Showing 237001 words to 240000 words out of 403653 words
kamar haka, a ina yake? A ina zata gansa? Yakamanninsa suke? Shin yana tinata ne ko ya manta da ita? Meyake yi a halin yanzu? A koda yaushe sai ta yi wa kanta waɗan nan tambayoyin da bata da amsarsu bata kuma da in da zata sami amsarsu, wata rana har kuka take yi idan ta tunasa. Amma har yau bata iya sanar da Ronnie soyayyar Kamran dake ranta ba, tabar sirrin a ranta.
Meyasa idan taga Black Tiger take tina Kamran? Shin suna da wata alaƙa ne ko dai kawai a ranta ne take jin kamar girma da cikar Kamran ya kai Black Tiger dan bata taɓa ganinsa ba?.
Cikin sanyin murya ta ce. "Big bro good morning".
Shiru bai amsa mata ba, bai ma yi kamar zai amsa ba, yana cigaba da dudduba abin da yake ra'ayi zai fita zuwa fada, anjuma za'a buɗe katafaren hospital da ya ginawa Ronnie, za'ayi taran partyn buɗe hospital ɗin, ba ƙaramin dukiya Black Tiger ya zubar a wannan taron ba, an shirya abubuwa sosai, and dik a cikin Daularsa za'ayi, kuma hospital ɗin ma a cikin Daular tasa take.
So yana da abin yi sosai yau, shiyasa ma yau dressing ɗinsa ta fita daban da kowacce rana, yau ranar Ronniensa ne.
Bata damu dan bai amsa maganarta ba, sai ta sake cewa. "Big bro na yi kyau?". Tana magana kirjinta na harbawa da karfi karfi, dan tasan bata taɓa zuwa wajensa ta fita lafiya ba, kullum sai sun yi dirama ɓatacciya kaman wasu tom and Jerry.
Nan ma shiru bai amsa ta ba, kuma dama tasan hakance zata biyo bayan, dan sai ka yi mashi magana sama da guda uku bai amsa ko ɗaya ba, ba wanda yake sanya shi yin magana sai time da ya yi ra'ayi.
Cikin natsuwa ta tako ta nufi in da yake tsaye, jingina bayanta da jikin drawer mirror ta yi, yazamana suna fuskantar juna, kallansa gabaɗaya yana a kan mirrorsa tamkar bai san da wata halitta a wajen ba. Shiru ta ɗan zuba mashi idanu na ƴan sakanni kafin ta sanya hannunta cike da tsoro ta shafi kyakkyawan bakin gashin dake kwance a gefe fuskarsa. Hannun nata har yana kerma saboda tsoro.
Hakan yasa dan dole ya dawo da kallonsa a kanta, wannan yarinya ta zame mashi kashin wuya, ya faɗa a ransa yana kallonta. Wlh Sweetie ta san kan duniya, ido ɗaya ta kashe mashi kafin ta ce. "Big bro na yi kyau?".
Zaman lafiya yau yake so, dan yana da abin yi masu muhimmanci a gabansa, dan haka sai ya ɗaga mata gerarsa guda ɗaya alamar yes ta yi kyau. Ajiyar zuciya ta sauke yau karo na farko ya amsata dik da bai buɗi baki ya yi magana ba, amma ta ji daɗin abin da ya yi.
Ita ma ta fahimci yau ya yi so sillent over, da alama akwai abin da yake gabansa sosai, dan haka ba zata ja tsokana sosai ba, saboda idan ta ce zata ja sosai zai iya yi mata illah dan yana aiki, yanzu tagama karatarsa tsab, tasan lokacin da zata ja shi da tsokana ba zai cutar da ita ba, wato idan ta same shi baya yin aikin komai, nan kam sakan jiki take yi ta hakura mashi.
Hannu ta sake kaiwa zata shafi sajensa da nufin ta yi mashi bye bye. Carap ya capki hannun nata da hannunsa ɗaya, dan idan tana taɓa shi ɗin nan tana sanya mashi kasala. Kallon juna ido cikin ido suka yi ba tare da kowannansu ya furta word ba. A hankali ya saki hannun nata tare da yin ƙoƙarin juyawa ya cigaba da abin da yake yi.
