan abin da yake buƙata bayan buɗe laptop ɗin.

In short cikin mintocin da basu gaza 30 ba ya ci rabi da kwatan yakin nan yana tsaye a in da yake bai motsa ba yana sarrafa kwakwalen robbot ɗin, dik abin da yake faruwa Sweetie da Ronnie sun yi shiru suna kallo ta cikin mirrorsa, zubar da jini kawai ake yi, maza zubewa ƙasa suke yi tamkar anyiwa sauro feshin magani, umarnin rashin imani ya bawa robbot ɗin nan nasa, dan kisan walaƙanci da rashin imani da tausayi suke yi wa mutane.

Wani irin tsorata Sweetie ta yi na ganin yadda maza ke zubewa ƙasa, a tsorace ta kai kallanta kan face ɗinsa, yana tsaye kamar mutum mutumi, sai ma kara ɗaure fuska da ya yi, yau bata ga fuskar iya ce mashi ko uppan ba, hasali ma jikinta kerma yake yi, yau karo na farko bata san kallan face ɗinsa, saboda tashin hankali da fargabar da zuciyarta yake ciki.
Sai dai fa ya jinjinawa Sweetie da Ronnien a cikin zuciyarsa, dan sun yi namijin ƙoƙari, da sun san password ɗinsa tabbas zasu yi nasara a wannan yakin, hakan yasa ya jinjina masu sosai, shiyasa ma ya yafe mata ciwon da ta ji mashi.

Suna tsaye a wajen har Black Tiger ya kammala abin da zai kammala, sannan ya umarci Robbot ɗin nasa da su haka mashi rami mai zurfin gaske a tsakiyar birnin, a kofar empeir ɗinsa kenan, sannan su cika ramin da dikkan mutanen da suka juya mashi baya, su bisu da fetur da matches, sai kuma ya sake umartar wasu robbot ɗin da cikin awa biyu su tsabtace mashi birninsa dan baya san ganin datti ko wani jini jini or gawarwaki ko kaɗan, dik gawarwakin da suka mutu a jefasu cikin ramin da za'a haƙa dan kona waɗan da suka juya mashi baya, daga karshe ya ce yana da buƙatar mutanen birnin waɗan da ba su juya mashi baya ba da su hallara a gaban fada nan da kwana uku!!!.

Wani irin zabura Ronnie ya yi ganin wannan umarni da yayan nasa ya kaddamar, hankalinsa ne ya yi mummynar tashi, da umarni ɗaya Black Tiger zai sa a kona mutane sama da dubu biyar? Kuma a konasu da ransu, kai wannan hukunci ta munana sosai, kun san yanzu musulunci ta ratsa zuciyar Ronnie sosa, da a baya ne ko mutane nawa Black Tiger zai sa a kashe baya damuwa, da kalma ɗaya Black Tiger yake sawa a tashi kauye guda daga cikin kauyukan birnin, a gaban Ronnien an sha bada umarnin kashe mutum sama da dubu kuma baya wani damuwa, amma yanzu sai ya ji ina wlh ba zai iya ɗauka ba, hankalinsa a tsakanin tashe ya ce.
"Yaya please ka yi masu afuwa tun da babu yadda zasu yi da kai, kasan ba zasu yi nasara a kan ka ba, ka yi hakuri ka kyalesu kawai". Muryarsa na rawa ya yi maganar.

