Showing 234001 words to 237000 words out of 403653 words

Chapter 79 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

38

ba wai raini bane Smart yake yi wa King, haka maganarsa take without respect, shi haka ya taso, daddynsa na France bai taɓa ƙoƙarin yi mashi katsalandan ko ya yi mashi wata gyara a cikin magana idan yanayi ba, so haka ya taso babu wani respect na kowa sai dai shi ayi respecting ɗinsa, amma su basu san cewa bawai baya san King bane yasa yake mashi hakan, ku kanku kun gani bama King da yake daddynsa ba, hatta su Ramish da suke ƴan uba tsananin kaunarsu yake yi bare iyayensa, shi dai haka yanayinsa take ne kawai, idan ka fahimcesa zaku zauna lafiya, akasin haka ciwon zuciya ya kasheka.

"Dama abin da zan yi kenan ai Akka, tarbiya zan sake basu daga farko, kuma da kuke maganar sarauta a wajen wasu ne daddy yake sarki ba a wajen mu ba, a wajenmu mahaifi ne, and zan zo ki san cewa nima sarki ne a nawa daular! Dan haka mind your tongue old woman". Without respect again ya yi wa Akka magana, hakan ya sosa ransu King sosai, saboda uwa ba wasa ba.

Cikin kakkausar murya King ya ce. "Omerish yana da kyau ka rinƙa sanin da waye kake magana kuma me zaka faɗa, ka koyi tauna magana kafin furtata!!".

"Dad I knew what am doing, so bana da buƙatar wani gyara kuma, sai dai in gyara maku........". Tashin hankali.

Tsawar da King ya daka mashi ne yasa shi yanke maganar, kun san su sarauta basa san katsa landan, kuma kowa yasan idan King yana magana ba'a bashi amsa ko a yi mashi gyara har sai ya bada izinin ayi magana, amma shi Smart bayan ya bada amsa ba tare da izini ba amsar babu girmamawa a cikinta sai ma kamar ƙasƙanci, dole su King su harzuƙa matuƙa.

Uncle Abbas ne ya yi ƙoƙarin tausayin King, dan yaga kamar ya ɗauki zafi sosai. Katsesu Smart ya yi da cewa. "Ku faɗa mun uban yarinyar nan dan na san irin hukuncin da zan yi mata ita da uban nata, na san wannan ba ƴarka bace dad".

Kallan momma King ya yi irin kallan nan na kinga abin da kika ja mun, dama momma da kyar yanzu ta samu ta shawo kansa, ga shi tin gari bai waye ba Smart zai sake haɗata faɗa da shi kuma, ya zo yana magana babu girmamawa irin na gidan sarauta, kuma dama a yanzu kafin su shirya da King sai da ya ce mata shi babu abin da ya fi yi mashi ciwo a cikin wannan al'amari kamar yadda Smart baya respecting ɗinsa, yana yi mashi magana gatse gatse haka, ya so ace shi ya bawa ɗansa tarbiya ya koya mashi yadda zai girmama mutane na gaba da shi, sai dai kash abin bai zo yadda yake so ba.

Da kyar momma ta shawo kansa a in da ta yi mashi alkawarin zata zauna da Smart, tabbas zata koya mashi girmama mutane, da kyar dai ya yarda da ita ya kuma yafe mata, yanzu kuma ga sabon aiki Smart ya ɓallo mata again, me kuke tinanin zai faru?.

Bala'i, wato akwai riki fa, a haka ma King bai san aikin da Smart yake yi ba, idan yasan ga aikinsa a tinaninku zai yarda ne? Wlh ko momma tasan gaskiyar aikin da yake yi ba aminta zata yi ba bate King, akwai cakwakiya a gaba fa.