Ita kuwa a ranta ta ji lallai kafin ta tafi sai ta sake taɓa sajensa, dan haka yana saketa ta sake kai hannun zata taɓa sajen nasa. A wannan gaɓan wuyarta ya damko da hannunsa tare da janyota ta matso dap da shi har suna iya jiyo sautin numfashin juna.
Dik da ya shake mata wuya bata damu ba, dan ta samu abin da take so ne, wato ya matsar da ita dab da jikinsa kenan. Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman lion chest ɗinsa, ɗayan hannun nata kuma ta shafi gefen face ɗin nasa. Tabbas ta ji shakar da ya yi mata, amma ta daure bata nuna alamar ta ji ba.
Can ƙasan maƙoshinsa ya furta. "Ke bakya da tsoro ne?". Cike da mamakinta ya yi maganar, har ga Allah tana bashi mamaki yadda bata nuna tsoro, kun san irin haka dole ya bawa mutum mamaki, wannan rashin tsoron da take nunawa yasa har yana jin kamar tana burgesa, yana san mutum mai confidence.
Ɗan ɗaga idanunta sama ta yi ta yi fari da su, hakan ba ƙaramin kyau ya kara yi mata ba, ga shi ya tsareta da idanu, shi kansa yasan ta kara kyau matuƙa yadda ta yi da idanun nan nata, amma bai nuna alamar yaga ta yi hakan ba, sai ya kara ɗaure fuska sosai.
Cikin wani irin sexy voice ta ce. "E to ban taɓa yin tinani a kan jin tsoron ba, amma tin da ka yi magana yanzu zan yi tinani in ga ko ina ji ko bana ji". Tana magana tana jujjuya idanu kyanta na kara bayyana matuƙa, ga shi suna kurkusa da juna sosai
Ya fahimci iyashege ya yi wa yarinyar nan yawa, dan haka sai ya zare hannunsa daga wuyarta yana kawar da kallonsa daga kanta.
"Big bro do you know something?". Ta faɗa tana cigaba da shafa kyakkyawan sajensa da hannunta ɗaya. Bai kulata ba ya mayar da hannunsa a saman mirrorsa yana ƙoƙarin bincikar in da Pretty take a halin yanzu. Kun dai san kingdom of power masarauta ce ta mahaddara Alqur'ani mai girma, King mahaddaci ne, ba karamar abu bane Black Tiger ya iya laluɓar Pretty a cikinta, sai in ta fito daga wajen da mahaddata suke ta kutsa ko ta irin part ɗin uncle Abbas da sauransu haka.
So Black Tiger ganin Pretty zai yi mashi wahala matuƙa a cikin kingdom ɗin, sai ya zage.
"Sau da dama ina challenging ɗinka da ka yarda mu yi muhawara kaki ko? Why? Ko kana tsoron zan kayar da kai ne?". Ta kai karshen maganar tana ɗaga mashi gera guda. Burinta kawai ya yarda rana ɗaya ya bata dama, idan ta fara faɗa mashi girman Allah, da niimomin Allah sai ya musulunta ba tare da ya shirya ba, idan kuwa bai musulunta ba to tabbas ta cire ran zai iya musulunta a duniya.
Shiru dai bai kulata ba, kamar bai san da ita a wajen ba. Ƙasa ta yi da kafafunta da ta ɗaga, ta gaji har sun fara yi mata zafi, a hankali ta zame hannunta daga lion chest ɗinsa, kallan kofar fita ta yi, ta yi readyn guduwa sannan ta yi wasu maganganu ƙasa kasa kamar word biyu haka wanda bata bawa kowa damar jin me ta faɗa ba. Tana kai karshen maganar ta yanka a guje zata yi waje.
Quickly ya juyo magic eyes ɗinsa, with his magic ya janyota ta dawo gabansa. Capka ya kai hannunsa zai yi wa wuyarta, zulle mashi ta yi ta faɗa kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya. Hannunsa yasa cikin zafa zai ɓanɓareta daga jikinsa, ina ai kin yarda ta yi, sai tasa magic ɗinta ta taresa.
