Showing 105001 words to 108000 words out of 403653 words

Chapter 36 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

138

ko da naje ban sameki ba, na ɗauki good 1h a wajen, shiru baki zo ba, ni kuma ban san ya zan yi ba sai kawai na koma ɗaki na kwanta, tin da na kwanta barci ya ɗaukeni, lokacin da na farka kuma sai na ji gabaɗaya gida ya rikice ana nemanki, na tambayi su Ansar, sune suke bani labarin wai an saceki, dalilin barina masarauta na fito nemanki kenan, dan ina ganin dik waɗanda zasu je nemanki ɓata lokaci kawai zasu yi, ina ganin kamar ina fita zan ganki, na sha wahala wajen nemanki, dan Allah ki yarda dani".

Tin da ya fara magana idanunta a kan face ɗinsa, tsantsar gaskiya ce kawai take fitowa daga bakinsa, magana babu in'ina bare kwana kwana, zallar gaskiya! Kuma tabbas ta yi mashi shaidar baya karya!. Akwai cakwakiya fa, kenan idan ba shi ya kasheta ba wanene?.

Ji ta yi jikinta ya mutu sosai, dama ga ciwonta yana yi mata zafi, kafafunta ne suka kasa ɗaukarta, nan take ta ji wani jiri ya ɗebeta, kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ji ta yi ta tafi zata kifa kasa. Cikin zafa ya tarota ta faɗa jikinsa, wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sanya.

Da gudu Pretty ta taho ta zube gwiwowinta a ƙasa kusa da su, ta kai hannu tana taɓa Autar tana ambatar sunanta.

Shi ma cikin girmamawa yake kiran sunanta yana faɗin. "Ranki ya daɗe dan Allah ki yarda dani, wlh bani bane, bata yadda za'ayi in cutar take! Hakan ba zai yiwu ba! Na tabbata da kin san matsayinki a raina da kwata kwata ba zaki taɓa yarda da cewa zan iya cutar dake ko da da cizon cinnaka ba ne, dan Allah ki fahimceni".

Allah sarki, bai taɓa shiga ruɗani irin na yau ba, bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba, ya shiga damuwa mara misiltuwa, sambatu kawai yake yi ba tare da yasan abin da bakinsa ke fitarwa ba.



P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=========🔥🔥🔥===========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️



E..............16




Tari sosai Auta ta fara yi, kuka ya ci karfinta, ta rasa me zata yi, idan ta ce ta yarda da shi ba shi ya kasheta ba, to kenan wanene? Akwai mai kama da shi ne a kingdom ɗin? Kai ina hakan ma ba zata taɓa yiwu ba, dole shi ne dan kamanninsa ba zai taɓa ɓace mata ba.

Idan kuma taki yarda da maganarsa wani ɓangare na zuciyar tata yana faɗa mata zata cutar da zuciyar bawan Allah, zata cuceshi ta sanya shi a damuwa bayan ita kanta tasan baya karya, iya gaskiya yake faɗe, to ita yanzu ya zata yi da ranta?.

Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsa. Shi kuwa sai magiya yake yi mata yana rantse mata da Allah akan bashi bane, sambatu kala kala yake yi mata. Ko Pretty da gigin giyar yarinta yake ɗebanta ta fahimci zallar gaskiya a tattare da shi bare ita Auta da tasan shi fiye da kowa, amma ya zata yi? Ta shiga ruɗanin da ba zata iya tsayar da zuciyarta a waje guda ta yanke abin da ya dace da ita ba.

Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, akwai tsananin ciwo zuciya ta zargi masoyin da ta fi kauna sama da komai ya cutar da ita ko ya ci amanarta, wannan zuciya ta kan iya kamuwa da ciwo, kuma da matikar wahala ta iya sake yarda da wani.

Kuka ita ma Pretty ta fara yi tana cigaba da ambatar Auta ta tashi, ta daina yin kuka................ Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda ta rikiɗe da yin tari mai sauti mai kuma karfi har tana kwarewa, cigaba da bata hakuri ya yi yana kara rantse mata da Allah bashi bane.

Bata kulasu ba, ta yi wannan kukan har sai da ya isheta, sannan ta tsagaita dan kanta. Yana ƙanƙame da ita, tin yana sambatu shi ma har ya ƙasa iya cigaba da yin magana ya yi shiru.

Pretty tin tana kuka har ta yi shiru dan dole. Dan sun lura Auta ba zata ji rarrashin nan da suke burin yi mata ba.

Sai da suka ji ta dakata da kanta ne Hoorain ya yi saurin ɗago da kallonsa a kanta, da kyar murya na rawa ya iya ce mata. "Dan Allah ranki ya daɗe ki yi hakuri, wlh bani bane, kuma ba zan taɓa iya cutar dake ba, please trust me!".