Sweetie ce ta bi Ronnie da kallo tana san karin bayani, dan bata fahimci komai ba. Kallanta shi ma Ronnie ya yi, cike da tashin hankali matuƙa ya kora mata bayanin abin da Black Tiger ya yanke. Innalillahi wa inna ilahir rajiun, shi ne abin da ta furta kafin nan cikin fitar hayyaci ta ce. "Saboda me zaka kashe rayuka masu tarin yawa haka? Saboda sun bijire umarninka? Ko dan saboda suna neman ƴancin kansu? Saboda suna ƙoƙarin gujewa mulkin injustice ɗinka?! Saboda suna nemanwa kansu sauki? Shi ne zaka sanya a konasu da ransu? Shin waye ya baka izinin kashe rai? Ko baka san cewa ba kai ka haliccesu bane? Ko baka san cewa mahaliccin waɗan nan rayuka ya yi hani da kashesu ba ne? Ko baka san cewa kai ma ka bijirewa mahaliccin bane shiyasa suma suka bijire maka? Kana tinanin kashesu shi ne mafita a gareka? To ka saurara ka ji hukuncin dik wanda ya kashe rai daga nan sai ka san a wani matsayi kake. Allah maɗaukakin sarki a cikin suratul Hijr surata 15 aya ta 29 ya bayyana yadda ya halicci mutum daga turɓaya kuma ya busa mashi rai, ka je ka karanta wajen dan kasan menene ma rai da kuma yadda aka samar da shi. Haka zalika cikin suratul tin sura ta 95 aya ta 4 Allah maɗaukakin sarki ya ce. Lalle ne mun halicci mutum cikin mafi kyawun sura daga halittuna, darajan ɗan adam ya fi dikkan sauran halittun Allah!! Allah ya bayyana a bayyane cewa kashe rai ba tare da dalilin da ya cancanci kisa ba haramun ne, cikin suratul isra'i Allah ya ce kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta, sai dai bisa haqqi. Wanda aka kashe ba bisa hakki ba, hakika mun ba wa magajinsa iko na neman hakkin ransa, amma kada ya wuce gona da iri a kisan, domin hakika wanda aka kashe ba bisa haqqi ba shi an taimake shi ne"

Kazalika a cikin Suratul Ma’ida sura ta biyar 5 aya ta 32 Allah ya sake yin magana a kan haramcin kashe rai. Allah ya yi gargaɗi mai tsanani ga al’umma da suke kashe juna da zalunci, a cikin Suratul Baqara sura ta 2 aya ta 195, manzan Allah ya ce kisa yana ɗaya daga cikin manyan zunubai".

Da alama tashin hankali ya rufe mata idanu da take zazzaga mashi waɗan nan karatun, ta mance a in da take, a wannan karon shi ma Ronnie sam bai yi gigin hanata ba, dan burinsa ta kowacce hanya su dakatar da Black Tiger daga kashe waɗan nan mutane, shiyasa ya kyaleta ta faɗa mashi girman Allah ko zai saduda ya hakura zuciyarsa ta sanyaya.

Sai dai kash, kamar babu alamar saduda a tattare da shi, dan kuwa babu alamar zatukanta sun ratsa ƙwaƙwalwarsa, sai ma juyawa da ya yi ya cigaba da yin abin da yake yi, babu alamar mutanen birnin zamu samu koda kwayar zarra na sassauci daga garesa.

Ganin hakan yasa suka kara shiga tashin hankali matuƙa, Ronnie ya shiga damuwar da har idanunsa sai da suka ciko da kwallah, ita kuma Sweetie a cikin zuciyarta ta sha alwashin yau ko mutuwa zata yi sai da ta mutu amma ba zata barshi ya cigaba da wannan bakin zalinci na CROWN OF INJUSTICE ɗin ba, yanzu ne lokacin da zasu rinƙa fito na fito da shi dan faɗa mashi gaskiya sai dai komai zai faru ya faru, dik wata rufa rufa da tsoro yanzu zasu ajiye a gefe su yi shahada su yi fito na fito.

Dan haka tana ganin bai wani saurareta ba ya cigaba da yin aikinsa a matsayin ta shiga tsakaninsa da laptop ɗin, hannayensa dikka biyu ta riko cikin nata, tsabar tsoro sai kerma jikinta yake yi, amma tausayin mutanen birnin ya rufe mata idanu a in da ta zaɓi mutuwa dan cetonsu. Cikin dakiya ta ce. "A gaskiya ba zaka kashe kowa ba big bro, ya isa haka nan, zunubin da ka kwasanwa kanka a baya shi muke ƙoƙarin ganin ka tsarkaka daga shi, dan haka Allah ba zaka sake kwasanwa kanka wani zunubi ba, dan muna kaunarka!". A wannan karan cikin sanyin murya ta yi maganar, dan ta lura dik wasu tada jijiyoyin wuyarta a banza yake tafiya, shi Black Tiger ma wlh idan ka yi mashi magana cikin natsuwa da tausasa kalamai ka fi cin riba a kansa sama da idan ka ɗaga murya, in ka ɗaga murya ma ai sai dai ka ci azaba a hannunsa ba dai riba ba.