Me kuke tinanin ta faɗa mashi tasa ya harzuƙa lokaci guda haka?. Wlh Sweetie sai shirin Allah, dama masu shiru shirun nan basu iya fallewa da rashin kunya ba, ku duba lokacin da take forest tare da su Kamran, salihar yarinya mai natsuwa, yanzu gabaɗaya Ronnie ya wayar da ita sai kuma ta zama tantiriya a rashin jin magana ga tsokanar bala'i.
Ganin ba zata sake shi bane yasa ya juya tare da ɗagata da kyau mai gabaɗayanta ya ɗaurata a saman lion chest ɗinsa, sannan ya nufi balconynsa da ita, magic walk ya yi hakan yasa ya isa da wuri. Tin da Sweetie take bata taɓa sanin a wani hawa yake ba, bata san yana da nisa da ƙasa sosai ba, da yake da elvator ko escalator suke haura sama sai bata ganin nisansa.
Yana fita balconynsa ya tsaya a dab glass dake wajen. Sai kallan face ɗinsa take yi tana yi mashi tsiya na sambatu kamar haka. "Big bro kana da kyau fa, amma matsalar baka murmushi, dik da hakan kuma kyanka bai ɓaci ba". Cike da zolaya ta yi maganar.
Hannunsa ya kawo saitin face ɗinta, kyawawan yatsunsa ya kyasta mata a saitin face ɗin nata, da sauri ta kai kallanta a kan ƴatsun nasa, kasa ya nuna mata a kan ta kalli wajen. Da yake bata san in da suke ba sai ta kai kallanta wajen with her full confidence.
Ai tana ganin nisan kasa wani irin ihu ta kurma, a miliyan tasa hannunta ta saƙalo wuyarsa ta ƙanƙamesa sosai. Ihu take yi tana faɗin dan Allah ya yi hakuri ya riketa kada ta faɗi kasa. Kun san idan kana sama ka kalli kasa mai nisa har wani irin jiri zaka ji yana ɗebanka, ka ji kanka yana juyawa.
Ganin ta tsorata sosai yasa tsabar mugunta irin nasa sai ya sa hannunsa da karfi ya ɓanɓarota daga jikinsa, tana ihu tana ƙoƙarin riƙesa ya jefata kasan kamar wata kayan wanki yana kallan face ɗinta.
Datse idanunta gam ta yi tana ihu tana kalmar shahada, ta gama saddakarwa mutuwa zata yi, tin da take da shi bai taɓa yi mata abin da ya razanata har hanjin cikinta suka kaɗa ba irin wannan. Gabaɗaya komai na jikinta sai da ya girgiza, cikinta ya kaɗa matuƙa. Juyawa ya yi ya koma cikin bedroom ɗinsa ransa fes, a cewarsa ko ba komai yau ya yi maganin yar ƙaniya.
Ita kuwa tana tsaka da kurma wannan ihu sai jinta ta yi a saman wani abin tattausa, a tinaninta dik kasa zata faɗa. A zabure ta waro idanunta waje tare da wani irin yunkurawa da karfi sabowa amai da ya zo mata da karfi.
Wato Black Tiger ɗan duniya ne, da magic nasa ya yi amfani ya dawo da ita saman bed ɗinsa, ya jinjiga mata yayan hanji a banza kawai. Amma kuma ya ɗarsa mata tsoro sosai a ranta, ya nuna mata mutuwa kusa da kusa, ba ta ce mashi bata san tsoro ba? To da alama yanzu kam ta sani.
Kasan bed ɗin ta sauko tare da durkushe gwiwowinta a ƙasa tana tari da karfi karfi ta dafe kirjinta da hannunta ɗaya, dan tsananin wahala da ta sha. Ƙoƙarin yin amai a wajen ta yi, amma ta kasa, dan aman yaki fitowa. Kamar ta fita a hayyacinta.