In short Smart bai bar parlon nan ba sai da suka yi kaca kaca, dan kuwa ana ƙoƙarin kashe wuta mammie ta ce bata yarda ba, tun da ya dakar mata ƴa sai ya biya, ai ba shi ya haifar mata ita ba, aikuwa ya gwada mata shi ma ɗan yau ne, dan har ya yi niyar zaneta ita ma, ya haɗesu ya zane uncle Abbas ya ce wannan kuma ba zata yiwu ba, a karshe da suka fusata shi har uncle Abbas ɗin ya yi niyar haɗewa da su ya hukunta King ya shiga tsakani.

Ran momma in ya kai miliyan ya ɓaci, hakan yasa ta ce Smart ya wuce bedroom ɗinsa kada ya sake yin magana da kowa a gidan sai komai ya sesetu, ransa ne ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, a fusace ya nufi bedroom ɗinsa har yana huci, kunsan akwai ciwo idan mutumin da yake da iko da kai ya baka umarnin da zuciyarka bata so, abin akwai ciwon da sai mai juriya zai iya dannewa, dan haka shi ya gagara dannewa saboda zafin zuciya.

Gudun kada ya ɓata ran mahaifiyarsa yasa yana shiga bedroom ɗinsa ya ɗauki wayarsa da key ɗin motar da Jaish ya ɗaukosa daga airport ya fito, suna parlon har lokacin momma tana bawa su Akka hakuri ya zo ya capki hannun Auta dake tsaye kusa da Pretty, sun rike hannun juna suna kallan wannan tashin hankali da yake faruwa, bai sake yin magana da kowa ba kuma bai bi ta kan kowa ba ya ja hannun Auta suka fice daga parlourn.

Allah sarki zuciya, a gaggauce King ya bi bayansa domin ya ji ina zai je a wannan daren haka shi da bai san ko'ina a ƙasar ba?. Momma ta yi mamakin ganin King ya bi bayansa, bata yi zatan zai yi saurin nuna zallar soyayyar da yake yiwa ɗan nasa a fili a cikin ƙankanin lokaci haka ba, ta manta da cewa ita zuciya bata da ƙashi, idan ta so abu dole a bata ko a samu matsala.

Ko da King ya fito bai same shi a wajen ba, a hanzarce ya nufi parking space ko zai same shi, sai dai kafin ya isa parking space ɗin sai ya hango ɗaya daga cikin motocin Jaish ta kutsa waje warriors sun buɗe mashi gate. Sosai King ya shiga damuwa, da sauri ya koma ciki domin ya sa momma ta kira mashi shi ya dawo gida kada ya ja mota yana cikin fushi a samu matsala.

To a tinaninku ina Smart zai tafi a cikin wannan dare? To mu je zuwa dai.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

A ɓangaren Dubai kuma, Ramish ya aminta ya baiwa Leesharh jini bisa umarnin Smart, dan ya yi mashi massage kamar yadda ya saba yi mashi, ya umarcesa da ya bata jini kuma ya kula da ita sosai har ta samu lafiya, domin da ita kaɗai zasu yi amfani wajen kama masu nikaf, ita ce kaɗai zata zama sanadiyar kamasu, dan tasan komai kuma tana da hujjijo a kansu, komai yana da sanadi, dan haka ita Leesharh ita ce sanadin da zasu yi amfani da ita wajen kamasu cikin ruwan sanyi, dan mutanen shegun kai ne, dole a kara masu tarko.

Wannan dalilin yasa Ramish ya aminta ya bada jininsa, (sorry ranan a wajen rubuta jinin Leesharh zan rubuta O negative na rubuta O positive, typing errors aka samu, sai daga baya da ina sake duba page ɗin na gani, so O negative take.)

Yanzu yana kula da lafiyarta sosai, a rana yana daurewa ya leƙa in da take sau ɗaya ya tabbatar tana cikin kulawa mai kyau, kwanaki sun suɗe amma har yanzu bata farfaɗo ba, sai dai jikin nata yana ta kara kyau tana samun lafiya yadda yakamata.

