Showing 270001 words to 273000 words out of 403653 words

Chapter 91 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

12

hannun da karfi ya fara watsi da gabaɗaya computers dake wajen, da karfi ya ɗaga dest ɗin mai gabaɗaya ya yi watsi da shi komai dake kai suka zube ƙasa suka tarwatse watsa watsa, dunkule hannunsa ya yi ya fara bugun jikin bangon wajen da karfi karfi yana huci har sai da ya yi raga raga da yatsun hannunsa ya jiwa kansa ciwo, gwanin ban tausayi ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen tare da haɗe kansa da jikin bango, a dik lokacin da ƙwaƙwalwarsa ta tina mashi cewa Leesharh ta gansa tsirara kuma har ya yi abinga da ita sai ya ji tamkar ya rataye kansa, ya ji kamar ya yi ta buga kansa da bango har sai rai ya yi halinsa, zuciyarsa na azalzala mashi da ya yi ajalin kansa kawai, sai dai shi ɗin mai addini ne yasan hukuncin wanda ya kashe kansa.

Lokaci guda mugu mugun tausayin Leesharh ya rufesa, kalamanta dake yawo a cikin kansa shi ne cewa da ta yi marainiya ce ita, hakan yasa ya ji wani irin kululun bakinciki ya tokare mashi maƙoshi, da kyar ya miƙe tsaye hannunsa na zubar da jini, in da take ya nufa har lokacin yana tangal tangal kamar zai faɗi.

Kallo ɗaya ya yi mata ya yi saurin kawar da kansa, kasancewar babu tufafi a jikinta sannan gata cikin jini. Gabaɗaya ya ji ya tsani kansa, Innalillahi wa inna ilahir rajiun. Shiru ya yi ya rasa madogara, dan kuwa ko kayan da zai saka a cikin wannan ɗaki babu, wancan kayan nasa kuma ya yagesu gabaɗaya ya zubar. Ya jima tsaye a wajen saboda rashin madogara, daga karshe dai ya laluɓo wayarsa can kusa da computers da ya farfasa, Allah ya cecesa wayar bata yi komai ba.

Uban tilin miss calls ya samu wanda ciki na Bilal ya fi na kowa yawa, ga na Ummie da ta yi ta kiransa daren jiya dan jaraba, wai so take ta tambayi ina yake sai ta je ta same shi, bata san a lokacin baya duniyar nan ba, yana can duniyar mercury. Sam bai bi ta kan miss calls ɗin ba, number Sharifat kawai ya laluɓo ya dannawa kira. Bugu ɗaya ta ɗauka, cikin kuka ta yi mashi sallama, yau karon farko a rayuwarsa ya ji faɗuwar gaba ta riskesa, tamkar yasan me Sharifat take yi wa kuka, wato ta nemi Leesharh bata ganta ba, kun san tun daren jiya take nemanta.

Daurewa ya yi ya yi ta maza wajen cewa. "Ki je bedroom ɗina ki ɗauko mun pjs set biyu ki kawo mun wajen stair case na ɗakin bincikenmu dake sama, ki ajiye mun a wajen ki tafi". Yana kai karshen maganar ya yi gaggawar katse kiran dan ma kada ta kawo mashi zancen dalilin kukanta, dan yasan kwanar zancen.

So ba karya ba, tana bala'in sonsa hakan yasa ta iya gane baya cikin kwanciyar hankali da natsuwarsa, ta tabbatar yana cikin tashin hankali daga jin voice ɗinsa, dan haka ita ma nata hankalin ne ya kara tsananta tashi, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daɗi, ga shi ta tambayi Ummie ko taga Leesharh Ummie ta ce mata kada ta sake yi mata batu kan Leesharh, gabaɗaya ta rasa wanda zata je wajensa ta ji sanyi a ranta, Abbie baya nan ya fita. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta fito waje, da yake tana cikin tashin hankali sai bata wani damu da ta yi tinani a kan me Ramish zai yi da pjs har set biyu ba, kawai ta nufi bedroom ɗin nasa.