A hankali Ronnie da ya shigo tun ɗazun ya matsa kusa da ita, shoulders ɗinta ya tallabo yana ce mata sorry. Tana jin voice ɗinsa ta yi saurin miƙewa tsaye tare da kai kallanta a kansa, sai dai tana miƙewa jiri ya kwasheta, dan har yanzu ƙwaƙwalwarta yana nuna mata tana faɗuwa ƙasa ne, a fili ta zame zata faɗi Ronnie ya riketa da kyau yana kara faɗa mata sorry.
Shiru ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi ƴar ƙaniya, dama bata taɓa haɗa inuwa da Black Tiger ta sha lafiya ba na faɗa maku. Rikota da kyau Ronnie ya yi suka nufi waje yana kara ce mata sorry, sai rarraba idanunta take yi tana neman ta ita zata ga Black Tiger? Sai dai babu shi babu alamarsa a ɗakin, da alama ya fita. Kumbura kumatu ta yi a ranta ta kudurta idan ta dawo daga school yau ba zata kyalesa ya zauna lafiya ba, zata takura mashi sosai, sai ta fance wahalar da ita da ya yi. A yarinya bata daddara ba, muje zuwa buga wasa, zamu ke waye zai yi nasara.
Kai tsaye Dining room Ronnie ya wuce da ita, bawan Allah shi yanzu ya dai'na tambayarta me Black Tiger ya yi mata idan ta je wajensa ya ganta a wahale, dan ya gaji da jin diramarsu, wani lokaci ma dariya suke bashi, wani lokaci kuma ya yi hawaye, kamar wasu maguna, basa haɗuwa inuwa ɗaya sam.
A baki ya rinƙa bata breakfast ɗin tana ci har ta ƙoshi, sannan ya ce su je ya kaita school idan ta dawo sai su je wajen koyan mota ya fara koya mata.
"Lovely bro kai baka yi breakfast ɗin ba". Ta faɗa kalamanta cike da kulawa sosai. "Sai na kaiki na dawo zan yi, time ya tafi ne". Ya faɗa tare da miƙewa, ya ratayo hannu ɗaya na school back ɗinta a shoulder ɗinsa. Hannunta ya ja tare da wucewa suka nufi waje.
Bata sake sanya Black Tiger a idanunta ba har suka tafi school tare da rakiyar motoci guda gona ciff, ita da Floris suka tafi. Primary 4 aka sanyata bisa umarnin Ronnie, dan ya ce zai rinƙa koya mata karatu sosai a gida, ba zai yarda ta fara daga primary one ba dan ta girmewa hakan, ita kuma Floris tana jss two yanzu. Dikkansu gidan baya suka shiga, Ronnie yana tsakiyansu. Sai hira yake yi da Sweetie, ta kwanto da kanta a saman shoulder ɗinsa tana ta farinciki yau zata je school, har yanzu cikinta yana juya mata tana jin kamar zata yi amai amma kuma aman yaki fita. Black Tiger shi ma yasan ta kan tsiya.
Ko da suka isa school ɗin sai da suka tsaya yi wa juna kalaman kauna na rabuwa da juna, daga karshe Ronnie ya ce mata. "Ki kula sosai da kanki, idan kin dawo daren yau zamu yi wata magana ki tina mun, sannan don't believe anybody kin ji?".
Kai ta gyaɗa mashi tana kallansa. Alama ya yi mata da kansa a kan ta matso. Matsawa ta yi dab da shi, sumbata ya bata a kumatu yana murmushi, ita ma sumbatar ta bashi. Takaici yasa Floris ta buɗe kofar side ɗinta zata fita kenan ya yi saurin riƙo hannunta, a hanzarce ta dawo da kallonta kansa, while shi kuma a hankali ya kai kallansa a kanta. Da ido Sweetie ta bisu da kallo, sumbata ya bawa Floris ɗin ma a kumatu ita ma. Thank you ta furta ba tare da ta mayar mashi da martanin sumbatar ba ta fice da sauri tana tinanin kalaman master Devil in da yake sanar da ita yana matsanancin sha'awar Sweetie, ta yi mashi hanya ya sameta zai yi mata kyauta na musamman. Ita fa Sweetie sam bata kishi da Floris, saboda babu wata alaƙa ta soyayya a tsakaninta da kowa sai Kamran, shi kaɗai zuciyanta yake so, Ronnie san yaya da kanwa take yi mashi, shiyasa bata kishi da Floris, ita kuma Floris kishi take yi da ita sosai da sosai, kamar ta kasheta take ji.