My people's me kuke tinanin zai faru? Black Tiger zai janye kudurinsa a kan mutanen birninsa kuwa? Zai yafe masu? Shi da Sweetie da Ronnie waye zai yi nasara?. Muje zuwa.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Washegari da safe, sai almost karfe 8 Ramish ya iya farfaɗowa daga sumar da ya yi bayan wannan aika aika da ya aikata, yana gama samun natsuwa dama ya sume kwance kusa da ita. Bilal ya buga wayarsa tun da daɗin rai har ya fara shiga tashin hankali, ya ƙasa zaune ya kasa tsaye, dan haka gari na wayewa ya fita gidan da sunan ya je nemansa, ko kaɗan bai kawowa ransa cewa Ramish na sama ba, sai ya yi waje nemansa.

A lokacin da ya farfaɗo ji ya yi jikinsa tamkar ba nasa ba, gabaɗaya ya canza, kansa ne take sara mashi tamkar zata fashe, wani irin jiri yake gani sosai, da alama har yanzu maganin nan bata gama sakinsa gabaɗaya ba bawan Allah, idanunsa tamkar wuta saboda ja, har lokacin jijiyoyin jikinsa a tsaitsaye basu koma sun kwanta ba, arab hairnsa tamkar wanda aka kwato daga bakin kura, gabaɗaya a hargitse yake, idan ka gansa sai ka tausaya mashi, shi ma kenan, to ina ga Leesharh kuma? Ya kuke tinanin zata kasance?.

Ya sha madarar mamakin ganin babu tufafi a jikinsa, ɗan waige waige gefensa ya fara yi, ai a miliyan ya zaro idanunsa waje lokacin da ya ga Leesharh kwance a gefensa cikin jini, ga sofar da suke kai ɗin fara ce tas, hakan yasa gabaɗaya jini ya yi kaca kaca da waje. Dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi ya yi, idanunsa ya datse gam, take ƙwaƙwalwarsa ta fara tariyo mashi abubuwan da suka faru daren jiya. Tsab ya tina komai, innalilahi wa inna ilahir rajiun shi ne kalmar da ya rinƙa maimaitawa a ransa, ya maimaitata ya fi sau hamsin a in da yake zaune, tamkar wanda ya yi mangaribar jemage, lokacin guda jikinsa ta yi mugun sanyi, da karfi ya dafe forehead ɗinsa, wani irin ihu ya kurma da karfi wanda bai san dalilin yinta ba, ga dikkan alamu zafin da zuciyarsa ta ɗauka ne yasa hakan.

Dama na faɗa maku dik ihun da za'ayi a cikin wannan ɗaki na waje ba zai iya ji ba, bangon wajen tamkar soundproof yake. Miƙewa tsaye ya yi, yana tangal tangal tamkar wanda ya sha barasa ya bugu ya nufi gaban computers dake wajen, da kyar ya iya ƙarisawa wajen, hannayensa dikka biyu yasa ya dafe dest ɗin, wani irin huci ya fara fitarwa da karfi karfi, numfashinsa na fita da wani irin ɗumi mai ban tausayi.

(Abin akwai ciwo gaskiya, ace tin da ka taso baka taɓa zina ba, baka taɓa sha'awar yinta ba, hasalima kyamatarta kuke yi, rana tsaka ka tsinci kanka da aikatata! Wlh dole ya ji zafin hakan, yanzu ya zai yi? Da wani ido zai ganta? Shin zai iya gane me ya janyo mashi aikata hakan? Idan ya gane wani mataki zai ɗauka? Shin zata yi mashi uzuri ta yarda ba halinsa bane?.)

Ƙwaƙwalwarsa ce ta sake tariyo mashi yadda ya haikewa yar mutane a daren jiya, take ya tuno kalamanta da take faɗin. "Yah Ramish kada ka yi mun irin wannan hukunci, ka yi mun dik abin da kake so da ya danganci azabtarwa, amma dan Allah kada ka rabani da mutumcina, wlh ni marainiya ce da bani da kowa, bani da iyaye, mutuncina shi ne kawai abin da ya rage mun mai daraja a tattare da ni, ka dubi girman Allah kada ka lalata mun rayuwa, ni ban karɓi wannan aiki saboda na cutar da kai ko wani abin makamancin hakan da gangan ba".

Tana kuka hawaye sharɓa sharɓa tana kora mashi waɗan nan jawabin. Ai hankalinsa ne ya kara tashi, ransa ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, cikin fitar hayyaci yana huci ya sake kurma ihu da karfin gaske, cikin zafa yasa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login