Shi kuma wurgi ya yi da wayarsa tare da kifa kansa da jikin sofar da Leesharh ke kwance tamkar gawa, sai wani irin zufa ce take keto mashi, gabaɗaya face ɗinsa tamkar wanda aka watsawa ruwa......... 10 mins tsakaninsa da kiran da ya yi wa Sharifat ya miƙe ya ɗauki short ɗinsa ya maida jikinsa, sannan ya nufi wajen romote na stair case ɗin. Jikinsa dik rashin kuzari, da kyar ma ya iya danna romote ɗin stair ɗin ta yi ƙasa. Allah sarki yau sai ga Ramish da leƙa waje wai dan zai sauko ƙasa, leƙawa ya yi domin ya duba akwai mutane ko babu, jikinsa har tana ɗan kerma.

Ganin babu kowa yasa ya yi zafin namar saukowa kasa ya ɗauki kayan da ta ajiye mashi kamar yadda ya buƙata, a gaggauce ya koma sama kirjinsa na harbawa da sauri sauri. Yana haurawa ya naɗe stair case ɗin sama, sannan ya hau ware set ɗaya ya sanya a jikinsa, jikin nasa ma ta wani sassa dikka jininta ya yi mashi wanka. Yana gamawa ya wuce da set ɗaya zuwa in da take. Dan dole ya ɗaura idanunsa a kan aika aikan da ya yi domin ya sanya mata kayansa. Dik da sun yi mata yawa haka ya sanya mata, sauri sauri ya kai hannunsa saitin bugawar zuciyarta ya ji tana raye ne ko dai ba'a iya fyaɗe abin ya tsaya ba har da kisan kai ya yi?.

Jin kamar kirjin nata na bugawa can kasa kasa ya sa ya yi gaggawar miƙewa tsaye ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufo ƙasa da ita, har lokacin hannunsa na zubar da jini, da kyar ya iya naɗe stair case ɗin sama. Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa da ita, yana shiga ya mayar da kofar ya rufe tare da murza key, dan ko Bilal bai yarda ya san abin da ya faru ba, shiyasa ma bai kaita A&E ɗinsu ba ya wuce da ita bedroom ɗinsa kai tsaye, a cewarsa zai rufe kayansa shi kaɗai, a cikin kwakwalwarsa ya fara tinanin ko dai ya yi mata allura manta komai ya shafe mata kwakwalwarta ne?. Wani zuciya ce ta ce mashi zai tabka manyan laifuka guda biyu kenan, idan ya yi mata hakan ya gama cutarta duniya da lahira, zata manta kowa ta manta komai, dik wasu mutane masu mahimmanci a rayuwarta zata manta su? Kai ina wanna babban zalinci ne, wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da kai tin da asirinka zai rufu ai kawai kada ka wani damu da dik abin da zai faru, dama ai marainiya ce bata da kowa, dan haka kayi mata alluran kawai.

My people's kuna ganin yiwa Leesharh allura da zai yi shi ne mafita a garesa? Shi ne zai sa asirinsa ya rufu? Ko shi ne zai sa komai ya wuce? Idan ya yi hakan kuna gani ya kyauta mata kuwa? Ya yi mata adalci? To muje dai zuwa.

A saman bed ɗinsa ya shinfiɗe ta tare da ɗauko remote ya kashe A.c, a gaggauce ya fito ya rufota a cikin ɗakin, kai tsaye ya wuce A&E, dik wasu abin da yasan zai buƙata ya haɗa a cikin A box sannan ya ɗauko ya dawo bedroom ɗinsa, sake kulle kofar ya yi, a gaggauce ya hau yi mata aiki dan kada a rasata.

A lokacin da yake yin wannan aiki a lokacin shi kuma Bilal ya dawo daga yawon nemansa, sai ya nufi ɗakin binciken nasu domin ya shigar da number Ramish ɗin a cikin computers ɗinsu ya yi traking na number dan ya ga in da ɗan uwan nasa yake. Ya sha madarar mamakin ganin yadda ɗakin ta yi watsa watsa, computers ɗin dik anyi raga raga da su, sai dai bai damu da fashesu da aka yi ba, dan yasan babu wanda zai yi wannan aiki sai Ramish, damuwarsa ɗaya shi ne meyasami ɗan uwansa har ya fashe masu kayan aiki haka?. A gaggauce ya juya ya nufi bedroom na Ramish.