Shiru ta yi kamar ba zata tanka mashi ba, idanunta a datse gam, jikinsa dik sai kerma yake yi, da kyar ta ɗaga hannunta izuwa saman hular yakin dake face ɗinsa dai'dai saitin kumatunsa. A hankali ta waro idanunta a kansa, sun yi jajir kamar wuta saboda ta sha kuka har ta goge Allah.

"Hoorain na san ba zaka yi mun karya ba, saboda baka yi baka saba ba, ina da tabbacin a kai'na kuma ba zaka fara ba, dik abin da yake fitowa daga bakinka zuciyata ta shaida zallar gaskiya ce kawai, na yarda da kai, amma zuciyata tana cikin tashin hankali da ruɗanin wanenen mai kama da kai da ya yi yunƙurin kasheni? Meyasa sai a siffarka za'a zo cutar dani? Dan kawai zuciyata ta shaku da kai? Shin akwai wanda shakuwarmu ta tare mashi wani abin ne ko ta takura mashi?".

Lalllai sai ka saurara da kyau zaka iya gane me Auta take faɗe, saboda yadda voice ɗinta ya dashe na kukan da ta sha. Tabbas ya ji maganganunta dikka shi kam, dan a matse yake da buƙatar san jin ta furta mashi ko da kalma ɗaya ne, dako yake yi dama shiyasa ya kasa kunne ya saurara da kyau.

Hannunsa dake cikin hand gloves ɗinsu na mayaƙa ya ɗaura mata a saman face ɗinta, zafafan hawayenta yake san goge mata amma kuma yana jin shakka shakkar yin hakan ba tare da ta bashi izini ba, dan haka sai ya ce. "Ina neman alfarma da ki bani izinin in share maki hawaye kafin na baki amsar tambayarki!!".

"Meyasa kake san goge mun hawayena?". Ta gefa mashi tambaya.

"Saboda bana san ganinsu a face ɗinki, da murmushi mai kwantar da hankula face ɗinki ya dace, kuma da shi muka sanki, bamu san wani abin bayan cool murmushi a kan face ɗinki". Idanunsa a kan face ɗinta yau kam ya yi magana.

"Da gaske Hoorain zuciyarka bata san ganin hawayena?". Cike da mamaki haɗe matsuwa da san jin amsar da zai bata ta yi tambayar.

Jinjina kansa ya yi. "Tabbas zubar hawayenki babban tashin hankali ne wanda zai iya zama barazana ga zuciyata, bana san shi, hankalina yana tashi sosai kuma rai'na yana sosuwa matuƙa idan naga kin haɗe rai ma ba sai an kai ga kuka ba".

"Meyasa kake jin hakan a kai'na?". Ta jefa mashi tambayar ne cike da yakinin abin da take san ji daga garesa zai furta mata ko ranta zai yi sanyi, tabbas ta yarda da shi, tasan baya yi mata karya, sai dai har yanzu zuciyarta yana cikin ruɗanin da Allah ne kawai zai iya warware mata, daɗin daɗawa da ace shi ya yi yunƙurin kasheta tin farko da tabbas ba zai taimaketa a cikin wannan dajin ba, tabbas daga haɗuwarsu izuwa yanzu da ya jima da gama ƙarisa hallakata ya jefar da ita, amma ransa ma ya sadaukar ya cecesu, ya kuma yi jinyarta, sannan ya zube gwiwowinsa a kasa yana neman ta tsaya ya mayar da ita gida, kai gaskiya ko iya waɗan nan hujojin sun isa a gaskata cewa bashi bane ya yi niyar kasheta, to yanzu tambayar a nan ita ce wanenen ya yi niyar kasheta? Sannan kada ku manta yana Kingdom of justice, wato wajen Queen Zarina kenan, to ya aka yi hakan? Lokaci ne zai warware mana komai In Sha Allah, muje dai zuwa!!.

"Ban san dalili ba, abin da nasani kawai shi ne bana san tashin hankalinki"..

Allah sarki, jin ba abin da ta yi tsammanin ji daga garesa bane yasa ta sauke wahalallen ajiyar zuciya tare da jawo yawu mai wuyar haɗiya ta haɗiyesa da kyar, ta yi tinanin zai ce saboda yana santa yasa baya san tashin hankalinta, sai ta ji akasin haka. Jikinta ne ya kara mutuwa sosai, yanzu ta gama yardanwa kanta da gaske baya santa, dama ranar ta ji yana faɗawa su Ansar baya santa, ashe ita kaɗai take dakon kaunarsa. Fahimtar hakan yasa wasu zafafan hawaye masu ɗumin gaske suka fara wanke mata fuska da gudun gaske.