Wannan kenan abin da yake faruwa a Dubai, mun ɗan ji halin da suke ciki, bari mu leƙa wani ɓangaren ma mu san a wani hali suke ciki, dan na lura rikicin dake cikin kingdom of power ba zai kare ba, yanzu ma wasan zai fara, so dole in rinƙa takaitawa muna laƙa wasu ɓangarori dan jin yadda ake ciki.

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

Bayan wasu ƴan kwanaki.

Abubuwa masu ɗan yawa sun fara a cikin waɗan nan kwanaki da suka shuɗe wanda suka haɗa da jinyar da Sweetie ta sha bayan dawowarta daga wajen wutar can da Black Tiger ya so konata Allah ya nufa tana da sauran shan ruwa a gaba, Allah ya ɗaurata a kansa ya sanya mashi ɗigon tausayinta a ransa, ba komai yasa ya tausaya mata ya barta ba kuma face yadda ta tuna mashi da akwai ranar da zai faɗi abin da ya aikata wato ranar lahira kenan, waɗan nan kalaman nata sun sa ya ɗan ji kamar zuciyarsa ta ɗan yi sanyi wanda hakan ya ja ya kyaleta.

Abu na biyu da ya faru a kwanakin da suka shuɗe sun haɗa da rokar Black Tiger da Ronnie ya yi a kan ya sanya Sweetie makaranta tun da tana da ilimi kuma tana da san karatu ga ƙwaƙwalwa. Da yake shi Black Tiger idan ba aikinsa bane ya biyo ta kanka sam bashi da mugunta, sai ya aminta a kan Ronnie ya yi mata komai da ya dace.

Hakan kuwa aka yi, Ronnie ya shige gaba wajen yi mata komai yadda yakamata.

A ɓangaren ita kuma Sweetie, sabon walaƙanci yarinyar nan ta karo, bare ma yanzu da Ronnie ya koya mata yadda zata yi amfani da magic ɗinta, ohohoho, yanzu tana bawa Black Tiger ciwon kai, ga shi ba yadda ya iya da ita, idan ya yi mata magic ita ma ta yi mashi, ta saka shi a gaba bata san ta barshi ya zauna lafiya, yana aikin neman Pretty dan yasan Spender yana hannunta a yanzu, ita kuma Sweetie tana distracting ɗinsa a nan, tin ranar da Sweetie ta ƙalubalancesa a kan ya nemo Spender da kansa daga lokacin ya shiga nema, a nan ne ya gano yana hannun wata yarinya mai kama da Sweetie wato Pretty kenan.

Yanzu haukar neman Pretty yake yi, ya fita harkar Sweetie dan yanzu bata da amfani a wajensa, ba dan Ronnie bama ai da Black Tiger ya jima da kasheta an rufe babinta ya nemo Pretty ya karɓi Spender, so Ronnie ya ce yana santa, kunsan shi ya nuna yana san su Floris ma yasa aka kawosu empire ɗin, a takaice dai yanzu Sweetie zaman Ronnie take yi a birnin, amma ta takurawa Black Tiger dan tana san ya musulunta, tana san kuma ta shiga jikinsa sosai ta yadda ko da ta kuresa ta ja yasa a kureta a gari to da kansa zai sa a dawo da ita.

Kun san idan mutum yana yawan shiga harkarka ko baka so ko kana so, to dik ranar da aka ce babu wannan mutumi sai ka ji wani irin a cikin ranka, irin abin da take san yi wa Black Tiger kenan. Kuma dayawan lokuta Allah yana ɗaurata a kansa tana tsira ba tare da ya yi mata hukunci ba.

••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Zaune Ronnie yake a bakin bed ɗinsa yana kallan kyakkyawar fuskar Sweetie dake zuba barci, tana shirya cikin wani kyakkyawan sleeping dress, tin da ta yi sallar asuba take zuba barci saboda gajiya da ta yi, daren jiya bata yi barci ba, ta bi Ronnie wajen casunsu da suka saba, har karfe 1 na dare suka dawo, da suka dawo kuma sai suka zauna zaman karatu har karfe 3, tana koya mashi karatun addini da dik abin da yakamata ace musulmi ya iya.