A dai'dai lokacin Ramish yana kan yi wa Leesharh allura, turo kofar ya yi da nufin ya shigo sai jinta ya yi a datse, hankalinsa ne ya tashi sosai, knocking ya fara yi dan yasan akwai mutum a ciki, idan ba ku manta ba shi ne ya yi na karshen fita ɗakin daren jiya, so yasan bai rufe da key ba, dole Ramish ya dawo yana ciki kenan.
Cike da tashin hankali yake knocking, amma shiru Ramish bai ko ɗago ya kalli door ɗin ba. Bilal na ƙoƙari juyawa ya bar wajen dan ya je ya tambayi Abbie ko yasan wani abin dangane da Ramish daga jiya zuwa yau kwatsam kallansa ya sauka a kan jinin hannun Ramish da ya ɗiga a wajen, ai hankalinsa ne ya kara tashi, take ya kara tabbatarwa da kansa ba lafiya ba, dole yasan me yake faruwa, sake sake daban daban ne cike a cikin ransa a kan Ramish.

Baya ya koma da karfi yasa karfi zai ɓalle kofar, wata iriyar duka ya kaimata, jijjiga kofar ta yi amma bata ruguje ba, sake yin baya ya yi ya zo da karfi ya daki kofar da shoulder ɗinsa, nan ma jijjiga ta yi bata ruguje ba. Sai a karo na uku ne kofar ta ruguje ƙasa, cikin zafa ya afka cikin ɗakin kirjinsa na harbawa da sauri sauri, yana ta raba idanu game da zarosu yana tinanin ta ina zai kalli ɗan uwansa.

Shi kuwa Ramish da iskanci ya gama cika mashi kai dik abin da Bilal yake yi yana jinsa, bai taka mashi birki ba kuma bai yi niyyar buɗe kofar ba, dan haka ko da ya rugujeta ya shigo ma ko ɗagowa ya kallesa Ramish ɗin bai yi ba, ya cigaba da abin da yake yi kawai.

Me kuke tinanin zai faru kenan? Shikenan Bilal ya gansu? Asirin Ramish zai tonu kenan ko yaya? Shin Bilal zai fahimcesa ya yi mashi uzuri ya rufa mashi asiri kuwa?............. To azimi ya zo ina gab da tafiya hutu, shiyasa nike san leƙa maku kowani part dan kusan halin da ko'ina suke ciki kafin mu tafi hutu, dan haka mu leƙa kingdom of power mu dawo.


🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥

Tafiya take yi tana ɗan ɗingisa kafafunta zata je part ɗin mama, bata gama warkewa daga jibgar da Smart ya yi mata ba, cikin daren ta fito dan ta je wajen maman Yah Ramish, kun san Sarina da mama suna shiri sosai, tana tafiya tana latsa wayarta tana ɗan turo baki, still dai tana cikin wannan karuwan shigar nata na sleeping dress. Alamar bata daku da kyau ba, dan babu alamar nadama a tattare da ita.

Dai'dai zata shiga part ɗin mama ita kuma Mahreen tana fitowa daga part ɗin momma zata je wajen mama Haulat a part ɗin Jaish. Tana fitowa suka ci karo da Sarina. Baya kaɗan ta yi tare da bankawa Sarina wani irin matsiyacin kallo na uku saura kwata kafin ta ce.
"Amma ke dai dabba ce ko? Dan naga dabobi ne suke tafiya basa ganin gabansu, suna sukuwa dik in da kansu ya nufa". Ta yi maganar tare da riko waist ɗinta da hannu bibbiyu, irin dai yadda take cin uwar sabada a kauye idan aka taɓota. Yanzu larabci ya fara zama sosai a bakinta, rashin mutum sabo take karowa, dan ta fara wayewa, infact kallan kauyawa marasa hankali ma take yi wa Aneesa and Fanan, gani take basu san me suke yi ba tun da basa kwalliya.