Bawan Allah, ya so faɗa mata amsar da take san ji, ya so ce mata saboda santa yasa baya san ɓacin ranta, sai dai tongue ɗinsa ta yi mashi nauyi, yana jin kamar ba zai iya furta mata ba, dan yana ganin kamar ba zai sameta ba, kamar ko ya faɗa mata a banza ne, ba za'a bashi ba kuma ita ma ba lallai ta yarda ta aminta da shi ba dik da yana ganin kamar tana san shi kuma abokansa suna yi mashi wannan hasashe na tana san shi ɗin.

Dagewa ta yi da karfinta ta yunkuro zata bar jikinsa. Cikin sauri ya rikota, ƙasa ƙasa a nitse ya ce. "Zaki fama ciwonki idan kika tashi fa".

Tabbas ya fahimci amsar da ya bata ne ta sosa ranta har take san barin jikinsa, amma sai ya yi kamar bai fahimta ba, dik dan ya yi ƙoƙarin tsare kansa daga shiga bala'i.

"Kada ka damu Hoorain, a yanzu na samu kwarin gwiwar son mutuwa fiye da rayuwata, babu wata amfanin zamana a duniya tin da burina ba zai cika ba, ka barni ciwon ya fama kawai na mutu............"
Bata iya ƙarisa maganar ba kuka ya cikarfinta sosai wanda ya tilasta mata yin shirun dole.

Wani irin bargon sanyin jikine ya lulluɓesa, sai ya ji ya yi nadamar faɗa mata hakan da ya yi, yanzu bata da lafiya, kamata ya yi ya faɗa mata kalamai masu sanyi da zasu kwantar mata da hankali, ba ya tsaya biyewa zuciyarsa ba.

"Ranki ya daɗe ki yi hakuri, ki sani rayuwanki shi ne namu, kada ki yi mana wasa da shi kin ji?".

Pretty dai kallansu kawai take yi, sun yi nisan zango cikin larabcin da suke yi, dama ita ba sosai ta iya ba, sama sama ne haka, ta fi iya turanci a kan Larabci, Sweetie ta fita iya larabci, dan haka sai ta dai'na fahimtar abin da suke faɗe dan sun yi mata nisa, kawai ta hau aikin binsu da kallo.

"Hoorain ina san ka dai'na yaudarar zuciyata haka nan, ka barni dan Allah, wai me na tsare maka ne ma da kake wahalar da ni?". Cikin kuka ta yi maganar.

Sam bai gane maganar da take yi ba, shi ya rasa ya zai yi, dan gaskiya ya san ko mutuwa yake yi ba zai sameta ba, yanzu haka mutuwa yake kwana yana wunin yi a cikin zuciyarsa dik a kanta, to ina ga ya furta mata soyayya sun kuma kara shakuwa da juna? Me kuke tinanin zai faru a lokacin da za'a rabasu?.

"Dik wani abin da bakya so daga yau na dai'na yi, ba zan sake ba kin ji?". A sanyayye ya yi maganar.............. "Ka tabbata dik abin da nikeso zaka yi?". Kai ya gyaɗa mata alamar ya tabbata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da zame hannunta daga face ɗinsa, a hankali ta yunkura zata bar jikinsa.

"Akwai in da kike san zuwa ne in kai ki?". Ya jefa mata tambaya. "A'a zan sauka daga jikinka ne kawai ina ga sai ya fi mun daɗin faɗin abin da nike san ka yi mun".

Jinjina mata kai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, sannan ya sauketa ƙasa a hankali cike da kula yana ce mata sannu. Zama ta yi a ƙasa suna fuskantar juna, tana matuƙar jin azabar ciwon da yake jikinta, amma haka ta daure.
"Yaushe zaka mayar da ni gida?."
Tambaya ta farko da ta fara jefa mashi kenan.

"Yanzu haka a kan hanyar gida muke, ƙoƙarin mayar dake nike yi, sai dai muna da nisa sosai, zamu iya yin kwana biyu a dajin nan kafin mu iya fita". Cikin girmamawa ya bata amsar.

"Ka zauna da kyau to sai mu yi magana". Ta faɗa a sanyaye.

Matsawa kusa da ita Pretty ta yi suka manne da juna. Kallo ɗaya Hoorain ya yi wa Pretty ya kawar da kansa, ya maida kallansa a kan ruwan dake gudu a gefensu, yana satar kallan Zunaira ta witsiyar ido.

"Ranki ya daɗe nafi san in tsaya a kanki dan tabbatar da babu wani abin cutarwa da zai tinkaro in da kike". .
Kai ta girgiza mashi kafin ta ce. "Kada ka damu, babu wani abin cutarwa da zai cutar da mu In Sha Allah, yanzu dai zauna".

Ba musu ya zauna, amma bai so hakan ba, sai ya lankwashe kafafunsa ya ƙarisa zama daga durkushen da yake.