Abin da yasa yanzu take yarda ta bi Ronnie ko'ina har church ɗinsu, saboda tana san ta shiga jikin mutanen birnin sosai, ta ga yanayinsu, ta san karfin tsaurinsu a kan addininsu, ta san zasu iya karɓar musulunci cikin sauki ne ko kuma sai an sha wahala, wannan dalilin yasa take yarda ta je ko'ina dan da'awarta.

Yanzu haka wajen casun da suka je jiya ta yi nasarar jan ra'ayin wasu ƴanmata guda biyu da suka yaba da kyan halinta har suka ce suna san kulla abota da ita, da taimakon Ronnie ta samu suka amsa zasu musulunta a sirrance suma, kunga kuwa ashe shiga cikinsu da take yi babban nasara ne.

Yau zata fara zuwa school, amma ta kwanta sai barci take zubawa. Ronnie yana san tashinta kuma yana san barinta ta huta.

Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallanta, sai yaga alamar kamar zara zaran eyelashes ɗinta suna motsawa, ɗan blinking eyes ɗinsa sau biyu ya yi ya sake kafesu a kanta, a nan ne ya fahimci idanunta biyu bata yi barci ba. Wani irin cool murmushi ya saki kafin ya ce. "Maza tashi ki shirya zuwa school".

Miƙa ta ɗan yi tare da waro kyawawan fararen idanunta, ganin yana murmushi ya sanyata sakin cute smile ita ma wanda sai da tasa Black Tiger dake kallansu ya ji murmushin nata ya burgesa. Hannunta ta kai ta saƙalo wuyan Ronnie kafin ta miƙe zaunta.

"My brother waye ya faɗa maka ba barci nike yi ba?". Ta jefa mashi tambayar tana kai hannunta saman kumatunta, irin mutum ya ɗan tallabo kumatunsa haka.

Miƙewa tsaye ya yi tare da riko hannunta. "Tashi ki shirya, idan kin gama shiri zan faɗa maki ya aka yi nasan idanunki biyu". Ya kai karshen maganar tare da janyota, tana yi mashi yauki da yanga ta sauko kasa, a hankali ta fara turo baki tana gallah mashi hararar wasa, bai wani damu ba ya ja hannunta izuwa toilet. Fitowa ya yi ya kyaleta domin ta yi wanka.

Shi yanzu ba school yake zuwa ba, dan ya gama saura bautar ƙasa, sannan kuma akwai partyn da zasu yi wanda aka ɗaga, da last week zasu yi sai aka ɗaga sai next week. Da kansa ya fitar mata da uniform ɗin nata, har bakin toilet ya je ya tsaya tare da yi mata knocking, kanta ta ɗan leƙo hannunta dik kumfa. Miƙa mata uniform ɗin ya yi an hi iron ɗinsu sun yi kyau. A maimakon ta karɓi uniform ɗin sai ta shafa mashi kumfar dake hannunta a face ɗinsa, siririn murmushi ya saki, da a baya ne lokacin da yake krista da ya shiga cikin toilet ɗin, amma yanzu Alhdulillah yasan wasu hukunce hukuncen na muslunci, sai kawai ya yi murmushi yana faɗin zaki fito ne ai.

Da biyu Sweetie ta yi mashi hakan, dan ta tabbatar karatun da take karantar da shi ya nutsa cikin kwakwalwarsa ne ko dai ɓata lokacinta take yi, ashe kuwa ya nutsa yadda yakamata kuma yana amfani da abin da ya karanta.

Karɓar uniform ɗin ta yi ta koma ciki tana cigaba da murmushin ta yi nasara ita ma. Shi ma komawa bakin bed ya yi yana murmushi haɗe da jinta a ransa tamkar ƴar uwarsa na jini.