Amma kuma tana matuƙar girmama Chuchu saboda ɗaukar wankarta, kun san mutuniyar da shegen san kwalliya, idan kana kwalliya ai biyayya zata yi maka sau da kafa ku zauna lafiya ka koya mata yadda ake yi, akasin haka kuwa ka gurji rashin kunya da rashin mutunci daga wajenta.

Mamaki ya hana Sarina yin magana, kallonta ta fara yi from head to toe, yau rashin kunya da fitsara ne suka haɗu waje guda. Wani irin faɗuwar gaba Sarina ta ji a lokacin da taga face ɗin Mahreen, dan ta ganta kyakkyawar gaske, gata yar siririya zubin turawa, komai dai masha Allah, ta sako kayan barcinta masu kyau, a daren ma sai da aka yi kwalliya, ai yanzu tun da ta iya kwalliyar nan kowa sai ya sarara mata, dan na safe daban na rana daban da dare daban, yanzu ta zama mace mai class kamar Chuchu tamu ta amana.

Ita kuwa Mahreen tana wannan girgiza tana binta da harara, wai a hakan ma ta raga mata ne dan ta ɗan yi simple make up a face ɗinta, shi ne ta samu rangwame, ba dan haka na masifar da Mahreen zata yi mata sai ya fi hakan.

Takaici yasa Sarina ta cire hannu ta zabga mata dalleliyar mari mai tsada, dan a cewarta bata da lokaci ɓata baki a kan yarinyar da bata wuce tasa bulala ta yi mata dukan mutuwa ba, dama ga takaicin Mahnoor ta kwacewa Fanan Jaish ya cika masu zuciya, sai ta nemi sauke hakan a kan Mahreen.

Aikuwa tana saukewa Mahreen wannan mari ta yi tsalle ta dira ta ce idan Sarina ta isa Allah ya kasheta, wlh bata ga mai hanata rama marin nan ba, Sarina bata yi zatan zata yi yunƙurin rama marin ba shiyasa bata wani kauce daga gabanta ko ta yi wani yunƙurin ba, unexpext ta ji saukar hannun Mahreen a face ɗinta ta dalla mata mari mai tsadar gaske, ji kake tass da karfin tsiya, kai tsabar Mahreen ta kware a faɗa ma sai da ta daka tsalle ta buɗe hannunta da kyau kafin ta dalla mata marin.

Ai wani irin baya baya Sarina ta yi tamkar zata faɗi kasa ta yi gaggawar dafa bango, har wani jiri ta gani yana ɗebanta, ta maru ba karya, lokaci guda ta ji kamar wadda aka ɗaura a saman fanka yana juyawa da ita. Mahreen kuwa ko da ta rama marin bata tsaya a iya nan ba, cikin jajjagen masifa ta ce. "Waye ubanki da har zaki mareni in kyaleki? Wlh kin yi kaɗan, kin ci karya kin kwana da yunwa, shegiya mai kirar akuyoyin Nenne".

Kunsan a kauye haka suke cewa idan suna faɗa, sai su ce waye uban mutun da zai dakesu ba zasu rama ba? So kalaman bala'inta na kauye ta yi amfani da shi a kan Sarina, dan ita bata ɗauka ma wani kalmar azo a gani bane, kawai faɗarsu na yara take faɗen hakan, ita kuwa Sarina wani irin mugun zafi kalmar ta yi mata, wai waye ubanta, lallai yana da kyau ta gwada mata uban nata kuwa.