Floris kuwa ta yi master Devil alkawarin ranar partynsu Ronnie idan kowa yana cikin hidima a cikin empeir ɗin, tabbas zata kawo mashi Sweetie har cikin bedroom ɗinsa, daga nan sai ya ƙarisa sauran aiki, wannan agreement ɗin suka yi da shi, yanzu abin da yake jira kenan, a wannan rana ta partyn su Ronnie an shiryawa Black world gagarumin shirin da a tinaninsu Black Tiger bai sani ba, a daren ranar suka shirya sace Ronnie idan jama'a sun yawaita, a cewarsu Black Tiger ba zai iya ganinsu ba dan dare ne kuma abubuwa sun yi yawa, dik tunaninsu capacityn Black Tiger ya gaza haka, master ya tsara zai yi amfani da Sweetie da rana, da daddare su ɗauke Ronnie. Kai wato akwai tashin hankali fa.
Sannan a wannan rana ta partyn akwai gungun mutanen da suka jima suna shirya hanyar kwatar birnin Black world daga hannun Black Tiger saboda ɗinbin arzikin da suke da shi, so zasu yi amfani da wannan rana ta party su yi shigar sunkuru su yakesu su kwace birnin. Daga gefe kuwa a wannan rana Duniyar shaiɗanu suke san zuwa ɗaukar autansu wanda shi kansa Black Tiger ɗin bai san da su ba, babansa bai bashi tarihinsu ba, so bai yi shiri a kansu ba, amma kuma zai iya zulle masu in har bai fita wajen wannan party ba, dan suna kan nemansa ne, fitar da zai yi zuwa wajen wannan party shi zai sa su gansa, suna ganinsa second ɗaya ya yi yawa zasu bayyana a in da yake.
Abin da baku sani ba shi ne, gabaɗaya in da Black Tiger yake fa a tsare take, in dai zai kasance a cikin gidansa ko fada to bazasu iya ganinsa ba, already babansa ya tsare wajen, so hall da za'ayi taron babu tsari, dan bayan mutuwar babansa ya gina wannan hall ɗin, dan haka yana fita wajen za'a iya ganesa. Fatan yanzu kuna kan fahimtar ɓoyesa da babansa ya rinƙa yi na tsawon shekaru a hankali hankali.
Shi kuma kunga bai san da wannan ba dikka, hakan ma tasa ya yi wa Ronnie alkawarin tabbas zai je wajen partynsu, shi Ronnie zai bawa cake idan ya yanka kafin ya bawa kowa, shiyasa na ce maku dukiya ta yi kuka, an ɓarnatar da ita a kan wannan taro, saboda manyan kai zasu je wajen, kujerun zama ma a musamman aka yi odersu daga ƙasar England, kujeru ne na masu bala'in kyau da tsada. In short abubuwa manya manya ne suke shirin faruwa a wajen wannan party.
A ta ɓangaren Sweetie kuma ta yi shirinta tsab na zuwa wajen, ta kuma shirya sanya Ronnie ya fara dik abin da zai fara da sunan Allah, kai my people's akwai cakwakiya a wannan rana wlh, za dai mu gani. Gabaɗaya masu kaunar Ronnie a birnin sai murna suke yi, Black Tiger da kansa ya sanyawa wannan rana suna red diamond day, saboda a wannan rana zai fara kyauta da dukiyar red gold ɗinsu da suka samo a ƙarƙashin ƙasa, sai ya saka wa ranar red diamond day.
Sai shiri suke yi, Ronnie buri ya cika zai shiga hospital ɗinsa ya