Wlh yadda suke gudanar da rayuwa ita da Ronnie haƙiƙa yana matuƙar burge Black Tiger, Ronnie bai taɓa kawo yarinyar da suka shaku suke wasa tamkar yaya da kanwa ba irin Sweetie, ga shi yanayin face ɗinsu yana shege, wani irin farinciki na musamman Ronnie yake yi idan yana tare da ita, hakan yasa Black Tiger yake raga mata sosai, saboda tana sanya ɗan ƙaninsa a cikin farinciki.

Wayarsa Ronnie ya ɗauko da nufin ya fara latsawa kenan dan ya gaji da zama shiru, sai ya ji an turo kofar toilet. Da sauri ya kai kallonsa wajen. Ai bai san time ɗin da ya miƙe tsaye ba. Ya ilahi Sweetie ta yi masifar kyau a cikin wannan uniform ɗin. Mini skirt ne da bai gama rufe mata santala santalan cinyoyinta ba launin ash colar, sai riga mai dogon hannu launin white color, ta ɗaure gashin a tsakiya ta saki jelar har baya, yau bata wanke kanta na dan daren jiya ta wanke.

Sai kyalli gashin nata yake yi sosai, abinku da golden white, kun san yana kyalli sosai. Ga sock ɗinta white color sosai. Haba ai Ronnie bai san time ɗin da ya fara santin kyan da ta yi yana yabawa ba. Kashe mashi idanu ɗaya ta yi kamar yadda yake yi mata, sannan ta kariso gabansa tana tambayar ta yi kyau?.

Wlh Black Tiger yana iya ɓata awa guda yana kallan rayuwar Sweetie da Ronnie, gwanin ban sha'awa da burgewa, yanzu ma haka zuba masu idanu ya yi yana kallansu.

"Haba my lovely sis, ai faɗe ma ɓatawa, kinsan ke makurar kyau ce". Ya faɗa yana buɗe mata tafin hannunsa. Buɗe nata tafin hannun ta yi kafin ta ce. "Ban mu sha my brother".

Tafa hannu suka yi kafin su kai tafin hannunsu saman ɗan bakinsu suka manna mashi sumbata sannan suka hurawa juna, lokaci guda suka saki ƙayatattcen murmushi kafin su rungumi juna, abin gwanin birgewa, na tabbata ba iya Black Tiger kawai ba, dik wanda ya gansu ba zai so ya dai'na ganinsu ba, saboda sun haɗu, idan suna tare suna bata show.

"Bro bari in je wajen big bro ina zuwa". Ta faɗa tana raba jijinta da nasa, yanayin tattarar skirt ɗinta gwanin birgewa, ya sha tattare sosai har ya ɗan yi kamar umbrella.

Bai tambayeta me zata je yi a part na Black Tiger ba, sai kawai ya bita da to, dan yasan ko ya tambaya ba faɗa mashi zata yi ba. Da sauri ta nufi waje, shi kuma ya shiga dressing room dan ya ɗauko mata school back ɗin nata da dik abin da ya dace.

Nima na haɗa kayana na tafi shan maltina.


P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️





Yanzu ita ma ta gama iya buɗe kofar Black Tiger, ko ya rufe da magic sai ta buɗe ta shiga, shiyasa ya daina wahalar da kansa dan rufewa ma, ya kyale masu kofar a buɗe kawai.

Ciki ta shigo yana dai tsaye a gaban mirror bai motsa daga in da yake ba, a tsakiyar ɗakin ta tsaya tana kallansa yadda ya yi kyau cikin wani irin shiga na musamman, ga wani zazzafar long coat da ya ɗaura a saman kayansa saboda sanyin da aka tashi da shi yau, ya yi kyau matuƙa.

A dik lokacin da ta kalli Black Tiger jaruminta na farko wato Kamran shi kawai take tinawa, a kullum tana tinaninsa fin sau a kirga, da shi take kwana take kuma tashi, burinta ɗaya ta gansa, a kullum sai ta yi wa kanta wasu tambayoyi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login