"Ina wayata take?". Ta gefa mashi tambaya.
Shiru ya ɗan yi, yana tinanin a ina wayar take, shiga tashin hankalin da ya yi a sanadiyar ɓatarta ya ja ya mance ina ma wayar tata yake.

Ganin yana tinani yasa ta fahimci ya ajiye wayar a in da ya manta ne, dan haka sai ta kawar da zancen da cewa. "Hoorain ina san ka mun wata alfarma guda ɗaya kafin mu koma gida".

A kanta ya tsayar da idanunsa, sannan ya ɗan jinjina mata kai kafin ya amsa da. "Wace alfarma kenan gimbiya?".

"Ina san idan ba damuwa dan Allah ka bari in kalli face ɗinka ko da sau ɗaya ne a rayuwata kafin mu koma gida, ina san kallanka sosai"............ Shiru ya ɗan yi lallai Zunaira ta zo da babbar magana, ga shi a wannan gaɓa ba zai iya yi mata gardama ba, saboda ta kuresa a yanzu, alfarma ta nema wanda ta wuci hakan a wajensa, innalilahi wa inna ilahir rajiun, shi ya zai yi yanzu? Tun yana ɗan shekara bakwai ya fara sanya hulunan yaki yana rufe face ɗinsa, kunga kuwa tin ba'a san za'a haifeta ba kenan, babu wanda ya taɓa matsuwa da ya ga face ɗinsa sai ita, dan haka bashi da kwarin gwiwar kallanta ya ce ba zai iya yi mata wannan alfarma ba, ransa dai bai so ba, amma ya zai yi tin da farincikinta yake so!.

"In Sha Allah ba zamu bar cikin wannan daji ba har sai kin kalli face ɗina ranki ya daɗe, na yi maki alkawari, amma ba yanzu ba dan Allah, kin ji ko?".

Jinjina mashi kai ta yi alamar to, sannan ta ce. "Ina Abbo?".

"Yana gida na barosa"....... Shiru suka ɗan yi kamar babu mutane a wajen.

"Hoorain". Ta ambaci sunansa a hankali. Ba tare da ya dawo da kallonsa a kanta ba ya amsa mata da na'am.

"Meyasa baka san kallona kai tsaye sai dai ka rinƙa satar kallona kamar wanda bashi da gaskiya?".
Ba tare da ya juyo da kallan nasa a kanta ba ya ce.
"Saboda in kina tare da ni bana iya ɗaukar minti ɗaya ba tare da na ganki ba, ba zan iya zuba maki ido in yi ta kallanki kai tsaye ba kamar yadda ba zan iya daure ban kalleki ba, shiyasa nike kallanki a sace".

Haka kawai baiwar Allah ta ji murmushi ya kubce mata, wato shi baya shakkar faɗar gaskiya fa, bawan Allah. Sosai ya ji daɗi harda sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da ya kalli ta yi murmushi, har ya ji ransa ta sanyaya sosai.

"Meyafaru kake sauke ajiyar zuciya?". Ta jefa mashi tambaya.
"Saboda kin yi murmushi shiyasa na ji sanyi a rai'na, ban ma san na sauke ajiyar zuciya ba sai da kika yi magana".

Allah sarki zuciyar masoya, sai ta ji wani irin daɗi ya kara ratsata, har tana ji kamar ta kasance da shi a cikin wannan yanayi a wannan waje na har abada, ita jin daɗi da daular da suke da shi ba shi ne a gabanta ba, Hoorain shi ne kawai damuwarta, in dai zasu zauna cikin wannan yanayi mai daɗi yana ganinta tana ganin shi to ta gwammaci zama a wannan daji fiye da ta koma wajen ƴan uwanta.

Wato soyayya fa hegiyar aba ce, ko da yake ayoyi sukutum ne da ita a cikin Alqur'ani mai girma, dan haka zata yi fin hakan ma in dai so ce, Allah dai ya taimakemu kada ya bamu damar san waɗan da basa sanmu, Allah ya haɗamu da masu sanmu na gaskiya!!.

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥

Sun jima a wannan waje suna hira, tun yana amsa mata kai tsaye har ya dawo binta da okey da kuma e or a'a, dan shi bashi da yawan magana, sai jansa da hira suke yi, dan yanzu Pretty ma ya ware ta fara tayata.

Sai da rana ya tsaga ne ya ce masu su zo su koma wajen da ya tanada masu bari ya nemo masu abin da zasu ci. Basu yi mashi musu ba, suka miƙe da kyar Auta tana jan kafafunta a ƙasa.

"Ranki ya daɗe ina neman wata alfarma". Ya faɗa yana kallan ƴan fararen kafafunta.

Jinjina kai ta yi. "Ina jinka". "Dan Allah ki bani damar in ɗaukeki zuwa wajen". "Meyasa?". Ta sake jefa mashi tambaya. "Saboda bana san ganin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login