A fusace ta cakumo wuyar kayan barcin jikinta da nufin ta naɗa mata ɗan banzan duka, to kun san a ɓangaren faɗa kam dai su Sarina kifin rijiya ne, babu wayon faɗa, basu iya faɗa da hannu ba dan ba yi suke yi ba, a barsu dai da faɗa da baki nan suka fi kauri, ita kuwa Mahreen ta yi dambe da mazan kauye ma bare wata Sarina, dan haka tana cakumo mata wuyar riga Mahreen ta yi kasa kamar wadda zata yi sujjada kawai ta finciko kafar Sarina da karfi, kan kace me sai ga Sarina ta zube ƙasa wanwar kafafu a buɗe, ɗaya ya yi can ɗaya ya yi can.
Tana ganin ta faɗi kasa ta yi gaggawar haye ruwan cikinta, yadda dai ta yi wa ƴaƴan ɓoɗejo bogaza, haka ta haye kan Sarina ta hau kai mata duka a kirji kan tula tulanta. Ba shiri Sarina ta fara ihun neman taimako, yau ga wadda ta fita hau ai.

Ai tana wannan ihu kamar tana kara ingiza Mahreen ne, hular kayan barcin dake kanta Mahreen ɗin ta ciro ta cusawa Sarina a cikin bakinta da ta wage take ihun, wai dan ma kada ta tara mata jama'ar gidan bata gama cin ubanta ba a zo a rabasu, dama Sarina ba karfi ba, yanzu kuma ga rashin lafiyar dukan da tasha bata gama warwarewa ba, hakan yasa ta gaza iya kwatar kanta, Mahreen ta rinƙa kaiwa tula tula naushi abinta, ga shi ta tura mata hula a cikin baki ba halin yin ihu.

A dai'dai wannan lokacin guyson ya zo giftawa zai je part na Mommarsa dan yaga Mahreen ɗin, yau throughout basu haɗu ba, ya je school, bayan ya dawo kuma yana tare da uncle Jahiz, yana san uncle ɗin nasa sosai dan yana da ra'ayi a kan kwallan kafa sosai, so ita zai je gani, har yau wajen da kunama ta harbesa tana ɗan yi mashi zafi kaɗan kaɗan. Amma ya rufawa su Omaid asiri bai sanar da kowa abin da ya faru ba.

Ai yana ga abin da yake kafuwa a miliyan ya kariso wajen, yana zuwa bai yi wata wata ba yasa hannu ya ɗagata cak ya sauketa daga kan Sarina. Kun san faɗarta baya karewa, da gudu ta yunƙura zata sake haye Sarina ya yi gaggawar ƙanƙameta yana tambayar me yake faruwa?. Ƙoƙarin kwatar kanta ta yi da ta cigaba da jibgar Sarina tana wani huci kamar wadda ita aka jibga, sai dai ina ta ƙasa kwace kanta, kuma da hannu ɗaya ya riketa, hakan zai tabbatar maku ba wai karfi ne bashi da shi ba, shi dai kawai goyon kaka ne.

"Lafiya meya haɗaki faɗa da Aunty Sarina a cikin wannan dare kuma?". Cikin wannan sanyin nasa ya yi maganar. Ganin ta kasa kwace kanta ne yasa ta ce. "Ni ka sakeni in gamasa cin ubanta". Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin kalamanta, ya ma rasa me zai ce.
Ita kuwa Sarina lallaɓawa ta yi ta miƙe tsaye, har wani tangal tangal take yi kamar zata faɗi. Hular da Mahreen ta tiɗɗa mata a cikin bakinta ta zaro shi tare da harbin Mahreen ɗin da shi, a fusace ta ce. "Yau sai na ga waye gatanki, sai naga waye ubanki a ƙasar nan, sai kin yabawa aya zaƙinta........".

Ai Sarina bata gama rufe baki ba ta wani daka sufa zata yi kanta tana faɗin. "Sai dai ubanki ba nawa ba, shegiya mai kama da akuyoyin Nenne, kuma tun da kika zagi bappana wlh sai na cire maki hakwaran sama". Wato dai kowa yana san iyayesa kuma babu daɗi idan aka zagan makasu, amma kuma kai a lokacin da zaka zagi wani ba zaka ji rashin daɗin yin hakan ba sai an rama ne zaka san iyaye suna da daraja kuma kana sansu, ita

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login